Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   12 / 53

33K to 36K   out of 156.9K words

wanda ransa yayi tsananin baci,daga gefan shahida tsoro ne ya kamata,tana daga zaune amma jikinta ya dauki rawa,cikin jarumta da dakiya tace
"Amma yaya anwar....dare daya wannan abun har yayi girman da zai saka ka manta soyayyarmu?"
"Soyayya?....soyayya kike fada shahida,daga yau ki sawa ranki nayi bikin bunne soyayyarmu,kisa a ranki baki taba soyayya da wani mai suna anwar ba" gabanta yayi mummunan faduwa,kalaman daya furta yanzu sunyi kama da wadanda ke rubuce cikin takardar dake qanqame yanzun a hannunta,da gaske anwar shi ya iya rubuta duk maganar dake kan takardar?,yana nufin ba bacin rai bane cikin hayyacinsa yake?,hakan yana nufin da gaske yana tare da wata?,ya sauyata da wata?
"Sam baki dace dani ba bakiyi dai dai da rayuwata ba" kalaman suka sake saukar ba zata daga kunnuwanta zuwa zuciyarta,saqon ya isa kai tsaye zuwa qwaqwalwarta ya soma barazanar dakatar da aikinta
"Nayi dana sanin saninki....nayi dana sanin kasancewa dake tsahon lokuttan dana diba a baya" ya furta cikin sanyi wanda hakan ya saba da ainihin abinda ke zuciyarsa na tururi da zafin da takeyi,idanunsa sun kada jazur dasu
"Ya....yayya...kasanme...me kake fada kuwa?" Ta fada cikin harhada kalaman da suke niyyar qwacewa daga bakinta saboda tsananin dimuwa dataji ta afka lokaci guda
"Shahida.....idan nace Allah ya yimin sakayya ba shakka banyi kure ba" qit ya katse kiran daga haka saboda numfashinsa da yaji ya soma yi masa tauri,kanshi ya kifa kan kujerar dake gabanshi yana fidda numfashi cikin wahala,ba shakka dashi ragon namiji ne kuka zai fashe dashi ko zai samu sassauci cikin zuciyarsa,domin a wannan yanayin da yake ciki kukan shine abunda yafi cancanta yayi.

Daga fannin shahida kuwa miqewa tayi hannunta aka,sai kuma ta saukesu ta nufi qofa gadan gadan,komawa tayi da baya kuma saboda katsewa da tunaninta yayi,ta samu gefan katifarta ta zauna,lallai ba shakka koma meye zai faru a yau tana da buqatar ganin anwar ido da ido,zuciyata bata gamsu ba hakanan nata nutsu da cewa shi yake gaya mata wannan maganganun ba.

Kusan wunin ranar gaba daya tsaho taga yayi mata,tayi sintiri sau babu adadi,takai ta kawo kaman wadda ta hadiyi tabarya,ko sha'awar zaman ma sam batayi har aka kirayi sallar magariba,magaribar tazo tadan gota sannan ta fito tsakar gidan sanye da hijabin sallarta.

Ummantace kawai zaune saman abu sallar wanda suna hada idanu takau da kai,daga ita har abban nata ta fuskanci kamar suna kunyar hada idanu ne da ita ko yin wata doguwar magana tun maganar data gaya musu ta qarshe ta fito ta barsu a dakin,da alama yau abban nata ya samu ya lallaba ya fita masallaci sallah kenan,gefe ta samu ta tsugunna a takure
"Zanje chemist din ado ya dubani"bata ce komai ba sai daga abun sallar gabanta da tayi ta ciro dari biyar ta miqa mata,sannan ta waiwaya ta kalli mubina dake zaune tana zane zanen 'yar tsana a paper
"tashi ki rakata" tsam mubina ta aje takaddun,ta dauki hijabinta itama dake gefe wanda da alama tare da umman suka gama sallar ta saka tabi bayan shahida da tuni harta fara takawa zuwa waje,tuninta kawai ya zatayi da mubina.

Dole ta fara zuwa shagon ado ta gaya masa qarya da gaskiya ya soma hada mata magani,sai tace masa tana zuwa,ta samu mubina zaune kan bencin dake aje a qofar shagon
"Zauna mubina naje na amso wata allura da yace zaimin,karki sake ki tafi ki jirani na siyo na kawo yanzu zaiyimin"kai ta gyada abinta,tana ci gaba da kallo ta cikin qaramat tvn dake cikin chemist din.

Sannu a hankali ta dinga tambayar gidan,karo na farko a rayuwarta data soma tunkarar gidanshi,bama gidan ba unguwar gaba daya.

