Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 53

6K to 9K   out of 156.9K words

safe,cimar da take burgeshi a baya,take rubuce cikin kundin abubuwan daya fiso,kunun gyada ne lafiyayye da yasha madara,sai qosai lafiyayye shima daya ji attaruhu da albasa ya bugu yayi luhu luhu kamar an saka masa qwai.

Tsam ya miqe ba tare daya ce da anty usaina komai ba ya soma sauka daga wajen
"A'ah,ina kuma zaka?" Ta tsaida abinda take ta bishi da kallo bayan ta tambayeshi
"Na qoshi anty zan wuce office ne na tuna ana jirana" maida kanta tayi tana duban kunu da qosan dake gabanta,saita sake daga kai tana dubansa sanda yake daukar wayarshi daya aje a hannun kujera dazu,ko bai waiwayo ba,ko baice mata komai ba ta fuskanci me ya faru cikin 'yan sakannin,cikin hanzari ta aje plate ta sauko,ta cimmasa sanda yake niyyar bude qofar falon don ya fice ta dakatar dashi
"Anya ko anwar anya?,har yanzu dai babu wani da zai sauya?,abun har yakai tsananin haka a zuciyarka?,anya ko wannan butulci ne kayi mata ko adalci?" Take idanunsa suka kada cikin qaramin lokaci,banda anty hasanan duk duniya baiga wanda zai tsaya ya soko masa zancanta ba tare daya kauda shi daga gabanshi ba
"Ka taba kwanciya dai dai da rana daya ka tariyo alkhairanta a gareka?,ka taba xama ka banbance aya da tsakuwa kuwa?" Kalamanta na masa wani irin suya ne a qirji bashi da jarumatar ci gaba da sauraronta saboda haka ya qarasa ficewa cikin sassarfa daga falon,ya fada motarshi ya tashe da gaggawa ya fice daga gidan.

Ta jima tsaye a wajen,dukkan wata laka ta jikinta tayi sanyi qalau,wannan wanne irin abune?,ko a mafarko ba wanda ya taba tunanin wannan kyakkyawar alaqa tarayya da abota zata juye watan watarana ta zama irin haka,jikinta ba qwari ta koma ciki ta samu d'aya daga cikin kujerun falon ta zauna tana tuna wasu daga abubuwan da suka shude cikin rayuwar muhammad da rahama.
"Ita ta rusa dukkan komai,ita ta kawo dukkan wata damuwa da baqinciki da nake kwana nake tashi da ita,ita ta butulcewa ni'imar Allah ta wulaqanta rayuwar da Allah yayi mata baiwarta" kalaman daya dinga fada kenan a sandaya samu qasan daya daga cikin bishiyoyin dake jere reras a harabar kamfanin ya faka motarsa,ya kashe wajen awa guda cur yana ciki yana qoqarin controlling kansa,yana ganin wayoyin jama'ar da suke da appointment dashi amma ya kasa daga ko guda daya,baisan me yasa yake iya dealing da duk wani daya tunkaroshi ba cikin qanqanin lokaci,amma akan wannan sabgar har yau ya kasa maida kansa jarumi,ya kasa daina jin ciwon dukkan abubuwan da suka jima da shudewq,ya kasa daina jin tsanarta,ya kasa tsayawa yayi mata adalcin dako yaushe antyn da zuciyarsa ke qoqarin gaya masa yayi mata.

Sai daya shafe awanni biyu sannan ya iya fitowa bayan ya rufe motar,ya dinga takawa ahankali zuwa babban ginin kamfanin daya mamaye iya kallon mai kallo,sauran mutane dake dakon jiranshi suka yo masa caa,yayi qoqarin ganin ya dawo da mode dinsa duk da yadda yake jin kwanyarsa a birkice.
Tsaki taja bayan ta kammala karanta saqon,kafin daga bisani ta cilla wayar gefanta,dawowarta kenan daga makaranta a matuqar gajiya ta zauna a falon,bata ma kai ga qarasawa dakinta ba saboda gajiya,gaba d'aya ta gundura da wannan d'an banzan shirye shirye da hukumar makarantarsu keyi na zuwa shugabanta,wanda ita a ganinta ko president ne zai kawo musu ziyara iyaka kenan,ta k'agu yazo ya tafi a wuce wajen,saiga saqon nuraddeen kuma wanda ta tsani gani kamar yadda ta tsani mutuwarta,batasan sai yaushe zai gaji da halin shakulaton b'angaron da take yi dashi yayi zuciya ya barta ta rayu ita d'aya ba kamar yadda ta sama ranta.

