Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 53

27K to 30K   out of 156.9K words

wadatar hasje sosai kasancewar babu wutar nepa,bata nemi kowa ba don bacin rai ke sake taso mata na yadda tabar gidan nasu dazu,uwa uba kuma wani sabon baccin take ji,gqba daya jikibta jibsa take kaman an tsoma lagwani a ruwa.

Kan katifarra ta fada rub da ciki tana lumshe idanu tanajin yadda gabobinta sukayi rauni,idanun nata na arufe taji wayarta na ruri,sam baki daya ta mance da ita,ta miqe cikin kasala ta daukota daga saman akwatin kayanta,anwar ne yake kira,take ta dannan ta kara a kunneta
"Ina kika shiga haka shahida?,nazo gida ana nemanki sama da qasa ba'a ganki ba?,na kira wayarki ya kusa sau hamsin ba'a daga ba" sai data lumshe ido sannan tace
"Babu inda naje fa,ina gidansu fiddausi,wayar kuma na manta ta ne cikin akwatin kayana,koka kira babu lallai aji sautinta" ajiyar zuciya ya sauke yana jin tashun hankalin da yaji dazu na sauka
"Karki sake irin wannan fitar,hankalin umma ya tashi sosai"
"In sha Allahu" ta fada amma cikin zuciyarta tana fadin koma meye sune suka ja
"Ya naji muryarki haka?,lafiya kike?" Saidata gyara kwanciyarta saboda baccin dake fisgarta tace
"Lafiya qalau....kawai...bacci ne yakeson saceni"
"Bacci yau kuma?" Ya tambaya cikin mamaki,sabida yasan a qalla suna kaiwa sha daya suna waya,a hakama shike datsewa yace tayi bacci,sam bata iya baccin wuri ba
"Wallahi" ta fada a gajarce,saiya raya a ransa jiki da jinine kawai don haka yace
"Alright,asuba ta gari to,tunda yau anmin ruwa gani da jin muryarki" murmushi ta saki a kasalance tace masa na gode ta datse wayar ta cillar gefe tana maida kanta saman filo hadi da sake lumshe idanunta.

Mubina ce ta dago labulen dakin ta shigo
"Yaya kizo inji umma...ashe kin dawo tun dazu ake nemanki" juyar da kanta tayi daya side din cikin muryar jin bacci tace
"Saida safe...kice mata nayi bacci" yau ba 'yan maganar bane akan mubinan don haka ta fita ta shaidawa umman tasu saqon shahida,sai gata ra taso da kanta
"Ke shahida....ina kika je tun dazu?"
"Gidansu fiddausi" ta bata amsa ba tare data juyo fuskarta inda umman tata ke tsaye ba
"Tashi ki dauko abincinki a kitchen kici"
"Ba qoshi" ta sake fada cikin muryar bacci,sam umman tata bata lura da sauyin dake tattare da ita ba,ga tunaninta fushi tayi kaman yadda ra saba a duk sanda wani abu ya gilma tsakaninta da mahaifinta,saboda haka ta tabe baki
"Indai ba zaki sawa ranki haquru da kauda da kai ba zakita ganin bacin rai,kije ki hadu da hawan jini a banza,babanku baida haquri kuma baida adalci,ni kuwa bazan tsaya ya tauyen haqqina ba atoh" tana gama fada ta juya ta fice,sama sama take jin abinda umman ke cewa,ga mamakin kanta da kanta,maimakon ta sake jin haushi yadda ta saba sai taji sam maganganun basu d'a d'ata da qasa ba,baccinta ya fiye mata komai,idanu ta sake rintsewa ba jimawa kuwa wani nannuyan bacci ya kwasheta.

Kwana biyu tsakani suka ci gaba daga inda suka tsaya,a lokacin tana daki zaune tana turawa anwar tex,tun tana daure zuciyarta harta kasa,ta toshe kunneta duk a banza,takai ta kawo cikin dakin ita kadai saita fita,haquri ta soma basu tana kuka kowa idanunshi ya rufe ba wanda ya saurareta bare yayi shuru ya ragawa dan uwanshi,dare yaui ba damar ta fice daga gidan ta huta,sai kawai maganin da fiddausi ta bata ya fado mata ta juya da sauri ta koma dakin ta rufo qofar don sautin tartsatsin fadan ya ragu,ta duba saman madubinta yana aje ta dauka ta bide ta shanye gaba daya,ta koma gefan gadon ta zauna tana kuja gamida addu'ar Allah yasa yayi mata aiki,Allah yasa baccin yazo da wuri ya dauketa kota huta dajin meke faruwa cikin gidan.