Sanda wani yaro ya nuna mata gidan saita tsaya cak zuciyarta na mugun bugawa kaman zata fito,addu'o'i ta soma karantawa tana neman agajin ubangiji,jin motsi daga cikin soron ya sanya tayi saurin matsawa ta rabe gefe tana kallon muhsin daya fito daga gidan ya miqe can layin nasu yana amsa waya.

Sai data tabbatar ya qule sannan ta fito sosai,ta doshi gidan ta saka qafarta asoron da bismillah a bakinta.

Dai dai lokacin yana zaune ne shuru,yayi nisa a duniyar tunani,gabanshi abinci ne aje,abincin da muhsin yaji haushin qin gaya masa damuwarsa da yayi ya tafi ya barshi yana mita.

Bai ankara ba baisan ta shigo ba sai ganinta yayi tsaye bisa kanshi.

Dubanta yake kaman yadda take dubanshi,kowanne da abinda qwaqwalwa da zuciyarsa take gaya masa,cikin hanzari ta isa gabanshi
"Baka da lafiya ya anwar dama?,me yas....."
"Dakata!" Ya fada a tsawace yana miqewa tsaye,ji yayi kamar ta dana mishi wuta a jikinsa,ganinta ita daya cikin wannan dare sannan kuma cikin gidanshi
"Me ya kawoki me kikazo yi?" Idanunta fal hawaye take dubanshi,tunda suke dashi dai dai da second guda bai taba mata magana da irin wannan amon ba,har kullum shi mai tattalin kwanciyar hankalinta da farincikinta ne,yau daya anwar din gaba daya taga ya sauya mata?,tun daga lafazi zuwa kamanni
"Na baki second biyar ki fita ki bani waje,idan ba haka ba saina baki mamaki wallahi" ya fadi idanunsa dake cike fal da kishi haushi takaici da baqinciki suka sake girma suka yo waje kaman zasu fado
"Ya anwar....ka daina irin wannan abun kana bani tsoro wallahi....ya anwar wani ya baka labarin abinda na aikata ne yasa ka sauya haka?" Wani murmushin takaici ya saki,wanda shi kansa ba abinda ya qarawa fuskarsa face wani yanayi mai ban tsoro
"Labari?,labari aka bani?labarin me?....shahida...ina cewa tun kafin kizo nan kinji me na gaya miki?" Kai take girgizawa kamar wata sabon tabi tana dubanshi,yayin da hawaye ya soma jiqa gaban hijabinta
"Ka fada ne kawai amma ba kana nufin hakan har zuciyarka ba,ba zaka iya rabuwa dani ba,ba zaka iya gujemin ba" matsowa yayi dab da itar har suna musayar numfashi a junansu,idanunsa sun sake girma daja,ya sunkoya da fuskarsa saitin tata
"So kike na maimaita miki abinda na fada a waya?,to ni anwar nayi dana sanin saninki da nayi,nayi dana sanin kasancewa da nayi dake a baya....shahida anwar bakya gabanshi a yanzu ki fita daga rayuwarshi,ya jima da yanke dukkan wata alaqa data taba hadaki dashi cikin tarihin rayuwarku keda shi" tunda ya soma maganar ta runtse idanunta tsam tana jin saukar hucin numfashinsa saman fuskarta,yayin da kaifi da dafin maganar ya dinga ratsa kowanne sashe na jikinta har ya isa ga zuciya ruhi da kuma qwaqwalwarta,duk da yadda idanunta ke a rufe hakan bai hana hawaye saukowa daga idanun nata ba kai kace lalataccen famfo aka bude,sanda ta ware idanunta itama akanshi sai yaja baya yana ci gaba da duban qwayar idanunta
"Ya anwar....me yasa?,me yasa zaka yanke wannan kyakkyawar alaqar?,me yasa zaka yanke kyakkyawar dangantakar da aka ginata tun tana jaririya harta girma?"
"Wannan kyakkyawar alaqar da kike magana akai ta dade da mutuwa,ta dade da juyewa zuwa mummunar dangantaka a wajena daga sanda na ganki kwance male male saman wa....." Sai ya kasa qarasawa saboda tuna mummunan ganin da yayiwa hotunan,wani abu mai tauri ya taho yaso ya toshe maqoshinsa,sabida haka cikin qaraji ya sake cewa
"Ki fita shahida!. Ki fita nace!" Kai ta kada cikin tashin hankali tanason taji qarshen zancan daya dauko,daga sanda ya ganta me?,ya ganta ne sanda suka tafi siyan syrup?,koko yana tsaye sanda matashin saurayin ya fiddo ta daga motar?
"Ba inda zani...kome zaka yimin ba inda zani" bata ankara ba taji ya damqi hannunta,karon farko a tarihin rayuwarsu,bai barta ba saida sukaje soron qarshe bakin qofar gidan sannan ya turata wanda hakan yayi sanadiyyar da tayi taga taga ta kusa faduwa Allah yasa ta turje
"Bana sonki shahida" kalmar data hadu da qarar rufe qofar gidan garam da yayi ta bada wata tsawa tsakiyar kanta data sanya komai nata ya tsaya cak na wucin gadi,da taimakon ambaton sunan Allah data soma yi ne ta samu nutsuwarta ta dawo.

