Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 53

30K to 33K   out of 156.9K words

tacewa drivern ya sauketa amma ta kasa bude bakinta bare ta furta komai,tana son ta yunqura ta sauka amma ta kasa,tanaji tana gani ya isa dab da anwar din,yayi parking din motar,ya fito daga mazauninsa ya bude mata qofa sannan ya kamata ya fito da ita yana cewa
"Saida nace miki kisha kadan kisha kadan amma da yake shegen hadamar tsiya ne dake,abu ya riga yabi jini saida kikayi tatul" lafazin daya sanya anwar dagowa daga danna wayarsa da yakeyi kenan,don tunda motar ta tsaya hankalinsa bai wajen saida yaji maganar dake fitowa daga bakinsa,yayi kuwa mummunan gani,yayi tozali da abu na farko daya ji kaman zuciyarsa zata tarwatse,shahida ce,shahida ce wani riqe da ita tana tangadi,wanda kana mata kallon farko kasan cewa cikin maye take,idanunta na cikin na anwar din,tana son qwace kanta,tana son yi masa magana,tanason qaryata abinda saurayin ke fada akanta,tanason tabbatar masa da meye ainihin abinda yake gani amma idan ta bude bakin shirme ne yake fita wanda shi kansa shirmen can qasan maqoshinta sautin ke fita,sakinta yayi daura da anwar wanda banda Allah yasa tayi hanzarin dafe bango zubewa zatayi a wajen,ya koma cikin motar ya riqo pant dinta da jakarta ya dawo inda take yana cewa
"Saiki kula wajen shiga gida,ga jini nan duk ya bataki,gaba kya sake bari ciki yayi qwari a jikinki kafin a cireshi" ya qarasa maganar yana sakin kayan hannunsa,jakar ta fadi dama zip din a zuge yake,take tarkacen ciki suka fado dai dai qafafun anwar,kwalaben syrup dinta ne da tarkacen qwayoyin da ba shansu ma take ba,bata taba kwatanta sha bama.

Anwar dake zaune daskare a wajen yaji kaman an jona mishi shociking,baisan ya akayi ba baisan kuma yaushe ya miqe ya kaiwa matashin kyakkyawan naushi a fuska ba,wanda karon farko yayi nasarar fasa masa baki da fitar haqorin bakinsa guda daya,sosai ya tsorata ya kuma razana da yadda yaga yanayin anwar ya juye ya zama,cikin hanzari ya juya don tseratar da kanshi,saida tuni anwar ya damqo kafadarsa ya juyo dashi ya watsa masa wani kyakkyawan mari,bai jira ya gama wartsakewa ba ya kwasa da gudu ya nufi motarsa,anwar ya rufa masa baya,kafin yakai wajen har ya shige motar ya kulle qofar,iya qarfinsa anwar ya saka ya dinga dukan glass din window din motar,wanda kafin yakai ga tasar motar anwar yayi nasarar fasa glass din motar dai dai da sanda matashin ya figi motarsa yabar layin a guje.

Hannunsa na digar jini ya dawo inda shahida ke zube,duk da bata cikin cikakken hayyacinta amma tasan cewa babban tashin hankali ne ya sameta,dubanta yayi sosai wani abu mai tauri ya tsaye masa a wuya,ji yake kaman ya farka maqogaronsa zuwa qirjinsa ya cillar ya huta,yau shahidansa ce yashe a qofar gida?,ba hijabi ba dankwali?,cikin maye?,cikin jinin da aka kira da jinin cire ciki ne?.

Wasu mutum uku da sukazo wucewa ne suka dawo da baya don ganin me yake faruwa?,yaga sadda suka dawo din hakan ya sanyashi cikin hanzari ya damqi kafadar shahidan da kayanta ya turata soron gidansu sannan ya jawo qofar soron.

Koda suka dawo din suna tambayar ba'asi banza yayi dasu har suka qaraci tambayarsa sukaji haushi sukayi gaba.

Tamkar shima d'an mayen haka ya dinga takawa yana hada hanya,tun daga gidansu shahidan har zuwa nashi gidan,yana shiga ya danna sakata,bai ma tuna da abokansa da zasu zo kallon ball yau a sabuwar qaramar plasmar daya sakawa falonsa ba cikin salary dinsa.

