Author : HUGUMA Category : African Stories & Novels
gayamin zaka hada soyayyata data wata ne fa,kana gayamin zamu hada miji da wata,zaka raba soyayyarmu,wai shinma yaushe ka ganta harkaji kana sonta kaji zaka iya aurenta?"
"Karki damu,ba wata sabuwa bace cikin rayuwata,mun jima tare,rabuwarmu da ita qaddarar haduwarki dani ce"
"Shahida?!" Ta fada cikin razana da kuma salo na tambaya,saiya zuba mata idanu yana kallonta tare da mamakin kama sunanta farat daya da tayi kafin daga bisani yace
"Eh,ya akayi kika santa?" Sam batabi takan tambayarshi ba saboda ji take kamar alqiyamarta ta tsaya,a ina ya tono shahida?,a ina ya ganta?,ya akayi suka daidaitawa?,ya akayi ta aminta zata aureshi?,ya akayi yaci gaba da kulata?,dama soyayyarta bata mutu cikin ransa ba?,inaa,har abada ba zata taba yarda ta hada anwar da shahida ba qarqashin inuwa daya,kuma ta kasance a tsakiyarsu?,ashe data cika shashasha
"Kacemin kawai ka koma wajen tsohuwar masoyiyarka donka samu damar wulaqantani idan ka aureni,har abada anwar bazan hadaka da wata ba,bazanyi zaman kishi da kowa ba,bazan zauna da kishiya ba" ta fada tana miqewa tsaye,cikin hargagi,hannunshi ya daga mata a nutse
"Ki nutsu nafisa ki samu waje ki zauna"
"Bazan nutsu ba,bazan zauna ba,ka daina kiramin nutsuwa a wannan yanayin,saidai ka zaba koni ko ita" furucin ya fito hade da kuka mai cike da tashin hankali
"Ba wanda zan zaba hakanan ba wanda zanqi zaba" ya amsa mata kai tsaye tana dubanta cikin yanayin dake nuna jarunta da mazantaka na jajirtaccen namiji,kai take jinjinawa hawaye na zuba daga fuskarta sosai yana hadewa da majina,ji take kaman ta cire ranta,ji take kama ta dauki numfashin shahida da bata tashi dawowa rayuwarta ba sai sanda ta sakankace take saka ran ta mallaki anwar,tana ganin da tayi faduwar baqar tasa,data shiga ta zama 'yar kallo gwara ta haqura dashi har abada
"Anwar!...kaje ka auri shahida bazan aureka ba,bazan aureka ba har abada" tana kaiwa nan ta juya da gudu gudu sauri sauri tayi cikin gida,yayi niyyar dakatar da ita amma sam bata tsaya ta saurareshi bama bare taji me zai sake fada,saiya furzar da numfashi,kana ya ture kujerar baya ya miqe yana daukar muqullin motarsa gamida da handkherchief dinsa dake aje saman teburin ya saka cikin aljihunsa ya nufi qofar fita,sai daya shiga parking space sannan ya dauki motarsa yayiwa mai gida horn ya bude masa gate ya fice daga gidan cikin nutsatstsen tuqi.
Yana tuqin yana furzar sa iska mai dumi daga bakinsa,wai me yasa mata dukka harkarsu matsala ce?,don kawai yace mata ba ita daya za'a daurawa aure dashi ba shine xata masa wannan jinnun?,to xaya zuba ido yaga iya nata gudun ruwan.
Wayarshi dake aje gefe ta dauki rura,yadan juya ya kalleta,ganin number anty usaina ce ya sanyashi dagawa,ya saka handsfree ya aje gefansa
"Kana wajen ta ina ne?"
"Ina hanya anty"
"To shikenan saika iso"bai amsa ba ya katse kiran ya aje wayar ya maida hankalinsa ga tuqinsa,duka hannayensa na zube saman sitiyarin,yayin da rabin tunaninsa ya tafi ga abinda nafisan tayi yanzu,me take tunani?,zaita binta ne yana lallashinta?,ko yace ta taimaka ta aureshi?.
Yana fitowa daga motar su sa'ida suka shigo gidan,dawowarsu kenan daga makarantar dare dake can daya bangaren na unguwarsu,ba yadda anwar din baiyi ta qyalesu ba amma tace sam batason zaman banza,zaman kallon bayan sallar magariba daga waccar tashar a koma waccar,dukansu suka iso suna masa sannu da zuwa ya amsa ya shiga cikinsu suka shige cikin gidan.
