Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   32 / 53

93K to 96K   out of 156.9K words

baki ta juya zuwa qofar da kitchen take,can dinma komai yayi mata a tsare,gidan gaba daya babu fariyar kashe dukiya hakanan babu qaranta,karon farko tun bayan da suka sake haduwa da yayi wani abu data ji abun ya burgeta,duster ta dauko ta dawo falon shima ta saitashi yadda takeso,daga nan kitchen ta shiga,store dinsu babu komai a ciki,amma taga kayan tea da qwai,saboda haka ta tafasa shayi mai kayan qamshi ta zuba a flask,sannan ta fasa qwai ta soya,sai a sannan ta tuna da ledar jiya,ta kyabe baki ko tabata batayi ba bare ta duba meye a ciki,saita debi ruwan zafin tasha,sannan ta fito da flask din da wainar ta jera saman madaidaicin dining dinta mai kyau wanda keda kujera shida tana cewa
"Ba don halinka ba" saidata aje sannan ta koma dakin,ta janyo ledar ta duba,kayan qwalama ne irin na kowacce amarya daren farko,kazar ciki kawai ta cire ta koma da ita kitchen,ta sake mata dan hadi cikin kayan qamshin da aka kawota dashi ta jona ovean dinta ta sake gasata da kyau sannan ta cireta taje ta hadata da 'yan uwanta saman table din,ta gyare wajen ta juya ta fice,bata tsaya a falon ba ta wuce dakinta don tana tunanin ba zata rasa abunyi ba a ciki.

Cikin baccinsa ya soma jin qamshin kazar da take gasawa,bai gama farkawa ba wayar muhsin ta tadashi,ya farka yana ware hanci yana shaqar qamshin wanda yasa tsohuwar yunwarshi motsawa,saida kiran ya katse ya sake shigowa sannan ya samu damar dagawa
"Haba malam,da ba zaka daga kiran nawa ba wato tunda mun gama namu aikinko?"
"Kai bakasan haqqina ka dauka ba?,ina tsaka da baccina ka tadani?" Murmushi mai kama da dariya muhsin ya saki
"Lallaikam,su bacci manya,ai dole kayi bacci tunda ka mallaki abinda rai keso ruhi ke muradi,barcin shekara shida zakayi ai...."
"Wannan ne dalilin kiran daka yimin?" Ya katseshi gami da jeho masa da tambaya kai tsaye
"A'a a'ah,so nake ince maka ka haqura hakanan fito muje gaisuwar surukai,idan muka dawo ka dora daga inda ka tsaya"
"Ban fara bama bare na dora shaqiyyin banza,ni zaka yiwa iskanci?,dadin abundai aiba haram bane ko?" Dariya ya qyalqyale da ita
"Dama waya ce haram ne?,banda kai dakeson haramtawa kansa,kayi sauri ka fito don Allah don nikam bazan shigo gidanku ba"
"Kai ka sani" ya katse wayar ya ajeta gefe sannan ya yaye bargon da yake lullube dashi ya sauka daga gadon ya shige toilet.

Tsaf ya shirya cikin manyan kaya,yayi masifar kyau daka ganshi ango xam,saidai babu wata walwala ko qyallin goshi da hausawa ke fada.

Har yakai bakin qofar falon xai fita saiya tuna da ita,ya sake komawa ya doshi qofar dakin nata,sau hudu yana knocking bata amsa ba sannan bata bude ba duk da tana jinsa,ganin lokaci kaman zai qwace saiya juya ya fito,idanunsa suka sauka kan dining ya hangi flask akai,ya qarasa ya bubbude yaga meye a ciki,hankalinsa ya kwanta da alama taci abinci kenan,dama damuwarshi ya sauke nauyinta daga kanshi,kada ya fita ya barta bai sani ba ko bataci komai ba.

Qaramin tsaki taja tana dauko wayarta ta soma danne danne,wani saqo data gani yadan ja hankalinta saita bude,nuradden ne ya tura mata shi,yana nuna yadda yayi rashi da kuma yi mata fatan alkhairi a aurenta,data duba date din sai taga tun ranar daurin aurenta ne,reply ta masa na godiya sannan ta fita ta laluba number anty zubaida tana son kiranta,duka yau babu wanda ya kirata kamar wadda tayi baqin jini ta raya haka a ranta.