Sun riga sunyi waya da anty zubaida tasan ta fita yau bata nan,don haka girkin gidan na yau na wuyanta,ga huda da suka dawo tare tasan yunwa takeji,don ma ta siya mata cake da lemo a makaranta kafin su iso gida.

D'aki ta shiga ta tube ta fada wanka,bayan ta fito ta sanya huda itama ta shiga tayi don yau babu islamiyya,a gurguje ta shirya tayi sallar azahar sannan ta shiga kitchen.

Indomie ta soma dora musu sannan ta dora girki a dayan wajen
"Anty kin gama?" Huda data shigo yanzu ta fada tana qarasowa inda shahida ke zaune sosai qasan kitchen din tana gyara kayan miya,don ta duba nasu markadadden da suke ajewa ya qare
"Sauran kadan hudallah....dadina dake bakya juriyar yunwa"
"Anty yunwa bata da hankali,haka d'an almajiri fa yake cewa" murmushi shahida tayi wanda ya qara kyawun fuskarta,hakanan ya bayyana wushiryarta,kafin tace wani abu hudan ta sake cewa
"Anty...dama d'an wake kika yi mana,inason d'an wake" a hankali ta juya ta dubi yarinyar saboda tuna mata wani abu da tayi,yana matuqar son d'an wake a rayuwarshi,a duk sanda taga abincin ko taji an ambaceshi saita tuna dashi.*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH)KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don samun shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi*

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*AA*
0️⃣4️⃣




Kasa cewa komai tayi,maganar hudan ta cillata tunanin wata duniya can baya,wanda duk yadda takai ga hana kanta batasan sanda ta fada ba.

Sai data sallami huda sannan taci gaba da sabgar girkinta,batasan me yasa ba sam batajin yunwa,ko zancan da huda tayi ne ya cushe mata cikinta gaba daya ya sanya har walwalarta ta ragu.

Tana tsaka da kwashe abincin cikin coolers huda ta shigo da sauri hannunta dauke da wayar shahida tana fadin
"Anty ana kiranki,zata katse" ta fada tana miqa mata,bata amsa ba ta kalli screen din wayar dake hannun huda,nuraddeen ne,saita dauke kai taci gaba da juye abincin tana cewa
"Ajiyeta kawai huda,aiki nake" juyawa yarinyar tayi ta fice da wayar zuwa falo da gudu don kada cartoon din da take kallo ya wuceta.

Tana cikin kintsa wajen sallamar anty zubaida ta karade falon sannan ta taddata cikin kitchen din
"Sannu da dawowa maman huda"
"Yauwa sannunki shahida,kin ganni sai yanzu ko?,wallahi layi yau na samu....me aka dafa mana ne yau da yunwa na dawo" nuni shahida tayi mata da food flask din dake jere a wajen,ta qarasa tana budawa
"Hmmmmm,kice yau na musamman ne abincin,bari wannan sai nayi wanka zan zauna sosai tukunna na kwashi dabge" qaramin murmushi shahida tayi mai fitar da d'an sauti tana duban anty zubaidan,har takai bakin qofa ta dawo
"Au....ni kuwa kinsan nuradden na qofar gida zaune cikin mota yana jiranki?" Asanyaye ta daga kai ta dubi anty zubaidan,sai ta sadda kanta tana goge plates din data wanke zata jerasu a muhallinsu,hakan da tayi shi ya tabbatarwa anty zubaida ya kira bata daga ba kenan
"Shahida.....wannan wacce irin rayuwa ce kika daukarma ranki?,mai sonka fa ya wuce ka wulqantashi,laifin wani dama yana shafar wani?" Shuru ta sake zabar tayi,saboda tana ganin sun gaza fahimtarta ne gaba daya,ta yiwa soyayya hidima,ta yiwa soyayya halacci,ta yiwa soyayya dukkan wata kara da alkunya,qarshe data tashi ita mai ta bata?,data tashi da wanne sakamako tazo mata?,sunfi kowa sani saboda haka sunfi kowa amsar dukka tambayoyinta,ko daya bata tsinci komai cikin soyayya ba face tsantsar butulci mummunan sakamako da kuma mummunar makoma,shin ta yiwa kanta a dalci kenan idan ta sake cusa kanta a wannan bigiren?
"Nidai ya roqeni alfarma,saboda haka idan na isa dake ki leqa ko gaisawa ne kuyi" zancan anty zubaida ya katse tunaninta,daga haka bata sake cewa komai ba ta ida ficewa daga kitchen din,tana jinta sanda ta kira huda suka haye sama tare,tasan kuma tayi hakanne don sanin halinta,ba qaramin aikinta bane ta fita ta baro masa huda ta cikashi da surutu wanda idan ya gaji da zama yake sallamar huda shima ya wuce nashi guri.