A hankali ta dinga takawa kamar wadda tasha wani abun,kalaman anwar suka soma amsa kuwwa cikin kunnuwanta,wani irin bushewar zuciya taji,dukkan wani tashin hankali ta nemeshi ta rasa,ba abinda takeji sai kalaman anwar a kunneta,bata ankara ba taji ana
"Subhanallahi....sannu...amma bakiji ciwo ba ko?" Sai a sannan ta daga kanta tana duban mutanen dake magana kamar wata doluwa,ashe qatuwar kwalbatin da ake haqawa unguwar ta fada,da qyar da taimakon wasu 'yammata da sukazo wucewa ta samu ta fito sunata mata sannu,taci gaba datakawa ba tare data tsaya duba ciwon data ji ba,burinta kawai ta isa gida,burinta Allah yasa ace mafarki take.

Bata tabbatar da cewa komai da gaske yake faruwa ba saida dare ya tsala,taji idanunta tarwai kaman yanzu ta tashi daga baccin wata uku,siya zuciyarta ta dinga yi irin wanda bata tajin irinsa ba,cikin qaramin lokaci qirjinta ya soma ciwo,numfashinta ya dinga fita da qyar,haka ta tsinci kanta har asuba ta risketa,sanda ummanta ke yunqurin tadata tayi sallah a lokacin taga halin da take ciki,basuyi wata wata ba suka wuce da ita asibiti.

Gwajin farko likitan yaga jininta yayi mugun hawa,don dab yake da yakai dari biyu,dole suka soma mata allurar bacci kafin sauran treatment su biyo baya,ba qaramin tashin hankali abba da umman suka shiga ba,don duk ga zatonsu iya halin da suka tsundumata ne kawai yayi sanadiyyar faruwar haka,duk da cewa shi dinma ya taka tashi muhimmiyar rawar.

Daga bangaren anwar tunda ya maida qofar gidan ya rufe da qyar ya kaishi daki ya zube saman kujerar falon qwalqwalwarsa na daukan zafi,yana maijin ciwo da zafin dukkan wani abu daya faru tun daga kwanaki uku da suka wuce kawo yau,ji yake kaman ya budi idanun yaga mafarki yake,yana jin bugu wanda yasan bazai wuce muhsin ba amma bazai iya tashi ba,bashi da sha'awar ma kowa ya rabeshi,daga bisani wayarshi ta dauki qara,ya qura mata idanu yana kallonta hartayi ta gana ta tsinke,sannan ya miqa hannunshi ya daukota,ba tare daya damu da duba mai kiran ba ya bude bayan wayar ya ciro layin wayar ya karyashi ya watsa tsakar gida sannan ya cilla wayar da batiranta gefe guda,a ranar yadda yaga rana haka yaga dare,dukkan laifukan kuma na wuyan shahida ita ta haifar da komai,haka ya dinga sintiri yana zarya,gaba daya duniyar jinta yake sama ta koma qasa.

Da qyar da sudin goshi ya samu bacci yayi awon gaba dashi.

Cikin watanni qalilan yaji gaba daya rayuwar ta juya masa baya,baya jin dadin komai,komai ya daina burgeshi,komai kuma ya tsaya masa cak,duk yadda yayi qoqarin moving forward ga aje komai hakan ya gagareshi,dalili na farko da yasa ya tattara dukkan abunda ya danganci shahida wanda idan ya ganshi zai iya tuna mishi da ita ya killace a muhalli daya,duk yadda yaso ga qonasu ko zubarwa hakanan ya kasa,abu na biyu ya aje aikin kamfanin da yake,domin kuwa duk sanda zai tafin saiya tuna mishi da ita,abinda sam ko kusa ko alama baida buqatarsa.