Cikin mintina qalilan bacci ya soma zuwa mata,kafin kace ta sheme a wajen,ba ita ta farka ba sao washegari da safe bayan gari yayi tarwai rana ta take,da hanzari ta miqe tana tariyo abinda ya farun,sosai taji dadi har ranta da Allah baisa taji qarshen masifar ba,don haka batasan ya aka qarke ba,ta bude sakatar dakinta ta fita tsakar gidan nasu,a share yaje fes saidai gidan nasu yayi tsit alamun ba kowa ko duka yaran basa nan,tasan da hakan don lokacin tafiya makaranta yayi,saita tari ruwa ta shiga bandaki,wanka tayi don tafijin qwarin jikinta sannan ta hado da alwala ta fito ta shiga dakinta ta sauya kaya ta tada sallar asuba da bata samu tayi ba,bayan ta kammala ta wuce dakin ummanta,ta sameta a zaune a falonta tana tsintar shinkafa,ta dago suka hafa idanu,kallo daya zaka mata kasan ranta a masifar bace yake,wanda tasan hakan bai rasa nasaba da kace nacen da sukayi jiya da babanta,gaidata tayi ta amsa sama sama
"Wato don wulaqanci da iskanci da asuba kina ji ana bugun qofarki ki tashi kiyi sallar asuba kikaqi ko?" Ita sam batasan anyi hakan ba,batasanma yaushe aka buga qofar tata ba,amma kawai sai tace
"Kiyi haquri umma,bacci ne yaci qarfina"
"Oho ke kika sani,naga alama kin fara goyawa mahaifinki baya,to wallahi kikace haka zakiyi wahala zakisha" ko kadan ranta bai baci ba sai tace
"Kiyi haquri" banza tayi da ita,sai bayan mintina wajen goma sha biyar sannan tace da ita
"Saikije ki dauki abun karyawarki a kitcheni,idan kin gama ki kunnan wuta na dora shinkafar nan"
"Toh" ta fada tana miqewa zuwa madafa.

Tana cin abincin tana tunanin abinda ya farun jiya,gaskiya baqaramin rage mata radadi maganin yayi ba,ko banza batasan qarshen abun ba,hakanan bata ji wani bacin rai ba,saita yanke kawai yau ta sake zuwa gidansu fiddausi ta gaya mata inda ake saida abun ta siya,duk sanda suka soma balahirarsu tasha ta samu bacci ta qyalesu.

To tun daga lokacin shahida ta shiga ruwa tsundum,batasan illa da giraman abinda takeyi ba,batasan yadda take rushe rayuwarta ba,kawai ita ta bada amanna ne tana shan maganin matsalarta,batasan tana sake qarawa rayuwarta matsala bane,tana tunanin maganin bacci kawai takesha,batasan ta fada shaye shaye bane tsundum,wanda ba wanda ya kula da sauyawarta banda anwar,lokaci zuwa lokaci idan yazo fira wajenta da zarar sun fara zata soma gyangyadi,haka zai mata sallama ya tafi,ya nazarceta sosai baiga wani abu daya sauya dangane da ita dinba bayaga yawan jin baccin,hakan ya sanya yayi tunanin ko shawara ce da ita?,baiyi qasa a gwiwa ba ya amso mata magungunan gargajiya harda na sanyi,ta amsa dai kawai ta jibge taci gaba da sha'aninta.

Zuwa sannan sam abinda ke faruwa tsakanin mamanta da bbanta ya daina damunta,wani lokaci takan iya shigowa gidan ma ta taddasu sunayi tayi wucewarta daki ta kwanta abinta tahau baccinta,dukkan wadan nan sauye sauyen basu ganshi ba,ga ummanta kawai tayi mata shaidar ta koyi nunqufurci tana goyon bayan babanta,yayin da abban nata yake ganin hankali tayi ta daina damuwa da al'amarin dake faruwa.