Kan carfet din dake malale a falon ya zube,bai damu da ciwon hannunsa dake zubda jini ba,ciwon da yakeji cikin zuciyarsa ya ninka ciwon da yake hannunsa ninkin baninkin,wani irin suya qirjinsa da zuciyarsa suke masa,baisan me zai tuna ba,bansan me zaiyi tunani akai ba,baya gane komai,shahida kawai yake hangowa a yanayin daya ganta a gabanshi,sai kawai ya zame ya kwanta a wajen.

Ranar haka ya kwana nan wajen,kafin gari ya waye ya zubda jini mai yawa,takwas na safe abokinsa kuma babban amininsa yazo ya dinga bugun gidan bai tashi ya bude ba,yana da tabbacin yana ciki tunda gashi ba kwado a qofar gidan,daga qarshe dai da hankalinsa ya kasa kwanciya saiya haura gidan kawai.

A lokacin ya samu a daddafe yayi sallah yana zaune wajen xazzabi nason rufeshi
"Wannan wanne irin abune haka anwar?,ya zaka kulle kanka cikin gida ayita nemanka?" Ya fada yana son karantar yanayin da anwar din ke ciki,baikai ga bashi amsa ba sukaji ana buga gidan,miqewa muhsin yayi don ya duba mai bugun gidan.

Minti daya sai gashi ya shigo riqe da envalope ya ajiye gaban anwar yana cewa
"Hala ma dai baka da lafiya ko?"muhsin yayi tambayar yana qare masa kallo
"bani da lafiya muhsin"
"Subhanallahi,kasha magani?" Kai kawai ya iya kad'a masa
"Ya zaka zauna haka?,bari naje wajen sule mai shayi na samo maka ruwan zafi kasha sai ka samu magani kasha,ko na rakaka asibiti a dubaka" bazai iya magana ba saboda shi kadai yasan me yakeji,yana kallon muhsin har ya fice daga gidan.

Sai a sannan idanunsa suka sauka kan envalope din dake gabanshi *SAQON GAGGAWA MAI MATUQAR AMFANI GA WANDA SAQON YA SHAFA* ya gani rubuce baro baro a bayan envalope din bayan ya juyata,hakanan yaji hankalinsa ya karkata gason sanin meye a cikin envalope din.

Ta sama ya farketa saboda yadda ta mannu,ya zazzage duk abinda ke ciki,hotom farko ya kusa tafiya da numfashinsa,shahida ce rungume jikin wani qato,wanda hoton an daukeshi ne jiya da sukaje siyan syrup sanda ta kusa faduwa ya tareta,hoto na biyu sanda sukaje gidan qawar fiddausi ta daga syrup tana sha,sauran duka hotuna ne na tsiraici tare da wani saurayi haihuwar mahaifiyarsu,kaf numfashinsa ya dauke saboda wani abu daya tokare kafar numfashinsa,ya tafi daga zaune zai kifa luuu,abu na qarshe daya ji kiran sunanshi da muhsin yayi cikin qaraji da razana,daga haka komai ya tsaya mishi cak.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/video

*Alqawarin Allah*
1️⃣4️⃣


Ta bangaren shahida kuwa mahaifinta ne ya turo qofa ya tsinceta cikin wannan halin,wanda hakan ba qaramin kadashi yayi ba,bai gane a cikin maye take ba sai daya kamata zuwa cikin gida yaji tana surutai irin na wanda yasha wani abu ya bugu,saiya saketa suka zuba mata idanu shida ummanta suna kallonta,kasa tsaiwa tayi saita fadi luuu ta zube nata ci gaba da surutanta,wanda a nata tunanin anwar take kira ya tsaya tayi masa bayani,kuka umma ta fashe dashi yayin da abbanta cikin tashin hankali yace
"Ina kika barmin 'yata taje mariya?"
"Ina kuwa zan barta taje abba?,gaisuwar mutuwa suka je ita da qawarta" ta fada cikin tsananin tashin hankali da kuma kuka
"Wallahi wallahi ki tabbatar da cewa indai wani mummunan abu ya samu 'yata toki kuka da kanki" ya fada cikin hargagi yana nunata da yatsa,a ranar dai umma babu bakin magana ta diyarta take,salati kawai take tana duba jikin shahida daya lalace da jini,bandaki ta kaita tayi mata wanka wanda shiya sanya bacci ya kwasheta bayan ta dawo da ita daki.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Da salati ta farka tana qarewa dakin kallo,ko ba'a fada ba tasan dakin ummanta ne,a hankali ta soma tuna me ya faru da ita,tun daga barinsu inda sukaje zuwa gidan qawar fiddausi,sauketa da saurayin yayi a qofar gidansu,daga nan zaren tunanin nata ya yanke,tayi tayi ta sake tuno abinda ya faru ta kasa,zuciyarta na gaya mata taga anwar,wata zuciyar tana ce mata bashi bane.

