Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   42 / 53

123K to 126K   out of 156.9K words

yasake mannata da jikinsa ya soma mata magana cikin kunne
"Ki taimakeni,minti biyar zaki baki don Allah,bazan iya miki fin qarfi ba,karkice a'ah.....mutuwa zanyi" yafadi qwalla na taruwa cikin idanunsa saboda wani irin abu da yakeji yana masa yawo cikin jiki wanda bai taba jin kamarsa ba,kalmar mutuwar ita ta sanyaya mata jikinta qwarai,saita daburce ta rasa abunyi,ya qarasa toshe mata dukkan wani tunani nata sanda yashiga aika mata da wasu saqonni,saita kasa tuna kome,ta kasa yanke kowacce shawara,ta tasa makama,a haka yasamu nasarar danganata da gadonta.

Duk yadda yaso ya daure amma ya kasa lokacin da muradinsa yasoma cika,kaman yadda take kuka haiqan shidinma kukan yake,abubuwa da yawa suka tarar masa sukayi masa yawa,yasha wuya kafin ya fitar da abinda ya tattarar masa ya hanashi sukuni,kaman qaramin yaro haka yaci gaba da fidda hawayenshi,kama hannunta yayi ya qanqame cikin nashi sannan ya hade fuskokinsu waje guda,idanunsu duka a lumshe saidai kowannensu qwalla ce ke fita daga nashi idanun,yayin da fuskar kowa tajiqe da hawayen dan uwanshi.

Har yanzu bugun zuciyarsa bai daidaita ba,ji yake kaman numfashinsa zai dauke,innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yake furtawa qasa qasa,yayin da wani sanyi da farinciki yake ratsa zuciyarsa,wata iriyar qatotuwar BAZATA ya tadda tattare da shahidan MEKE FARUWA?,ya jefawa kanshi da kanshi tambayar daya tabbatar baida amsa face sanyashi cikin rudu data sakeyi,ya jima zuciya dagangar jikinsa na gaya masa,ya jima yanajin cewa kamar hakan ba zata kasance ba,ya dade yana kokwanto,ya dauki lokaci yana shakka,saidai ya kasa samun tabbaci saboda rashin gamsashishiyar hujjar da zata sanyashi ya yarda yakuma nutsu kamar yadda ya samu cikakkiyar hujjar data jefashi a wancan ko kwanto.

Gaba daya ya sanyata cikin jikinsa yana matseta gam,yanajin yadda take sakin wani marayan kuka mara cikakkiken sauti me hade da sheshsheqa,ya sani koda bata fada ba ta wahala,habarshi saman kanta yana shafawa a hankali yana hadiye wani abu mai tauri,ya kasa cewa komai illa
"Amsorry" da yaketa maimaitawa,tunani barkatai suka addabi qwaqwalwarsa kamar zai zauce haka yakeji a sannan,sauqinta daya wata iriyar nutsuwa da sanyin zuciya daya samu,uwa uba yanayin kaman an dauke wani qaton dutse ne daya danne zuciyarshi
"La'ilaha ilallalah" yaci gaba da fada hadi da fitar da numfashi,ya rasa wanne tunani zaiyi?,da wanne zai fara?.

A hankali ya dagata daga jikinsa yana kallon fuskarta wadda hawaye ya jiqeta,idanunta suka dan tasa kadan,bai ankara ba yaji wasu hawaye masu dumi sun kubce daga idanunsa,randa aka cillota gabanshi cikin jini da sunan zubda ciki shine abu na farko daya fado masa,saiyaji kuka yakesonyi,dada hali irin kukan nan me sauti ma,ko zai daina jin wani murdadden ciwo da radadi daya riqe masa wuya,whose behind this???,ya furta cikin murya dake nuna zafi fushi da tashin hankali.

