Author : HUGUMA Category : African Stories & Novels
za'a karbi sadakina abawa wani aurena ban sani ba?"
"Saboda mun isa dake" lallabawa take ta samu a kwanceta daga tarkon da aka sakata,sabida haka tayi qasa da murya
"Na sani daada,amma don Allah ina roqon alfarma ku maida masa kudinsa,nuradden ya jima yana tare dani,ya dade yana bibiyata,sannan kuma shima yana da dukkan nagartar da za'a iya baiwa mutum aure saboda ita"
"Duk nagartarsa bazai kama qafar wannan ba" mamaki duka ya cika shahidan,wai waye wannan da daada ta kafe kai da fata taketa faman yabo da kodashi haka?,taqi ji taqi gani saboda shi?,ko wani cikin 'yan uwanta nanan dake qwaqwar sonta dai daadan ta baiwa ita?
"Taya kika sani?,bafa sanin nuran kikayi ba?"
"Eh ban sanshi ba kuma bana son na sanshi,bazamu zama qananun mutane ba magana an riga da an gamata,ki sauko ki dauki abincinki kici" daga haka daadan ta miqe tayi ficewarta,alamar dake nuna cewa ba qaramin abu bane zai saukar da ita daga kan bakanta ba.
Ajiyar zuciya ta saki cikin tashin hankali idanunta na tara sababbin hawaye,ta zurafafa tunaninta tana neman dukkan hanyoyi da take ganin zati ba don sauke daada daga qudurinta,tunaninta yakai ya kawo,babu wata qofa guda daya,tunda kowa kusan da umarninta yake aiki,mafita daya ce ta dage da nacin roqonta kawai kafin nan da ranar lahadi ko Allah zaisa ta janye tun maganar batayi qarfi ta watsu a dangi ba.
Ba irin tunanin da bata kawo ranta ba kafin bacci yayi awon gaba da ita.
Koda ta idar da sallahr asuba wani baccin ne ya sake kwasheta,saboda rashin samun isashshen bacci da batayi na daren jiya.
Cikin baccin taji kamar muryar huda na tashinta,ta bude idanunta da qyar wadanda sukayi nauyi ta zubesu kan huda
"Anty shahida,kizo inji kawu ummaru" tuni ta nemi sauran baccin idanunta ta rasa shi,saita zauna dangwargwar saman gadon tana duban shahida
"Yaushe yazo"
"Bai jima da zuwa ba,muna cikin cin abincin safe"
"Kice masa ganinan" ta fada cikin fargaba,miqewa tayi ta dauki hijabinta dake saman jakarta ta zura,ta tsaya gaban mudubi ta kalli fuskarta gabanta na faduwa,tasan halin kawu ummarun sarai,yafi kowa zafi cikin kawun nan nata,Tana dage labulen tana addu'ar Allah yasa koma da meye yazo ya zamana mai sauqi ne.
Cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa,shuru yadan biyo baya kafin daga bisani ya ciro kudade daga aljihunsa ya zube kusa da ita
"Nasan tuni daada tayi miki bayanin cewa mun karbi kudin aure da sadakinki,to gasu,inaso nayi magana da mahaifiyarki kan meye ya dace ayi da kudin" da sauri ta dago kai tana duban kawun idanunta ya cika taf da qwalla sannan ta sauke qasa,ya karanci me takeson cewa,don tuni daada ta gaya masa
"Rahama,karki wani ce zaki damu,yaron ya cancanta,banda haka babu abinda zai saka mu bashi ke,muma muna sonki fa" cikin muryar kuka tace
"Kawu,wallahi bansanshi ba,bani bace na turoshi,akwai wanda muka riga mukayi alqawarin aure dashi,harma yana shirin zuwa gaidaku" murmushi kawun yayi
"Rahama,indai cancanta take sa a baiwa mutum aure wannan yaron ya cancanta,matar mutum kabarinsa,Allah baiyi shi wancan din shine mijinki ba,saboda haka kiyi addu'a kawai,Allah yasa hakan shine alkhairi a gareki" kai ta sadda kawai qwalla na silalo mata,tana jin kawun harya gama maganganunshi yayi sallama dasu yayi gaba,miqewa tayi kawai ta fita daga falon zuwa tsakar gida ta wuce bandaki,ta tara ruwa tayi wanka sannan ta sake zuwa ta wuce daada zuwa daki.