Ta bangaren fiddausi kuwa da akayi amfani da ita don cusa shahida cikin wannan harkar nasara ce a wajenta,don duk yadda aka tsara abun ya tafi dai dai,hakan yayi sanadiyyar samun kudade mai yawa daga wajen nafisa,plan dinsu na gaba shine cusa samari masu kudi 'yan duniya rayuwar shahidan,saidai duk yadda sukaso ga ganin hakan ya yiwu abun bai kasance ba,saboda sam shahidan tun asali a jininta yake,bata da kule kule,haka suka qaraci shirya plan din nasu suka gaji,hakan ya sanya suka sauya dabara,suka sake sabon shiri sabon taku da sabon tsari,wanda suke fatan shine mataki na qarshe da zai tarwatsa mu'amalar dake tsakanin anwar da shahida komai qarfinta.

*_SHARRI KAYAN KWALBA_*



Kusan a yanzu babu wata qawa kuma aminiya da shahida ke da ita data wuce fiddausi,kusan koda wanne lokaci suna tare,hudubar farko data soma yiwa shahida shine anwar ba son shahidan yake ba,yasha fada cewa mai zaiyi da yarinyar da iyayenta suka kasance tamkar karnuka saboda fada,sosai xancan ya daki shahida,saidai iya saninta anwar baisan badaqalar dake faruwa a gidansu ba,don tuni ta yanke yin zance dashi a gidansu bama gidansu kawai ba unguwar baki d'aya,yanzu kacokam gidan anty amina take tafiya su hadu a can,saidai kuma akace yau da gobe tafi qarfin wasa,sai maganar ta dinga tsayewa shahidan aranta,duk da cewa ko daya bata yarda ba bata gasgata ba,hakanan ba abinda ya ragu game da son anwar daga zuciyarta,duk sanda taso yin wani dogon nazari kan maganar fiddausi na kadar da hankalinta ta bata wani abun mayen sai zancan yasha ruwa.

Ta gefan anwar gaba daya hankalinsa ya ta'allaqa ne kan nemawa shahida gurbin karatu cikin daya daga cikin makarantun gaba da secondry dake jahar kano tunda aka yi musu qarin albashi,bai gaya mata ba saboda yana sonne yayi mata ba zata,yaci wahala ya kashe kudi kafin komai ya kammala.

Ana ya gobe zai shaida mata yana gurinta,ranar sun jima tare suna hira,sunyi hirar da suka jima basuyi irinta ba,kowanne yan jaddadawa d'an uwanshi yadda yake jinsa cikin jikinsa da zuciyarsa,sun tsokani juna sunyi raha wasa da dariya sosai,har anwar ta saka ranakun cikin daya daga cikin kundin ranakun farincikinsa da bazai taba mantawa dasu ba,ta bashi hotunan data dauka musamman sabodashi wanda ba qaramin kyau tayi cikin hotunan ba,kyanta ya fita muraran,ya qurawa hotunan idanu yaga kada kai
"Wannan hotunan bazan iya maidasu enlargment ba" dubansa tayi tana narke ido tana dubanshi
"Saboda banyi kyau ba ko?" Dariya ya saki yana cewa
"Dama akwai wani lokaci da zaki qiyin kyau a idanuna koda wankan kashi kikayi?" Dariya sosai ya bata har shima ya tayata darawa
"Dama ana wankan kashi ya anwar?" Girarsa ya dage
"Eh waikoda ace anayi din...kyan da kikayi ne shahida yayi yawa,ina kishin mai aikin budawarma ya ganki" baki ta bude tana dubanshi
"Ya anwar"
"Shahida....kaman har yau kina kokwanton yadda nake sonki da kishinki ko?" Kai ta girgiza tana dariya
"Xaki fahimta,sai ranar da aka kawoki dakina a matsayin matata" kunya ta sata sadda kai tana qiyasta ranar a ranta,gata ita dashi a matsayin miji da mata.

Daya tashi tafiya saita miqo masa dari biyar bayan wata baqar leda,wadda daya bude links ne da agogo guda biyu masu matuqar kyau irin wanda tasan yana masifar so,kallonta yayi itama shi take kallo
"Kada kacemin komai,na fuskanci yau miskini kake baka dako sisi(ta furta cikin sigar zolaya)"murmushi ya saki,gaskiya ta fada,don duka albashinsa ma na wajen wata uku ya qare ne wajen sama mata admission,dan abinda yaje riqewa bamai yawa bane,kudi ya dinga badawa don ta samu gurbin karatun,don yasan cikar burinta kenan shida ita,hakan bai dameshi ba ko kadan,yana jin zaiwa shahidan fiye da hakanma indai ita dince
" har saika fada?"ta katse masa tunaninsa
"Ina iya karantar zuciyarka ba tare daka furta abinda ke cikinta ba" ta fada cikin sanyi da taushi,sun riga da sun zama daya,sai ya saka hannu ya amsa yana murmushi
"Na gode matata" kalmar data yi mata dadi sosai,cikin farinciki walwala da qaunar juna suka rabu,yana tafe yana tariyar dukka kalamanta,saiyakejin kyautar data masa tayau din daban take,hakan ya sanya ya kasa fasa kudin ya hau mota,ya taka har zuwa gida da qafa yana juya ledar data bashi gift din a ciki,gift din data bashine da sunan tayashi murnar xagayowar ranar haihuwarsa,wanda sam shi ya mance ma da yaune ranar haihuwarsa.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe biyar na yammaci da 'yan mintuna ta sauke wayar daga kunneta tana sakin ajiyar zuciya,itakam har cikin zuciyarta sam batajin zuwa ko ina,haka kawai taji batason fita.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/video


