Author : HUGUMA Category : African Stories & Novels
minti daya ba tare da wani daga cikinsu yace komai ko yayi wani qwaqwaqwaran motsi ba,ture kujerar da yake kai yayi baya sannan ya miqe tsaye yana kwashe wayarshi da muqullin motarsa
"Zamuyi magana later" ya fada yana sauka daga step din da dining din yake kai,da hanzari ta biyoshi a baya tana son tace wani abu,kacibus sukayi da hajiya bilkisu mahaifa ga nafisa,dan dakatawa yayi kadan cikin girmamawa
"Au harka kammala kenan?"
"Eh zan wuce office ne ana jirana"
"To ko saika dawo din?,da akwai maganar da da nakeso muyi"
"To ba damuwa" ya fada yana ja da baya,ta wuce yabi bayanta zuwa cikin falon.
"Alhaji ne yace na tuntubeka,me zai hana ka dawo cikin gidan nan kaci gaba da zama damu kamar yadda ake a baya?" Nafisa dake lafe kusa da hajiya bilkisu ta daga kai a hankali tana satar kallonshi,addu'a take a ranta Allah yasa ya amince da hakan,da tafi kowa jin dadi a duniya,koda yaushe bata da burin daya wuce ta ganta kusa dashi
"Ayima alhj godiya na gode sosai,saidai yanayin aikina bazai bani damar hakan ba,hakan ma alhmdlh babu wata a matsala" dan shuru tayi sannan ta jijijjiga kai
"Toh shikenan...babu damuwa Allah ya dafa...."
"Don Allah ya an....." Nafisa tayi hanzarin fada don ba hukuncin dataso anwar din ya yanke kenan ba,harara hajiya bilkisu ta jefa mata wanda shine silar yankewar sauran maganar tata,miqewa yayi yayi mata sallama kana ya fice daga falon gaba daya zuwa inda ya aje motarshi.
"Ke wace iriyar yarinya ce ne nafisa?,bakiji gargadin da nake miki koda yaushe akan ki dinga kama kanki gaban anwar?,a haka kike tunanin zaki samu qima da daraja wajenshi?" Langabe kai tayi cikin sigar tausayi tace
"Afwa mom...." Bata sake ce mata komai ba ta gyara zamantabta dauki wayarta ta shiga danne danne,hakan ya sanya nafisan itama miqewa ta haura sama inda dakinta yake.
Kai tsaye gaban mudubi ta isa ta tsaya sosai tana qarewa kanta kallo,har yau cikin zuciyarta bata jin ta mallaki anwar yadda takeso,tanaji a jikinta har yau zuciyar anwar ba tata bace,meta rasa?,meye bata shi?,ta fita komai,ta kere mata a komai,tun daga kyau,kudi zuwa matakin karatu,amma tana jin har yau kamar ta kashe maciji ne bata sare kanshi ba.
Da hanzari ta koma da baya ta lalubi wayarta dake aje gefan pillow dinta,sai data fara tura mishi saqo dake qunshe da kalaman soyayya sannan ta lalubi number mema ta kira,bugu hudu ta d'aga
"Yayinki ake" mema ta fada cikin daga murya mai cakude da dariya dariya,murmushi nafisa ta saki tana shaf fuskarta zuwa wuyanta,yayin da take sake qarewa kanta kallo a madubi,wannan kalma na mata dadi,amma gaba daya kaman bata aiki akan anwar,duk da cewa bata da wata qwaqwqwarar hujja da zata nuna cewa babu sonta cikin zuciyarshi,saidai ita din bata gamsu da yadda mu'amalarsu ke gudana ba har zuwa yau
"Wannan kalma mema taqi amfani akan anwar har yau"
"Kai haba?,wane mutum?,shi ya isa?,me ya fiki dashi da zai...."
"Dakata mema....kice komai a kaina amma banda akan anwar....mema,ina tunanin mun kashe maciji ne amma bamu sare kanshi ba,zuciyata da ruhina har yau basu gamsu ba,ta yaya zan sake binneta da ranta?,ta yaya zan sake b'atar da ita daga duniyarshi?,inason haskena shi kadai ya wanzu a cikin ruhi da rayuwarshi"
"Yanzu me kike tunani?,me kike gani?"
"Ke zanwa wannan tambayar" shuru mema tayi na wasu 'yan sakanni sannan tace
"Alright ina da wadansu 'yan dabaru da shawarwari,amma yanzu bana qasar,ina benin republic...."
