Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   50 / 53

147K to 150K   out of 156.9K words

kan ganin mace cikin gidan kurkuku tace
"Ban sansu ba" wani tausayinta ya tsirga masa matuqa,har sai daya kasa daurewa ya saka hannunta cikin tafin hannunshi,sunyi kutse cikin rayuwarta,sun kafa mata baqin tarihi,sun dasa mata bacin rai da baqinciki banda Allah ya nuna buwayarsa da isarsa,sun hanata sukuni na tsahon wasu shekaru alhalin ita ko fuskokinsu ba zata iya shaidawa ba,wannan wanne irin zalunci ne,mima yasoma nunawa
"Wannan,ita da nafisa sune ummul aba'isin na rabuwarmu dake da dukkan wani abu daya biyo baya,wannan kuma...." Ya fada yana hadiyar wani abu me daci,kishi da bacin rai na taso masa,musamman idan ya tuna yadda yariqo shahidan a jikinsa,ya taba pant dinta harya cillo mata,banda shari'a da zatayi aikinta ba shakka shi kadai yasan wanne hukunci zai masa da zai sanyashi ya huce
"Wannan,dashi aka hada bako aka bako abinda kika bugu,ya kawoki qofar gidanku ya zubda ke da sunan ciki kika zubar" idanunta dukka tafito ta qura masa idanu tana kallonsa,wani irin suya qirjinta yake,gumi ya karyo mata,abinda yafarun a baya ya soma dawowa qwaqwalwarta
"Kuyi mata bayani da bakunanku azzalumai macuta!" Ya fada cikin tsawa,cikin rawar jiki mima tasoma bayyana dukkan wani abu daya faru,tundaga ganin da suka yiwa anwar din na farko a qofar hall din biki har ranar da anwar yaji meya faru,bayan ta dire shima saurayin yadora da bayanin dukka abunda yasani.

Ko kafin su kammala kuka shahida take shabe shabe da hawaye,sun zalunceta da yawa sun kuma zalunci anwar,babu shakka anwar yacika masoyin qwarai daya rufe wannan mugun sharrin ba tare daya barshi yayadu a bakunan al'ummaba,idan yana da laifi ma cikin kashi dari laifinsa kaso biyarne na rashin bincike,tabbas koda ita taga anwar a wannan yanayin da wadan nan hujjojin,a yadda take mace mai qaramin tunani da gajeran tsinkaye qasa da wanda da namiji yake dashi Allahne kawai yasan me zata aikata,anwar yayi qoqari matuqa gaya daya iya rayuwa da irin wannan bacin ran da baqincikin,da qazaman hotunan dako maqiyiyarka ka ganta cikin wannan yanayin zaka dade kana ta'ajjubi,zaka jima cikin mamaki da nema mata shiriya.

Kasa zama tayi sai kawai tamiqe da hanzaei tafice daga wajen,anwar yatashi shima cikin wani sabon bacin ran ya rufamata baya,ba tare daya damu hurwa da nema gafararsu da suke ba.

Tuni harta isa bakin mota,kuka take haiqan,haqiqa ta jahilci kanta kenan data tsani anwar,tazurfafa kan laifin dayayi mata,ba tare data bashi dogon uzuri ba,ta kuma zurafafa bincike kan dalilin daya sanya tashi guda yajuya mata baya,anwar din data sani cewa ranshine kawai bazai bata ba,harda fiddausi cikin wadanda aka hada baki dasu?,ta tsammaci fiddausin ta aikata ne cikin rashin sani ashe harda ita cikin shirin maqiya?,amma idan tasan fiddausi yaushe tasan nafisa?,me ta yiwa nafisan?,kawai donta ganta da anwar,hadin data tabbatar Allah ne kawai yayishi?,shine zata nemi jafata cikin wannan ramin mai wahalar fitowa banda Allah ya dubeta?.

