Author : HUGUMA Category : African Stories & Novels
wannan karon harda inna kakar anwar,wanda ta manta rabonta da kano,shi yasa wannan karon anwar din ya matsa sai tazo,tunda ta fuskanci shahidan bata da ra'ayi hada wani taro sai ita ta hada a gidanta,saidai sa'idan ta gaya mata anjima zasuzo karban amarya.
Kaman babu abinda yake damunta haka suka dinga sabgoginsu da yaran,anwar din yana daga sama,wani lokaci ya leqo yayita kallonsu bata sani ba,wani lokaci kuma yana daga daki yakejin motsinsu,shi ya aika akaje aka dauko yaran yasa aka kawo mata,yasan koba komai zasu hanata zaman dakin daya tsira,ta kuwa ji dadin zuwan nasu,duk wata damuwa da take jinta liqe da ranta sai takejin ta ragu.
Ko data gama abinci iya ita da yaran suka zauna sukaci,bayan sun gama tasa suka kwashe suka kai mata kitchen zata wanke,tana tsaye a kitchen din ta soma dauraye kwanukan ya shigo,ta waiwaya ta dubeshi ta dubeshi sai kuma ta dauke kai tana ci gaba da wanke wankenta
"Ni ban taba ganin ango irin wannan ba,ba abokai ba komai,ka dawo gida ka samu waje ka zauna?" Take tadin ita da zuciyarta,wanda harya iso bayanta dab da ita bata sani ba,kallonta yake hakanan qirarta da shape dinta yake daukan hankalinsa fiye da qima,saiya dinga tuna baya can da bai taba ganin komai nata ba,saboda a sannan ma'abociyar sanya hijabi ce,a lokacin da yake cike da buri da fatan Allah ya bashi kudin da zai aureta ya mallaketa a matsayin matarsa,yanzu gata a matsayin matarsa,amma wani abu ya ma rayuwarsu karan tsaye,saiya kauda wannan tunanin yace
"Ni ba za'a bani abincin ba?" Gocewa tayi gefe jin maganarsa dab da ita,da alama tsaye yake kenan a bayanta
"Ban dafa dakai ba" ta amsa masa tana ci gaba da wanke farantan ba tare data juyo ta dubeshi ba,shuru yayi yana dubanta,bata taba hanashi abinci ba sai yau,sai baice komai ba ya matsa gefe kusa da inda tukwane suke,ya dauki daya ya dauraye ya ya tari ruwa a fanfon dake kusa da ita,ya hada kayan qamshi ya dora ruwan shayi,ya jingina da jikin kwabar kitchen din yana kallon ruwan yana jiran ya tafasa,duk abinda yake tana kallonshi ta gefen ido,ta rugashi gamawa don haka ta fita tabar masa kitchen din,suna falon yazo ya wucesu da ruwan shayin,harya soma hawa saman saiya waiwayo yana dubanta,hankalin yaran duka nakan arewa24 yace
"Banfa ji haushi ba,wanda ma aka dinga bani a baya Allah ya amfana ko?" Ya qarashe maganar yana daga mata gira,kauda kai tayi yadda ta saba kaman bata ganshi ba,yayin dashi kuma yaci gaba da hawa saman.
Da yammaci suka sake gyare gidan tsaf suka cikashi da qamshi tako ina,har turarukan da bata taba amfani dasu ba sai ranar,kama daga na labule carfet da wanda kebin iska,sun gama kenan sai gashi ya sauko cikin shadda brown sabuwar qarr,kyau uya kyau yayishi,sai taga kamar wannan shigar ta musammance,duk da dama shidin koda yaushe cikin saka sabbin sutura yake,hakanan taji wani abu ya tokareta sanda suka hada ido ya dage mata gira guda,saita aje pillow din hannunta ba tare data bari ya iso inda suke ba ta shige kitchen,tana jinshi da yaran suna uncle kayi kyau,ya gama dan hirarsu dasu ya fice daga gidan bayan ya dauki daya daga cikin motocinsa.*Alqawarin Allah*
46
Sanda takoma dakinta da niyyar shiga wanka taga wayarta na haske,ta jawo ta bude sannan ta duba,saqone daya shigo minti biyar baya
"Haka kike kishina?,ki rage kishina wallahi" kalmar da aka rubuta kenan,tsaki tadan ja tana ture wayar,tasan ba kowa bane sai anwar,batasan me yasa yake wasu abun kamar da gayya ba,sautari yana hakanne kawai donta biyeshi ko yaji tabakinta musamman idan yafuskanci batason magana ko batason kulashi.