Kafin takai ga kiran kiran mubina ya shigo,ta daga ta kara a kunneta,gaidata ta soma yi ta amsa tana tambayar umma
"Anty 'yan katsina zasu koma gobe da sassafe,zan rakosu zasu miki sallama"
"To shikenan,idan kun tashi tahowa mubina,ki biya ta wajen anty zubaida ki taho min da laptop dina dana bata ajiya,zan kirata na gaya mata"
"Tohm" ta amsa mata sannan ta sata ta kaiwa umma suka gaisa,tana ji tana cewa ga daada ta katse wayar tana sane,me daadan zata gaya mata kuma bayan tayi yadda takeso da rayuwarta me kuma yayi saura?,gwara a kawo mata laptop dinta don ko aiki zata koma abinta,bata ga kuma zaman da zatayi a gidan ba,aure ne dai sun daura bashikenan ba kuma?.

Daga bakin qofar falo taji knocking,ta tashi ta saka hijabinta ta bude,dattijon dake musu gadi ne,ta gaidasji cikin girmamawa sanda shima ke qoqarin gaidata
"Alhaji ne ya aiko dasu,amma yace yaron karya shigo masa gida yana waje,zan debosu yace a aje a qofar falo idan yazo zai shiga dasu"
"Toh baba,ba damuwa" ta fada tana kaucewa tabar masa qofar a bude,koda ta dawo don rufe qofar bayan ya gama saita tadda kayan abinci ne,babu nau'in abinda babu naci da sha,hatta dasu maggi da curry,ba zata iya kwashewa ba saboda haka ta maida qofar ta rufe ta koma dakinta.

Awa biyu sai gasu mubina sun iso,matan yayyen babanta biyu dana qannen babanta uku,sai su hasina mubina da khadija,sosai ta ware cikinsu aka shiga sabgogi,suna hira da matan kawunnan nata su hasina ana gyare gyaren indai takega ya kamata a gyara din,duk suka shigar da kayan abincin store suka jera,abinda ba zasu iya dauka ba kaman manyan buhunhunan shinkafa suka barshi a falon a gefe daya da zummar idan mai gidan ya dawo ya shiga dasu tunda ya hana wani ya shigo masa bare a shiga dashi,tunda suka zo hasina minti daya biyu sai tace amarsu ta ango tana mata dariyar shaqiyanci,tana sane da ita amma tayi banza da ita,bata tanka mata ba sai qarfe biyu na rana suna shirin yin sallar azahar bayan sun gama cin abincin rana
"Amarya amarya,aina tsammaci zanzo na tadda angon naki" harara ta balla mata
"Au da kika shiga dakina baki ganshi cikin handbag dina ba?" Sosai tasa su rafi'a cousin dinta da sukazo su dukka kwashewa da dariya,har ita hasinan da aka baiwa amsa
"Banson wulaqanci,duk take takenki ina sane dashi,idan kika cikani kuwa zaki gane shayi ruwa ne"
"Allah ya baki haquru,kawai na tsammaci sai munzo mun miki ruwan zafi ne"
"Yanzu ma bata baci ba"tana amsata ta miqe ta shige bandaki donta daura alwala,tana jiyo dariyarsu,ita abunma saiya bata dariya,hasina duk yadda zata qular dakai ta iya,ina ita ina wani anwar,abinda hasinan ke hasashe akai bata tsammanin yiwuwarsa har abada a tsakaninsu,don masoyi akewa wannan halaccin,ita kuwa ta jima da cire anwar daga layin masoyanta can wani zamani daya jima da shudewa.

Tana idar da sallah mubina data barsu a falo ita da matan kawuna nanta ta shigo tana gaya mata an kawo aike,cikin mamaki tace aike kuma?,ta amsa mata da eh,saita miqe kawai tabi bayanta.

Manya manyan baqaqen ledoji ne data duba ciki nama ne da kifi danye
"kai kitchen ki saka cikin freezer dake kusa da sink"ta fada tana juyawa sama abinta,qarfe uku hasina tace bari a dorawa ango,tasan tsokanarta take,don haka ko kallonta batayi ba,tana zaune suka shige kitchen din kuwa itadai tana cikin baqinta suna hirarsu.

Qarfe biyar suka kammala lafiyayyen abinci,hasina ta bude sabbin warmers din shahida ta zuba komai ta tsarashi saman table,sannan suka gyare kitchen da gidanma duka suka soma haramar tafiya.