Fuskar saurayin ta dawo masa tarrr a fuskarshi kamar yanzun yake tsaye a gabanshi,hotunan da aka aiko masa suka dawo masa
"Shiri ne?" Ya tambayi kansa qwaqwalwarsa nason shirya masa dukkan yadda abun yake
Kada dai ace plan ne?"baisan sanda ya diro daga saman gadon,ya nufi safe dinshi gadan gadan ya duqa a gabansa ya saka pin din da yake amfani dashi,saboda rawar jiki da tsabar sauri har yayi mistake,ya sake sakawa ya bude,ya zira hannu yaciro envalope din,cikin sassarfa ya bude dakin yafice,ya sauka qasa ya durfafi dakin karatunsa ba tare daya duba cewa dare yasoma nisa ba,baiko damu da kunna qwan lantarkin dakin ba yayi amfani da hasken bayan gidan da yake ratsowa yake shigowa tacikin dakin,ya kunna cumputer yazauna sosai kaman zai shige cikinta,ya bude littafin da suke karatu ya dudduba wasu bangarori a gurguje bayan ya tashi cumputer din yasoma shige shige bayan ya saita camera din laptop din yadauki hoton katin dake hannunshi ya maidashi cikinta.

"La haula wala quwwata illa billa,la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalim,astagfirullah" ya dinga ambata dukka hannayensa guda biyun saman kanshi kamar wanda ke shirin rushewa da ihu,idanunsa qyar bisa allon cumputer din,aikin dabai xaci xai iya ba sai gashi cikin awanni uku yayi shi,tunda suma karatun bai taba practicing abinda yake karantawar ba,sai a yau a karon farko,fuskar shahida da aka dora saman ta fice tas,ainihin me fuskar ta bayyana,wanda take tsirara haihuwar uwarta ita da saurayin dake jikin hoton,sosai yazubawa fuskar idanu yanason tunata
"Fuskar wace wannan?" Ya dinga maimaitawa idanunsa na sake kadawa suna komawa kalar ja,FIDDAUSI sunanta yafado masa bayan ya tuna inda yasanta,qawace ga shahidan,yasha ganinta tare da ita,shahidan tasha kai masa qorafin yadda zunnurah ke qinta ba gaira ba dalili,yasha maganar da xunnurah,sau tari takance
"Wallahi ni kawai batayimin bane anwar,saboda ina shakkar tarbiyyarta,banason tashiga jikin qawata kuma alhali tana da wata mummunar dabi'a,kabar abinda kake kokwantonsa izuwa abinda baka kokwantonsa kawai" kasa zama yayi saman kujerar kawai saiya sulale yazauna sosai saman carfet din dakin,bayan ya saka remote ya kunna duka qawayayen dakin,dukka tunaninsa da kwanyarsa sun dauki zafi,hoto daya tak shine wanda wanda yake nuna ainihin fuskar ta shahidan ce(wanda aka dauka randa ta raka fiddausi siyan syrup takusa faduwa wani ya tarota),dukkan wani tunani nashi ya tsaya cak,ya soma tattara dukkanin hotunan yana yamutsasu bayan ya cire iyakan shahida dana saurayi,koda komai nashi zai qare saiya nemo wanna yaron,koda xai rasa duk abinda ya mallaka saiya nemosu,fiddasi?,ina zaiga fiddausi?,sai a yanzun ya tuna ma tunda ya soma haduwa da shahidan karo nabiyu cikin rayuwarsu bai taba ganin fiddausin tare da ita ba,anya wannan ba YANKAN BAYA BANE?!.

kiran sallara asubar daya soma ratsa kunnuwanshi ya sanyashi tashi ala dole yabar dakin,ya dinga takawa tamkar wanda yasha wani abun maye,yana tafe yana yamutsa gashin kansa,duk wata kafa da qofa ta tunaninsa ta dinke tsaf!.