Qaramin falon anty usaina suka shiga suka bar yaran a babban falo,idanunsa nakan tauraruwa tv anty usaina ta shigo ta aje masa abinci,kallon abincin yayi
" banajin yunwa anty"tana shirin zama tace
"Kaci a gidan abinci kenan?,gwanda dai kayi auren nan suma sa huta da ganinka" murmushi ya saki yana shafa kanshi,zama tayi suka gaisa
"Ya za'ayi da kayan lefen?,na ina za'a fara kaiwa?" Tsaki yaja can qasa sannan yace
"Ni kaina ban sani ba,ina tunanin iya nasu za'a kai,don nafisa tace ta fasa" idanu anty usaina ta fiddo
"Ta fasa kamar yaya?"hannayenshi ya watsa sannan yace
"Oho,na shaida mata kawai su biyu ne dalilin da yasa tace ta fasa kenan" saita sauke ajiyar zuciya tana dubanshi
"Don tace ta fasa bawai yana nufin ta fasa dinne ba,kishi ne kawai da bacin rai,lokaci qanqani zata sauko,saboda haka ba za'a fasa shirin komai ba,zuwa gobe ka kirata ka bata baki duk yadda kukayi saika sanarmin" kai kawai ya gyada yana mita qasan zuciyarshi,yadan jima anan suna tattaunawa sannan daga bisani yayi mata sallama ya wuce.
A guje nafisa ta shiga falon gidan nasu ta wuce momy dake zaune tana kallo ta haye sama dakinta,da kallo momyn ta bita harta shige,saita dauke kai tana sauke ajiyar zuciya,dama ta sani za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,yadda nafisan ta dora burinta da rayuwarta duka kan anwar din tasan za'a sha gwagwarmaya duk sanda labarin ya shiga kunnenta,qyaleta tayi bata bi ta kanta ba,ta barta ta gama kukan zuciyarta ta huce tukunna.
Tamkar zata zauce haka taji,ta kai ta kawo ta kasa zama kamar wadda ta hadiyi tabarya,wannan wacce iriyar masifaffiyar shahida ce?,wanne irin mayen anwar ne?,ace duk yadda takai ga rabasu haqanta ya gaza cimma ruwa?,iya abinda ya kamata tayi don rabasu tayi amma ace bayan shekaru shidda sun sake dawowa sun jone?,idan ma kisa ba batasan me zatayi don rabasu ba,wayarta ta rarumo ta kira number mima,saidai hartayi quginta ta katse bata daga ba,haka ta dinga kira ba qaqqautawa amma bata daga ba,cillar da wayar tayi cikin muryar kuka mai cike da bacin rai da qunan zuciya tace
"Shegiya mahaukaciya,wai ina kika shiga ne?!" Ta qarasa fada cikin qaraji wanda banda sautin tv dake aiki ba abinda zai hana momyn jiyo sautinta.
Haka ta dinga qaramin hauka ita kadai cikin dakin har sha biyu saura na dare sanda wayarta tahau kuka,ta daukota da hanzari tana tsammanin mima ce,maimakon mima anwar ne,aje wayar tayi kawai tana kallonta harta qaraci kukanta ta gama,sai daya kira sau uku bata daga ba tana zaune da kallon wayar ruwan hawaye na fita daga idanunta,tana ganin hakan da zatayi kawai shine zaisa anwar din ya janye qudurinsa ya haqura shahidan.
Washegari qarfe goma na safe tana gaban mudubi a zaune tana kallon yadda fuskarta ta qojale saboda kukan data kwana tana yi wayar ta sake burari,wannan karonma anwar ne a maimakon mima,bata da mafita tilas ta daga wayar ta sake gaya masa kalaman da zasu tabbatar masa da cewa ta rabu dashi kp hakan zai tsoratashi ya janye nufinsa
"Karka sake kirana matsawar kana kan qudurinka na hada aurena da wata macen daban,na gaya maka tun jiya nikam nafisa bazan aureka ba anwar muddin kana a matsayin mijin mace biyu,na haqura dakai har abada" daga haka ta yanke kiran,saiya furzar da numfashi daga bakinsa ya baiwa banza ajiyarta,ya aje wayarshi yaci gaba da shirinsa,shikam ya yankema ransa babu sauran wata mace da zata sake bashi wahala,bazai sake son wata ba bare ta gasa mishi zuciya yadda ya faru dashi a baya,ya saki qaramin murmushi sanda ya tuna cewa da sonta yake da tuni yanzu yana cikin tashin hankali da dimuwa a sanda tace bata sonshi,yanzun kam hankalinshi kwance yake jinsa,saidai kuma wani bari na zuciyarsa yana dan jin damuwa,musamman idan ya tuna da mahaifanta yadda zasu dauki maganar,da wannan tunanin ya gama shirinsa ko abinci yau bai saurara ba ya dauki muqullinsa ya fito,kafin ya tashi motarsa ya tsaya ya turawa anty usaina yadda sukayi da nafisan,don baison kiranta ma bare ta bijiro da wani abun da zai hanashi uzurinsa nayau.