Cikin minti talatin ta gama shirinta gami da hada kayanta tsaf,daidai lokacin daada ta leqo dakin tana mata magana ta fito ta karya,saita ganta saqale da jaka tana shirin fitowa,binta tayi da kallo
"Ke kuma meye hakan?"
"Gidan zan wuce,tunda nazo na karbi saqon naki" baki ta tabe tana dubanta
"Allah ya raka taki gona,dadin abundai bake kadaice jikata ba,kuma su bayau zasu tafi ba,saikin dawo" duban daadan tayi,zuciyarta na mata zafi matuqa idan ta tuna abinda suka mata,yanzu kamar ita da hankalinta da wayonta da komai amma ace an baiwa wani ita?,waninma da batasan waye ba?,tsabar qarfa qarfa kota bakinta ba'a jiba aka amsa harda sadakinsa?,ranar daurin aure kawai suke jira kenan?,saita juya da kayanta ta koma cikin daki ta zube gefan katifa,tana jin wayarta na rurin shigowar kiran nuradden amma bata da qarfin gwiwar dauka.
Dole ta haqura da tafiyar sabida wani zazzafan zazzabi daya saukar mata wunin guda,ba ita ta samu sassauci ba sai washegari da safe,kafin sallar azahar ta sake shirin tafiya,wannan karo daadar bata hanasu ba,suka shirya tsaf suka wuce,saidai tafiyar bata musu dadi ba kamar yadda tayi musu a zuwansu,saboda gaba daya hankalin shahida bai kansu,sosai ta shiga tunani mai zurfi ita daya,har suka qaraci surutansu suka haqura.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Kwana biyu da dawowarta tana gaban system dinta tana tura saqon daukar uzurin ba zata samu damar komawa office bakin aikinta ba anty zubaida ta shigo dakin,saita samu gefan shahidan ta zauna sanda ta gama tura saqon ta soma kashe system din,cikin qaramin lokaci gaba daya shahidan ta sauya ta wani sukurkuce kamar wadda akace an daura auren nata,ta sauya gaba daya ta auri zaman daki,duk wata hira da walwala data dawo da.ita cikin gidan yanzu ta janyeta,kamar wadda ke shirin komawa 'yar gidan jiya,anty zubaida batace da ita komai ba saidata gama ta ture computer din gefe sannan ta kira sunan shahidan,daga kai tayi tana dubanta
"Yanzu shahida daga maganar karbar kudin aurenki saiki ki tsangwami kanki haka?,kina neman maida kanki 'yar gidan jiya?" Kamar mai jira sai kuwa ta soma hadiyar zuciya,idanunta suka soma yaji tare da tara qwalla,ta bude bakinta tana jin wani abu ya tokare mata wuya cikin muryar kuka tace
"Haba anty,ko waye aka yi masa haka anty ba'a kyauta masa ba,ta yaya za'a badani kamar an gaji dani,yanzu an siya min mutunci kenan?,kina gani fa shi wanda akace an bawa din bansan ko waye ba,uwa uba yau kwanaki nawa shi dinma bai nemeni ba,qafa da qafa kiran waya ko text,me kike tunanin sun jawomin kenan anty?" Ta qarashe maganar da sigar tambaya idanunta kan anty wanda gab suke da ziraro da qwallar dake cikinsu,kai anty zubaida ke kadawa,ita kanta abun bai mata ba amma uncle hisham ya dakatar da ita kan babu ruwanta,duk wata hanya da zata bi tasha cikin uncle din ya gaya mata na ko waye donta gayawa shahidan ta samu dan relief ya tosheta
"Haka zaki haquri shahida,qaddara ta riga fata,amma sai nake ganin idan da laifinsu kema da naki laifin,kinyi wasa da damarki qwarai,shekara nawa nuradden na bibiyarshi ki bashi dama kikaqi,idan da ace kin bashi dama da tuni yanzu wani zancan ake ba wannan ba,nidai bani da wani abunyi bani kuma data cewa saidai ince kiyi haquri kiyita addu'a kawai,nima kuna zan tayaki" kai kawai ta kada,ta bude baki zata ce wani abu wayarta ta sake kadawa karo na barkatai,tare idanunsu yakai kan wayar,nuradden ne,sai anty zubaida ta kalli shahidan
"Babu hujja ko alfanun boye masa komai,kawai ya kamata ace ya sani ni a ganina" tana kaiwa nan ta miqe don ficewa ta bawa shahidan damar amsa wayar.