Ta rasa me zata basu,saita tuna salary dinta na watan nan da company ya biyata duk da batakai qarshen watan ba biyu ta raba ta saka rabi cikin jakarta,jakar ta bude ta dauko musu ta hada musu da snacks na gararta,kamar kada su tafi haka taji,hakanan ta rakosu har farfajiyar gidan,daidai sanda wasu baqin katsinan suka shigo cikin motar gidan anty usaina bisa jagorancin sa'ida,suka gaisa dasu hasina su suka wuce su kuma suka shigo ciki.

Cikin girmamawa da mutuntawa suka gaisa da juna,taja sa'ida kitchen ta hada mata kayan abinci tace takai musu,idan takai ta dawo ta dauki ruwa da drinks,sanda ta dawo shahida na ta gama shirya cups din da komai sa'ida ta qaraso tana murmushi ta dubi shahida
"Anty,baki tambayi uncle ba,yana gidanmu wajen ummi,kinsan me yacemin?" Kai shahida ta kada tanadan murmushi badon hirar ta mata ba,kawai sa'idan na burgeta hakanan
"Wai idan munje mu duba masa ke,ko kunyar ummi dake wajen fa baiji na anty,wai ki bashi abun dadi nakai masa" wato sai zaiwa siyasa kenan saboda yaga anty usaina a wajen?,lallai kam to su zuba,saita saki dan murmushin yaqe don kada yarinyar ta gane
"Nikam inajin kunyar ummi,qyaleshi zai dawo gidan ai" daga haka yarinyar ta dauki ruwa da lemo,ita kuma shahida ta dauki kofuna suka fito.

Ba laifi sun dan taba hira dasu suma,babu ruwansu kaman anty usaina,hakanan suna da girmama mutum kuma suna d sauqin kai.

Gab da za'a kira magriba don har sun soma daura alwala motar anwar ta shigo gidan,shahida na tsaye tana shimfida musu manyan abun sallah ya shigo,donsunqi shiga dakin data ce su shiga suyi sallar a can,idanunshi akanta,karo na farko a rayuwarsa daya soma ganinta a haka gayarta,ba hijabi babu mayafi,cikin riga da skert na atamfa da suka xauna mata das a jikinta,suka fidda shape dinta sosai,wani kishinta yaji ya sake kamashi sosai fiye da baya,saiya dauke kansa yana son hana bacin ranshi tasiri,duk sanda zai ganta hotunannna dawo masa,abun ya zame masa kamar jarraba,bai taba zaton yana da halittar kishi ba haka,bai tama tsammanin yana kishin wata halitta a bayan qasa kamar yadda yake kishin shahidan ba,a yanzun da take cikin gidanshi sai yake jin yayi wani abu daya dace,yake jin hankalinsa yafi kwanciya da samun nutsuwa a hakan koda ba zaman dadi bane akan tana waje ba tare dayasan me take yi kuma aina take ba,tare dawa take,duka yanzu ya samu aminci game da wannan.

Ita ta soma yi masa sannanu da zuwa,yadan tsaya suka sake gaisawa dasu,yace bari ya shiga ya daura alwala kada a kira sallah,daya daga cikinsu data ke zaton qanwar babansa ce tace
"Ai muma muna idar da sallahr xamu wuce don zamu koma mu shirya kayanmu gobe sai ta dikko dakin kara" murmushi ya saki
"Dakin kaara ko dakin kara?" Dariya suka saki ta maida masa amsa da alama akwai dan wasa haka a tsakaninsu
"Oho kai ka sani,koma dai dakin meye ta maka komai,tunda gashi sun baka mata da nan kanon suka kasa baka saida kayi kamun qafa damu,kai din kanka su suka samar dakai"
"Gaskiya ne,kin gama magana" ya fada yana dariya dariya gami da gyada kai
"Kafin ku wuce na fito in sha Allah"
"Toh babu damuwa" ta amsashi,saiya juya da dan sassarfa ya soma hayewa saman.

