Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 53

42K to 45K   out of 156.9K words

Sautin fitar murmushinsa shi ya soma dukan kunnenta,bisa alama wani cikin daliban ya fadi abinda ya bashi dariya
"To shikenan...next question....who is the best teacher in dis school?"
"Anty rahama...aunty rahama!" Suka hada baki dukkansu suna fada,abinda ya sake sashi dariya qwarai,irin dariyar daya jima baiyi irinta ba,baisan wanne irinso yaran kewa malamar tasu ba,komai anty rahama anty rahama,wai wace anty rahama nan
"Auntyyy" wasu daga cikin yaran da suka hango tsaiwarta bakin ajin suka fada cikin shauqi da nuna qauna tamkar sunji tambayar da yakewa kanshi,duban yaran yayi sannan a hankali ya waiwaya yana son yaga wace.

Shahida....shahida ce dai tsaye cikin shigar kamala ta lafaya,jakarta rataye a kafadarta idanunta saye da farin gilashin daya zamto yana taimaka mata wajen gani,sakamakon matsalar idanu da taso gamuwa dashi tun shekarun baya saboda yawaita kukan da take,wani irin abu yaji yana zagayawa saman kanshi,tsigar jikinsa gaba daya ta zuba,zuciyarsa ta kasu kashi biyu,kowanne sashe na zuciyar tasa da abinda take ayyanawa.

Gaba daya jin jikinta tayi tamkar an zare dukkan wata laka data yi saura,,nutsuwa tayi qaura daga jikinta a take,idanunta cikin nashi a hankali taga yana juye mata daga anwar data sani zuwa wani mutum daban,matashin saurayi mai kyau kwarjini kamala da haiba,matashin saurayi daya jiqu da hutu da naira,matashin saurayi mai cikar zati,tsayayyen namiji wanda tambarin ilimi nutsuwa da wata qasaita ta daban ta bayyana muraran kan fuskarshi,dukkan wani abu daya gani tattare da ita shekarun baya suka soma dawowa idanunshi daya bayan daya,hotunan da idan ya tuno dasu suke hanashi bacci duk dare,ganinta cikin halin maye,jinin zubda ciki na gangarowa daga qafafunta,yaci gaba da kallonta yana takowa inda take tsaye cak,sai yaga kaman a sannan ne abinda ke jikin hotunan ke faruwa,take cikin 'yan sakannin da bai wuce ka qirgasu da yatsunta biyu zuwa hudu ba idanunsa ya sauya launi,jijiyar kanshi ta motsa ta tashi,sai daya zo dab da ita sannan yace
"Kina nufin a haka zaki baiwa yaran mutane tarbiyya?,a haka kike koyar da yaran jama'a?,na tambayeki ma me kike koya musu?,uhmmm gayamin,?,yadda zasu....." Sai kuma ya kasa qarasawa ya kaiwa iska wafta da hannunshi sannan ya dunquleshi tsam kaman zai tatse dukkan jinin dake cikin hannun nashi gaba daya,dai dai sanda shugaba kula da dukka sashen makarantar ya iso ganin shuru har yanzu bai iso ba,cikin girmamawa ya rusuna
"Sir....."
"Dakata!" Ya tsaidashi cikin tsawa
"Dama irin wadan nan malaman kuke baiwa yara su koyar?" Cikin mamaki ya dubi shahida da yake nuna masa,wadda take tsaye qam a wajen kaman an dasata idanunta kan anwar,tana jin wani fushi na ratsata amma tana ta qoqarin hana hakan tasiri
"Sir.....kodai wani akasi aka samu,amma malama shahida na daya daga cikin malaman da kaf makarantar nan babu kamarsu a kowanne sashe"
"Sauraramin" ya kuma dakatar dashi wannan karon har yana daga mishi hannu,ya maida idanunsa cikin nata
"Indai wannan ce malamar da babu kamarta tabbas bakusan abinda kuke ba,babu abinda ta iya!,bata iya komai ba!,daga yau na koreta!,na koreta cikin malaman makarantar nan.....kar qafarki ta sake tako mana makaranta,you are fired!" Dukkan wani qwarin gwiwa da taso tattarowa ya tarwatse da kalmarshi na qarshe saboda yadda sautin ya fito ya bada amsa kuwwa cikin ajin,qoqarin tattaro abinda zata fada take saidai bakinta ya gaza fidda sautin saboda karayar da zuciyarta tayi,idanunta suka hada qwalla fal suna shirin ga gangarowa,saiya sake saka idanunsa cikin nata cikin wani qwarin gwiwa da yake ji yace
"Uhmm...kina da wani abun cewa ne?....say it....say it mana!" Ya kuma fada cikin hargagi yana dan dukan qirjinsa da yatsunshi gaba daya,jakar dake kafadarta ce ta sulmiyo saboda yadda jikinta ya soma rawa,gaba daya kayan ciki suka tarwatse a wajen ciki harda kwalaben magungunan huda,a kansu idanunsa suka soma sauka,wani tashin hankali da baisan na meye ba ya rufto masa,saiya daga kai da sauri yana kallonta,sam ko daya bata da nutsuwar da zata iya tsaiwa ta tattare kayayyakinta ko ta dauki jakar,hakan yasa ta juya da sauri ta soma takawa,fatanta da burinta kawai shine tabar makarantar,tabar wajen,tabar inuwar da anwar yake tsaye a cikinta,burinta shine ta nesanta dashi kawai,ta daina ganinsa ta kuma daina jin sautinsa
"Ki dawo ki debi wannan kayan zatar naki" maimakon dawowar kamar yadda ya buqata saita qara sauri kamar wadda aka biyo,don burinta shine ficewa daga makarantar ta tserewa sautinsa,wannan sautin da ta jima da neman tsari dashi da mamallakinsa.

