Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   31 / 53

90K to 93K   out of 156.9K words

karyawa shahida gwiwa tunda ta fuskanci kamar ta aro dakiya da juriya,daidai sannan huda ta shigo da sauri,ta isa gaban shahida ta rungumeta,zata fara kuka anty zubaida ta zare mata ido gamida korata don karta karyawa shahidan gwiwa,a haka aka fita da ita zuwa gidansu.

Can dinma gidan cike yake da jama'a 'yan yinin biki,uwar dakan ummanta aka ajeta,'yan uwa suka dinga shigowa aka dinga gaisawa ana yi mata Allah ya sanya alkhairi,tayi qoqarin tarbar kowa cikin mutuntawa,tunda kusan dangin ummanta ne duka,ba wani bare ko baquwar fuska.

Sai gab da magariba sannan umma ta zauna da ita ita da sauran yayyenta,fadane dai irin wanda uwaye kewa diyarsu,daga bisani kuma umma ta taba nata,ta nemi yafiyarta cikin kuka tana tunawa da abbanta
"Bakiyimin komai ba shahida,saidaima ni nace ki yafe mana nida mahaifinku" kukan da bataso ba a yanzu shi take haiqan,kaman ba zata fita daga gidan ba haka ta tako suna riqe da ita aka fito da ita,saitaji wani qauna da kewar mahaifiyarta na ratsata,taji kaman karta tafi,taji kaman taci gaba da zama dasu,a yanzu bata buqatar anwar sam,bata da buqatarsa cikin rayuwarta.

Tun daga harabar gidan anty usainan zaka gane wata walima ake ta daban saboda yadda harabar ta qawatu,uwa uba ankon da yake jikin duk wanda ke farfajiyar dama cikin gidan cikin wata atamfa mai azabar kyau da tsari.

Sabon shagali na walimar da dangin ango suka hada aka bude,nan aka zaunar da shahida suka dinga mata barin liqi tako ina,ba'a tashi ba saida akayi sallar magariba,anty usaina bata bari an shiga da ita cikin gidan ba,can wani babban falo dake da daki da bandaki aka kaita,babu kowa wurin da niyyar ko zatayi sallah,aka aje mata abinci aka barta ita daya donta sake,tuni 'yan uwanta suka koma gida ba wanda ya zauna,fashin sallah take hakanan abinci bata sha'awarsa,kuma batajin zai iya wucewa ta maqoshinta,saboda haka ta zauna kawai idanunta kan tv din dake aiki ita daya,volume dinta can qasa don ba'ajin ma me ake cewa,sam ba tv dince a gabanta ba,sabuwar rayuwar da zata fuskanta itace a gabanta,abu na gaba tsakanin kunyar anty usaina,ta yaya zata kalleta?,idan ta tuna kalaman data gaya mata na batason dan uwanta sai taji duk nauyi ya sauko mata,batasan itace wannan yayar tashi qwaya daya da bashi da kamarta ba,da duk yadda take qin abun ba zata yarda bakinta ya fada ba,addu'a take cikin ranta Allah yasa kada ta shigo.