******* ****** *********
A hankali ya miqe daga gaban qaramin akwatin mai lambobin sirri yana sauke nannuyar ajiyar zuciya,duk sanda ya budeshi koda wani abu zai ciro daga ciki saiya tayar masa da wawakeken mikin dake danqare a zuciyarsa,cikin nutsuwa wadda ta cakudu da kasala ya isa gaban akwatinshi ya jefa abinda ya dauko daga ciki ya rufe zip din akwatin sannan ya saukeshi daga saman gadon ya soma janshi har zuwa falonshi.
Saman dining ya isa ya zauna a nutse ya soma duba abinda aka dafa din,rabin hankalinsa nakan wayarshi da haka ya zuba abincin ya soma ci,knocikin din da akayi shi yaja hankalinsa,saiya dan daga kanshi yana duban qofar,kafin yace komai aka turo aka shigo,nafisa ce,sanye cikin doguwar riga ta atamfa da madaidaicin mayafi,idanunta bisa kanshi yayin daya dauke nashi idanun ya maida kan abincinsa,hakan yasa tayi hanzarin tunawa da batayi sallama ba,saita dan koma da baya tayi sallamar sannan taci gaba da takowa cikin falon a hankali tana nazarin falon,falon ya jima yana burgeta,duk da wannan shine ganinta dashi na uku,saboda haidar din bai lamunci ta dinga zuwa masa gida ba bayan shi kadaine cikin gidan.
Bata tsaya ba har sai data isa dining din,fuskarwa a washe take kallonshi,ta dora jakarta saman teburin tana kallon abincin da yake ci,saita zari spoon ta saka cikin farantin nashi tana cewa
"Goodmorning boss" idanunshi ya daga yana janyewa daga cin abincin yana cewa
"Morning...me kika fito yi yanzu?" Zama tayi saman kujerar dake daura da ita,ta langabe wuya tana kallonshi bayan ta aje cokalin hannunta
"Rakiya mana dear....uhmm....ji nake kaman na bika wlh,kaika janyo mana kaga da tuni tare zamuyi tafiyarmu babu me tuhumarmu" saiya yagi tissue yana goge bakinsa,ya cilla dan qaramin dust bin dake gefanshi yana miqewa daga saman kujerar
"Amma dai kinsan akwai wadanda zamu fita tare,kuma duka maza ne,bai kuma kamata ki shiga cikinsu ba ko?" Itama tashi tayi tana daukar jakarta,cikin hanzari harta cimmasa tasha gabanshi
"Amma dear,tafiyar wata biyu fa banan kusa bane,ni a wajena ba laifi bane don nayi maka rakiya"
*ga mai buqatar sabon littafina da zan fara bayan alqawarin Allah,sai yaje youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,da zarar sunan ya fito akwai rubutun SUBSCRIBE da jan rubutu,ki danna shi sau daya zai koma black,saikiyi screenshot ki turo zuwa number dake qasa,za'a saki a group din in sha Allah*
07038670166*Ziyarci tasharmu ta youtube don samun qawatattun litattafan hausa,masu qunshe da zallar soyayya darasin rayuwa da kuma nishadi*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
https://youtu.be/H7M7h6l6wNM
*Alqawarin Allah*
2️⃣8️⃣
Bata tsaya ba har sai data isa dining din,fuskarwa a washe take kallonshi,ta dora jakarta saman teburin tana kallon abincin da yake ci,saita zari spoon ta saka cikin farantin nashi tana cewa
"Goodmorning boss" idanunshi ya daga yana janyewa daga cin abincin yana cewa
"Morning...me kika fito yi yanzu?" Zama tayi saman kujerar dake daura da ita,ta langabe wuya tana kallonshi bayan ta aje cokalin hannunta
"Rakiya mana dear....uhmm....ji nake kaman na bika wlh,kaika janyo mana kaga da tuni tare zamuyi tafiyarmu babu me tuhumarmu" saiya yagi tissue yana goge bakinsa,ya cilla dan qaramin dust bin dake gefanshi yana miqewa daga saman kujerar
"Amma dai kinsan akwai wadanda zamu fita tare,kuma duka maza ne,bai kuma kamata ki shiga cikinsu ba ko?" Itama tashi tayi tana daukar jakarta,cikin hanzari harta cimmasa tasha gabanshi
"Amma dear,tafiyar wata biyu fa banan kusa bane,ni a wajena ba laifi bane don nayi maka rakiya".