Da sauri ya tarota wanda hakan yasa envalope din hannunshi subucewa ta fadi qasan gadon sanda yake niyyar shiga ita kuma tana yunqurin tashi daga saman gadon xuwa toilet dinta,jikinta ya dauki zafi sosai,saiya kalli qwayar idanunta,bai iya tantance meye saman fuskartata saidai yunqurin jaa da baya da tayi
"Kada ka sake tabani,ka qyaleni haka tunda muradinka yacika,na hadaka da Allah",ta qarasa fada tana hade tafin hannayenta alamun roqo,duk da cewa ta kasa kallon koda fuskarshi ne bare idanunsa
"Kafita,na roqeka"ta kuma furtawa muryarta a karye,da alama kuka takeson saki,kasa ci gaba da tsaiwa tayi saboda azabar da takeji saita koma tazauna bakin gadon badon taso ba,kaman wanda aka rufe mishi baki haka yaji ya kasa cewa komai sai kallonta kawai da yake,kowane daqiqa daya yana tariyar duk wata magana daya gaya mata ne a baya,inama zai iya,inama kuka zaizo masa?,inama zai iya rusa ihu,yayita rusawar harsai yaji sanyi cikin ranshi,saidayaga takoma ta zauna sannan ya qarasa gabanta,yazube dukka gwiwoyinsa a qasa,yakai hannu zai kama hannayenta tajanye hadi da janye gwiwar tata
"Kome zaki fada na yarda da hakan,ki bari na taimakeki don ke kanki kinsan baki da qwarin aiwatar da komai" batace masa komaiba idanunta na runtse don batason kallonshi,duk da hakan hawaye bai hana fitowa ta qasan idanun nata ba,wani babban tashin hankali yaji yana saukar masa,da wanne ido zata kalleshi a sanda tasan dalilin da yasa yaqwafeta yake xarginta?,yanajin kaman zunubinsa wajen Allah na qaruwa duk sanda qwalla daya tafito daga idanunta,taqi ta tankashi,saboda haka yamiqe ya shiga toilet dinta,ya cika mata bathtube da ruwa mai azabar dumi sosai,sannan ya sake kunna water heater din yatsaya saida koriyar danja ta kama alamar wanda yakeciki ya tafasa sannan yakashe yafito,har yanzu tana zaune a inda take bata motsa ko nan da can ba,inama ace dukkan abinda yafaru bai farunba?,inama ace komai daya faru a baya mafarki ne?,ya dade yana gina wannan daren cikin tunaninsa,ya dade yana suranta yadda daren zai kasance,ashe duka bazata samu ba,ashe duka zaizo musu ne a hugunce shida ita?da xaiyuwu zaici gaba da rufe komaine kamar yadda tsahon shekara shida yake rufe da abinsa,amma hakan bazata yiwu ba,dole ya gaya mata komai saboda babu wata hanya da zai gane wanda keda hannu cikin lamarin saida goyon bayanta.

Sau uku yanace mata tashiga tayi wankan amma kamar da dutse yake,ya daga kai ya dubi agogo,saura kadan lokacin sallah ya kubce musu,yatuna da yadda yake tafi da ita wanda kafin sannan basirar hakan tabace masa tas saboda yanayin da yake ciki,saboda haka ya soma tattare hannun rigarsa
"Indai kika bari na qaraso nan baki tashi ba ba abinda zai hanani qarasa ladana,tunda na fahimci so kike ki mana asarar samun sallah akan lokaci,zumbur tamiqe wanda har sai dataji a jikinta,ta soma takawa da daya da daya,ganin hakan yasanshi qarasowa gaba daya ya dagata yayi bandakin da ita,saidaya ajeta sannan ya fito yaja mata qofar bandakin.

Fita yayi daga dakin dasauri yana gaggawar yarigata gamawa kada ta rigashi fitowa.