Bakwai da rabi zuwa takwas na dare taji hayaniyar gidan ta ragu sosai,da alama masu tafiya sun tafi kenan,masu shigewa cikin gida sun shige,turo qofar da akayi shi yaja hankalinta,ta dan dage mayafinta kadan tana kallon mai shigowar,sa'ida ce saidai ita batasanta ba,fuskarwa a washe ta qaraso falon tana takowa a hankali tana waigawa,da alama ba'asan tayo.nan ba,dab da shahida ta zauna tana kallonta
"Anty,saike kadai?,nayi nayi da ummi tabarni nazo tace a'ah zamu takura miki kina hutawa ne,da qyar na samu na sallabo" murmushi shahida tadan saki tana duban sa'ida
"Ina yini anty,ya gajiyar biki"
"Lafiya lau,me sunanki"
"Sa'ida,'yar anty usaina ce ni,kuma qawar uncle anwar" girarta shahida ta dage duka biyun tana dubanta alamun tambaya,dorawa tayi
"Wallahi kun dace sosai anty keda uncle,uncle ya samu mata me kyau" tana murmushi sosai ta fada tana kuma sake kallon fuskar shahidan data ji tana burgeta,murmushi shahidan ta kuma saki
"Ko?" Tace cikin sigar tambaya,kaita kada
"Qwarai kuwa,amma anty,don Allah ki kularmin da uncle dina,wallahi inason uncle anwar,yana da kirki sosai,yana sonmu shima,yana kula damu sosai da sosai,don Allah anty" saita tsaya tana sake dubanta kafin ta kuma sakin murmushi,ta dora hannunta saman hannun sa'ida
"Uncle din naki nima zai iya kula dani ne sa'ida?" Dariya ta saki
"Tabdi,sosai kuwa anty,kinsan uncle anwar kuwa?,ai matarshi ta caba" saitayi qasa da murya
"Na zaci fa zai iya aurena harna cewa ummi ina sonshi,ranar saida na daku sosai,ashe babana ne" dariya ta kubcewa shahida da sa'idan duka,da sauran dariya a fuskar shahidan tace
"Babanki ne sa'ida,amma kita addu'a Allah ya baki wanda ya fishi nagartar halaye"
"Akwai wanda yafi uncle dina kuwa?" Ta fada cikin tantama da tunani,kaita jinjina
"Qwarai kuwa,duk wanda kika gani kome kika gani a duniya akwai wanda ya fishi akwai wanda baikaishi ba akwai dai dai dashi"
"Tohm shikenan......" Bata qarasa maganar ba suka jiyo taku ana nufowa wajen,saita fiddo idanu
"Na shiga uku anty,Allah yasa ba ummi bace" riqe hannunta tayi
"Karki damu,zance nina kiraki ki tayani hira" shuru sukayi suna jiran ganin wanda zai shigo din.

Sallamar mutum biyu ce,ummin sai muryar anwar daga bayanta,mummunar faduwar gaban data sanya shahida maida kanta cikin mayafi ta saukar mata,ummi anty usaina ce a gaba sai anwar din daga bayanta,idanunta akan sa'ida nashi idanun nakan shahida da kanta ke sunkuye lullube da mayafi,kama baki tayi
"Na shigesu ni usaina,sa'ida...sa'ida ki shiga hankalinki da wannan rawar qafar taki,dama da akacemin ba'a ganki ba nan kikayo?,to tashi ki wuce ki bama mutane guri" da sauri ta zame hannunta cikin na shahidan sannan ta miqe,duk da haka da zata gifta anwar din saida tace
"Uncle,kayi kyau sosai yau,amma wallahi in gaya maka gaskiya?,anty shahida ta fika kyau ashe" anty usaina batasan sanda dariya kubce mata ba,yayin da murmushi ya subuce masa shima ya bita da kallo harta fice daga dakin,ba ruwanta hakanan take,idan taga gaskiya saita fada,kusan halayenta suna kamanceceniya dana mahaifiyarsu,duk cikin yaran anty usaina tasu tafi zuwa daya,kusan sanda aka haifi sa'ida tare sukayi rainonta shida anty usainan tun lokacin mahaifansu suna raye,idanunsa ya sake saukewa akan shahidan a hankali duk da bai ganin fuskarta,yana tsaye a wajen har anty usaina ta zauna
"Zauna daga can" ta fada tana masa nuni da inda takeso ya zauna din,kujerar da shahida ke kaine,duk da cewa mai yalwa ce amma saiya zauna a hannun kujera,cikin hikima da nutsuwa ta soma magana dasu
"Alhamdulillahi rabbil Aalim,komai na rayuwa a tsare yake zuwa daga wajen ubangiji mai kowa da komai,basai na tsaya wani tambaye tambaye ba don nasan ba amsa zan samu daga gareku ba,abunda nakeson na fada shine,wannan auren naku ya isheku dama sauran mutane ishara,kun rabu da juna kun guji juna ba tare da dayanku ya sake tunani Allah zaiyi ikonsa ku sake haduwa a wannan bigire ba na aure,wannan kadai ya isa ya nunawa bawa yana tashi ne Allah yana tasa,ta Allah kuma itace dai dai,saboda haka ku sanyawa zukatanku salama,ku zauna da juna cikin aminci da bin umarnin mahalicci,kada ku yiwa Allah butulci wanda ya baku aron rai da lafiya ya kawoku wannan lokacin koda cikin zukatanku bason hakan kuke ba,dubunku na nan na fatan samun kamar takun,ya sake hadaku a sanda kowannenku rayuwarsa ta sauya ta samu ci gaba,ta yuwu hikimar rabuwar daku dama don kowanne ya cimma gacinsa ne,wanda wala'alla idan kuna tare da zaku cimma wannan abun ba,ku kauda hayaniya da tashin hankali ku ajeshi idanma kun daura azamar hakan,kuyita addu'ar Allah ya baku mafita ya sanyaya zukatanku" saita waiwaya ta dubi anwar
"Kai kaine babba sannan kaine shugaba,kai keda hankali fiye da mace,sabida haka fiye da rabin nauyi da yanayin yadda zamanku zai kasance ya ta'allaqa a wuyanka ne,kasan komai basak na fada maka ba,iyayenmu kafin su rasu makarantace a gareka,ka dauki matarka ku tafi daga kai sai ita,ina muku fatan alkhairi,shahida...Allah ya bamu alkhairinsa kinji" kasa magana tayi kunya na kamata,ta fuskanci hakan sabida haka tayi murmushi taga bari kawai ta murje mata kunyar a wuce wajen
"Ki daina kunyata,don kincemin bakison anwar wallahi banga laifinki ko daya ba,hasalima burgeni kikayi,donko nice kw abinda zanyi kenan,kawai saika rabu dani tsahon wasu shekaru ka zagaya ta bayan fage ka aureni haka akeyi?" Ta qarashe maganar tana duban anwar gamida harararsa
"Kuma ka nemi yafiyarta kukan daka sa ta dinga yi da aurenka data yi bayan bata shirya ba bata amince ba" murmushi ya qwace masa mai dan sauti,itama antyn tana murmushin ta fice ta barsu.