Shiya bude mata qofar tashiga ya mayar yarufe,ya zagaya yashiga shima ya tashi motar,yadda yaga tana kuka ya tabbatar tana buqatar tafitar da abinda ke damun ranta ne,shi kansa a sanda abun ya bayyana a gareshi yaso ace yayi kukan kozai samu saasauci.

Suna shiga harabar aje motoci na gidan yayi parking din motar ya waiwayo yana dubanta,hannunta ya kamo ya saka cikin nashi hannun ya riqe dakyau yana dubanta cikin wata tattausar murya
"Shahida,dukka wannan kukan bana buqatarshi daga wannan wajen,inda na kaiki kinji labarin abinda yaruga ya wanzune a rayuwarmu wanda ina fata da yaqinin cewa yariga daya wuce a yanzu,inason ki saki ranki mu koma shahida da anwar da kowa yasanmu a baya,inasonma fiye da haka,no more rigima tashin hankali zargi da rashin yarda da juna daga yau,iname neman afuwarki shahida,ki yafemin,ki yafemin ki yafemin" da sauri ta dakatar dashi
"Ashe ni wawiyace ban sani ba saiyau?,ashe da nake zargin ka rabu danine saboda bakasona bansan shine soyayyar da zaka nunamin ba,ka rufe maganar danake da tabbacin fitarta kamar fitar mutuncine daga gangar jikina,abune da zaita wanzuwa yana yaduwa a bukanan mutane,koda inada da gaskiya kowa da yadda zai juya maganar a kaina,inada tabbacin data fita a yanzu gaskiyata ta bayyana koda wasu daga cikin mutane zasu gasgatani wasu ba zasu taba yarda ba,zasuji gaba da dorar da abinda sukaji,wasunsu ma gaskiyar maganar ba zata kai kunnuwansu ba,zasuyita daukarta a yadda sukaji da fari,xancan zai iyaci gaba da wanzuwa a doron qasa yakai ga kunnuwan 'ya'yana harma da jikokina,koda na mutu wani bazai iya shuru ba saiya fada abu mara dadi akaina koda bayan shekara dubune,dukka wannan sharrin ka tunkudemin shi,ka yarda karayu da zancan yana cinka cikin zuciyarka,ka yarda da hukunci daya da zaka iya yimin shine ka rabu dani,babu wani alkhairi anwar dayakai haka,babu wata soyayya datakai wannan wadda zaka boye dukkan wani abu na masoyinka komai girmansa kaqi yadda wani yasani,ba abinda zance dakai sai godiya,sannan inason ka yafemin bisa mummunan zaton yaudarata dakayi kan ka sauya nafisa dani,ashe duka hoton hadine?,me yasa hankalinmu duka baikai kaiba?" Ta qare maganar tasigar tambaya muryarta na rawa kukan na sake taso mata
"Allah ya qaddara dole mu rabu da juna kowa yaje yasamu rabonsa na tsahon shekara shida,amma dayake ALKAWARINSA ne saimun auri juna yanxu ba gashiba?"
"Me muka musu haka rayuwa?" Ta jefa masa tambayar abun na sake mata ciwo
"Ka yefemin,duk ni na janyo dana yarda na karbi abun maye a matsayin magani,bansan cewa matsala na qarawa kaina ba,yanzu gashi ya barwa rayuwata babban tabo,yayi sanadin dana rasa mahaifina,ina dab da rasa mutuncina Allah ya rufamin asiri daya sanyaka masoyi mairufun asiri ga masoyinsa,bamai tonon asiri da kwaroroto kan....." Kuka ya sarqe ta ta kasa qarasawa,wanda hakan ya sanyashi fitowa da sauri ya zagayo kujerarta,ya saka dukka gwiwoyinsa a qasa