Ta jima tsaye gaban mudubin bandakin tana kallon fuskarta tare da sakin wani sabon kukan,ayau bata da wani sauran alfahari daya rage mata anwar ya karbeshi a yanayin da ko kusa ko alama bata shiryawa hakan ba,sai data gaji don kanta sannan ta fidda kayan jikinta ta soma gyara kanta,wanda dataji azaba kawai takeci tabarshi tasoma wankan.

_kuyi manage_🥰*Alqawarin Allah*
48



Yaci sa'a kuwa,sanda yadawodin bata fito ba,saiya haura gadon ya yaye zanin gadon dake samanshi ya hada da pillow case din ya sabule gaba daya,ya bude sif dinta duk da baisan kanta ba ya soma lalubawa,cikin sa'a yasamesu a jere yazabi daya ya budeshi ya shimfida,ya tattara duk wani abu daya baci a dakin ya share gami da gogewa,fes dakin yayi,ya riga yasaba kusan tun can baya daya rayu shi kadai cikin gidansu,shi yakeyin komai,don haka irin wannan hidimar bata bashi wuya saidai bai samu lokaci ba ko bai sanya kanshi ba,ya kunna turaren wuta a burner daya gani jone kusa da gadon.

Qofar bandakince ta bude a hankali shahidan tafito,tana ganinsa ta dauke kai kanta,yayin dashi kuma yaci gaba da kallonta,tafiyarta gaba daya ta canza,tana takawa kamar mai tausayin qasa,kanshi ya girgiza da alama bata shiga ruwan zafin dakyauba,baice mata ba ya zagayeta ya koma toilet din,ya hada ruwan zafi dakyau ya dawo dakin ya taddata tana zaune zata soma shafa mai,yasan ma batun ya mata magana tayi kai tsaye bata bakine,saboda haka yayi mata irin na dazun ya sunkuceta kawai,bata tsammata ba saboda haka abun ya bata tsoro ta riqe wuyanshi da hannunta tana jin kaman zata fadi
"Ka saukeni....banaso...meye haka?" Ta dinga fada cikin fada,saidai hakan bai bayyana ba sakamakon laushi da muryarta tayi,bai saurareta ba sai daya sanyata cikin ruwan yana zare qaton towel datayi daurin qirji dashi,tana qoqarin riqowa ya sake zare na saman kanta,saita koma cikin ruwan tayi laqwas duk da zugin da takeji,babu damar fita saboda ya amshe duka towel din,sai qwalla kawai data dinga sauko mata zuwa saman fuskarta idanunta a runtse,ta rasa ina zata kalla,ko bata fada ba dole yadinga hango jikinta tacikin ruwan tunda garai garai yake.

Hakan take kuwa,yana tsaye ya jingina da wata 'yar cupboard dake bandakin yana kallonta tacikin ruwan,wani bari na zuciyarsa farinciki ke ratsashi mara misaltuwa hadi da godiya ga Allah daya kare mishi shahidarshi,ya tsareta,yasa duk abinda yake tsammanin yafaru din ya zama zato da hasashe,na biyu kuma idan ya tuna yadda suka zama abu guda sai abun yayita masa dadi da qayatar dashi,abu na uku kuma shine yadda Allah yajuya akalar tunaninsa,ya kasa haquri da shahidan awancan lokacin har sai daya taka da kanshi yaje ya nemi aurenta,da tuni yabarwa wani banza da baisan ciwonta ba ita?,da tuni wannan zumar dayasha a yau din wani ne zai sameta?.