"Ubanme kike jeyi can?,ke mema???" Nafisa ta katse meman cikin zabura,tun kafin ta gama bayanin nata,dariya mema ta saki sannan tace
"Share kawai"
"Ohk....ya zama dole ki dawo to"
"Saboda me?" Ta fada a dan tsiwace
"Saboda matsalata,kin sani sarai bana son jira?"
"Haba hajiyata....kinsan me ya kawoni nan din?,asara kikeson janyomin kenan"
"Har ta nawa?" Ta tambayeta kai tsaye
"Dubu dari ce ba yawa"
"Zan biya....ki tabbatar gobe kin dawo,wajen yammaci mu hadu a indomie joint"
"Allah ya barmin hajiyata,karkiji komai,bari na fara hada kayana" ta katse wayar yana fadawa saman katifar dakinta,ba wani benin da taje,ba nisa tayi ba,don a yanzu haka ma tana cikin katsina.
Aje wayar nafisa tayi,sannan ta juya ta shige bandaki.
Jujjuya wayar yake a hannunshi bayan ya kammala karanta saqon nafisan,sau tari bai fiya maida mata amsa ba,har hakan ya zame mata jiki bata fiya damuwa ba,har zuciyarshi yake hakan bawai da gayya bane,bayajin wani abu dangane da duk wata kalma da zata fito daga bakinta ko ta saqon waya,maida wayar yayi aljihunsa sannan ya fito daga motar tashi ya kashe ya tunkari ginin kamfanin.*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*KO KUMA*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ku danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGππ½*
ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*AA*
0οΈβ£6οΈβ£
Saida gari ya danyi duhu kadan sannan ya dawo cikin gidan,ya duba garinsa yayi laushi,ya zuba suger dai dai gwargwado ya zauna gefan 'yar katifarsa ya soma sha,inda ya kunna redio da wayarsa qarama keypad samfutin tecno yana sauraren labarai.
Kafin ya kammala an kirayi isha'i,sake miqewa yayi ya fice zuwa masallaci,don sam baya wasa da sallar cikin jam'i,koda aka idar nan majalisar dake kusa da gidanshi yadan xauna aka taba hira,bai jima can da yawa yayi sallama dasu,kasancewar yana da masaniyar gobe yana da lacture ta qarfe tara,kuma dama bai fiya zama cikinsu ba ba dabi'arsa bace wannan,hakan yasanya wasu kejin haushinsa tare da yi masa kallon mai girman kai,yakan zauna lokaci zuwa lokaci saboda kauda wannan zargin daga ransu,bugu da qari ya sani dole kuwa ya fita tun bakwai,don kuwa da qafarshi yake takawa har zuwa makarantar,zuwanshi mota a abun hawa abune mai matuqar sa'a,imma wani aikin qarfin ya samu yayi ya samu kudi,ko idan anty usaina ta d'anyi samuwa ta kirashi ta bashi wani abun,ko Allah ya hadashi da d'aya daga cikin 'yan makarantarsu ya rage masa hanya.
Allah ya taimakeshi yau cikinsu ba wanda ya shigo masa gida,saboda haka ya kulle ko ina yayi nafilfilunsa kamar yadda ya saba,ya roqawa iyayensa da 'yan uwanshi gafara sannan ya kwanta bayan ya sake kunna rediyon yana sauraren shirye shiryen da sukeyi.
Sannu a hankali tunaninta ya kutso cikin kaiwa da kawowar da qwaqwalwarsa keyi tun dazu,ya dan saki murmushi yana wassafo kamanninta,yanayinta tsarinta da tafiyarta,da ganinta zatayi hankali,da ganinta akwai nutsuwa tattare da ita,da ganinta ba maison hayaniya bace
"Duk taya akayi kasan hakan?" Ya tambayi kansa da kansa,saiya sakarwa kansa murmushi yana girgixa kai gami da runtse idanunsa,shima baisan ya akayi ya tsinci kansa da fadawa wannan bigiren ba,saiya juya zuwa daya barin yana son maoda hankalinsa kan programe din da ake gudanarwa a gidan redio a sannan.
