Author : HUGUMA Category : African Stories & Novels
nan nata har yanzu cikin hancinsa kamar tana jikinsa ne,ya lumshe idanu yana tuna yadda yaji laushi da taushin jikinta,yasaki murmushi mai sauti shi daya cikin motar kamar zautacce yana fata da burin daidaituwar komai,don zahirin magana yana buqatar matarsa,ta lasa masa zuma mai azabar zaqi da wuyar mantawa kuma tana neman ta gujewa rayuwarsa?.
Har sanda yafita tana kwance tana jinsu,idanunta a lumshe tana qoqarin controlling kanta,tana jin wani azababben feelings na saukar mata,wanda kaf rayuwarta bata taba jin abu makamancin haka cikin jikinta ba irin yanzu,bayan wasu da suka shude tana kwance a haka,tana tuna fuskarshi da adonshi,tanajin buqar kasancewarta tare dashi,daada ce tashigo dakin,tana sane tadinga qananun mita da sababi kala kala kan anwar din,shuru tayi mata tana kafe akwance,tun tana shuru har batasan sanda tabude bakinta ba muryarta tayi sanyi sosai
"Tunda dai yatafi daada ba shikenan ba don Allah" cikin mamaki saman fuskarta,farinciki qasan ranta tawaiwayo
"Au,ni shegiya kaza,me kike nufi 'yar nan?,idan son mijinki kike kiyi bayani karna zaqe da yawa" haushi ya kamata harta gaza shuru
"Daga magana?,ni maganarce banaso,ciwon kai take saka min"
"Auto,yanzu naji batu" harta saka qafa zata fita tadawo
"To alalen naki fa,zaifa huce,kin zubo kin barshi" fuska ta yatsina,don batajin ko taci zataji dadinsa yadda ta tsara ma ranta
"Zai ciyu kuwa,na qoshi gaskiya" ta fada tana canza yanayin kwanciyarta ko zata samu sauqin abinda takeji,dariyar mugunta daada tayi qasa qasa sannan tasa kai tafice ba tare data sake cewa komai ba.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Qarfe biyu daya na rana daada tafito tasamu shahida kwance saman doguwar kujera iskar fanka na ratsata,sanye da doguwar riga ta yadi mai talewa,yankakken hannu ne da ita,kanta babu dankwali don sam yanzu jinsa take yana damunta,wayartace a hannunta wadda dazu da sassafe daada ta bata,itama tajima batayi amfani da wayar ba shiyasa take marmarinta,tajima kuwa a hannunta tana game,babu wanda tayi kira duka saqonnin data gani.
Kanta tadaga tana duban daada wadda tayi shar cikin atamfa riga da zani da hijabinta dayasha guga,daada badai tsafta ba
"Nins shirya,zanje barkar jikar sahura,idan la'asar azahar ta gota ki dora mana tuwo kafin nadawo na amsa,karki cemin kin dafa bazaki iya ciba" fuska tadan bata,batason zama a gidan ita kadai
"Kai daada don Allah,yanzu barkarce tun yanzu?,ina laifi ma kibari sai anjima"
"A'ah,gwara dai naje na huta,yau kwana uku ban samu naje ba"
"Shikenan saikin dawo" tafada tana maida kanta ta kwanta,fitar daada yasa gidan yasake shuru,don haka tasake bude wayar taci gaba da game dinta.
Bata jima ba kasala ta saukar mata,wayarma taji ta maya nauyi,saita sauke wayar tayi shuru iskar fanka na ratsata tako ina,idanunta a lumshe amma ba barci take ba.