Gefe daya na zuciyarsa kuma tunaninsa yayi nisa qwarai ta inda zai binciko dukkan wani wanda yake da hannu wajen shiryawa da faruwa lamarin,ya quduri aniyar koma waye bazai taba sassauta masa ba,saiya biya duk wani radadi da suka shiga suka dandana shida shahidan tsahon shekaru shida,saiya dandana dacin daya lasa musu tsahon lokaci,bazai masa afuwa ba,a yanzun kam bayason ya bayyana komai wa shahidan,yafison saiya kammala zaluqo duk wanda keda alhaki kan abun,babban burinsa shine a yanzu ya dawo da soyayyarsa cikin zuciyarta,yanada buqatar dukkan wani abu dake nuna qauna da soyayya daga gareta kamar yadda suke a baya,shima zuwa yanzu ba'a zancensa,yadda yakejin shahida a yanzu cikin ruhi da rayuwarsa,koda ace da gasken ta aikata wancan abun da abaya yayi tsammanin bayajin zai iya rabuwa da ita,ta zama shi ya zama ita,bazai iya barwa wani ita ba,bare daya bayyanar masa cewa akwai wani boyayyen lamari da shiryayyen shiri cikin lamarin,to waishin wa suka tsayawa haka a rayuwarsa dahar ya zabi yi musu wannan mummunan hukuncin?.

Yayi nisa a tunanin nashi yadinga jiyo kaman shashsheqarta,yasake kai dubanshi gareta zuwa yanzu tana cure waje daya cikin ruwan,saiya aje towel din hannunsa ya matso inda take
"Kin hade jikinki gaba daya,ta yaya ruwan zai ratsaki?"
"Don Allah kafita ka bani waje don Allah ka qyaleni"
"Kiyi haquri shahida....bazan iya ba" ya fada yana durfafarta,qarfi yasa mata ya tabbatar tazauna sosai ruwan yana ratsata yadda ya kamata,hakanan tanaji tana gani ta zuba mishi ido,don bata da wani sauran abunyi,sai daya canza mata ruwa sau uku sannan yamiqa mata towel din yace tadaura,yadan bata space ta daura din sannan ta fito,yana binta a baya kamar bodyguard,ita akaran kanta taji dadi sosak,ciwon da radadin ya ragu,a takure tashafa mai saboda yana tsaye gefanta kamar wanda aka bashi gadinta,ta zaluqo kaya zata sanya tarasa ya zatayi
"Kabani wuri nasa kaya" ta fada ba tare data dubeshi ba
"Ki saka kawai,gwarama ki saba da sanyawar a gabana,don daga yau na daina rabuwa dake,meye ma ban gani ba da za'a boyemin" hararasa takeson tajuya tayi amma batason su hada idanu,haushi ya kamata,wato yagama da ita kenan,ko bai fada bai ai itama kanta tasani,ganin ta tsaya ita bata saka ba ita bata aje kayan ba saiya matsa gab da bayanta,zataja baya yayi hanzarin hadata da jikinsa yariqeta tsam yanajin kewarta kamar ba kusa dashi take ba,cikin kunnenta yace
"Zaki iya yafemin shahida?,zaki iya yafemin bata miki ran dana tabayi a gabaki dayan tarayyarmu dake?" Mamaki ne ya kamata,meya sauyashi haka?,ko dadin baki yake mata?,kodon ya samu amfani da ita ajiya yakeson yayi mata dabara yayi yayi mata dadin baki?,to bazata sake barin abunda yafaru yafaru dinba,wannan dimma shammatarta yayi,don haka shuru ta masa,don idan tace zata tureshi ba ta bata lokacinta ne tasan ba zaya matsa ba,saiya amshi bra din hannunta ya soma qoqarin saka mata,ta rasa ya zata masa,itakam ya matsanta mata,tafison ya qyaleta tayi jinyar kanta,saboda haka ta sakar masa kuka,kaman ana masa kida tsakar ka yaji sautin kukanta,cikin daburcewa ya soma rarrashinta,dole daga qarshe ya bata space ta canza kayan tunda ya fahimci haka takeso.