Muryar umma ta jiyo tana kiranta cikin kakkausar murya wadda tasa hanjin cikinta kadawa
"Shahida....ina kikaje jiya?" Saita kasa amsa mata,indai har a wannan yanayin ta shigo gidansu to tabbas bata da bakin kare kanta,kafin ta sake cewa wani abu umman ta zube dukka kwalaben da suka fado a jakarta wanda tuni ta gama karantawa ta kuma fahimci kayan shaye shaye ne a ciki,idanun umman jajur tace mata
"Meye wannan shahida?" Kasa hada ido tayi da umman,hankalinta yayi qololuwar tashi,lafiyayyen mari umman ta sauke mata wanda ya gigitata,sannan yayi dai dai da shigowar abbanta dakin,wanda tunda ya fita sallar asuba daya daga cikin maqotansa ya masa jajen anga shahida an kawota qofar gida an yasar me ya sameta bai sake samun sukuni ba,yasan tabbas maganar akayita tattaunawa a jiya ana kuma sauya mata kamanni,yasan halin anguwar da 'yan unguwar kaf.

"Ai kibar dukanta bari na gaya miki mariya,koma meye shahida ta zama laifinki ne,kin zaki baki kin kasa bawa diyata tarbiyya shine yanzu zaki zo kina wani hargagin banza da wofi?" Cikin bacin rai da shiga zafi biyu ta maida masa amsa
"Indai shahida ta lalace ne kaima akwai laifinka,tunda kaima ubane ai ba'a dauke nauyin haqqin kula da ita daga kanka ba"
"Au haka ma zaki ce?"
"Eh na fada din,dame kakeso naji ne iye?"
"To mariya nidai tsakanina dake saidai nace Allah ya isa ban yafe ba..." Cikin qaraji gana zubda hawaye tace
"Nima Allah...." Qarar da shahida ta saki ita ta katse sauran magabar da umman tata taso furtawa,kuka take sosai hawaye wani yana bin wani
"Ku dainawa juna Allah ya isa kune sila....dukanku ku kuka zama silar koma meye na koma a yau...ku ku kaini ga afkawa halin da nake ciki a yau,wannan abun da kukeyi shiya janyo komai,duk d'a na halak bazaiso yaga rana guda tak data zama ranar da mahaifansa sukai cecekuce ko jayayya ba a gabanshi,sai gashi ni nawa mahaifan a gabana suke xagin juna,a gabana suke aibata juna,a gabana suke debewa juna albarka,a gabana suke fada da junansu,duk yadda naso da ganin gyaruwar al'amarin hakan ya gaza,duk habyar da nabi ta ganin kun gyaru ba wadda ta bulle min,zafi da radadin haka yasa na nemowa kaina gurbatacciyar mafita,nake shan abinda ni a nawa tunanin bacci kawai zao sanyi ni,ban sani ba cewa ya shiga cikin abinda annabi ya haramta tunda zai gusar da hankali,zai saka maye,idan zanyi kuka bazanyi da d'aya saga cikinku ba,zanyi kuka ne sa dukkaninku,kun kasa fahimtata a sansa ya dace,kun kasa gane illar abinda kuke aikatawa a gabamu mu 'ya'yanku"daga haka ta miqe ta miqe jiri da kuma rashin qwarin jiki ya sanya ta dinga layi,amma bata dakata ba har sai data fice daga dakin zuwa nata dakin.

Dukkaninsu sai jikinsu yayi sanyi,kowannensu ya shiga nazari da dogon tunani,bai sake cewa komai ba abban ya fice daga dakin,saiya zura takalmansa ma da niyyar ficewa daga gidan gaba daya.