Tun bayan sallar magariba ummantata keta sintirin aiken qannen nata kan ta fito taci abinci,saidai sam ta qiya,tayi kwanciyarta abinta,ranta ne kawai ke mata suya,a duk sanda irin wannan balahirar ta faru a gidansu idan da safe ne wuni take cikin qunci da damuwa,hakanan idan da yammaci ne koda dare kwana take cikin qunci shima da damuwa,wani lokacin takance inama kurma Allah ya halicceta?,inama makauniya ce ita ta huta da ganin wannan baqon lamari,wanda ya zama tambarin gidansu,ya kuma zama abinda jama'ar unguwa ke goranta musu dashi,don babu wanda baisan irin rayuwar da ake tsakanin uammansu da babansu ba,tayi kuka har sau babu adadi,tabi hanyoyin gyara bila adadin amma babu alamun ma sauyi bare akai ga gyaran gaba daya,tayi tunani iri daban daban masu kyau da marasa kyau amma bata samu hanya mai bullewa ba,tayi yaji tabar gidan batasan adadin sau nawa ba amma sun bita sun dawo da ita kan alqawarin komai ya wuce zasu gyara amma babu alamun sauyawar lamuran,ta tambayesu me yasa suke hakan amma su kansu basu san amsa ba,abu d'aya ta sani shine,dukkaninsu tsakanin ummanta da babanta babu wani mai haquri acikinsu,ummanta bata da haquri ko kad'an kamar yadda mahaifinta yake,bata raga masa ko daya,idan ya mata taga bai mata dai dai ba take zata rama,shi kuma yaga ta rainashi kenan haka zai biye mata suyita yi.
Basu san ciwon da hakan ke mata a qirjinta ba,basu san illar dahakan ke haifarwa ga tarbiyya yara da tunaninsu da ginuwar hankalinsu,iyayenka a wannan bigiren na fada da juna kulli yaumin har sauran jama'a su shaida hakan kai me yayi saura a rayuwarka?.
Saida umman taga da gaske take bazataci abincin ba kamar yadda ta saba a duk sanda ta samesu suna cecekuceb da suka saba,saita dire faruqu ta nufi dakin nata,ta yaye labulen tana tsaye daga dokin qofa tace
"Tunda sai abinda kikaga dama zakiyi bismillah,dadin abun cikinki ne ba nawa ba,yunwa kuwa dai dai take dake matsalarki ce wannan,ki tashi ki gayamin ya akayi sauran botikaina sabbi suka fashe haka?" Da qyar ta juya daga kwancen da take ta d'aga kai ta dubeta
"Wasune garin wawaso suka fasa su"
"Botikan duka?" Kai ta gyada mata
"K'nnnn,ai shikenan,Allah ya kyauta" ta fada tana sakin labulen,maida kanta tayi ta kwantar,inama ace haka takewa mahaifinsu a duk sanda wani abu ya hadosu?,ta tabbatar da shine tsautsayi irin haka ya faru da yau Allah ne kadai yasan qarshen fadansu.
Mubina ce ta shigo da kwananon abincin ta dire mata ta juya ta fice,bata dai kallesu ba tana ci gaba da kwanciyar
"Idan baki tashi kin kama abinci kinci ba na shigo sai nayi mugun saba miki" ta jiyo muryar umman daga tsakar gida tana gaya mata,hakanan badon son ranta ba ta sauko ta tanqwashe qafa ta dinga cusa abincin har sai dataji kaman zatayi amai sannan ta maida murfin ta rufe ta sake kwanciya.
Runtse idanunta tayi tana fatar bacci ya dauketa,sai taga wata fuska data sanyata saurin sake bude idanunta,dawo mata yayi tar a kwanyarta,bacin ran da take ciki yasa bata sake tunowa dashi ba sai yanzu,saita gyara kwanciyarta tana kallon bango,ta dinga tuno fuskarsa da yadda tafiyarsu ta kasance daga bakin masallaci har zuwa gida,hakanan taji nauyi da bacin ran zuciyarta ya ragu sosai,ta shagala da tunanin daya d'auketa zuwa bacci mai nauyi.
Qarfe biyu na rana gaba ya tsinci kansa hankalinsa ya tafi bakin masallaci gurin da ba wajen zuwansa bane idan ba shagin balarabe zashi ba ko wani babban uzurin ya kamashi na zuwa wajen,sai ya sake tsintar kansa da sake yin wanka bayan ya gama hutawa duk da kusan dabi'arsa ce a duk sanda ya dawo daga makaranta,amma wannan karon saiya laluba kayanshi har ya zaro zai saka ya maida ya sauya wasu,abinda bai taba yi ba,bai taba damuwa da suturar da zai saka,kawai dai yasan dukka kayan sawarshi a tsaftace suke kullum,hakanan basa rabo da guga,duk da cewa ba wasu masu shegen kyau da tsada bane,Allah dai yayi masa wata baiwa ta duk kayan daya saka jikinsa na dauka,hakan yasa matasan anguwar da dama ya tsone musu ido,wanda yawancinsu dukka sunfishi gata rufin asiri da komai da komai,tsaftarsa tasa baka gane kaashinsa.