Anty zubaidan tafi qarfin komai a wajenta,don haka ta dauraye hannayenta ta wuce dakinta,ta zari hijabi ta saka ta sanya slipper dinta ta wuce qofar gidan.

Kamar kowanne lokaci yana zaune cikin motar,bayanshi jingine da seat din kujerar dayake kai,da alama ya jima zaune a wajen,duk da haka ganin fitowarta bai hanashi miqewa ba yana sakar mata murmushi harta qaraso
"Barka na tunda na samu kin fito" ya fada tamkar wanda baiyi zaman jiranta ba
"Inda kayi aiki da shawarata tun a karon farko da duk bamu kawo wannan matsayin da muke kai yanzu ba" ta fada kanta tsaye tana dubanshi,kafin daga bisani ta janye idanunta,har ga Allah wulaqanta dan adam ba dabi'arta bace,zatafi kowa farinciki idan har noraddeen ya janye daga qudurinsa daga kanta,ga sabanin tunaninta sai taga ya saki murmushi
"Bani da damuwa shahida,nasan cewa mahaqurci mawadaci,zan iya jure koma meye indai a kanki ne shahida" idanunta ta lumshe tana jin kamar jiri zaya kada ta,a rayuwa yanzu babu abinda ke damunta sama da matsalar nuradden,ya soma shiga jiki da zuciyar makusantanta,bata da buqatar a yanzu dukkan abinda zai kuma d'aga ma rayuwarta hankali.
"Koma meye tabbas mai wucewa ne watan wata rana" furucin nuradden ya sake ratsa dodon kunnenta,a sanda take kiciniyar dai daita kanta
"Don Allah.....shahida inason ki bani dama,ki saurareni koda wayata ce kadai ki dinga dagawa,bazan takuraki kan koda yaushe saikin fito na ganki ba,amma ki daga wayata,hakan kadai ya isarmin....don Allah" ya fada yana hade hannayensa waje d'aya alamar roqo
"Naji ya isa,ka sameni ta wayar" ta fada tana juyawa don ta shige gida kamar wadda take kan qaya ko wuta
"Tsaya mana shahida....." Yayi hanzarin fada,tsayawa tayi cak kamar yadda ya umarta,saidai bata waiwayo ba a haka ya cimmata,gabanta yasha,yana murmushi ya miqa mata wata leda
"Ga wannan,ki karba don Allah....." Batason doguwar magana saboda haka ta saka hannu ta amsa kawai ta shigeshi,kallo ya bita dashi yana jin dad'i cikin ranshi,yau an samu wani ci gaba da har shahida karo na farko ta amshi abun hannunsa,tabbas watarana yana saka ran komai zai wuce,bai taba tsammatar tsintar kanshi cikin soyayya makamanciyar wannan ba,saidai shahida ta cancanci komai,tana da nutsuwa tana da hankali uwa uba kyau,shahidan tayi masa,tako ina ta amsa sunan irin macen da yakeso,yake da burin mallaka,macen da cikin dubu sai an duba.

Tana shiga a nan falo ta ajewa huda ledar,tace ta dauka ta bata,tana jin huda na tsallen murna da kacaniyar bude ledar tawuce dakinta ta hau sabgar gabanta,duk don ta yakice komai,wanka ta soma yi,sannan ta jawo plate din abincin data shigo dashi daxu sanda zata fita wajen nuraddeen din ta soma tsakurar abincin ciki,ci take kawai,amma ko za'a rutsata da bindiga batasan wanne taste ke ga abincin ba,tana cusa wa ne kawai maganin yunwa,duk sanda taji irin wannan yanayin tattare da ita tasan cewa can cikin zuciyarta ba lafiya qalau take ba,ta hanata kanta dukkan wani tunani,ta bude jakar makarantarta ta dauko exams din dalibanta ta shiga marking tana shigarwa cikin paper din dake dauke da sunayensu.