*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata saiya tuntubi wadan nan lambobin*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*Alqawarin Allah*
1️⃣3️⃣


Fiddausi ce ta kirata tanason ta rakata wajen da take siyo musu kayan zaqi kamar yadda ta sawa syrup din da take baiwa shahidan suna,duk sanda shahidan ta buqata tana amsa ne kawai daga wajen fiddausin,wanda nafisa ce ta baiwa mima kudin da za'a siya a jibgewa shahidan,ita kuma mima ta baiwa fiddausi kudin ta saya ta aje din take bata,don ita bata harkar shaye shaye,barta da biye biyenta kawai,shahidan taso ta tirje don yau din anwar ya gaya mata zaizo akwai wata muhimmiyar magana da zasuyi,amma sai fiddausin taji haushi ta katse wayar sanda tace ba zata samu zuwa ba,ita dinma a karan kanta sai taga bai kamata taqi rakata ba,tunda abun nan tare suke amfana dashi,bugu da qari duk sanda takeso kyauta take bata shi ba tare dako sisinta ba.

Tilas ta shiga bandaki ta sake gyara jikinta kasancewar tana al'ada ne,kuma idan tanayi din tana bleeding ba laifi,hakan ya sanya duk sanda zata fita take saka always biyu ko kuma pant biyu,yau always din tata ta qare saura daya saboda haka ta saka pant biyu duk da tana tunanin Allah yasa ya riqeta.

Tsaf ta shirya ta shuga wajen umma
"Umma....zan raka fiddausi gaisuwa,baban wata 'yar ajinsu ya rasu"
"Ina ita fiddausin?"
"Ta gidansu zan biya ai umma yafi kan hanya"
"Saikun dawo" ta fada tana miqa mata dari biyu kudin mota,ta amsa ta miqe ta fice daga gidan.

A qofar gida suka hadu da fiddausi
"Amma karmu jima don Allah fiddausi saboda anwar kar yazo bai sameni ba,kinsan baison yawan fita" baki ta tabe cikin ranta tace
"Yau za'ayi mai gaba daya ma ai" amma a fili sai tace
"Sannu matar kulle,yaushe aka daura auren naku ban sani ba?" Harararta shahida tayi
"Kinga banason wulaqanci,kome zakiyi ki tsaya iyani,koda ba'a daura aurenmu ba ya isane dani"
"Allah ya baki haquri...shi yasa har na kira daddy A yazo ya kaimu saboda mufi sauri sai kuma nace ya barshi,don nasan halinki yanzu zakice ba zaki shiga motarsa ba" dan hade rai shahida tayi
"Kinfi kowa sani ai,nifa banason kina hada alaqarmu data wadan nan tarkacen samarin naki,tunda dai mu ba 'yan bariki bane"
"Iyee,wato samarina ne ma tarkacen,ba komai zan rama"
"Saidai ki rame" da haka suka qarasa wajen.

Tunda suka shiga wajen gabanta ke faduwa,gaba daya jinta take a tsarge,har qasan zuciyarta takejin kaman tana aikata wani abu daba dai dai ba,wajene da yake kama da gida daki daki,kaman gidan masu zaman kansu,daya daga cikin dakunan suka nufa ba tare da sun kula kowa ba,saida fiddausi ta tura qofan suka shiga taga ashe falone babba,akwai maza wajen biyar ciki,ga kayan da sukazo nema zube a gabansu da alama ciniki ake,guri daya shahida ta samu ta zauna duk ta takura,sai taga fiddausin ma ta samu waje ta zauna bayan sun gama gaisawa da mutanen cikin sanayyar juna.