Tunda yashigo gidan ya fuskanci daadan bata nan,me yiwuwa shi yasa tace masa yadawo yau?,wato yasha shagalinsa kenan?,murmushi mai qayatarwa ya qwace masa,ya shafi Fuskarsa zuwa gemunsa yana qare mata kallo a sanda batasan da zuwanshi ba,saidaya gama morewa kallonta sosai sannan yakoma daga bakin qofar dakin yayi sallama cikin wata murya mai taushi da nutsuwa,idanunta tabude fes sai cikin nashi,tayi zumbur tamiqe tazauna sannan tasoma yunqurin shigewa dakin daada
"Indai kika dara daga nan ban yafe ba" ya fada da sauri don yasan cewa shine kawai hanyar da zai tsayar da ita,cak kuwa ta tsaya din,hakan yayi masa dadi,ya dinga takowa a hankali harsai daya qaraso bayanta,da sauri ya janyota ya mannata da jikinsa,dukkaninsu suka lumshe idanunsu lokaci guda,kowannensu wani saqo na gudana cikin jini da bargonsa,sun jima a haka sannan yasa hannunshi ya hade mata jelar kalbar kanta waje daya,ya saka bakinsa saman wuyanta yasakar mata tattausan kiss dayasa numfashinta daukewa na wucin gadi,har batasan sanda tasaki ajiyar zuciya ba mai sanyi
"Shahida....nasan na bata miki,hakanan na aikata dukkan wani nau'i na laifi kuma zunubi a rayuwar masoya,gani gareki na kawo kaina,nasan ni riqaqqen me laifi ne shahida,ki hukuntani yadda kikeso,ki kima yimin dukkanin hukuncin da kike ganin ya dace da rayuwata,amma don Allah,karkice baxaki yafemin ba,kada kice zaki rabu dani shahida,zan iya jure komai amma banda wannan,idan ma zama zakiyi anan harsai kin huce duka na yarje miki,bana iya bacci shahida,kullum ciwona kaman zai tashi a haka nake wayar gari,kiyimin afuwa karna rasa raina don Allah"ya qarashe maganar yana hura mata iska cikin kunne,jikinta yayi sanyi matuqa,kalmar mutuwa daya ambato yasa jikinta yasake sanyaya,saita soma qoqarin zame jikinta daga nashi amma yaqi bata dama
"Nayi missing dinki shahida,ko yayane ki bari naji dumin jikinki mana" nema yake yarusa mata dukkan wani makamin yaqinta data tanada,saboda haka ta tattara sauran qarfin dake gareta ta tureshi takuma zille,yakai mata cafka amma tuni ta fada dakin daada ta kulle qofar,tazauna bakin gado tana haki kamar wadda taci uban gudu,jikin qofar yatsaya sosai yana jingina jikinsa dayaji ya masa nauyi,cikin wata tattausar murya yace
"Shahida please,inason inji kalaman bakinki,inason kice wani abu don Allah shahidana,please"
"Sai yanzu anwar?,sai yanzu kake tunanin kana da buqatata?,sai yanzu daka tabbatar da ingancina kenan?,wato da hakan nake da gaske anwar bazaka iya zama dani ba kenan?" Ta jefa masa tambayar data sashi duqawa bakin qofar dakin saman qafafunshi,ko banza furucin bakinta kawai da tanka masa da tayi yanajin wata rahama ce tattare dashi
"Inda wata matarce shahida zan zauna da ita,amma bazan iya kallonta ba yadda na kalleki a baya,bazan iya hada shimfida da itaba yadda na hada dake,bazan iya sauraren kalaman bakinta ba yadda nake kwana datashi da daukin jin naki,koda kinja bakinki kin qulle saina tabbatar da cewa na sakaki magana,shahida....keta dabance a rayuwata,daban kike da sauran mata,hakanan yadda nake kishinki duk duniya babu wata halitta da nake kishinta kamar haka,ko meye nayi kishinki ya kaini aikata haka,daidai da aurenki shahida kishin ganinki da wani yasa na nemi aurenki baya da yardarki ba,zan tafi tunda bakison ganina,amma ban miki alqawarin cewa bazan dawo ba" sanda yamiqe ya soma takawa don barin falon itama saita miqe tsaye tana duban bakin qofar dukda bata ganinsa,duk takunsa daya don barin falon saitaji wani abu ya motsa zuciyarta,baikai ga fita ba daada tayi sallama ta kunno kai,suka hada idanu yamata nuni da dakinta alamar shahida naji,saitaja baya tana kallonshi bayan ta zabgo salati kamar wadda taga mutuwa.........