Yana sanya qafarsa a waje yaci karo da mutum uku cikin maqotansa
"Yauwa malam nuraini...dama yanzu muke neman yaron da zai mana sallama dakai" qoqarin dai daita fuskarshi yayi ya basu hannu suka gaisa
"Ashe haka abu ya faru?,wallahi sam bamuji dadi ba,yarinyar da kowa ke mata kallon hankali da nutsuwa" daya daga cikin maqotan nashi da ake kira da malam sallau ya fada
"Wallahi kuwa malam sallau,amma nidai ina kyautata zaton sharrin qawaye ne tunda kowa ya shaidi nutsuwar yarinyar....amma cire ciki aiba qaramin abu bane,sanda haruna ke gayan qaryatashi nayi saida yatabbatar min da kunnensa yaji saurayin yana fada" a hautsine abban shahida ya dago yana musu wani bahagon kallo,kusan bai fahimci me suke fada ba gaba daya
"Yata shahida ce tayi ciki harta cire?" Sai suka koma kallon kallo tsakaninsu,malam sallau ya dubi abban
"Errrhmmm malam nuraini kodai mata sun maka irin halin nasu ne an boye maka bakasa me yake faruwa cikin gidanka ba?,banda haka wannan zancan ai ya karade unguwarnan daga daren jiya zuwa safiyar yau"
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" ya dinga maimaitawa yana dafe da kanshi,me yayi jama'ar unguwarsu haka sa cikin qanqanin lokaci zasu jefi diyar cikinsa da wannan sharrin,kansa ya dafe da yaji ya soma juya mishi sai kawai ya juya zuwa cikin gida
"Allah ya tsare gaba ya kiyaye" ya juyo malam sallau yana fada cikin daga murya,dai dai sanda shahida data fito don shiga bayi ta kama ruwa ta saki butar hannunta cikin tsananin tashin hankali ta koma dakinta,dukka jikinta rawa yake,tana tariyar kalaman da saurayin ya dinga fada bayan ya saketa a qofar gidan,kenan duk abinda ya fada sun yarda dashi?,kenan yanzu kallon da kowa zai dinga mata?,innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha"shine abinda ta dinga maimaitawa kenan.

Cikin kwana biyu kacal ta rame ta fige ta fita a hayyacinta,bata taba tunanin akwai tashin hankalin daya wuce na fadan iyayenta ba saiga wanda ya ninkashi ya risketa,duk ta silar kaucewa wancan bacin ran ashe zata fada wanda yafi wancan tsanani rusa farinciki dama ruguza rayuwa gaba daya.

Ba ita kadaiba gidanma gaba daya ya zama shuru,baya ga abinda ya faru abbanta ya kwanta ciwo sosai tun randa su sallau sukazo masa jaje,wanda ba komai bane ya taba ranshi irin maganar da suka furta,qarshe da aka aunashi jininsa ne yayi mugun hawa,hakan ya saga hankalin ummanta itama ta shiga wani sabon tashin hankalin da firgici.

Kwana uku amma shahidar jinta take akwai ya babu,gata nan dai kawai amma komai ya fice mata aka,ranar kwana na ukun da yammaci wani yaro yayi sallama tsakar gidan nasu dauke da takarda wanda yace gashi a baiwa shahidan.

Mubina ce ta bita har cikin daki a sannan tana kwance saman abun sallah ta miqa mata,saita saka hannu kawai ta amsa ta aje saman kanta tana ci gaba da lazuminta,wanda kusa fiye da rabi istigfari take da salatin annabi.

Sai data idar sannan ta dauko envalope din,tana daga kwance ta farketa,takarda ce qwaya daya a cikinta ta fado,sai wata azurfarta guda biyu data siya ta baiwa anwar ajiya,da sauri tasoma warware takardar tana zumudin jin daga gareshi,don tunda abun ya faru taji dif daga bangarensa,tana zaton wala'alla yazo ance mishi bata da lafiya,don bata da maraba da mai lalurar,ita kuma wani kunya da nauyin kiranshi take,gani take kaman daga muryarta zai karanci komai,zai karanci halin data fada,wasiqace cikin rubutun anwar din mai tsari

_Basai nayi miki sallama ba don baki cancanceta ba,saqo nake son isar miki dama ba wani mai tsaho ko yawa ba,shahida,sam baki dace dani ba,kuma sam bakiyi dai dai da rayuwata ba,tuntuni ina zaune dake ne kawai don bani da abinyi kuma bani da wata qwaqwaqwarar sana'a,gashi ina da buqatar macen da zan di ga rage dare a wajenta,to zuwa yanzu al'amura son suma yimin kyau,bana jin zan iya ci gaba da zama dake,ki sani ni muhammad anwar ban taba sonki ko qaunarki ba,na miki alfarma ne kawai a baya,kuma ki saka a ranki cewa baki taba soyayya da wani mai kama dani ko suna na bar har qarshen rayuwarki,wasiqar na tafe da guzurin sabuwar masoyiyita wadda nake da tabbacin ta fiki komai,idan nace komai ina nufin komai da komai da kikasan diya mace na mallaka_