"Nina cancanci naroqi alfarmarki bake zaki roqi tawa ba" sa sauri takama hannayensa daya hade waje daya tace
"ka daina don Allah,ka tashi daga gabana" sosai ta riqe hannayensa nasa saiya tsaya yazuba mata idanu tausayinta na kamashi,tanata qoqarin hadiye kukan
"Zan tashi amma bisa sharudda biyu,wataqila idan biyun sun fada na sako sharadi na uku" ya fada cikin son maida mode din bacin rai da suke ciki su duka zuwa wasa da raha,kai ta gyada masa alamun tana jinsa
"Na farko daga yau kimin alqawarin ba zaki sake cewa abba ya rasu ta sanadinki ba,ki yadda da qaddara cewa ko babu abinda yafaru dama kwananshi ya qare,hakanan bawa baya tsallake wa'adinsa,babu me kashewa ko rayawa sai rabbul izzati" kai ta gyada masa da dakusashshiyar muryarta tace
"In sha Allah" kai ya gyada cikin jin dadi sannan yadora
"Nabiyu karki qara tunama ranki ko saudaya cewa kin taba shan wani abu da sunan abun maye,kinsha bisa kuskure da rashin sani,kin tuba kuma tuba maikyau irin wanda Allah yakeso tuntuni,sabida haka ko cikin babin zunnuban da kika aikata babushi,kin yarda da wannan?" Shima kai ta gyada yace
"Good,na uku daga nan wajen,nan wajen da muke" ya sake fada yana jaddadawa gamida nuna wajen da yatsa
"Kin bar duk wani kuka tunani ko bacin rai,kimin Alqawari don Allah"
"In sha Allah" ta sake fada cikin confidence taba goge hawayen da tafin hannunta
"Ma sha Allah,matata 'yar aljanna,sai abu na hudu duk da ban lissafa dashiba na fada?" Ya fada yana fiddo ido kamar qaramin yaro wanda hakan yasata murmushi
"Fadi mana,ka manta tsakanin anwar da shahida babu wani boyeyyen abu,sai wanda shahidanu suka so hadawa,Allah yadubi dukkan zuciyar kowannensu ya fallasa abin?" Kai ya gyada cikin jin dadi da gamsuwa
"Inaso kimin alfarma,don Allah alfarma nace,ki dawo dason anwar kamar yadda yake cikin zuciyarki"
"Fiye dana baya ma" qirjinsa yadafe ya lumshe idanu kamar yadda ya taba mata randa tace tana sonshi
"Wayyo ni dan gatan rahamatulshahida"
wani kyakkyawan murmushi ya subuce mata,duk wani feelings nata a kanshi daya tafi a baya taji a hankali a hankali yana dawowa,ya miqa mata hannunsa tadora nata akai,cikin muryar dake nuna tsantsar qauna da kulawa
"Na miki alqawarin maidake sarauniyar mata,saikinji a jikinki cewa babu wadda takaiki sa'ar miji cikin mata" idanunta ta waro tana murmushi
"Karfa ka fasamin kai da yawa"
"Ki bugi qirji ako ina,ki tsaye kan kowanne bigire ki daga murya ki fada,kice kuma ni anwar nina gaya miki haka" daga hakan ya dagata,yana riqe da hannunta sukaci gaba da takawa zuwa cikin gidan,jinsu suke cikin wata sabuwar duniya,sunajin kamar su kadai suka rage daga ita saishi,dan dubanta yayi kafin su qarasa falon
"Ammafa kafin mu taho daga katsina daada ta kiranu tace baki da kafiya na kula dake,meya sameki?" Baki tadan turo tana tuna tsiyar da daadan ta dinga mata
"Ni lafiyata qalau,kawai wai cewa tayi........" Sai kuma ta kasa qarasawa
"Uhmmm,cewa tayi me?" Shuru ya sake masa,ganin kamar bata da interest kan maganar ya watsar da ita.