*karku manta,ku ziyarci tashar SAUTIN HIKIMA,ku saurari litattafanmu,mun gode*🙏🏽🙏🏽🙏🏽53
"Yanzu saida ka faki idona kayi wuuuuffff ka shigomin gida?,tsaya ma tukunna,takardarta ka kawo mata ko kuwa?" Tayi tambayar kamar gaske tana miqa masa hannu,dai dai lokacin shahida tayi zumbur ta miqe,ta tako da sauri ta dage labulen taleqo tana kallon abinda ke faruwa,russunawa anwar yayi cikin sanyi
"Bazan iya sakinta ba daada kiyi haquri"
"Abun nan dai nina hadashi?,tona raba,wuce maza kaficemin daga gida,ka tabbatar nan da gobe ka kawomin takardar jikata na gaya maka,idan ba haka ba kada na sake ganin qafarka a gidan nan" yana sane yahangi tsaiwarta jikin labulen,saiya dauko handkherchief a aljihunsa kamar mai share hawayen gaske ya juya ya fita.
Fuskarsa a matuqar washe,farinciki na cika zuciyarsa yafada sit dinsa yana lumshe ido murmushi na fita daga fuskarsa,ba shakka akwai alamun nasara,akwai alamun shahidan zata sauko cikin ruwan sanyi,ya tada motar cikin qwarin gwiwa da karsashi yana tsara yadda rayuwarsu zataci gaba da kasancewa,tunanin nafisa yakutso cikin ranshi,take bacin rai ya bayyana saman fuskarshi,duk sanda yatuna da ita da irin abunda ta aikata saiyaji gaba daya ta sake futa daga kanshi,yaja dogon tsaki tare da kauda tunanin nata.
Kamar yadda daadan tasaba haka tashigo tana mita,wannan karonma shurun shahidan tayi mata,tana lafe saman gadon ta soma bubbuga qofar
"Budemin mana munafuka,halama kece kika kirashi ko?,don kinga nataho zan shigo shine kika rufe qofar don kada nace da saninki yazo" jiki a matuqar mace tasauko tabude mata qofar,daadan tazuba mata ido
"Kwanciyar me kikeyi ma?" Tayi maganar cikin salon tuhuma,hakanan taji ranta yadan sosu,tome daadan ke nufi?,kamar wadda ta kama da kwarto?
"Nibansan zaizo ba,bansan kuma yazo ba,ina kwance naganshi kawai" salati tahau
"Anya ko zan yarda dake,ke yarinya idan dakinki kikeso toki tattara ya naki ya naki kibi mijinki,idan yaso ko dafaki zaiyima ya dafaki ba ruwan habiba" ranta ya qarasa baci gaba daya,saita juya mata qeya tana gunguni
"Sai ana abu rimi rimi dake daada saiki dinga soko wasu maganganu,idan kora da hali kikemin kawai ki fada" ta qarashe maganar tana komawa saman gadon cikin jin haushi,boye dariyarta daada tayi,tanajin dadin yadda taketa ganin ci gaba
"Yo ba gwara nafadi gaskiyata ba tun kafin keki fada?,wannan yaro saina saka an soma masa atire indai yaci gaba da takura mana" idanu shahidan ta fiddo tana kallonta
"Atile daada kamar wani kwarto?" Waiwayowa tayi tana dubanta
"Ai qanin kwartonne tunda saki muke nema amma yake biyomu har cikin daki"
"Wallahi shikam.baiyi kama da kwarto ba" tayi subul da bakan fada,saboda furucin daadan ya daketa sosai,Har taji wani abu ya sosa mata zuciya
"Shahida!,iyeeee,to bari yazo ya tattaraki ku koma,dama qaryar neman saki kike" da sauri tace
"Ba haka bane daada,kiyi haquri,kawai maganar ce naga kaman bata kamata ba,bazan sake magana ba tunda haka ne" sosai daadan tasamu abunyi,tadinga sababi,so take kawai ta qarasa tunzura shahidan tace zata tafin.
