Author : HUGUMA Category : African Stories & Novels
nusashesheni tun damata bata qarasa subucemin ba,haqiqa babu wani abu dake fidda damuwa cikin zuciya yasa nutsuwa irin ambaton Allah,karatun qur'ani,istigfari ko hailala,Allah ya tsaremin zuri'ata,ya karesu daga jin mummunan tarihi akaina" ta qarashe maganar abun na taba ranta,hannunta yariqo yana murzawa
"Kin karya alqawarin da mukayi,munyi dake wannan babin mun rufeshi a rayuwarki"
"Kaima alqawarin ka karya,ka maida maganar dana gaya maka nima mun rufeta,ta yaya ina lawyer dinka mai baka kariya zan tsaya ina kallonka kana laftawa kanka laifi" murmushi ya saki,wannan kalma na burgeshi,koda yaushe koda shi yayiwa shahidan laifi qoqarin bashi kariya da uzuri take,wani lokacima kanta take qoqarin maidawa laifin,shi yasa yake matuqar kiyayewa,tare dajin kunyar yi mata wani abu dazai sosa ranta
"Naji my depender....." Ya fada yana murmushi
"Au nafisa ta baki saqo" saita daga kai yana dubanta itama shi take kallo,ya saki murmushi
"Karfa ki tsorata,nifa na shahida ne ita daya,saidai wani qadarin na ubangiji,shekaran jiya danaje kaiwa umma hamdan na biya na kaiwa alhj abba da mummy shi don basusan anyi haihuwar ba,amma mummy zatazo tamiki barka,saina hadu da nafisan" shuru yadanyi sannan ya dora
"Totally ba nafisan dana sani ba,wannan nafisan cikin hijabi da sanyi,tabani saqon ki yafemata kan cutarwar data miki,jini abba zai daura mata aure,ya zaba mata miji yace bazataci gaba da zama masa a gida ba gwara tayi auren" idanunta talumshe kana ta bude
"Na yafe mata tuni komai Allah ya sauyaminshi zuwa alkhairi,Allah ya bata zaman lafiya ya hada kansu ita da mijinta"
"Amin"ya amsa yana sake shigewa jikinta
"Kinci sunanki RAHAMA,kin dade da zama rahamaa a gareni,ina fatan rahamar Allah ta tabbata a gareki,inason mu riqe daada tazauna damu saboda gaba,ina qaunar daada shahida qwarai,ta taka muhimmiyar rawa arayuwarmu duka mu biyun"
"Hakan yayi gwarzona"
"Nikam bazance miki gwarzuwa ta ba harsai ranar da kika cikashemin yara goma sha daya,har hamdan nasha biyu" zame jiki tayi da sauri ta miqe tana zaro idanu,batace komai ba sai hannu data miqa masa ya bata hamdan,donta lura da miscal din mutane iri iri a wayarta ciki harda zunnura,da alama sunzo ne suna jiranta,bai bata shidin ba,saiya miqe dashi yana cewa
"Jirana su muhsin suke sun hada walimar suna,muje na takamiki uwar gida ran gida kuma amaryata"dariya ya bata,tayi gaba tana takwa yana kodata wanda har cikin ransa,wani dadi da farincki yana ratsata,alfahari da dacen da tayi da miji irin anwar din na shigarta,ta tabbatar da cewa dai daikun mata ne keda miji irin nata,saida suka kusa gab da falo hayaniya nata tashi ta 'yan taron suna yamiqa matashi bayan ya tofesu da addu'a ita dashi
" ki kularmin da kanku keda yarona"
"Kaima ka kulamin da kanka alfaharin duniyata" a goshi yayi kissing dinta,ya tsaya yana kallonta harta shige cikin mutane,ya daga hannu yana musu addu'a gamida miqa godiya wajen Allah,ba shakka babu abinda zaicewa Allah a rayuwarsa sai godiya,ya gama masa komai ya mallaka masa duk abinda rayuwa take da buqata,sai fatan samun dacewa a lahirarsu,ta qofar baya shima yashirya yafice zuwa taron walimar suna qawatacciya da suka shirya.