Bayan sun gama shirin kwanciya zama na musamman sukayi ko ace zaman tuna baya,ya dinga zaqulo wasu daga cikin kyaututtukan data masa,mamaki yadinga kamata,ta tsammaci yarabu daduk wani abu daya shafeta ai kamar yadda ya rabu da ita,lallai wannan kawai ya isheta hujja kan cewa taba ranshi,kuma qauna ta domin Allah bata mutuwa,saidai wani abu yaso murqusheta.

Babban abinda ya qara masa kima da daraja cikin wannan lokaci shine duk wata takarda daya mata fadi tashin samun makaranta tana hade waje guda kamar yadda ya amsosu,takaddu da albishir din dayaso mata kenan ranar da aka tarwatsa tarayyarsu,duk yadda taso saida tayi kuka,tana sake amanna da qaunar anwar din gareta,kafin wani lokaci kuwa zazzabi ya rufeta ruf wanda shiya tarwatsa musu daren nasu,yayi yayi kuma suje asibiti tace zata warke,cikin taimakon Allah zuwa safiya zazzabin yasauka,ta shiga sabgoginta.

Wunin ranar gaba daya yana maqale da ita,hira ba kalar wadda basuyi ba,kowanne ya baiwa dan uwansa labarin yadda yarayu bayan babu daya,abu guda taboye masa shima kuma bai tambaya ba wato silar soma shaye shayenta,abinda yasa bai tambaya ba shi harga Allah ya rufe wannan babin daga rayuwarshi,ita kuma tana ganin hakan kamar tona asirin mahaifanta ne,duk da cewa anwar yana ganin qima da darajar iyayenta fiye da kima da tunanin mai tunani,tun a wunin ranar tagama karantarsa tsaf,ta masa uzuri tasan kuma yayi haquri hakanan ya jigata,saidai ta bari daya tsoro yacika gaba daya na yadda zata kaya musu,don bata manta wahalar datasha ba a baya,duk saita koma sukuku,ya ganeta sarai ya dinga mata dariya yana tsokanarta.

Koda daren tayi mamakin yadda komai yazo da sauqi ba kamar yadda ta zata ba,ya tafi da ita cikin lallabawa da nuna qauna da soyayya,saidai bayan sallar asubama bai batta ta huta ba,nan ta baje kolin shagwabarta tayi abarta son ranta shi kuma ya biye mata,wuni sukayi suna shayar da juna zallar madarar so da qauna da kuma kulawa,dukka sun fanshe wani rashin kasancewa da juna da sukayi na tsahon shekaru shida.

Kwanansu biyu kafin yasamu ya lallaba a safiyar ranar yace zaije office,kaman ta hanashi fita haka taji,saidai kuma tana tunanin wala'alla daganan zai zarce gidan nafisa ne,haka ta wuni sukuku a kwance bata iya tsinana komai ba,kishinsa da batayi ba a sanda zai qara auren sai a yanzu yake nuqurqusarta,amma ga mamakinta sanda tagama wanka tana tsaka da shafa turare bayan tasauya kaya aka turo qofar,take taji zuciyarta ta washe,duk wani quncinta yatafi,ya qarasa inda take tsayen ya rungumeta ta baya yana sakin ajiyar zuciya mai qarfi,yana kallon fuskarta ta mudubin dake gabansu
"Kaman na shekara daya ban ganki ba Allah shahidana,ya Allah wannan wanne irin sone mai qarfi haka?,anya baki roqi Allah ba kan duk sanda yatashi sake dasa min sonki ya dasaminshi bada wasa ba?",dariya yabata saita murmusa kawai
"Ni don bakasan ya nakeji bane,ya naganka ka dawo?,na zaci kawuce?"
"Ina?" Ya tambayeta ba tare daya saketa ba
"Gida?" Ta amsa masa a taqaice
"Wanne gida?,dama inada gidan daya wuce nan ne?,pls banason ki sake cewa komai,daganan har zuwa wani lokaci duk abinda zanyi ki zuba ido kawai,don Allah karkice komai"
"Kome dai zakayi nidai abu daya zance maka,ka yiwa kowa adalci"
"Abinda nake shirin yin shine kawai adalcin da zan iya nunawa" daga haka ya janyeta bandaki,ya bata duka wankan da kwalliyar saida suka sake wani tare.