Ganin lokaci nata ja fiddausin bata sake cewa komai ba hakanan basuyi abinda ke gabansu ba ya sanya shahidan tabo fiddausin ta mata magana
"Sorry....sallamemu uban gayya...qawata na sauri zata koma gida ne"
"Kuxo ku xaba mana" ya fada ba tare daya dubesu ba yana ci gaba da lissafin uban kudin dake gabanshi,fiddausi ce ta soma zuwa wajen kayan dake tsakiyar mazan ta zazzaba kaloli daban daban sannan tacewa shahida taje ta zaba itama,a darare ta tashi ta nufin wajen,tana zuwa tsakiyarsu dab da zata isa wajen kayan wani santsi da batasan na meye ba ya kwasheta ta tafi zata fadi,daya daga cikin mazan wanda tunda sukazo yake tsaye a wajen yayi caraf da ita ta fada jikinsa.

Cikin wani irin hanzari da tashin hankali tayi yunqurin miqewa daga jikinsa saidai ya riqeta gam,ta tattara dukkan qarfinta ta hankadeshi ta miqe,harara ta dalla masa kana taja tsaki cikin bacin rai da dana sanin zuwanta wajen,ko fiddausi bata kalla ba ta fice a wajen,kanta take baiwa laifi tare da jin haushin kanta da kanta,me ya kaita zuwa iri wadan nan wuraren?,sam wannan ba tarbiyyarta bace.

Har taci rabin tafiya don bata tsaya taren abun hawa ba sannan ta biyota,gabanta tasha
"Matsamin na wuce,dama wajen wadan can watsattsun zaki kaini?" Kan fiddausin ta langabe tana share qwalla
"Wallahi na fiki baqincikin abinda yayi miki shahida,abinda ya tsaidani kenan ma yace na baki haquri shiba don wani abu yayi ba ganin zaki fadine" ta iya dadin baki da tsara kalamai,haka ta dinga baiwa shahida baki harta sauko
"Kin fasa daukan abun ne?,kinga ni gobe zanyi tafiya kuma zan dan kwana biyu ban dawo ba,shi yasa nace kizo ki dauki wanda zaki amfani dashi kafin na dawo"
"Inaso,amma bazan sake komawa gidan wadan can 'yan iskan ba" da haka tasha kan shahida tace gidan wata qawarta zasuje.

Gidan qawartata ne,wanda itama ta fito musu da kayan,fiddausi tace bari tayi testing,bayan tasha ta dubi shahida
"Kai wannan sunyi,kinji taste dinma daban da irin namu,don Allah sha kiji shahida" kai ta girgixa
"Ni bani da qarfin jini irin naku,bacci yake sakani sosai,kuma yau banason inyi baccin nan da wuri,saboda anwar zaizo" juna suka kalla suka tabe baki ba tare da shahidan ta kula ba sannan qawar fiddausin tace
"Lahhh,wannan na musamman ne baya saka komai,mai kyan ne,banda ma fiddausin da babu wadda zan bawa shi" qawar ita ta hada mata ta miqa mata kwalbar,ta karba ta dan sha,sai taji yayi dadin fiye da wanda suka saba sha kamar yadda fiddausin tace,saboda haka ta shanye duka.

Tun tana jin hirarsu sama sama har sai data fara ganinsu bibbiyu ta kuma kasa gane me suke fada,abu daya zata iya tunawa,sun dagata sun cire pant da pad din jikinta,taga jini na sake fitowa sosai daga jikinta,wanda batasan cewa cikin syrup din suka saka mata qwayar da zata sake sakata yin bleeding sosai ba.

Tsahon wasu awanni wanda batasan awa nawa bane jikinta yayi danshin jini sosai,tanason tashi ta gyara kanta ta maida pant dinta ta kasa,sai malelekuwa take a tsakar dakin qawar,saita tashi saita koma yaraf,da qyar ta iya hada kalmar fiddausi ta kaita gida
"Yanzu kuwa" ta fada.

Tasan sanda ta kamata suka sata a motar wani saurayi gaban motarshi wanda ba zata iya tantace waye ba,suka rufe yaja motar.

Tun daga nesa ta hangi kaman anwar zaune saman dakalin da lokaci zuwa lokaci suke zama,kanshi a duqe wayarshi na hannunsa yana dannawa da alamu ita yaketa qoqarin kira,hankalinsa na a tashe saboda ya iske gida suna bulayin nemanta ne su dinma.

,tanaso

10 / 53