Daren ranar tsaf bacci yadauke mata,duk juyin da zatayi tana tuna lokacin data kasance cikin jikinsa ne,ta kasa mancewa,idanunsa masu matuqar tasiri,wadanda shekarun baya suka dinga dagula mata lissafi,suka dauketa suka jefata can qurya a duniyar qaunarshi,wannan karon tanajin wani abu dangane dasu,kaman wancan yanayin yanason tasiri cikin jikinta.
Tana tsaka da wannan kira yashigo wayarta,daada na falo tana nafilfilinta,ta duba agogo daya saura na dare,tayi mamakin dadewarta a kwancen tana juyi ta ba tare da baccin yadauketa ba,baquwar number ce,sai gabanta yafadi zuciyarta tasoma raya mata kodai wani mummunan abu yafaru ne a kano,da sauri tadaga ta kara akunnenta
"Allah ya taimakeki!" Lafazin yafito daga bakinsa kamar yadda yasaba kiranta shekarun baya,hakan ya karya duk wani laka dake jikinta,ta lumshe idanu,sunan ya tuna mata da abubuwa masu yawa,ta koma can baya duniyarsu da suka taba wanzuwa a ciki shida ita,batasan tayi nisa ba saida tasake jiyo muryarsa
"Allah ya taimakeki bakiyi bacci ba kema ko?" Ya jefo mata tambayar,sai tayi hanzarin turbune fuska da sauri tace
"Saboda tsabar rashin sanin haqqin mutanen ne dai yasanyaka kirana cikin wannan talatainin daren?" Murmushi mai sauti ya qwace masa har cikin kunneta
"Meye nasaurin kawo uzuri kuma?,kina abu kaman kin manta waye anwar da shahida?,Kin manta na sanki ciki da bai?"
"Hakan bai maka amfani ba,tunda harka kasa fahimtata a lokacin daya dace"
"Na yarda shahida,kiyita fada indai hakan zak saka zuciyarki tayi sanyi,nidai na sani cewa koma meye yafaru kishinki ne ya jawomin" shuru dukkansu sukayi,kowa yana suraren ko dan uwanshi zaice wani abu
"Shahida" ya kira sunanta cikin matuqar sanyin murya,bata amsa mishi ba amma tana saurarenshi,kiran sunan nata ya taba ranta sosai
"Ki yarda ba zamu taba iya rabuwa da juna ba,koda munyi hakan iya na idanuwan al'umma ne,zaki yarda dani idan kika zauna kika tuna yata kasance miki shekara shidan da mukayi ba tare da juna ba...,nasani cewa na cika azzalumi,mai gaggawar yanke hukunci,amma idan aka dorash duka bisa mizanin yiwa masoyi hukunci na cancanci a dubeni,ayimin afuwa akuma yafemin,anwar dinki ne shahida,kin manta?" Gaggawar datse kiran tayi ganin yana neman karya lagonta,dukka furucinsa qwaya daya yana kwance duk wani dauri data daura kanshi,saita saki wayar ta kwanta rigingine tana sakin ajiyar zuciya,idanunta a lumshe fuskarsa na mata yawo cikin idanun nata,hannu tasa ta dafe goshinta saboda zuciyarta data soma zillo,tana mata amsa kuwwa,tare da tuna mata tarayyarsu ta baya,tarayyar da kowa ke sha'awa,kowanne masoya manya sa qanana suke burin inama sune a bigiren?,saita sake komawa rub da ciki tanason shafe babin wannan tunanin.
Qarar shigowar saqo a awayarta ya katse mata nazarin da takeyi
"Anshad,indai har da gaske kin daina sona,indai dagaske bakison ganina kicemin na tafi,ni kuma na miki alqawarin tafiya nabarkin kamar yadda kakeso" tsaki taja da sauri tasoma maida masa amsa
"Go please go,it will never hurt me anymore,na rayu shekaru shida baya ba tare dakai ba,me kaga ya canza?,kaiba komai bane cikin rayuwata".