Tana tsaka da haka wayarta dake aje can gefe ta soma haske,don dama abadan wayarta a silent take,batason wani qwaqwwaran motsi da xai dameta,daga kai ta dubeta,kamar ba zata daga ba saita miqe tsam tace ta duba,anty amina sunan dake yawo saman screen din kenan,dan qaramin murmushi ta saki wanda bai bayyana ba koda saman fuskarta ba bare mutum ya gane,saida ta bari wayar ta katse da kanta sannan tabi kiran
"Ranki ya dade yallabiya,don naga alama kin xama hukuma saida lallashi,kinbar rayuwar kowa bare ki nemeshi ko?" Wani murmushin ta kuma saki wanda yafi ja daxu armashi fa bayyana,sai data koma ta zauna inda ta tashi sannan tace
"Ni na isa,ta yaya zan manta da anty amina ta?" Ta fada tana tura hular kanta zuwa baya,hakan saiya qara fidda kyanta,sakamakon gashinta mai santsi daya bayyana
"Gashi kuwa?,kin d'aura aniyar mantawa dani din?,anya duniya da amana kuwa shahida?" Duk sai komai ya tsaye mata cak,duk da cewa gaskiya anty aminan ta fada,abinda bata sani ba tana gujewa kiranta ko haduwa da itane,saboda tana daga cikin abubuwan dake tuna mata baya,wanda take ra yaqi shafe komai shekara da shekaru
"Yanzu dai ayimin afuww,inayini anty amina mun yini lpy?"ta fadi tana kada biron dake hannunta hagu da dama
"Lpy alhmdlh....ya gida?"
"Lpy qalau muke,ina yarana?"
"Yaranki duka sunyi fushi" murmushi ta sake saki
"Suyimin afuwa,ina nan zuwa,zuwan ba zata"
"Haka dai,kullum maganar kenan,fafur kin qimu kin gujemu,na rasa ma LAIFIN NA WAYE?" jin anty aminar nason fadawa wani bigiren na daban ya sanyata soko wata hirar don kauda waccar maganar
"Zan baku mamaki anty amina,kedai ki sharen hanya"
"Yo sharar hanya kuma ta nawa,na share na share har na gaji,kedai sai an ganki kawai" sai ta miqawa yaran nata wayar suka shiga gaisawa d'ai d'ai da d'ai,su dinma bikonta sukeyi duk tace musu tana nan zuwa susha kuruminsu,daga bisani suka miqawa mamarsu wayar suka dan sake tattaunawa sannan sukayi sallama da juna.

Tana shirin aje wayar wani kiran ya sake shigowa,anty zubaida ce take kiranta
"Ki sameni a falo" ta fada kawai ta yanke kiran,saita sauke wayar daga kunnenta tana miqewa tsaye ta gyara daurin zaninta,tana zura hijabinta wayar ta sake haske,nuradden ne ke kira saita dauke kai ta qarasa saita hijabin nata ta fice a falon.