Tsaiwa tayi ta rasa abunyi,duk saita tsargu taga kaman kowa idanunshi a kanta yake yanason yaga ya zatayi,duk da cewa ba haka bane kowa sabgar gabanshi yake
"Jeki mana shahida?,mu ai ba baqi bane karki damu" anty aminan dake shirin tada sallah ta fada,saita miqe cikin jin kunya ta soma takawa a hankali ta isa inda hasina ta shirya kayan abinci,ta dauki jug data hada lemo ya fara qanqara shi yasa ta fito dashi,tasan wai kafin lokacin cin abincin ya huce yadda za'a iya sha,ta dauki cup daya cikin mutuwar jiki ta nufi saman ta soma taka step din,xataso ta sanya koda mayafine,amma batason tayi wani abu da zai bar alamun tambaya game da ita akan baqin,fatanta daya Allah yasa taje ta taras dashi a bandaki,shine kawai zatayi saukowarta ba tare dashi yasan taje ba,hakanan suma ba tare da sunsan cewa bata je din ba.

Qaramar varender mai kyau itace zaka soma taddawa bayan ka gama tsallake matattakalar benen zuwa qarshenta,wadda aka qawata da tiles da kuma shukes shuke na roba wanda idan ba tabawa kayi na zaka rantse da Allah rayayyu ne na gaske,cikin qananun kwandunansu masu ado suma,sai qofar glass wanda ta mamaye gabanka,daka tura zaka tadda wani ni'imataccen falo,wanda iskar dake kaiwa da kawowa ma daban take,komai na falon farine sol idan ka debe kayan kallon dake ciki,don hatta da frames masu sunayen Allah dake jikim bango farare ne,qofofine guda uku a saman kowacce tana dan nesa da 'yar uwarta.

Bata gama wannan nazarin ba taji motsi daga gefanta,ta juya saita ganshi tsaye yana cire agogon hannunshi wanda dorashi da yayi saman teburin gilashin ya bada sautin daya jayo hankalinta,ya dan dosana gefan kujerar ya cire takalmanshi hadi sa safar gaba daya ya hadesu waje daya,safar agogon takalmin da muqullin motarsa,sau daya ya daga kai ya kalleta,saiya dauke ya taka zuwa inda ya aje remote na ac ya dauka ya soma rage sanyin da take kwararowa sannan ya ajeshi.

Takawa yayi kaman zai shigeta ya wuce bedroom,sai kuma ya dakata saitinta,sunyi kusanci da yawa,tanason jan baya amma batason nuna masa tsiawarsa ta wani dameta kota dadata da qasa,idamunshi cikin nata ya sanya hannu ya dauki jug din ya daga cup daya ya zaunar dashi saman tray din dake riqe a hannunta tunda ta shigo,ya tsiyaya lemon a ciki ya aje jug din sannan ya dauko cup din yakai bakinsa,har ya gama shanyewa idanunsa na kanta,yayin da ita kuma taqi duban sashen da yake,sai daya shanye tas sannan ya aje cup din ya wuceta,sai daya dora hannunshi saman handle din sannan yace
"Baiyi dadi bama" ya tura qofar zai shige,sarai ta jishi,haushi ya cikata,takaici ya qumeta
"Dama badon kai na kawo ba,albarkacin wasu kaci,idan ka isa kuma ka amayomin da abina mana,aiba matse bakinka akayi akace sai kasha ba dama" fasa shiga dakin yayi,yayi taku uki da baya sannan ta juyo gaba daya,cikin takun nan nasa dai ya iskota,kaman xai hadeta cikin jikinsa har yanzu idanunsa na narke cikin nata yace
"Zan amayoshi,amma nima ba zakimin asarar ruwan jikina ba,saidai idan zaki shanye amanne tas" ba shiri ta ware duka idanunta tsakiyar nashi ta watsa masa harara
"Allah ya kiyaye ya sawwaqe,in sha amanka ni shahida?" Kafe juna sukayi da idanu,fuskarta na nuna bacin ranta muraran,yayin da nashi yanayin ya kasa nunawa,bacin rai ko walwala?,yaci gaba da duban qwayar idanunta,yana tuna wani lokaci can baya da ya taba zuwa mata yana zazzabi,kwananshi uku baida lafiya amma yaqi yarda ta sani don karta tashi hankalinta,duk da haka ta fahinta,ta kuma nuna rashin jin dadinta na yadda ya boye mata,tace da shine da baida zaune saiya tabbatar ta samu lpy donme ita zai boye mata?,da qyar ya lallasheta kan ya samu sauqi aisuna tsaka da fira yaji bazai iya daurewa ba amai na taso masa,ya sanar mata kan zai wuce gida,cikin damuwa ta tsaidashi tasha gabansa tana duban yadda yanayinsa ya sauya,aman ya taso masa,yasa hannu da hanzari don ya kaudata gefe amma taqi ta matsa din,da haka ya soma wanke mata jiki dashi,daqyar ya matsar da ita gefe ya qarasa a qasa,yana ta jikinta daya bata mata amma ita sai yaha ba damuwarta bane,qarshe ma dayaqi tsaiwa ta gyara wajen tace
"Idan baka bari ba wallahi kana kallo xan shanye aman gaba daya" cikin mamaki yake dubanta,qaramin murmushi ya subuce masa,ya zaci da wasa take
"Toh shikenan bismillah,amma dai ni bazan barke ki wanke wajen nan da kanki ba alhali gani a tsaye" bai ankare ba ta durqusa,cikin zafin nama ya riqe gefan hijabinta gam da mamaki yake cewa
"Kina hauka ne shahida?!,amaine fa qazanta" rai ta bata sosai
"To matsa gefe idan ba haka ba na aikata" haka ya matsa din yana kallonta ta gyara wajen.