*ALHAMDULILLAH*🤲🏽🤲🏽
*HAQIQA ALKAWARIN ALLAH TABBATACCENE BAYA TASHI,BA ABINDA KW SAUYASHI KOMAI GIRMA DA QARFIN IKONSA,BAKA ISA KA HANA ALLAH YINSA BA,KOWANNE BAWA DA NASHI RABON,BAZAI KUMA MUTU BA SAIYACINYESHI TAS,DON HAKA BABU GAGGAWA A RAYUWA IDAN KASAN HAKA,BABU MUGUNTA BABU RIGE RIGE WAJEN QOQARIN TOSHE RABON WANI,WANI BAICIN ARZIQIN WANI,KAMAR YADDA WANI BAI HANA WANI RABONSHI SAIDA YARDA DA IZININ ALLAH,KOME ZAKAYI A DUNIYA DAURE KAYISHI KAN TSAFTATACCIYAR HANYA,KA KAUDA KAI DAGA BARAGURBIN HANYOYI KOMAI DADINSU,HALAK ZATA TABBATA HALAK KODA KOWA BAI AMFANI DA ITA,HAKANAN HARAM ZATA TABBATA HARAM KODA KOWA NA AIKATAWA,SABON ALLAH DA HARAM TANA DA DADI,SAIDAI ILLARTA DA GUBARTA YAWA GARETA,IRIN GUBAR DA ZATA HALLAKA BAWA BA TARE DAYA ANKARA BA,KA TSARE DOKAR ALLAH SAIYA HANA KOWA YA CUCEKA,KARKA ZALUNCI KOWA SAI ALLAH YA FIDDA MAKA HAQQINKA DAGA WANDA YA ZALUNCEKA KODA SHI BAI SANI BA,YA ZAMA MAKA KATANGA KUMA MAKAEI DAGA DUKKAN SHARRIN MAI SHARRI,HIKIMAR ALLAH KENAN,KABAR ABINDA KAKE KOKWANTONSA IZUWA ABINDA BAKA KOKWANTONSA HAKA ANNABI ALAIHISSALAM YACE*
*Anan na kawo qarshen labarina na alqawarin Allah,ina fata Allah ya yafemana kurakuren dake ciki,ya hadamu a ladan yasa mu dace duniya da lahira*
*bazan gusheba saina miqa godiyata ga fans dinmu na haqiqa dake cikin dukka zafafa paid group namu,da kuma zafafa singles groups suka kasance damu cikin kowanne irin yanayi,suka qarfafa mana gwiwa kuma suka dafa mana suka riqe mana amana ba tare da sun mance da alkhairanmu ba abaya,Allah yaci gaba da haskaka lamarinsu,Allah yaci gaba da buda musu kada ya hanasu abunda zasu siya labari su hucewa kansu takaici ba tare da jira ko tsimayi ba,Allah ya amintar dasu suma a ranar da kowa keda buqatar aminci daga wajensa*🤲🏽🤲🏽
*Allah yasani duk wanda ya juyamin labarina ta wata siga ba tare da amincewata ba,koya sanyashi a wani bigire ba tare dana sani ba kama daga YOUTUBE,OKADA FACEBOOK da sauren wuraren da ban ambata bama,idan nina zulunceshi Allah ya saka masa,idan kuma shine ya zalunceni ubangijin sammai da qassai ya fini sanin hukuncin daya kamata yayi*
_Allah ya amintar damu,ya zama jagoranmu a dukka lamuranmu,kada yabarmu da iyawarmu,ya iya mana da iyawarsa,ya bamu kariya ta sama da qasa hagu da dama gabanmu da bayanmu_
*subhanakallahumma wabi hamdika,ashahadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'a tubu ilaika*🤲🏽🤲🏽
*mrs muhammad ce*👑