Shuru ya ratsa dakin na wasu mintina masu dan dama,idonsa akanta da yake lullube,zuciyarsa na masa bitar wasu shekaru can baya,yasha kwana idanunsa biyu yana wassafa yaya zai kasance duk randa shahida ta zama mallakinsa,yasha raba dare yana tsara ranar da irin abubuwan da zasu faru a lokacin,ga komai yazo ga lokacin yazo saidai cikin bahagon yanayi da dabaibayi,ajiyar zuciya ya saki a bayyane sannan ya furta cikin sanyin murya
"Tashi mu tafi" yi tayi kaman batajishi ba,yayi tsai yana dubanta,ya tabbatar taji,har tsahon minti guda sannan yace
"Kin sani sarai tun da can banason musu da taurin kai ko?,indai zaki dauki wannan dabi'ar zakisha wuya a wajena" daga haka ya miqe yayi gaba,tasan idan ta bari yafice batasan hanya ba,dole ta miqe itama ta bishi".

Bangaren ajiye motocin gidan suka isa,yasa muqulli ya bude motar ya shiga,saita soma qoqarin bude gidan baya da zummar zata shiga,lock ya sakawa qofar ba tare daya waiwayo ya dubeta ba,hakanan ta gaji da tsaiwa ya yunqurin budewar ta matso gidan gaba ta bude,a hankali ta shiga ta zauna sosai sannan ta kame jikinta waje daya bayan ta sake jan mayafinta ta rufe fuskarta,karon farko bayan wasu shekaru masu tsayi ta sake hada mazauni dashi cikin mota,gaba dayansu jinsu suke banbarakwai,kowa yanaji kamar yana tare da baqonsa ne,ya dage dukka gilasan ya kunna ac dukda sanyin dake dan kadawa a garin,ya tashi motar suka fice daga gidan.


Wani tuqi yake kaman bazasu gida ba ko kuma yana lallaba kwalta,duk da titin da sukabin fetal yake babu yawaitar jama'a sai haske fitilun titi tako ina,shuru ya ratsa motar babu me cewa komai har suka isa wani waje da sukeda saida kayan ciye ciye,kama daga ice cream,burger shawarma kaza da tsire da sauransu,saida yadanyi gaba kadan inda babu mutane sannan yayi parking,ya kashe motar ya fita.

Bai jima ba ya dawo hannunsa dauke da leda ya sakata a sit din baya,sannan ya tashi motar sukayi gaba,hannunsa ya saka ya kunna rediyo freedom wanda minti biyar ya rage su fara shirin siyasa na kowanne gauta,waqar jarumar matace ta soma plying,waqar tana taba zuciyarsa sosai,yana son ya kashe amma saiya samu kanshi da barinta tana ci gaba da tashi,sautin na karade motar yana shiga kunnuwansu cikin sauti madaidaici gami da haifarwa da kowa yanayi na daban.

Ta gefan ido ya saci kallonta,tayi laqwas cikin sit din motar,idanunta a lumshe,zara zaran gashin idanunta sun fito sosai,juyawa yayi duka yana kallonta sosai,daidai sanda ta bude nata idanun,saiyayi hanzarin dauke kanshin ya maida ga titi yaci gaba da tuqa motar cikin nutsuwa da qwarewa.