Bayan ta fito ta shirya kanta cikin wani lace mai azabar kyau da tsada,qirar qasan switherland,wanda anty zubaida tun a sannan taso ta sakashi ranar da za'a kawota nan gidan amma taqiya sam,blueblack ne me yarfin adon peach a jiki da green dan kadan kadan,gaba daya baki yaran suka saki suna kallonta sanda ta fito kafin daga bisani kowa yahau sharhi,saida suka saka ta koma ta sake kallon kanta a mudubi,ba qarya sukayi ba,kamar amaryar haka ta koma,ga uban qunshi dama hannu da qafa,saita kalli kanta ta sake juyawa ta kalla,har batasan sanda murmushi ya qwace mata ba.
Tana daga dakin ta jiyo 'yar hayaniya,mubina ta shigo ta gaya mata su anty usaina ne suka zo,saita laluba mayafin da zai dace da kayan ta saka sannan ta fita.
Cikin girmamawa suka soma gaidawa,kanta a qasa don harda inna a ciki,karon farko data soma ganin innar a ido,har qasa ta tsugunba ta gaidata,innar ta amsa cikin walwala saboda yadda suka samun shahidan wanda basu tsammaci zasu ganta haka ba,ta gabatar musu da abinci amma sukace a qoshe suke,ganin magariba ta gabato suka soma yin alwala,wanda a sannan anty usaina ta samu ta kebe da shahida,maganganu ta mata masu kwantar da hankali da saka nutsuwa,wanda hakan ya qara mata nutsuwa qwarai.
Suna idar da sallar ayarin amarya suka qaraso,saboda yawansu yawanci a qofar gida wasu motocin suka tsaya,a sannan idarwarta kenan da salla tana saman abun sallarta,wani matsananciyar faduwar gaba taji saidai bata bari ta dirirce kota rude ba,saita dinga ambatar la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahla,wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla,bata miqe ba hakanan bata yi magana ba tana zaune a wajen tana sauraren hayaniyar mutane.
Mubina ce ta shigo ta sameta
"Yaya wai ki fito,ga baqin nan sun iso" amsa mata tayi tana miqewa mubina tafice ta barta,sai tayi tsai gaban mudubi kawai tana duban kanta,faduwar gaba da fargabarta na qaruwa,powder ta dauka ta sake shafawa,ta fesa turare sannan ta gyara daukin dankwalinta,ta dauki mayafinta daya dace da kayan ta saka ta zira plate din takalmi sha daya shiga da kayan,tanayi tana addu'a sannan ta fito.
Kusa da ita anty usaina ta matsa mata tace ta zauna,basu da wani yawa mutanen cikin falon,sai tayi shuru kawai tana sauraren yadda zuciyarta ke bugawa,wanda ita kanta batasan dalili ba.
Gudar data karade gidan yasanya suka gane motar amarya ta iso,sai anty zubaida dake zaune a daya barin na shahidan ta kalleta
"Kina addu'a dai ko?" Kai kawai ra gyada mata saboda yadda taji jikinta yayi sanyi kamar an zare mata laka,dukkansu hankulansu nakan qofar har aka shigo da nafisa.
Kanta na lullube kaman kowacce amarya,tana riqe hannun qanwar mummy suka qaraso da ita inda su inna ke zaune,aka gaisa sannan suka damqata a hannun shahidan kamar yadda al'ada tanada,anty zubaida ita tayi musu addu'a sannan suka qarasa da ita gefanta.
*10:30 pm*
Ruwa mai azabar dumi ta hada tayi wanka dashi wanda hakan ya taimaka wajen saukar gajiyar jikinta,ta dawo gaban mudubi ta zauna,sannan ta bude manta ta soma shafawa,tanayi tana sauraren yadda gidan yake shuru,kusan kowa yatafi,daga ita sai nafisa sai wasu daga cikin qawayenta da suka kafe kai da fata kan ba zasu ko ina ba sai ango ya shigo an siyi baki,kusan kafin ya haura samanta tana jiyosu sunata shaqiyancinsu da iya shege,nan ta tattara ta wuce tabar musu qasan,duk abinda take ba cikin kasala da mutuwar jiki takeyinsa,haka kawai takejin zuciya da ruhinta babu dadi.