Bai amsata ba saida ya ciro wayarshi ya amsa kiran dake shigowa sannan ya maidata ya daga kai ya zuba mata idanunsa da kullum kwanan duniya ke sanya nafisar sake dilmiya cikin so da qaunarshi,kallonsa kawai yakansa taji wani sanyi da sassauci cikin ruhinta,taji tamkar an mata rahama
"Waye ya kawoki?"wuya ta noqe tana jefa masa wani kallo da take fata ko yaya yayi tasiri a zuciyarsa
"da kaina na taho"hannu ya miqa mata,ta kalleshi tana son qarin bayani
"Bani muqullin motar"ba musu ta zuge jakar tata ta dauko muqullin ta miqa masa,saiya sakashi a aljihunsa sannan yace mata muje.
Tana gaba yana bayanta,a hankali yakai idanunshi kanta,saiya lumshe idanu yana tuna wani lokaci can baya,lokacin da yake mata rakiya zuwa gida,lokacin da take sadakar shinkafa da wake,ya tuna randa ta zura da gudu tabar mishi botikinta saboda ya furta mata kalaman soyayya,murmushi ya sube masa cikin qiftawa da bismillah kuma murmushin ya bace bat,bacin rai ya maye gurbinsa,ya hadiyi wani abu mai tauri yana girgiza kai,hotunanta ita da saurayin suna yawo a idanunshi,fuskar saurayin daya ajeta a mota har yau taqi barin idanunshi,ya dunqule hannunsa daya yana jin wani abu mai dumi na zagaya jikinsa,har kwanan gobe takaicin dukan da baiwa saurayin yake ba,amma yaci alwashi...yaci alwashin dashi kadai ya barwa kansa sani......
Inda yaje aje motocinsa ya nufa,ta bishi a baya,ya bude daya daga cikin motocin ya mata alama da hannu kan ta shiga,wani dadi ya kamata,yau din taga kamar wani dama dama yake da ita,ta rabeshi ta shiga ta zauna,maimakon shima ya shiga sai taga ya maida murfin motar ya rufe,ya duqa bakin window din idanunshi cikin nata,wanda hakan ya sake narkar da ita ya kashe mata jiki,qamshinsa ya cika mata hanci,kamanninsa suka fito sosai,cikin daddan muryarshi yace
"ga driver nan zai kaiki gida,karki sake irin wannan fitar da sassafe haka,zamuyi waya kafin na tashi,motarki kuma zansa a kawo miki ita,sai Allah yayimin dawowa?" Kai kawai ta gyada,ta kasa cewa komai saboda gaba daya jikinta a mace yake dakyau da kwarjinsa,baya yaja ya miqawa drivern muqullin,yana tsaye har suka fice daga gidan,ya saki ajiyar zuciya yana duba agogon hannunsa,da yana da yadda zaiyi ya ragewa nafisa sonshi ko yadda ta damu dashi da yayi,sam baiso ta zura kanta da yawa kamar yadda yayi,shi a ganinsa wannan shine babban kuskure ko gangancin da mutum zaiyi a soyayya.
***** ****** ********
A hankali take takowa zuwa qofar gidan nasu,sanye da dogon hijabi har qasa mai hannu,kallo daya zaka yiwa fuskarta kaga yadda ta fada,ta dashe hakanan tayi fayau,duk yadda anty zubaida taso ga kwantar mata da hankali kan lamarin hakanan taji hankalinta ya kasa kwanciya,tana ji ba auren dole za'a mata ba,a'ah nata ya xarce wannan ya koma auren qarfa qarfa.
Tunda ya hangota ya fito ya tsaya yana jiran qarasowarta,ji yake kamar ya isketa ya tarbeta,tana isowa suka hada idanu sai taji zuciyarta ta karye gaba daya,tausayin nuradden din ya kamata fiye da ita kanta,don dama ita tuni ta sallamawa soyayya bare tayi mata kamun da zata jigata aduk sanda ta tashi gwada izzarta,saidai ko babu komai sabo mugun abu ne hakanan turken wawa ne,da hanzari ya zaga ya bude mata daya seat din ya kalleta
"Shiga ki zauna,kar tsaiwar tayi miki yawa" karon farko ba musu cikin kasala ta zagaya ta shiga din,saidai duka qafafunta na waje,shima saiya zagaya ya shiga mazaunin direba yabar qofar a bude.