Sam bai zaci amsar da zai samu kenan daga wajenta ba,yana tsaye saida yasamu waje yazauna,kanshi ya wani sara,yasoma baiwa kansa baki kada hawan jininsa yatashi,aqalla ya kashe mintuna kyawawa ashirin yana zaune wajen,inda daga qarshe ya amshi shawarar da zuciyarsa ta bashi,yana fatan samun mafita kan hakan.
Washegari yanemi daada sukayi magana kan qudurin daya yanke,hakan kuma yayi mata itama ta bashi goyon baya,sai kawai yashirya tafiya jahohin da makarantunsa suke yaje ya dubasu,bai gayawa kowa ba banda muhsin,don yasan idan yafada anty usaina zata dorawa tafiyar ayar tambaya,yayi mamaki ma da har yanzu nafisa bata shaida mata abinda ke faruwa ba.
Washegari ya hada komai nashi ya tsallake ya tafi.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Kallon daada kawai take wadda tazage tana bata labarin sa sam ita bai mata armashi ba,don sam hankalinta ita bai wajen,batasan me yake damunta ba gaba daya kwanaki biyun bataji wani walwala,zuciyarta a quntace take,hakanan ranta babu dadi,duka abinda take daadan na ankare da ita,kuma tana sane ta dage take bata labarin wanda kusan rabinshi gugar zana ce,taqi yarda ne kawai cewa kewar anwar take,wanda yau yacika kwanaki takwas kenan baizo gidan ba,koda wasa bata taba mata maganar ba tana jiran lokacin da zata sake tunzuratane yayi,kuma kamar yanzun shine gabar yin maganar,saboda haka tace tana gyara daurin dankwalinta
"Ummm,kwana biyu dai kunnenmu shuruuuu,wannan yaron me shegen naci yabarmu mun huta,wala'alla yayi zuciya yadda nake fata,ba mamaki cikin satin nan ko satin gaba kiga takardar sakinki,haka nake tunani" wata mummunar faduwar gaba tasami shahida saboda kalmar sakin data fito daga bakin daadan,hakan na nufin zasu sake rabuwa karo nabiyu,zasu nesanta da juna?,zata barwa nafisa shi?,zata tashi daga sunan matarsa?.
"Kinga saikiyi zamanki a nan harki gama iddarki,ki samu wani wanda kikeso ki aura abinki hankali kwance,ki zaba ki darje" maganar daada ta katse mata tunaninta,saita tsaya kawai tana duban daadan yadda take maganar bilhaqqi,wani tashin hankali taji yana sauko mata,aure?.
Aure kuma dai?,tunanin wa zatama aura yafado mata,kanta taji ya soma juyawa,saita koma ta jingina da baya a hankali tana lumshe idanunta ba tare data baiwa daada amsa ba,ita kuwa saita miqe abinta kamar bataga yanayin da take ciki ba tana ci gaba da cewa
"Ja'iri,ko baizo ba nan da jibi ni zan nemeshi"
"Don Allah ki barshi daada,basai kinyi ma kiransa ba" waiwayowa tayi
"Kamar yaya?" Saita rasa amsar bata,don saida maganar tafito tagane tayi baran barama
"Kawai ganinsa ne banason yi"
"To ai kuwa dole yazo ya sallameki,da an rabu kuma ba shikenan ba?" Bata iya amsa mata ba wannan karon,ita kuwa tasa kai tawce uwar daka tana ci gaba da maganganunta,wadanda suka sanya shahidan taji kaman tadora hannu aka tasaka ihu.
Tafi tafi saiga anwar ya kwashe sati uku cur babushi babu duriyarshi,dif kakeji kaman anyi ruwa an dauke,daadan ma ta daina maganarsa kwata kwata,tun tana iya jurewa harta soma qananun zazzabi a tsaitsaye,batasan cewa dan gantalallen zaman da sukayi sabuwar shaquwa ta soma shiga tsakaninsu ba sai yanzu.