Cikin rawar jiki ta miqe zaune dungurgur,sannan ta jawo envalope din ta sake lalubawa ciki,saiga hotuna guda shida rigis sun fado,dukkaninsu anwar ne cikin hotunan da wata matashiyar budurwa cikin kyakkyawar shiga ta alfarma,kana musu kallon farko zaka tabbatarwa kanka lallai masoya ne da sukayi zurfin cikin qaunar juna,saboda yadda kowanne ke kallon danuwanshi cikin fara'a da shauqi,sosai ta tsurawa fuskar yarinyar ido zuciyarta na wani qara gudu tamkar zata faso qirjinta,suya zuciyar tata take mata tanason yin kuka amma bataji koda alamarsa ba bare yazo,nazarin fuskar yarinyar take take ta tuno inda ta santa,ranar bikin umaima,ranar bikin umma zaune gaban motar daya amso don ya kaita ya daukota,saita saki hoton tana girgiza kai tare da laluben wayarta duka lokaci daya,tamkar tababba take zancan a fili ita kadai
"Nasan wasa kake min ya anwar ba zamu taba rabuwa....nasan wani ya kaima labarin abinda ya faru dani,ranka ya baci ka furta min wannan kalaman saboda kishina da kake" maganar tata ta katse sanda wayar ta shiga ta soma ringing.

Wata murya daban ta dauka,cikin matuqar sauri da zaquwa tace
"Don girman Allah ka taimakeni ka bawa anwar" dan jimmm yayi cikin tunani,don a yanzun bayajin anwar din zai iya wata dogon magana,tunda Allah yasa suka miqashi asibiti yayi kwanaki biyunsa cur ya farfado yace a dawo dashi gida yazo ya dauke wata envalope dashi kansa muhsin baisan meye a ciki ba ya adana yake zaune waje daya,kana kallon yanayin fuskarsa kasan ya dulmiya cikin wani qunci,iein quncin dake kama zukata ya riqe tamau ya dinga yankarta a hankali yana saka rudani damuwa da baqinciki mai yawa a rayuwa,irin baqincikin dake tasiri kadan kadan daga ruhi zuwa gangar jiki ya illata mutum ta farat daya ba tare da an ankara ba.

Miqa masa wayar yayi,sai daya daga idanunsa da suke nuna alamun gajiyawa da damuwa ya dubi muhsin sannan ya maida kan wayar,hannu ya saka a hankali ya masa,muhsin ya sakar masa yana tashi gami da cewa
"Bari naje gida na dauko wayata na barta a chargy" kai kawai ya iya gyada masa yana kara wayar a kunnensa.

Abu na farko da tayi kuka ta sakar masa,wanda yake bayyana rauninta qarara,gajiyawa da rashin samun madafa,idanunsa ya runtse yana jin zuciyarsa cikin wani inji ana hautsinata sama da qasa ko zata faso qirjinsa ta fito.

*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina buqatar siya ki tuntubi wannan number*

07067124863

*ko kuma*

09032345899https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos


*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki nemi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*Alqawarin Allah*
1️⃣5️⃣


Tamkar ana hautsinashi shi kanshi,wani irin abu ya dinga ji mai kama da tsana qyamata da haushi cike fal a zuciyarsa,wannan runtse idanun da yayi ba abinda ke gilmawa cikin idanunsa sai hotunan daya gani kwanaki hudu baya da suka shude
"Dama akwai wani wani lokaci da zaizo da zaka daina sona ka juyamin baya ya anwar?" Shuru yayi ba tare daya ce komai ba,duk sanda yayi yunqurin cewa wani abu sai yaji wani dunqulallen abu ya tare masa maqoshi
"Ashe dama saboda wata qaddara ta fadawa rayuwata saika gujeni?"
"Qarya kike!.....babu ruwab qaddara" ya fada cikin qaraji da daga murya,wanda har sai daya tashi daga kashingidar da yake yana fidda huci irin na

11 / 53