Ta bangaren shahida kuwa sanda ta farka kalamansa ne abu na farko da suka soma dawo mata aka,ji ta dinga yi kaman zatayi hauka,ta ina zata iya rayuwar da babu anwar,yadda ta koma din ya sake daga hankalin abba da umma,yayin da tarin damuwa da nadamar abinda suka aikata ya sanya ciwo ya shigi abban,ya dinga fama dashi shi kadai yana cinsa kadan kadan.

Abubuwa sai suka taru suka yiwa umman yawa,ga shahida har yau bata gane kanta,ga abbansu ciwo nason kayar dashi,sannu sannu lamuran suka ci gaba da kwabe mata da tafi mata a haka,har zuwa rana mafi muni da tashin hankali a garesu,ranar da ciwo ya yiwa abbansu shahidan farat daya aka tadda gawarsa cikin daki,fadin irin tashin hankalin da suka tsinci kansu ma bata baki ne,shahida kam tunda ta suma bata farfado ba sai datayi kwana biyar,wata iriyar dakiya ta dinga shiganta,ta yadda tabbas wani tashin hankalin baida misali,yadda take jin kanta da rayuwarta ta zama wata mara gane komai,zaqi ko d'aci,baqinciki ko farinciki,murmushi ko kuka,ta koma kamar mutum mutumi,tana jin tamkar ita ta kashe mahaifinta,tana jin alhakin mutuwarsa na bisa wuyanta,abinda ta aikata ba shakka shi ya kashe mata mahaifi,awannan halin anty zubaida ta cimmasu,don dukkan abinda ya farun ya faru ne basa qasar ita da uncle hisham.

Kuka umma ta zauna tayi sosai a gabanta,tana fatan ta samu wasu shawarwarin da zasu kawo silar warwarewar matsalarta,bata boyewa anty zubaidan komai ba,labarin dukkan abinda ya biyo bayan yayi masifar girgizata,tana qaunat shahida har cikin ranta,tasan kuma Allah ne ya sallada wannan qaunar a tsakaninsu
"Ba shakka kun tafka kura kurai arayuwarku duk da cewa shi tashi ta riga data wuce kaman yadda kika shaidan yabar wasiyyar neman afuwa a gareku gaba daya saidai muyita masa addu'ar samun dacewa,cece kuce ko fada gaban 'ya'ya babu abinda baya haifarwa ku kunga irin naku sakamakon dayazo dashi,daga ciki yana haifar da qiyayyar uwa kota uba,saboda kan yara zai rarrabu,kowa da wanda yake goyawa baya,daga haka zakiga an samu jam'iyyu daban daban,wanda kowanne yaja tinga ne yana taya gwaninsa nashi fadan,walau yana taya uwa ko uba,wannan sai yasa hatta a tsakaninsu 'yan uwan junan ma basa jituwa saboda wani baya ra'ayin bangaren da wani yake,bugu da qari idan da namiji gareku kai uba kana koya mishi ko ya tara iyali haka zai mu'amalanci iyalinsa?,ke uwa kuma kin koyawa diyarki haka akewa miji,illoli ne masu tarin yawa da qalubake kala daban daban,yanzun kunyi silar jefa diyarku ga tafarkin shaye shaye sabida tashin hankalin da take shiga sanda kuke yaqar juna harta gwammace ta zama ko yaushe out of sense yadda ba zatasan meke faruwa cikin ahalinta ba..."dan shuru anty zubaida tayi abun na mata ciwo
"Yanzu bazanyi kaffara ba cewa kun korarwa diyarku manemi...saboda halin data fada ya isa kunnenshi...wala'alla abaya yana mata kallon managarciya yanzu ya sameta kan wannan turbar,kowanne namiji burinsa shine zabawa yaransa uwa ta gari kun bata wannan kyakkyawar shaidar daga kan shahida...inajin ciwo...inajin ciwon abinda ya samu shahida...amma nayi alqawari bazan bar rayuwarta ta gurgunta ba" daga haka ta miqe zuwa dakin shahida cikin bacin rai amma kafin ta shiga sai tayi qoqarin dai daita yanayinta sannan ta daga labulen a hankali ta saka kai cikin dakin da babu kowa ciki sai shahidan qwal ita kadai.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos


*Alqawarin Allah*
1️⃣6️⃣


Daga kai tayi ta dubi anty zubaidan maimakon yadda ta saba yi mata a baya duk sanda ta ganta,takan tashu cikin farinciki tana mata sannu da zuwa dama tambayarta yaushe ta iso,hadi da tambayarta su faruqu,a nutse anty zubaida itama take qare mata kallo bayan ta zauna dab da ita,cikin mintina qalilan ta gama karantarta
"Shahida" ta soma kiran sunanta a sanyaye,sake tada kai tayi ta dubeta saita sake saukewa,shawarar da zuciyarta ta bata tabbas itace mafita,dole ne saita fara tayar mata da mikin dake zuciyarta don da ala zuciyarta ta riga data daskare,dab take da rasa feelings,dole ta sata tayi kuka ta rage radadin da yake damun zuciyarta wannan shine hanya daya na farkar da zuciyar tata,dole ta sakata da kan kanta ta nuna akwai ciwo a zuciyarta wanda ta wannan hanyar ne kawai zata dawo da feelings da emotion dinta na fushi,sannan asan yadda gyara zai iya yiwuwa,tana son maida zuciyarta ne matacciya idan ba'ayi gaggawar gyarawa al'amarin ba
"Shahida!" Ta kirata wannan karon da mugun tsawar data taba zuciyar shahidan,ta kuma sanyata dago kai tana duban anty zubaida gami da zuba mata idanu,yadda ta kafeta da idanu shi ya sanya itama tsaiwa tana kallonta
"Shahida bansan ke shashasha bace,ban kuma san ke wawiya bace sai yau,ban raina wayonki ba sai yau,ashe ke banza ce?!" Shuru tayi kaman wata sokuwa tana duban anty zubaida,qwaqwalwarta nason tariyo mata meta aikata haka?,ganin yanayinta ya baiwa anty zubaida qwarin gwiwa
"Shahida....saboda namiji kikeson maida rayuwarki haka?,saboda wani da dacan baki sanshi ba?saboda wani daya nuna bai damu da rayuwarki ba?,wace iriyar shashasha ce ke wadda batasan ciwon kanta ba,shi din banza?...waye shi?,kina da 'yan uwa,kina da mahaifiya...mahaifinki ya rasu,waishin shi da mahaifinki wanne ne yafi miki muhimmanci,kin rasa mahaifinki ma ya tafi kuma har abada,kun rabu kenan da wanda yayi silar kawoki duniya,inaga wanda ya tsinceki rana tsaka da girmanki,shahida!....kisan me kikeyi,ki shiga taitayinki!" A hankali ta soma girgiza kanta,yayin da hawaye ya cika idanunta,zuciyarta ta soma motsawa,mikin dake danqare ciki ya tashi,kuka ta saka mai sauti qwarai wanda hatta mutumin dake tsakar gida zai iya jiyo gunjinta,sai anty zubaidan ta matso da ita jikinta,ba musu ta kwantar da kanta saman cinyar anty zubaidan taci gaba da gursheqen kukanta,bata ce mata komai ba hakanan bata hanata ba,shuru tayi tana sauraron yadda kukan nata yake fita,ta sani duk sanda hawaye daya ya sauka yana sauka ne da wani radadi daga cikin radadin dake danqare cikin zuciyarta,hannu anty zubaida ta dora saman kan shahidan ta dinga shafawa a hankali a hankali tana tayata jin radadin.

Aqalla sun shafe awa guda cur a haka,harsai da kukan ya soma sassauta ta soma rage sauti ya koma sai hawaye,mintina talatin ta sake qara mata zuwa sannan hawayen ya sake raguwa
"Me ya faru shahida?,garin yaya haka ta kasance?" Bata boyewa anty zubaida komai ba kanta na saman cinyarta ta warware mata dukkan yadda akayi ta soma shan wani abu da niyyar rage baqinciki da bacin ran dake damunta,sannan ta zarce da rabuwarta da anwar sannan ta dora da cewa
"Baqinciki na shi ya kashe abbana anty,shaye shaye yabarmin tabon da har na mutu dashi zan mutu,na kashe abbana da takaicina!" wanda hakan ya sake bude sabon shafin kukanta,kai anty zubaida take girgizawa
"Kuskurenki na farki shahida shine da kika saki Allah,kika manta da cewa babu wani babban abu dake yaye qunci da baqincikin a zuciyar bawa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali irin kusanta kai da Allah,babu wani abu da zai kawo miki farinciki da walwala irin karatun qur'ani,shan wani abu a wajen dan adam domin gusar da baqinciki bacin rai ko kuma damuwa bashi da wani tasiri a gareshi,baya haifarwa da bawa komai face sake sanyashi cikin damuwar,baya yaye damuwa ta har abada face ya sake sanyaka cikin

12 / 53