"Ki kulamin da botikai na,karki sake bari su fasamim botiki,kai jamilu idan ka aje mata ka dawo ka kaimin shara" cewar ummanta wadda take rufe botikin abincin data gama zubawa almajirin ya qaraso wajen ya dora a kanshi suka fice tanawa umman sallama.
Har sunje soron gidan hakanan taja ta tsaya,saita juya da hanzari ta koma ciki
"A'ah,lafiyarki kuwa?" Umman tata da taga wucewarta ciki ta fada
"Lafiya umma ina zuwa" kai tsaye ta dauko dan kwandon kayan kwalliyarta dake saman akwatin kayanta,ta ciro ruwan madubi mai fadi dake soke a ciki ta kalli fuskarta
"Hoda na miki kyau wallahi shahida,don Allah ki dinga d'an shafawa mana" ta tuna maganar da qawarta ta gaya mata daxu a makarantar boko,saita samu kanta da ciro hodar ta bude ta shafa,data sake kallon fuskarta sai taga ta canza din kuwa,sosai hodar tayi mata kyau ta sake fidda kyau da qyallin fuskarta,murmushi ta saki ta aje mudubin ta juya ta fice da sauri.
Yana zaune daga shagon balarabe yana kallon duk wani motsinta dake bayyanar da hankali da nutsuwarta da kuma ainihin ita wace,duk surutu da hirar da balaraben yake masa baya gane abinda yake fada sam,shi kuma bai fahimta ba bare yaja bakinsa yayi shuru ya barshi.
Haka ta dinga raba abincin kamar yadda ta saba,saidai tanata dube duben kadan kadan da batasan meye dalili ba,harta kammala tsaf ta hada kwanukanta waje daya,haka kawai saitaji ranta ya baci lokacin data gama shirin komawa gida,duqawa tayi don daukar botikan taga an sako hannu an dauka,da hanzari ta dago don ganin waye?,ta tsammaci ma su ahmadi ne ma basu gargadin da aka musu jiya ba yau suka dawo,saidai ga mamakinta saurayin jiya ne,gaba yayi abinsa sai tabi bayansa sukaci gaba da tafiya ba tare da kowa yace da d'an uwansa wani sbu ba.
Basuyi wani nisa ba ya janye ta koma ita ce a gaba shi yana baya,bata kawo komai a ranta ba ta tsammaci bazai gane gidan nasu ba shi yasa yayi hakan,kamar tafiyar jiya har suka je inda ya dakata a jiya ya aje mata botikin,saidai yau din ta daga ido ta kalleshi,akaci sa'a shima ya kalleta a sannan,wani irin zallar kyau da kwarjini idanunta suka gani,sai taji wani abu tun daga qwaqwalwarta har tafin qafarta,mazewa tayi gami da d'auke kai tana jin izzarta ta diya mace na motsawa,a nashi bangaren ma wani abu mai qarfi yaji yana janshi game da ita tamkar maganadisu da mayen qarfe,sai bakinsa yayi nauyi,bai furta mata komai ba ya juya ya soma takawa don barin wajen,daga manyan idanunta tayi tana bin bayanshi da kallo har sai daya bacewa ganinta,batasan me yasa ba bakuma tasan sanda ta saki murmushi ba ta daukin botikin nata ta fada gida.