_zaku iya jina shuru gobe saboda wani uzuri daya tasomin,amma idan na samu dama zaku jini in sha Allah_
😊 _kuci gaba dai dayi mana uzuri,kana taka ne Allah na tashi,ta Allah itace dai dai,har kullum burinmu mu sauke nauyinku dake kanmu,muna godiya_ 🙏🏽*Alqawarin Allah*
3️⃣7️⃣

_ziyarci tasharmu ta youtube SAUTIN HIKIMA,don sauraren littafanmu sabbi dama tsofaffi_

https://youtu.be/H7M7h6l6wNM




A maidaidacin qawataccen wajen ajiyar motocin gidan ya ajeta kusa da 'yan uwanta biyu qasan wata rumfa,ya kashe motar can qasan ranshi yana furta
"Alhamdulillah Ala kulli haal" sai a sannan shahida ta bude idanunta tana duban gabanta
"Ki fito" ya furta yaba bude side dinshi ya fita,cikin kasala da fargaba ta bude ta fito ta soma bin bayanshi sanda yake takawa ta wata qawatacciyar doguwar hanya mara fadi sosai wadda kai tsaye ta sadasu da falon gidan.

Ci gaba yayi da tafiya bayan shigarsu falon,saita tsaya cak cikin baqunta tana qarewa falon kallon,ba wani mugun qato bane,amma wadatacce ne sosai,wanda jeran ciki ya bala'in birgeta tare da fito da kyawunsa,komai na ciki yayi kyau ya dace dashi hakanan ya dace da gidan.

Mintuna biyu ya dawo idanunsa a kanta ya mata nuni da wata hanya wadda zata sadaka da farfajiyar da dakunan baccin gidan suke
"Dukka qasan nan mallakinki ne,ga hanyar dakinki nan,duk abinda baki fahimta ba kina iya tambaya,zaki iya tafiya ki kwanta" a hankali ta soma takawa zuwa direction din daya nuna mata ba tare data bashi amsa kotace wani abu ba.

A nutsewa takebin yalwataccen dakin da kallo mai dauke da seat din gado dressing mirrow da wardrobe,sai wasu kujeru qwaya biyu masu dogon makari,daga dan qaramin carfet xuwa labule zuwa teburin mahadin kayan gadon duka dark purple ne da light ash,shima dakin ya qayatar da ita matuqa,komai ya tsaru yadda ya kamata,qamshi kawai yake fitarwa da sanyin raba,ta taka a hankali ta zauna kan daya daga cikin kujerun dake jere gefe daya zuciyarta nason soma rawa tana hana kanta,qofar dakin aka turo ta daga kai ta dubeshi sanda yake shigowa da leda a hannunsa,baice komai ba harya shigo ya aje ledar kan dan teburin wanda yake daura da ita ya fice daga dakin hadi da jaa mata qofar.

Ta jima zaune a wajen tana saqa da warwara,ta dade tana tunanin wanne irin dama zasuyi?,ta dade tana wassafa yadda zata mu'amalanci anwar din ta ina zata soma kallonsa a matsayin miji?,yaya zamantakewarsu zata kasance?,sai da jikinta ya soma gaya mata irin gajiyar da yayi ya soma gazawa sannan ta bude toilet din dake cikin dakin,shi kansa abun kallo ne,ta dinga amfani da komai na ciki yadda ya dace ta sauya pad din jikinta ba tare data nemi ta sauya kayan jikinta ta dawo ta nemi waje ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya.

Duk da gajiyar da yakeji saidaya kammala komai nashi daya saba kafin yin bacci,ya nade saman nashi gadon yana sauke nannauyan ajiyar zuciya idanunshi a lumshe kafin daga bisani ya budeshi,hakanan yakeson gidan,duk da bai kama qafar girman wanda yake ciki ba da haduwarshi gami da cin kudi ma baki daya,fili ne daya siyeshi a zamanin da yake hada kudi da qyar,a zamanin daya tara kudin tun daga qananu zuwa manya,gininsa ne kawai yayishi sanda yake cikin wadata,yanayin yadda aka tsara gidan yakan burgeshi shi kansa,ba yadda anty usaina batayi ya zauna a wancan ba tunda yafi girma amma yace a'a yafison wannan,yabi dakin da kallo a hankali idanunsa ya sauka kan ledojin daya shigo dasu,ci gaba yayi da kallonsu yana tuna wani lokaci can baya,lokacin da yake anwar din take shahidanshi,a lokacin yakan tsokaneta da cewa awara zai siyo mata duk randa aka kawota gidansa ranar farko tunda mayyar awara ce,dariya take ta sunne kanta a hijabi sannan tace
"Ko haka ka shigomin ya anwar bazan damu ba,saboda kaidin da aka bani yafi komai da zaka shigomin dashi" ajiyar zucuiya ya sauke idonshi ya sauka kan safe dinshi daya daukoshi daga gidansa ya dawo nan dashi,zuciyarsa na gargadarsa amma sai daya sakko,ya saka lambobin sirrin ya budeshi,a hankali ya ciro envalope din da har yau yadda aka kawota haka take,ko takardar bayan ba'a canza ba bare saqon ciki,har rubutun jiki yana nan baro baro kaman yadda aka rubuta din.