Cikin mintina qalilan tagama komai,ta mulke jikinta da cream perfume,ta cire sabuwar rigar baccinta cikin kayanta mai santsi da kwantawa a jiki ta zirata ba tare data buqaci bra ba,don jin qirjinta take kaman yana mata ciwo kadan kadan,ta kashe qwan wutar dakin nata tabi lafiyar gadonta,saidai fafur bacci yaqi zuwa,haka ta dinga raba ido cikin duhu tare da tunani barkatai cikin zuciya da qwaqwalwarta,harta gaji da ruf da ciki ta koma rigingine.
Sha daya saura na daren taji shigowar motarsa,ba jimawa taji shigowarsa cikin gidan da fitar 'yammatan amaryar suna mita,ta runtse idanunta sanda taji qarar rufe gate din gidan gaba daya,saitaqi bude idanunta tabarsu a rufen tana fata da addu'ar zuwan bacci.
Ta cikin rufaffun idanunta taga haske ya gauraye dakin,cikin mamaki ta bude idanunta da sauri,saita waiwaya tana duban bakin qofa,sam batasan sa'adda daya bude dakin ba.
Yana tsaye qyam goye da hannunshi,sanye da kayan daya fita dasu dazun,idanunshi zube fes a kanta yana qare mata kallo daga sama har qasa,surarta cikakkiya ta gama bayyana cikin rigar baccin data lafe a jikinta ba tare data sani ba,wani abu yaji yana tsirga masa daga kanshi har qafa,sai ya kasa dauke idanunsa daga kanta,kauda idonta tayi da sauri sannan ta soma lalubar mayafi donta lullube jikinta,bata ankara ba ta jita cikin jikinsa gaba daya ya rungumota ta baya,zuciyarta tahau bugawa da sauri da sauri,kafin tace komai ya rigata
"Wai me yasa kikemin haka ne?,ko don kinga na qyaleki?" Ya fada da muryarsa wadda tayi laushi,saita kasa aiwatar da komai maimakon daa da tayi niyyar qwace kanta,a qalla minti uku sukayi a haka sannan ya janye jikinsa yayi baya ganin idan baiyi da gaske ba zai saki layi,baison hakan kuma ta kasance a lokacin dabai dace ba,ledar daya aje a baya ya dauko ya aje mata a gabanta sanda ta sulale ta zauna a gefan gadon tana tattare jikinta waje daya,don bata da kuzarin dauko mayafin nata,dubanta yake cikin tsakiyar idanunta sannan yace
"Kika samu waje kika zauna,waye zai kaini dakin amaryar?" Ya fada can qasa,so take tace masa kada Allah yasa yaje din indai itace zata rakashi,amma saita kasa fada,tayi banza dashi kawai,harya gaji da kallonta da kuma jiran amsarta,saiya saki ajiyar zuciya yana qoqarin yaqi da abinda yakeji a kanta
"Shikenan,saida safe" ya furta yana takawa zai fice daga dakin,har yakai bakin qofa sannan ta bude bakinta tace
"Karka sake shigomin daki bada izinina ba" fasa bude qofar da yake shirin yi yayi,saiya sake takowa yadawo cikin dakin,sai dayazo gab da ita sannan yace
"Maimaita abinda kikace,banji ba" banza tayi dashi tana kauda kai,saboda yadda ya tsareta da ido,uwa uba kuma kusancinsu da bataso wanda ke haifar mata da wani yanayi wanda yake saka wani abu dake kama da kishi yana taso mata daga ranta,wanda itasam batason hakan,ya tsaya gab da ita da yawa,idan kuma ta biyeshi tasan zai jima bai fita mata a daki bane,wala'alla ma daga qarshe saiya jangwalo abinda xaisa ta bige da kuka
"Ashe ana tsoron iya inji dan mayya,zanyi maganin bakinkin nan" ya fada yana kai yatsanshi lebanta,saitayi saurin kauda kai tana balla masa harara,ya gani sarai wanda har baisan sanda murmushi ya subuce masa ba
"Yaushe wai shahida ta zama mara kunya me tsiwa ne?,shahidan dana sani mai kunya,idan naje zance bata iya......" Kasa qarasawa kuma yayi,sam ya mance baisan yana sakin layi ba sai dayaga ta tattara dukkan hankalinta kanshi ta zuba mishi ido,dukkaninsu kowa yaji cikin jiki da zuciyarshi,ya tuna musu wani abu ya kuma famawa kowannensu tabo da miki,har ya futa daga dakin yaja mata qofar bai iya sake cewa komai ba.