Tunaninsa ya yanke sanda shahidan dake gabansa ta soma motsawa da alamun barin wajen dauke da farantin lemon
"Kin makaro tunda ada kinsha ai" da hanzari ta dago ta dubeshi suka hada idanu,ta tuna lokacin da yake nufi din itama,amma saita yatsina fuska kamar bata gane ba
"Kama zancan xamanin jahiliyyar shahida,kuma da ana maida hannun agogo baya da sai na maidashi na kuma goge wajen don baka cancan......" Bata kai ga qarasawa ba ta tsinci bakinta cikin nashi,ya riqe fuskarta da dukka tafin hannuwansa,ta tsorata sosai don bata zaci haka ba,garin yunqurin qwacewa ta saki jug da cup din duka suka zube anan qasa suka tarwatse,sai daya tsotse duk lips dinta da cikin bakin iya son ranshi sannan ya saketa,bacin rai a sannan ya bayyana qarara a fuskarta,ta bude baki xatayi magana cikin fushi ya rigata
"Tunda wancan xamanin ya shude ba zaki iya gogewa ba saiki goge wannan ai na sabon zamani dake wanzuwa a yanzu,ki saku reza ki yanke bakin kiyar ki canzashi da wani" daga haka ya juya abinshi,rasa amsar bashi tayi ga kuka nason qwace mata kuma bata son tayi a gabansa,saita juya da sauri zata fice,tana bude qofar yana sake shan gabanta,fuska a turbune yace da ita
"Wannan zaqin da bakinki yake ina fata ba syrup kika sha ba ko?,don nan gidan ba'a haka ciki" yakai qarshen zancan yana dage mata girarsa qwaya daya,kukan da take riqewa ya qwace mata,hawaye suka soma layi,duka girarsa biyun ya kuma dagewa
"Au....shi kika sha kenan?,sauka ki tafi to kafin ya fara aiki" ya fada yana matsawa gefe gamida kafeta da ido
"Allah yasakamin ban yafe ba" kawai tace tana ficewa cikin sassarfa,wata dariya ce taso qwace masa sanda ta fice din ya maida qofar ya tura,saiya tuna shahida 'yar 16 shekaru shida baya da suka wuce,bata da tsiwa amma bata iya bacin rai ba,baiji dadin kukanta ba amma yasan wannan ce kawai hanyar da zai sata tayi magana,tunda can mutum ne shi da bai iya gaba ba sam,duk da har yanzu bacin ranshi game da ita na nan danqare cikin ranshi amma bazai yarda ayi xaman maqiya dashi ba.

Yana kwashe fasassun gilasan yana tuna abinda ya farun,yakai tatsunsa saman lips dinsa ya shafa,yadan cije lebansa na qasa kadan,tabbas yaji zaqi a bakinta,saidai yasan ba kayan maye bane,don tunda ya bada sadakinta ya zuba ido akanta sosai amma bai taba ganin wani abu da zai sashi ya zargeta ba,ko da shahida nakan halayenta nada da idanunsa suka gani,koda bazai dore a zaman aure da ita ba zaiyi qoqarin ganin ya maidata saitinta kodon soyayya da amanna da mahaifinta ya bashi a baya,duk da hakama baiga wani mummmunan abuba game

32 / 53