***** ****** ****** *****
"Wannan sakarcin banza ne ai sakarcin wofi,ta isa ta haramta abinda Allah ya halatta?" Alhj abba mahaifin nafisa ya fada cikin fushi da bacin rai yana duban mummy mahaifiyarta,kai ta gyada itama,sau tari tana mamakin halayen nafisan,ta rasa inda take debo wasu baqaqen halayen,abubuwa da yawa ita dai ta sani ba halayyarta bace kota mahaifinta ba
"Atoh,nayi mata magana daxun da safe ta nunamin tana kan bakanta" mummy ta baiwa alhj abba amsa,shikam anwar yana daga gefe kanshi a qasa cikin girmamawa yana saurarensu,baice komai ba sai a sannan
"Kuyi mata uzuri,duba da yadda zancan ya sameta a qurarren lokacin da bata zata ba,ni kaina bani da masaniyar abun zai kasance haka sai gab da zanyi tafiya,sai naga yafi kyau idan na dawo na shaida mata mu fahimci juna,to sai kuma aka samu sabanin fahimta"
"Qarancin hankali da tunani dai,ita zata zauna maka da ita?,ko ita haqqin kula da ita yake kanta?,bilki....kiramin ita maza" a nutse hajiyan ta miqe ta fice zuwa dakin nafisan.
Kwance take rub da ciki tana aikin kuka,tana son anwar tana tsoron rabuwa dashi,tana tsoron yaqi janye qudurinsa,don itakam ba abinda zai sata ta sauka daga kan bakanta,matsawar ta yarda ta aureshi to yaqin da tayi shekara da shekaru tana yi,kudinta data kashe,lokacinta data fansar duka sun tashi a babin badinuhu bataci riba ba kenan
"Kin hadu da aiki kuma kin gama kanki da wahala wallahi,tunda kin daukama kanki aqidar banza da wofi,ki tashi kije mahaifinki nason ganinki" cewar mummy daga haka bata qara ba ta juya tayi ficewarta.
Sanda ta isa falon anwar ta soma gani,kishinsa ya sake lullubeta ganin yadda kamar ma sake kyau da fresh yayi abinsa tsakanin kwanakin da ita take fama da quncin zuciya,gefan abban nata ta zauna ya dubeta
"Nafi,wanne irin shashanci da sakalci kike shirin aikatawa haka?,saboda Allah ya halatta masa auren daga daya zuwa hudu saikice ba zaki aureshi ba saboda haka?,zaki sauya hukuncin Allah kenan?,koke kikayi kanki?to kar naji karna gani,banason wannan shirmen banza,yana da damarma yace biyu zaiyi kece ata uku" Kuka ta saki sosai
"Abba...wallahi bazan aureshi ba,bazan iya zama dashi da wata ba"baki bude alhj abba ya watsa mata daquwa
"Kinci gidanku,kajimin fitinanniyar yarinya?,to saikin aureshin naga wanda ya isa ya hana" miqewa tayi cikin kuka
"Wallahi abba zan gudu,zan barku idan aka aura min shi" mummy na shirin kai mata duka saboda takaici ta fice a guje daga falon.
Shuru ne ya ratsa falon,kunya da takaici na kama alhj abba da hajiya bilkisu,sai suka rasa ta inda zasu kama zancan,sunsan halin nafisa sarai sai addu'a,karta aikata wani abu da zai zama musu illa nan gaba,anwar ya fahimci shurunsu saboda haka yace
"Alhj,karka damu,Dukkaninmu ni da kai da mummy bamu da ikon da zamu sauya mata ra'ayi,sannan duk yadda mukaso abin itace zata zauna,dole saida gamsuwarta sannan komai zai tafi yadda ake buqata"ajiyar zuciya suka saki dukansu kusan a tare cikin bacin rai da takaici
"Yarone ka haifeshi baka haifi halinsa ba,kayi haquri anwar" cewar alhj abba yana jin babu dadi har cikin ransa,yana jin kaman ya muzanta
"Haka Allah ya qaddara" anwar din ya furta kanshi a qasa,shima yana jin babu dadi saboda yadda sukejin laifin kaman a kansu yake.