Dakinsa ya tura yashiga,ya zube bakin gadonshi yana fitar da iska daga bakinsa,bayajin karsashi ko wata walwala ko kadan tattare dashi,yabi dakin da kallo kamar yau ya soma ganinsa,sannan ya miqe ya soma cire kayan jikinsa,ya hada ruwan wanka mai zafi ya dauki towel yashige.
Dai dai lokacin ta hauro saman,tsam ta tsaya tana qarewa falon saman kallo,ya qawatashi matuqa wane falon qasa?,wani kishu bacin rai baqin ciki da tsanar shahida suka cikata,takalli sashen da akace mata dakin shahidan na nan ta zuba mishi harara kamar shahidance a tsaye,sannan taja wata doguwar qwafa kana tayi gaba,tura qofar dakin nashi tayi ta shiga,ko ba'a gaya mata ba tasan wanka yake don ta jiyo qarar ruwa,ta qarasa bakin gado inda ya tube kayanshi ta dauka tana shinshinawa,qamshin kayan ya ratsata kamar ba kayan daya cire ba,ta lumshe ido tana sakin murmushi,ba shakka zata morewa rayuwarta da miji dan gayu,inama ace mima batazo yau da wannan maganin ba,yau da sai tayi ihu iya ihu,ihun da zai hana shahida bacci,idan banda tsabar wulaqanci ta ina amarya na qasa uwar gida na sama?,ita zata yiwa bariki,baridai magani ya kammala abubuwa su fara daidaita yadda ta tsara,kowa zaizo hannu ne,da wannan tunanin tasaki kayan,ta isa bakin mudubin dakin tadan jaye yalolon mayafin data yafawa kanta,tana kallon kanta da kanta ta mudubi cikin rigar baccin data saka,juyawa tayi baya ta tabbatar ko ina yafito,taso ace ma ta tadda shahidane a falo tazo ta wuceta tana kallo kuma babu yadda ta iya,amma babu komai ajuri zuwa rafi da tulu
"Toke daba kwanciya zakuyi ba inake ina wannan shigar?" Ta tambayi kanta da kanta tana riqe haba,saita saki murmushi tana baiwa kanta amsa
"Ko babu me gaba daya ai ba'a hanamu romance ba ko?" Tuna hakan yasake faranta mata ranta,lallai yau zata morewa jikin anwar,saita kai maqura a romancing dinsa.
Tana tsaka da karanta wannan wasiqar jakin yaturo qofar bandakin yafito,sak yayi cikin mamaki yana dubanta,murmushi ta sakar masa tana dan sadda kanta alamun kunya tana tsaye a wajen,sai daya gama qare mata kallo da suturar dake jikinta cikin sanyin jiki sannan yajuya ya rufo qofar bandakin ya soma takowa zuwa cikin dakin,ita tasoma magana
"Na jika shuru ne inata jiran kuma naji ban sake jin motsinka ba" yana shafa mai sanda take qarewa qirarsa kallo tana hadiyar yawu,ta qagu ya qaraso kodan rungumeta ne yayi amma saiya zauna shafa mai,sai yabata amsa dacewa
"Da kinyi zamanki ma,zan qaraso nan din ai" bayanshi ta tako ta tsaya,ta miqa hannu ta dauki man shafawar ta soma shafa masa a baya,wanda hakan yasa wutar jikinsa ta dauke gaba daya,yaci gaba dayi masa magana cikin shagwaba
"Na kasa jira ne,so nake naganka,yau sau daya fa na ganka" sam kasa amsa mata yayi saboda gaba daya jikinsa yadauki wuta,saiya ture hannuwan nata ya miqe don baiso ta sakashi abinda baida niyyar yinsa ayau,ya isa ma'ajiyar kayan sawarshi yacire wasu kayan bacci yakoma bandaki yasanya.
Tana tsaye har yanzu,ya karanceta a nutse,ya fahimci yanayinta,amma ta yaya zaiyuwu su zauna saman shahidan na nan?,hakan saiyake ganin kamar anci fuskarta ne,saboda haka ya dauki ledojin yace da ita
"Muje" saita narke
"Nan fa?,ni nafison wannan dakin" kaiya girgiza yana kewayeta yayi gaba,dole ta biyoshi,amma taso su zauna nan din ko motsin qarya tayi duk da babu wani abu da zata yadda yafaru tsakaninsu tasan zata matuqar baqanta nata rai tare da barinta cikin tunanin ko komai ya wakana?.