Abbi anty zubaida da huda ne zaune gaban kwanukan abincin,kamar yadda al'adar abbi take bai hawa dining saidai a sauke masa abinci a qasa a shimfida masa table mat,yanzun ma abincin suke ci,ta qarasa cikin nutsuwa ta zauna gefan huda tana gida abbun,ya amsa mata fuska a sake kamar kullum yana tambayarta dalibai,murmushi tayi ta sani sarai baison koyarwar da take ko kad'an,amma ya haqura ya bata damarta don baison ya tauyeta ko ya hanata abinda ta zabawa kanta,duk da cewa tana koyarwa ne bisa wani sharadi da bata tunanin ma akwai randa sharadin zai gindaya yayi sababin afkuwar barinta makarantar
"Wannan kayan da kika baiwa huda fa?" Cewar anty zubaida tana nuna ledar da baki,waiwaya tayi yana duban ledar don sam ta mance ma tayi kyautarta,kunya ce ta dan kamata ganin kayan da suke ciki,katuna ne masu dauke da kalaman soyayya sai sauran tarkacen kaya da suka shafi masoya,idan ma akwai abinda ya shafi huda a ciki bai wuce choculet masu tsada dake ciki ba,dan satar kallon uncle abbu tayi taga shi sam hankalinshi ma ba'a kansu yake ba,saita maida wajen antyn
"Ki cire mata choculets din saiki ajemin sauran kayan"
"Eh da yake ni aka bawa ko?,to tattara kayanki ki bar wajen dasu tun ban gayawa abbu abinda kike yi ba" da hanzari ta miqe tana miqawa anty zubaidan ban haquri da ido,haka ta tattare kayan tana jin kamar ta watsar dasu a wajen
"Yaushe zakuyi hutu ne khadija?,inason wannan karon kuje kankia kuyiwa su dada hutu,tanata qorafin kin yada su gaba daya bakya ta tasu"
"Kwana uku ya rage,donma sun tsaya jiran zuwan mai makarantar ne"
"Na qagu abbu ranar tazo wallahi...." Cewar huda cikin zumudi,waiwaya shahida tayi tana duban hudan,batasan me yasa take yawan zumudi da zuwan mutumin da kowa yake masa shaidar baida sauqi ko rangwame ba,kamar anty zubaida tasan tadin me take a ranta tace
"Oh hudaaaa...irin wannan zumudi kullum zancanki kenan?"
"Ummi....yana da kirki wallahi,yanasonmu,idan yazo kowa sai an bashi chaculets masu dadi da biscuits manya manya"
"Sarkin kwadayi...." Abbu ya fada yana lakuce mata baki,dariya sukayi gaba daya
"Ina tunanin randa zakuyi hutu ranar su faruq zasu dawo suma" abbu ya fadi yana zuba lemo a cup,shahida dake niyyar barin falon ta dakata,fuskarta qunshe da murmushin data kan jima bata yi ba,tayi kewarsu sosai,duk sanda suka koma makaranta gidan baya mata dadi,tace
"Abbu amma baka gaya mana ba sai yau?" Dubanta yayi,yana mamakin shaquwarsu
"Eh,saiku hanamu sakat da shirin zuwansu,kaman su kadai ne mutane a gidan" ya qarashe zancan nasa yana duban anty zubaida,tasan sarai su yake tsokana ita da shahida,don haka ta dauke kai kaman bata jishi ba,murmushi mai sanyi shahida ta saki ta juya tana ci gaba da tafiya
"Allah ya dawo dasu lafiya"
"Amin" ya amsa,huda kam ta kasa zaune ta kasa tsaye,yayun nata kamar qawaye suke a wajenta,ita daya ce mace banda zuwan shahida gidan itama idan suka koma makarantar ita kadai ke watangaririya a gidan,saidai idan ta gaji ta gudu gidan kakanninta na wajen uwa.

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

A nutse yake kai abincin bakinsa,yayin da rabin hankalinsa ke kan wayarsa dake aje gefan plate dim abincin,zaune take kan kujerar dake fuskantar tasa,tasha kwalliya iyaka,kai kace zata je wajen wata dinner dinne,cikin dinkin lace riga da skert take,hannayenta gaba daya biyun ta tallafe kumatunta dasu,yayin data zuba masa idanunta,duk wani wani motsinsa yana yinsa ne kan idanunta,batasan wanne kalarso take masa ba arayuwa,saidai koma meye tasan cewa son da take masa wani bangarene mai girma a rayuwarta.

Kanshi ya daga daga wayar yana sake kai wani spoon din abincin bakinsa,sai a sannan ya lura da irin kallon da take masa
"Hey!" Ya fada yana murza yatsunsa,hannayen ta sauke tana dan qaramin murmushi bayan ta sauke ajiyar zuciya
"Kallon fa?" Ya tambayeta a taqaice,muryarta cikin rauni da nuna fargaba wanda ya wanzu har saman fuskarta tace
"Ina tsoron kar na rasaka anwar,ina jin kamar watan watarana zan rasaka" ta fada can qasan ranta tana jin kishinta na cin zuciyarta,tana jin kamar zata dawo rayuwarshi ta rabasu,ta san cewa a yanzu sun yiwa rayuwar juna nisa saidai ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali duk da haqarta ta cimma ruwa,aje cup din da yayi niyyar kaiwa bakinsa yayi,ya hade hannayenshi waje guda gami da saka yatsunsa cikin na juna
"Meye abun jin tsoro a ciki?" Kai ta kada tana gyara zamanta bayan ta goya hannayanta a qirji
"Kai din kalar namijin da kowacce mace keso da buri ne,don me bazanji tsoron kar a rabani dakai ba?" Bai bata amsa ba sai kofin daya aje dazun yanzu ya sake dauka,yana mamakin yadda take daukar abubuwan da suka shafe shi da girma haka,saidai har yanzun baya jin wani feeling na daban ko na musamman tattare da ita,yana dorata ne kawai bisa mizanin wasu abubuwa da martabarta ke alaqantuwa dasu
"Shine dalilin kenan da kikai qorafi wajen anty hasana?" Ya jefo mata tambayar yana kafeta da ido,gefe guda kuma yana karantarta a fakaice
"Aure kikeso?" Kai tsaye ta gyada masa kai a sanyaye tana mai fata da addu'ar cikar burinta,shuru ya ratsa na tsahon

3 / 53