Tana zaune har yanzu inda ta zauna tana rusar kuka a haka mummy ta tura qofar dakin ta sameta,da hanzari ta daga kai cikin fargaba da razani tare da taraddin furucin da zai fito daga bakin mummyn,tana son anwar tana fata ace ya karbi muradinta
"Shikenan ko?,burinki ya cika?,saikije ki samo wani mijin wanda yafi anwar" daga haka ta juya abinta ta fice tabar mata dakin,cikin tashin hankali ta miqe kaman zata bi bayan mommy don samun qarin bayani,sai kuma ta dawo da baya qwaqwalwarta na gaya mata ma'anar maganar mummyn,anwar ya barta?,anwar ya zabi shahida akanta?,wahalarta ta tashi a banza kenan?,kai ta shiga girgizawa tana fadin bazaiyiwu ba,ta dauki wayarta ta soma kiran layin mima ba qaqqautawa don tana da buqatarta a yau fiye da kullum,saidai amsar dai daya ce wayar a kashe take.
A qalla ta kwashi awa kusan biyu a haka,bata da wata mafita ayanzu banda ta kira anwar,ta soma laluben number dinsa ta kira.
Fitowarsa kenan daga kitchen dauke da cup na coffe wanda ya shiga ya hada da kansa,cikin mamaki yake duban mai kiran,saiya samu daya daga cikin kujerun falon ya zauna yana amsa wayar
"Ni zaka yiwa haka anwar?,ni nafisa zaka gujewa saboda wata banzar shahida da bata kama qafata wajen qaunarka ba?,idan baki sani ba bari yau na fada maka,ni nafisa nice silar duk wani arzqinka,nice silar duk wani matsayi daka taka a yau,nice silar zamantowa abinda kake a yanxu,amma sakayyar da zaka yimin kenan?,ka zabi wata akaina?"
"Kin gama?" Ya furta a nutse yana saurarenta,jin batace komai ba yasa ya dora
"Na farko ba wani bawa daya isa ya azurta wani bawa dukkaninmu muna cine cikin taskar ubangiji,abu na biyu banyi zabe ba hakan ban fifita ba,kece wadda kika zabarwa kanki haka,ko a yanxu kika yarda da abinda nazo dashi,kika amince da cewa qaddararmu ce gaba daya ina maraba da hakan,saboda haka zabi ya rage game shiga rijiya" daga haka ya datse kiran ya aje wayar gefanshi,yadda yake tsammanin zai damu ko zaiji ciwo saiyaga duka ba haka bane,abu daya cikin daruruwan daya sanya ya kasa baiwa nafisa koda digo daya cikin dari na so ko qauna a zuciyarsa kenan,bata da lafazin magana,bata da tarbiyya yiwa kai waigi a duk sanda rai ya baci,ya godewa Allah daya sanya ya maida dukkan kudaden da kamfani da kuma alhj abba ya bashi a wancan lokacin ya zabi yaci gashin kanshi ba tarema da yasan waye yayi silar zuwanshi wajen ba,saiya dauki coffensa a hankali ya soma kurba ba tare daya ji wata gagarumar damuwa ba.
Kira ya sake shigowa wayar tashi,ya dauka itace dai sai yaga anty usaina,ya amsa wayar bayan sun gaisa ga gaya masa komai ya kammala kuma jibi ne zasu miqa lefan
"Shikenam babu damuwa,Allah ya nuna mana,saidai na nafisa ki ajesu wajenki,zan shigo gobe zamuyi magana"
"Allah ya nuna mana" ta amsa masa.