Tsahon kwana uku irin hakan na faruwa tsakaninsu,ba wata magana data taba shiga tsakaninsu,duk sanda tayi yunqurin yin wata magana saita kasa sabida kwarjinin da yake mata,tana son tace ya daina rakota saboda ganin yadda idon sa'idinawan unguwa ya soma dawowa kansu saidai ta kasa furta masa hakan,cikin ranta takejin nishadi a duk sanda suke wannan tafiyar ta kurame tun daga masallaci zuwa qofar gidansu,ko sunanshi bata sani ba,sai taga meye nata na tambayar sunansa ma,aishi ya kamata ya soma tambayarta sunanta,wani sashe na zuciyarta ya qalubalanceta da a'ah ba haka ake ba,ke yakewa alkhairi,ko godiya baki taba yi masa ba kan rakokin da yake,ta jinjina kai tana tabbatarwa da kanta rashin kyautawarta,ta kuma quduri aniyar a gobe zata masa godiya ta kuma tambayi sunanshi,kai ta girgiza kuma tana sake sakin murmushi,batasan dalilin daya sanya take yawan tunashi ba,batasan me yasa takejin wani baqon yanayi game dashi ba tun ranar data soma dora idanunta a kanshi,bata da amsa,tilas ta aje tunaninta a gefe sanda ta jiyo muryar babanta sun soma rabon halin nasu shi da ummanta,saita miqe a hankali ta isa bakin windon dakinta,ta yaye dan labulen net din dake maqale jikin window din tana kallon yadda suke dagawa juna murya kamar zasu yagi juna,batasan lokacin da wani hawayen baqinciki ya sauko mata ba,baqinciki da b'acin rai ya bata dukkan wani farinciki data tsinci kanta a ciki,wannan wacce irin rayuwa ce?,ina zata je ta daina ganin wannan baqincikin da bacin ran?,tabbas da akwai inda zata ta qauracewa wannan masifar da tuni ta jima da tafiya,tana son mamarta,hakanan tana son bananta,duk cikinsu babu wanda take goyon baya a cikinsu,batasan me yasa suka zabi wannan rayuwar ba bayan ga zuria suna tarawa,hakanan kowa yayi musu shaidar kyakkyawar mu'amala a waje amma me yasa gidan aurensu ya gurbace haka kamar sansanin yaqi?,haka ta zauna cikin dakin ita d'aya tana rusar kuka harta gaji da jin sautukansu ta dannan kanta qarqashin filo tana ci gaba da zubda ruwan hawaye.
Kamar kowanne lokaci yauma ta shirya tsaf cikin atamfa riga da zani,sai hijabi mai hannu da yasha guga,kasancewar ummanta mai tsafta ce,hakan ya sanya dukka yaranta tun daga kan shahida zuwa faruqu zaka samesu fes dasu,hakanan ma gidanta da duk abinda ya shafi gidan,sosai higabi mai madauri purpule colour yayi mata kyau sosai,yau shigar ta musamman ce ita kanta tana jin hakan a jikinta,yau mai d'aukar matan bai qaraso ba tilas tadan zauna jiran zuwansa,tun tana jin ba komai harta soma qaguwa,haka kawai taji ra zaqu taje wajen,ta leqo agogo yafi sau nawa amma shuru yaron bai iso ba,saita kasa zama taci gaba da duba agogo har ummanta ta fuskanci haka,iya saninta shahida na zuwa kai sadakar abincin nan ne don kawai tana tsananin jin nauyin uncle isma'il,kusan kullum fuska a hade take tafiya a haka kuma take dawowa
"Ya akayi ne shahida?,ko tsoron makara islamiyya kike?" Cikin rashin jin dadin ranta ta kada kanta
"Toko yau zaki zauna kawai idan yazo saiya kai shi?"
"A'ah umma....zan kai bari dai yaxo din" ta fada da hanzari,don bata jin zata iya jurewa rashin zuwanta wajen
"To ai shikenan" umman tata ta fada tana kwashe shanyar kayan sawarsu da shahidan ta gama wankewa daxu,ciki harda ba mahaifinta don sam bata da quya ko gandar aiki.
Yana isowa ko zama bata barshi yayi ba ta sakashi ya dauka suka wuce,sai taga kaman bata sauri,kamar tabar wani yana jiranta,haka dinga ji har suka isa wajen.
Daga nashi bangare shima har ya soma tunanin me ya hanata zuwa har yanzu?,yana daga zaune cikin shagon bala yana duba agogon wayarshi,sama sama yake amsawa bala hirarsa,ya daga kai don sake kallon muhallin da take zama din sai yaga isowarta,wata ajiyar zuciya ya sauke ya zuba mata ido daga inda yake,kaman ance mata ta waiwayo sai suka hada ido,ta danso ta dirirce amma saita maze,ta samu waje ta zauna yayin da kowa ya soma fitowa da kwanonshi yana amsa.
Duk motsin da take sai taji kama idanunsa ne a kanta,eh ba kama bane kallon nata yake,a yau ya hana kansa kallonta,duk da ta kamashi yana kallon