Ta fannin shahida kuwa qur'ani ta saka a wayarta qira'ar shaik shuraim wadda ta karade dakin gaba daya ta ratso har falon,hakan yasanya mata nutsuwa qwarai,har taji bacci yasoma fisgarta,sanda zai gifta dakin karatun yaratsa kunnuwansa,a karon farko tun bayan wasu shekaru yaji tausayinta ya ratsashi,a haka suka sauka shida nafisan zuwa qasa.
Amaryar zamani ta yadda da wannan sunan ta kuma yiwa kanta laqabi dashi,saboda haka bata yiwa kanta qauro ko cutar kanta ba taci kazarta sosai,hakanan da suka kammala shirin kwanciya ma,abubuwa suka soma tafiya ta zage sosai tana aika da nata wasannin,tunda tasan cewa ba zata yarda komai ya wakana ba,to ba shakka zatayi iya bakin qoqarinta ta ragewa kanta zafi ta wannan hanyar,uwa uba a nata tunanin gwara ta rikita anwar din,ta yadda ko wata shida tayi bata barshi yayi ba bazai iya haqura ba bazata fita daga ranshi ba,zaita bibiya ta yadda duk randa akace komai zai wakana zai zamto tamkar salla a wajensa a ranar.
Mamaki qwarai yakama anwar din,yadda take tafi da lamuran nata ba kunya ciki,amma bashi da wata hujja dazai hanata,tunda haqqinta ne ta kuma nema,ko a wajen Allah idan ya hanata yayi laifi,saboda haka ya bude mata nashi salon wanda yakusa tafiya da ita har taso mance sharadin maganinta,saidaga baya data ankata ta tattakura ta tureshi gaba daya,wanda yatafi luu saboda dukka qarfin jikinsa babu,gaba daya hankalinsa yana gab da tafiya shima,da farko ya zaci tsoro takeji yabi hanyar da zai amintar da ita amma furrr taqi,dole daga qarshe ya miqe dukka jikinsa rawa yake,yakai wani stage da shine na qarshe,yakai matakin da yakejin ya kamata ace shima ya wuce sahun samartaka,shi yasa yadda tazo mishin ya tabashi sosai,amma bazai sake taba koda yatsarta ba ayau tunda bata da muradi,saiya bude toilet din dakin ya shiga ya budewa kansa shower tun daga saman kanshi,sanyin ruwan na ratsashi yana qoqarin controlling kanshi,ya jima ahaka kafin ya samu yanayinsa ya daidaita sannan yayi wanka ya fito,a sannan ya sameta zaune,ba alamun tsoro ko kunya a fuskarta,ta maida rigar baccinta tana shirin kwanciya,gefen gadon ya samu shima ya kwanta yana sakin numfashi,ta matso da niyyar rungumeshi ya kada mata yatsa,don ba shakka idan ta sake ta tabashi a yanzun komai zai iya wakana,shi kuwa baijin zai yiwa nafisan dole,don badon tun farko ta nuna aniyarta bama ba abinda yayi niyyar nema daga gareta,har sai lokacin da zuciyarsa ta gama gamsuwa da aminta da ita,haka takoma can qarshe tana kallonshi,baisan me take ji bane,tanajin ta fishi buqatuwa zuwa gareshi,amma dole tabi sharadi saboda tacika muradin zuciyarta.
Qarfe goma da rabi na safe ya tura qofar dakinsa ya fito,dai dai lokacin da shahida ke haurowa saman bayan ta gama kintsa inda zata kintsa din ta dafa abubda zataci dai dai cikinta,don batajin zata iya musu wani abinci suci daga nafisan har anwar din,hada idanu sukayi,ita tana dubanshi ne cikin mamakin me yake a dakin,yayin dashi kuma yake kallonta saboda yadda tayi masa kyau matuqa gaya cikin wasu riga da skert,kanta babu dankwali saboda saurin da take ta gama komai tahige dakinta,don batason ganin kowa cikinsu,take abun jiya ya taso masa,har sai daya rintse ido gami da dunqule hannunsa yana dan cije lips kadan
"Ina kwana" ta gaidashi tana niyyar wucewa,qamshin nan nata mai sanyi ya