Ta bangaren nafisa ma tana can cikin wani irin yanayi,ta rasa wanda zata dosa da maganar,idan tace zata je gida takai qara tasan halin abba da mommyn sarai saisun buqaci dalilin abinda tayi masa wanda ya sanyashi dauke mata wuta haka,tunda sunsan halinsa sarai ciki da bai,idan suka buqaci dalilin kuma tace musu me?,tace meta aikata mishin?,batajin zatayi ganganci ko saken da dukkan abinda ta aikata zai fito,aikata hakan kuwa dai dai yake da tafka babban kuskure Da zata tafka,bata da wata abokiyar shawara ko qawa shaqiqiya kamar mima,ita kuma ga abinda ya hadasu wanda take tunanin ya rabasu kenan,amma daga bisani taga me miman tafi buqata?,kudi,ta baiwa kanta amsa,tana iya lallabo miman ga sakar mata bakin aljihu,taji shawararta kan lamarin,idan yaso ta toshe mata baki da kudi,suyi yarjejeniyar idan komai ya fada duk abinda tasamu za'a dinga rabawa gida uku,ita tadauki biyu,miman ta dauki daya,da wannan shawarar tata ta soma kiran layin miman,saidai duk layin data kira nata sai a gaya mata a kashe yake,kwana biyu kenan tana kiran layin amma yaqi shiga,daga bisani takoma kiran duk wanda tasan yana alaqa da miman,amma kowa sai yace mata baisan inda miman ta shiga ba,shima kwana kaza yana nemanta,abun duniya haka ya sake taruwa yayi mata yawa,lallai idan batayi da gaske ba wankin hula yana neman kaita dare,gwagwarmayarta ta shekara da shekaru tana neman tashi a banza.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Sam gaba daya bacci yayi qaura a duniyarra cikin wannan daren daya cika da sanyi da kuma nutsuwa,duk yadda taso tunkude tunaninsa abun yaci tura,da gaske tunaninsa so yake ya hargitsa zaman lafiyarta,anya ko lafiya yake?,lafiyarsa qalau kuwa,yace idan tace yatafi zai tafi kada dai ace da gaske tafiyar yayi?,gabanta yayi mummunan faduwa da wannan tunanin ya fado mata,ta miqa hannu ta dauki wayarta ta kunnata haske yakawo,saita zuba mata idanu kamar me tunanin amfanin da wayar take a rayuwar mutum,kwanaki da yawa da suka shude haka ta tsinci kanta da saurare da kuma tsammatar ganin gilmawar waya da lambarsa tacikin wayarta saidai shuru maqatau,ta kwatanta ta kirashi yafi sau nawa amma saita kasa,kamar yanzun data nemo lambarsa ta tsaya tana kallonta,saita maida wayar kuma ta ajiye,ta sake maida kanta saman filo,tana jin wani rauni yana ratsa zuciyarta,tana jinta kamar wata marainiya data rasa uwa da uba,tanajin tamkar ta rasa wani muhimmin sashe daga cikin rayuwarta,sanyin jiki da kasala suka sake qaruwar mata,da qyar tasamu bacci ya sureta cike da mafarkansa barkatai.
**** **** ***** ****
Tana idar da sallar asuba ta sake kifewa idanunta cike da wani azababben bacci wanda rashin samun isasheshen baccin da batayi ba daren jiya ya zamto sila,tun daada bata leqota har nauyin baccin yasa tadinga leqota don ta gani ko lafiya,saidai ta leqo ta koma haka ta dinga sata zirga zirga,inda daga bisani data gaji ita kadai tasoma mita
"Wannan yarinyar bata gama sanin ciwon kanta ba,ya zama dole taje asibiti,don naga alama idan na qyaleta ba zuwa zatayi ba,haka zatayi zama da abu a jikinta bata sani ba,taje tayi wani gangancin ma ya zame mata matsala"
Cikin nutsuwa yayi sallama