Zaman dirshan yayi qasan tiles din dakin,zuciyarsa na masa zafi tun bai fito da hotunan ciki ba,ya daga ya zazzagesu duka suka zubo,dai dai sanda wani abu ya tokare masa maqoshi,idanunsa suka soma sauya launi zuciyarsa na suya,haka ya dinga daga hotunan daya bayan daya yana kalla abinda ya jima baiyi ba donko sashen da suke ajiye bai fiya son kalla ba,kowanne hoto yayi a qalla minti biyar yana qare masa kallo kamar maison sanin dai dai lokacin da aka daukeshi,haka ya gama kalla baiga wani abu da zainuna akwai kuskure koba dai dai ba game da hoton,kowanne ya fito tas ya fita kar hakanan komai na jikin shahidan ya bayyana baro baro,gudun zuciyarsa yaji ya sake daduwa kansa ya soma daukan dumi,haka ya janyo envalope din ya soma maidasu ciki jin alamun hawan jininsa na neman tashi,yasan shiya jawa kansa daya kalla hotunan,amma hakanan kawai yaji kaman an tsunkulinsa kan ya jawosu ya duba,saiya miqe a daddafe ya shiga bandakinsa ya saje daura alwala ya fito ya tada sallah.

Kamar yadda ya saba kafin ya idar sanyi da nutsuwa sun saukar masa,ya daga hannu yayi addu'a sosai sannan ya shafa,saman abun sallar yaci gaba da zama,kwanan da baiyi ba kenan kan gadonshi a darensa na farko cikin gidan aurenshi,sai akan abun sallar ya kwana,wanda bai sake farkawa ba saida ya rage mintuna kadan a tada sallar asuba sannan ya sake wata alwalar bayan yayi wanka,ya bare wata jallabiyyar ya saka bayan ya feshe jikinsa da turare masu sanyi da taushin qamshi.

Har zai fice saiya tuna da ita,ya tabbatar haqqinsa ne ya kula da addininta,koma meye a yanzun tana wuyanshi,saboda haka ya sauya akalar tafiyar tashi zuwa sashen dakunanta.

A sannan itama ta farka tana gefan gado tana shirin shiga bandaki ta sauya audigar jikinta taji knocking,tasan ba kowa bane saishi,tana ji amma tayi banza kaman bata ji ba,saida yayi a qalla wajen sau goma sannan tadan ja gyaran murya kadan,hakan yasa ya gane ta tashi sai kawai ya juya ya fice zuwa masallaci.

Sanda ya dawo kashe wayoyinsa yayi baki daya ya haye saman gadon sosai bayan ya cire jallabiyar jikinsa daga shi sai gajeran wando,ya kwanta dai dai saman gadon yana sauke gajiyar da jiya bai samu saukewa ba.

Duk da gajiyar datayi qarfe tara saura taji baccin ya fita a kanta,saboda haka ta miqe ta fada bandaki ta tara ruwa mai dumi sosai tayi wanka ta dawo cikin dakin ta shirya cikin atamfa riga da zani simple mara ado,bayan mai sai powder da kwalli kawai data zizara a fuskarta,tayi daurinta sosai ta feshe jikinta da turare,dakin tadan kakkabe tayi goge goge ta sake shareshi ta dame gadonta sosai,sai a sannan ta bude qofar dakin nata tabi 'yar hanyar data sadata ta falon.

Daga tsaye take sake kallon falon,sai yanzu ta sake ganin kyau da tsaruwarshi,komai yayi mata perfect daidai da ra'ayinta,ta daga kanta ta kalli saman wanda da alama anan dakunan baccinsa suke,saita tabe

31 / 53