Wayarsa ya dauka yana duba jerin numbers din dake cikin wayar,kaf wayar babu number dinta,ba abun mamaki bane don yasan dama da zaman hakan,rabonshi da number dinta ta rabi wayarshi cikin xamanin da yake amfani da waya keypad,wayar da har yanzu bai rabu da ita ba,hakanan baisan dalilin qin rabuwa da ita ba,saiya koma neman number wayar sulaiman,bugu uku ya daga,suka gaisa ya gaya masa ya kaiwa daada wayar,ya shaida masa yana kusa da ita,sabida haka ya miqa mata wayar,bayan sun gaisa cikin mutunta juna sun dan taba wasa irin na jika da kaka da suke lokaci zuwa lokaci,don jin anwar din take kamar jikanta na jini
"Jibi xasu miqa kayan daada,na nemi number dinta ban samu ba,ko zaki nemi wani cikin gidan a shaida masa"
"Karka damu,sule nada lambar zubaida,yanzu zansa ya kirata ya gaya mata" hira suka dan qra tabawa kadan yana tsokanarta sannan sukayi sallama.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana kurban coffensa idanunsa saman tv da aka ragewa volume sosai,tunani nason fisgarsa yana jefashi wata duniya can,zamanin da dukkaninsu shida shahidan keda buri da fatan mallakar junansu,zamanin da kowannensu yake kwana ya kuma tashi da marari soyayya da begen dan uwanshi,a sannan dukkan mafarkinsu da fatansu ya ta'allaqa ne akan lokacin da zasu zama mallakin juna,lokacin da dukansu shida ita quruciyarsu ta ninka ta yanzj qwarai,bai mantawa wani lokaci daya je hira suna hirar qawar shahida da aka kaiwa lefe,ganin yadda yake nuna buri da fatan yiwa shahidan lefe mai yawa na kece sa'a yasa tace
"Nifa yaa anwar,basai ka takura kanka ba,nifa ba wani lefe da zakamin,ni ba kaya nakeso ba..."
"Me kikeso...?" Ya fada yana tsareta da ido cikin wani salon kallo da baisan yana mata ba saboda shagwabarta data tafi dashi,yasandai cewa sanda yake kallonta din soyayyarta da qaunarta na narkewa tana sake kwaranya cikin magudanan jininsa,kallon da yake mata ya sanyata jin kunya harta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana dariya
"Kai nakeso ni"
"Na sani shahida,amma kullum burina shine na daga darajar shahida cikin mata,kullum burina shahida tafi kowacce mace a duniya,indai ina dashi dole shahidana ta fita daban,kita min addu'a shahida,idan na tashi zan miki lefe irin wanda kowacce mace xatayi burinsa" idanunta ta zaro tana kallonshi
"Ya anwar?,ranar kuwa zanyi bacci?,ya anwar dina yayimin kaya irin haka ranar kowacce mace saidai ta biyo bayana"
"Qwarai kuwa,wannan dan qaramin bakinkin ya iya furta kalmomi masu zaqi da tsayawa a rai" dariya sukayi a tare tana kife fuskarta akan cinyarta.
Yana kawowa nan wani qaramin murmushi da bai shirya ba ya subuce saman fuskarsa,saiya aje cup din,lokaci guda wani abu yayi kutse cikin farincikin daya tsinci kasa,ya soma juyawa zuwa bacin rai,da sauri ya soma furta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,saiya miqe ya dauki cup dinsa ya haura sama inda bedroom dinsa yake dashi.
***** ******* *********
"Ina kwana anty" shahida ta fada sanda take sanya kanta cikin kitchen tana daura agogon hannunta,anty zubaida ta amsa hankalinta na wajen siyayyar da akayi mata tana dubawa,sai data gama daura agogon sannan ta daga kai,turus tayi yadda taga kitchen din ga kacame da kayyaki
"Anty,wadan nan kayan kuma fa?" Ajiye dan qaramin botikin butter din data duba tayi
"Kayan aikin abincin masu kawo lefe ne" wani mummunar faduwar gaba taji ta ziyarceta,duk wani dan kuzari data samu ta sauko dashi yau ya soma yin nashi waje,saita dan dafe kujerar dake kusa da ita
"Lefe kuma?" Kai anty zubaida ta kada tana karantarta
"Eh,jiya da dare daada ta gayamin" sai kawai ta kada kai tana qoqarin hadiye wani abu,ba tare data ce komai ba ta juya ta fice a kitchen din,ko abincin break dake saman tebur bata saurara ba ta fice daga gidan,ta samu mai adaidatanta na jiranta ta shiga ta zauna yaja suka bar gidan.
Ko data isa office rufe kanta kawai tayi ba tare data bar kowa ya shigo ba,ta rasa shin kuka zatayi ko kuwa,idan tayi kuka babu mai sauraren kukanta,idan bore zata ci gaba dayi wanda zatayiwa borenma bata ganshi ba,wannan wanne irin cin zaline anwar ya shiryawa rayuwarta?,me yasa zai bibiyi rayuwarta da irin wannan sakamakon na daban,tunda bai ra'ayinta ya barta tayi rayuwarta cikin salama,irin rayuwar da zata samu nutsuwa mana,saiya shigo don ya rusata?,ya rusa dukkan walwala da farincikin data jima tana tattalinsu da rainonsu?.