Tun daren jiyan daya fita daga dakinta hankalinta ba'a kwance yake ba,gaba daya komai ya dagule mata,itama a matse take fiye dashi,dogon tsaki taja,wannan maganin sharadinsa yafiya tsauri,dole ta nemi mima asan abunyi,bata duba dare ba tajanyo wayarta tahau kiranta,sai data kusa tsinkewa ta daga,muryarta na nuna alamun ta fara bacci
"Lafiya kike kirana a irin wannan daren?,koni da bani da aure ai bana kiraki a irin wannan lokacin ba bare ke dake da aure" tsaki ta sake ja
"Yo wane aure?,auren da yake a suna ba"
"Kaman yaya?"
"Wannan maganin naki mana,ya tsaida komai ya hana komai yin gaba,komai yaqi daidaita,yanzun ya kama hanya yafice daga dakina cikin bacin rai,saboda kwana shidan nan duka janye masa nake naqi bada hadin kai,ina tsoron karya tafi dakin wancan baqar matsiyaciyar,mima,na samu dama irin wanda ban zaci zan sameta ba amma tana neman kubcemin,ban tsammaci zan samu anwar haka ba na sameshi amma komai nason tsama mai jinkiri"
"Damar da xaki rasa nan gaba ta ninka wadda kike magana akai a yanzu,kin manta cewa da kwanakin sun qare shikenan?,zaki samu fiye da abinda kike nema?"
"Na sani mima....amma ba wani sauqi da zaki tambayomin wajen malam,koda sau daya ne ayi shikenan sai a dora daga inda aka tsaya?"
"Yin hakan dai dai yake da haukacewarki,don yace idan aka soma aka kuma dakata toba shakka haukacewa ake" idanu nafisa ta zaro cikin tsoro,harta hango kanga cikin hauka,sai hankalinta yasake tashi
"Mubar wannan batun,meye mafita?,yanxu ya zanyi dashi?" Murmushin mugunta miman tasaki can qasan ranta,a yanzu haka tafi jin mugun haushin nafisa fiye da shahida,donta shahida tana ganin mai sauqice a wajenta,tunda harta iya fadawa tarkonsu a baya to a yanzu ma bazaiyu wuya ba,amma ta fuskanci qwaqwalwar nafisan babu komai fanko ce,ba kasafai take aiki ba,uwa uba ta maidata kamar wata yarinyar gidanta kenan
"Ina tsoron karya farmiki kizo hauka ya tabbata a kanki,a shawarce kawai kibar mata kwanakinki na tsahon lokacin da zaki gama magani,idan kika duba ba wani abun damuwa bane,da magani ya kammala zaki fanshe fiye da abinda kika sadaukar,idan kikaso ma kina iya amsheshi gaba daya ki hanashi ko kallon qofar dakinta bare akai ga shiga" shuru nafisan tayi,shawarar kam ita kadaice mafita,amma kuma tana tsananin kishin anwar din
"Idan kuma bazaki iya ba to nan gaba karki kuka dani,karkuma ki nemi shawarata idan lamura suka kwabe,amma idan baki wasa ba rashin haqurin wata uku zai iya jaza miki kwabewar lamuranki muddin rai" sosai maganar miman ta gamsar da ita,saita gyada kai cikin gamsuwa,ko kafin tace wani abuma miman ta datse layin,donta tabbatar mawuyacine ma nafisan taqi aiki da shawararta,uwa uba sai tana nuna bata damu sosai da abun ba kafa taga ta matsa da yawa tasawa ranta wani abu kan batun.

Da wannan shawarar ta miqe da hanzari ta nufi bakin qofarta tasanya key tarufe,ga tsammaninta anwar dai zai dawo,kar kuma ya kasa haquri yafar mata kaman yadda miman tayi mata hasashe.

Fitsari shiya tada ta,ta sauko a hankali daga saman gadon zata wuce toilet,qamshin da hancinta ya jiyo shiya dawo da ita da baya,ta waiwaya ta dubi kwanukan dake aje saman mudubinta,cikin mamaki ta qarasa ta soma budewa,qamshinsu ya cikata,yawunta ya tsinke,mamakin wanda yayi girkin yakamata,saita tuna da anwar din,tasan ya

42 / 53