Kwana biyu yayi yana fita office don yanason yayi handling komai hannun muhsin na wasu watanni,don yanason ya tattara shahidan subar qasar gaba daya su huta.

Cikin sati daya komai ya kammala,bai gaya mata ba sai daya zama saura kwana uku tafiyar,taji dadi qwarai donko babu komai tafiya mabudin ilimice,ya dauketa yakaita gidan anty zubaida ta wuni,itadai anty zubaidan nata kallonta,tanason tace wani abu amma tayi shuru ko tana tunanin hasashenta ne kawai,sannan ita kanta shahidan bataji tace komai ba,washegari kuma yakaita gida nanma ta musu sallama,anan ta tadda bikin mubina saura watanni uku kacal,tayi farinciki sosai da irin mijin data samu,sai yamna lis gab da magariba yazo ya dauketa suka wuce gidan anty usaina don itama suyi mata sallama,haka ta tafi tana kewar 'yan qannen nata kowa na bata sautun abinda yakeson ta siyo masa.

Gidan anty usaina ta sake abinta sosai kamar ba yayar mijinta ba,batasan me yasa Allah ya hada jininta da ita haka ba,sunsha hira taci tuwonta acan san ranta,itama anty zubaidan binta take da kallo da kuma ayar tambaya,saidai itama taga kaman su anwar din basu fahimci komai ba,iya kallon kulawa da anwar din kebin shahidan dashi duk wani motsinta kawai ya isa ya gaya mata komai,ta dinga sakin ajiyar zuciyata tana yiwa Allah godiya ita kadai,sai bayan shahidan ta basu wajene ta dubi anwar din
"Don Allah anwar kakula da yarinyarnan dakyau"
"Meya faru anty?"
"Inaganin kaman bata da lafiya sosai,bayaga haka kuma inason ka kula da ita kulawa irinta soyayya tausayi da jin qai,shahida mutumce anwar,tasoka tun bata da tabbacin xaka zama wani,ta sadaukar da komai nata saboda walwala da farincikinka,banajin duk duniya zaka samu soyayya makamanciyar tata" murmushi yasaki
"Anty,wannan fadan tun kafin ayimin nayiwa kainashi" zancan sosai yayiwa anty usaina dadi,saiya dora
"Kwanaki haka daada tacemin bata da lpy,to amma na tambayeta tacemin qalau take,sannanma bata wani ciwo,tayi zazzabi dai sau biyu daganan bata sake ba,saicin abincinta ma daya qaru kinga ko babu batun cuta" murmushi kawai tayi ta gyada kai tace gaskiya kam.

Wajen tara na dare suka baro gidan anty usainan,saidai abinda ke baiwa shahida mamaki shine ba wanda ya mata magana kan abinda yafaru na tafiyarta katsina,kenan babu wanda daada ta gayawa abinda yafaru?,murmushi tasaki,daada kenan,daada ta wajenta,tabbas dada ta musamman ce,badon tsananin rabo ba da Alqawarin Allah akansu ba,da yanzu ba wannan batun ake ba,da tuni tabar anwar,anwar yabarta,sun rabu kenan rabuwa tahar abada.

Amwar ne daya lura da murmushin da takeyi ya damqe hannunta
"Yadai tawan?,naga kinta murmushi ke daya,hala an tanadarmin wani babban abun anjima" ya qarashe maganar yana daga mata gira,saita ture hannunsa dake saman cinyarta tana jefa masa hararar wasa
"Ba wani nan,nikam baccina yau zanyi"kai ya langabe mata yayi kalar tausayi
"Haba mana anshad,a tausayamin mana,jiyafa ba'a sanmin ba,yauma kuma sai ace a'ah?"
"Badon halinka ba" ta fada tana murguda masa baki,yadda tayin yabashi dariya sosai,daga bisani tayi shuru tana tunanin ina nafisa wai?,kodai sakinta yayi bai gaya mata ba?,ya gaya mata ba huruminta bane karta sake magana hakan yasa dole tayi shuru.