Idanu ya zuba nata gaba daya yana hasaso ta ina zai soma daukar rashinta,sam yana jin bazai iya ba,a hankali ta bude baki zatayi magana ya daga mata hannu ya tsaidata
"Karkice komai shahida,maganar gaskiya bazan iya rabuwa dake ba,bazan iya rabuwa dake ba shahida matuqar ba aure aka daura miki ba,zanci gaba kuma da yaqi tuquru don ganin na sameki,koda hakan na nufin zanje wajen daada da kaina na roqeta tabarmu tare ne" da hanzari ta bude baki
"Ina nan ina gwada sa'ata,kuma ina saka ran samun nasara,idan hakan ya cimma tura zan sadaka da ita daadan taci daga bakinka" ajiyar zuciya ya sauke yana kallon shahidan,wani qaunarta yake sakeji,baya fata ko sau daya ya sakejin kalmar rabuwa a tsakaninsu.
Tsahon mintina ashirin suna tare suna baiwa juna baki kafin yayi mata sallama yace zai wuce amma ta dakaceshi a waya,hakanan suka rabu kowa jiki babu qwari musamman nuradden din.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Cikin satittikan da suka biyo baya suka fara zama watanni shahida tayi dukkan iya yinta don ganin daada ta janye qudirinta,an maidawa koma waye kudinsa da suka amsa amma abun yaci tura,bata taba ganin daadar ta dage kan abun haka ba irin wannan,sannu a hankali taji ta soma tsanar kona waye wannan,da wanne irin abu haka yazo da tashin farko za'a dauketa sukutum da guda a bashi ita?,sannan ta kowanne fanni kowa ya cije yace sai anyi?,hatta da anty zubaida ma yanzu ta soma bin layi,balle ummanta data ga kamar ma tafi kowa murna da farincikinda abun,don ko rannan data je gida bacin rai da baqinciki ya hanata wuni,wai umman har tarin biki take mata,hakanan su mubina har sun fidda anko,ita bata ma sani ba,sai 'yan uwanta 'yammatan dake sa'anninta daketa kiranta kan zasu sayi anko akwai a gida wajen umma?,ko sau daya ta kasa amsa musu saidai taja tsaki ta kashe wayar.
Batun ya tsaya mata qwarai a rai,harta lura ta soma ramewa,bacin ranta da har zuwa lokacin wanda ake budurin a kansa bai gabatar da kanshi a gareta ba barema tasan waye,hakan ke nuna ma bata da wani daraja ko muhimmanci a wajensa kenan?.
A haka aka shiga azumin ramadana,Allah ya taimaketa batayi sake da kwanakin ba,ta tsawaita ta kuma nace da addu'ar neman mafita wajen ubangiji babu dare ba rana,duk ta zama wata sukuku da ita,sauqinta daya wurin aiki sun bata hutu data tura cewa bata da lafiya,ba zata koma ba har sai bayan sallah,ko daya taqi samun nutsuwa cikin ranta,bacin rai fargaba da qunci da batasan na meye ba gaba daya sun cikata.
Da sallah kuwa tana ganin su mubina dasu faruqu suka shirya tafiya katsina tace saisun dawo bata zuwa,ita lallai sai daada ta fuskanci fushi take da ita,daadan dako a jikinta wai an mintsini kakkausa,hakan na sake qona ran shahida,an shiga wata na biyu har ya cimma qarewa a yadda ma taji suna fada biki saura sati biyar amma bata yaba sashi a qwayar idanunta ba?,itakam taga yadda za'ayi wannan abu haka take yawaita fada cikin ranta,saitakejin ma abun kamar wasa,kamar bamai yiwuwa bane,hakan ya sanya ta sake baiwa nuradden qwarin gwiwa da kyautatan zaton lamarin bazai dore ba.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
*_SO DANGIN MUTUWA_*
Satu guda cif cif da sallah ranar litinin daada ta buqaci shahidan tazo ranar juma'a mai zuwa,qememe tace bata zuwa ba inda zata,mubina ce 'yar isar da saqon data ji abinda tace bata ce komai ba harta gama wuninta tayi tafiyarta gida.
Qarfe tara da rabi na dare suna gama waya da nuradden ta maida wayar chargy ta dawo tana cire hijabin jikinta don taji dadin kwanciya tana son saurarar littafin JARRABI na huguma (littafin da nan gaba kadan zaizo muku a SAUTIN HIKIMA TV dake youtube,idan baki subscribe ba ki hanzarta zuwa kiyi don kar a fara babu ke) ta gyara daurin dankwalinta