Kai tsaye qasar germany suka soma yiwa tsinke,ya kama musu hotel mai kyau da tsari wanda zai dace da yanayinsu da kuma tsarinsu,kwanakin da sukayi a germany kwanakine masu matuqar tsayawa a rai,kwanakin da suka zamto musu haske a rayuwarsu,kwanakin da cikinsu babu wanda yakejin zaya manta dasu cikin kundin tarihin rayuwarsa,an zuba soyayya iya soyayya,an barji amarci,an tada tsohon tsumin soyayya wanda akaso kashe musu shi,wata irin soyayya ke tasiri cikin zukatansu,take habaka kullum kwanan duniya,yanayin garin ya karbesu gaba dayansu,wanda kallo daya zaka musu gaba dayansu kaga sauyi tattare dasu,kada ma shahidan taji labari,wanda sau tari anwar din kan koma saikace wani dolo,yazauna yayita binta da kallo duk inda tayi,idan tayi qorafi kuma maimakon ya amsata sai kawai taji yana hamdala,tun bata saba ba har abun ya zame mata jiki,sunyi yawo gurare daban daban har shahida ta gaji,zata iya cewa wannan lokaci bata yaba spending time me dadi a rayuwar ba irin wannan lokaci.

Wani kwanciyar hankali da salama ta ratsasu gaba daya,sun manta da dukkan wata matsala,sun daina tuna kowa da ganin kowa sai junansu.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Zaune yake kan kujerar dake falon dakin nasu na hotel,yayi kyau cikin wasu kayan sanyi da wando three quater,qafafunsa miqe saman wani abu mai kama da tum tum yana amsa wayar da yanzun nan anty usaina ta kirashi,wanda hakan yasanya shahida miqewa wanda daa tana kwance ne a jikinsa suna hira,tahau kintsa dakin daya hanata dazu,yace tayi zamanta shikam sanyi yakeji yanada buqatar duminta.

Wayar yake amsawa amma duk inda ta gifta idanunsa na kanta,dogon wandone a jikinta wanda ya kamata dam,ya fidda shape dinta sosai,rigar jikinta ruwan hoda me wani irin adon duwatsu masu haske ta haskata qwarai,hakan yasa tasake daukar hankalinsa,rabin hankalinsa naga wayar,rabi naga shahidan
"Kiraka nayi inji dalilin daya sanyaka jingine matarka kana mata wannan wulaqancin dacin kashin anwar"
"Matata?,nafisa?" Mamaki ya kama anty usaina,tsoro da taraddadin karya soma halin nasu na zama ganin yasamu shahida
"Auni kake tambaya?,bayan shahida da nafisa kana da wata matarne halan?" Shuru kawai yayi yana sauraren anty usainan,don sunanta kawai yasa yaji ranshi ya cunkushe
"Ina iliminka hankalinka da tunaninka yatafi anwar?,me tayi maka haka zata janyo abinda zai jefaka cikin halaka ranar gobe qiyama,ashe har diyar alhj abba ta cancanci haka daga gareka?,kaga yadda tarame ta fige ta lalace?,kana tunanin idan mahaifanta sukaji ko suka gani ransu xai musu dadi?,me tayi maka?"
"Ashe bata gaya miki abinda tayimin ba ko?"
"Eh bata fada ba,tace dai ta rasa gane kanka,don me yasa zaka aikata mata haka?" Ciki sanyin rai da salama yace
"Kiyi shuru anty don Allah,ki sata gaba ta gayamiki abinda yafaru,idan ta gama kuma ki sakata ta rantse kan gaskiyar maganar ta gaya miki,daganan sainace miki kiyi hukunci kan batun"
"Kai me yasa ba zaka gayamin da bakinka ba?"
"Ita tasoma kawo qara kinga a bakinta yakamata aji komai da komai,ni ban kawo

50 / 53