Titi kawai ta miqa bata ko waiwaye,bata buqatar abun hawa don ji take kaman qafafunta zasuyi mata aiki fiye da abun hawan,sauri kawai take zubawa wani irin radadi na keta zuciyarta kamar ana yankarta da reza,anwar dai anwar dai?,tabbas da tasan akwai wata rana da zasu sake haduwa kaman haka da tuni ta yiwa kanta kandagarki da ita,wannan wace irin baqar rana ce a wajenta
"Anty shahida...anty shahida" taji ana qwalla mata kira wanda sam bata tsaya ba har sai da akasha gabanta,shugaban sashe ne riqe da jakarta ya miqa mata
"Don girman Allah kiyi haquri anty shahida,ya dauki hukuncin da dukkanmu bamu isa mu sauya shi ba"

👑*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina buqatar siya ki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*kuyi subscribing youtube channel dina don samun damar ganin shirye shiryenmu,subscribe kyauta ne!*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos


*Alqawarin Allah*
1️⃣9️⃣


"sabon abune wannan a wajenmu,abinda bamu taba gani yayi ba tunda muke dashi,kowa ya shaidai wannan kirkin nasa....anty shahida kodai wani abu kika masa?,mutumin qwarai irin haka canzawarsa...."da sauri ta yanke masa hanzari
"Na gode malam,haka Allah ya qaddara" gaba tayi da sauri don ita kadai tasan me take ji,ita daya tasan ya take ji,baifi taku biyar ba adaidaita sahu tasha gabanta tana tambayarta ina zata je?,sai data shiga sannan ta gaya mishi inda zai kaita,duk yadda taso daure zuciyarta ta bari saita isa gida saita kasa,ta tattakura ta rushe da kuka wanda har sai da dan sahun ya waiwayo
"Hajiya...lafiya?,kiyi haquri komai yayi zafi maganinsa Allah" ita dai bata iya tanka masa ba illa kukanta data ci gaba dayi.

Komao nata ta wurgar tsakar dakinta sannnan ta zauna dirshan tana risgar kuka,tanajin kaman ranta zai fita ne,duk wata nutsuwarta a yanzu babu ita,anwar dai shi idanunta suka gani?,anwar shine ya mata wannan tozarcin?,wanne abu tayi mai munin da har zaikai anwar ya kasa mantawa irin haka ya sake binta da mummunan shaida da wulaqanci?.

Kusan haka ta dauki dogon lokaci,wanda ita din batasan wadanne awanni ta shafe haka ba,sai tsintar muryoyin anty zubaida tayi da huda,taso qwarai ta tashi amma ta kasa saboda wani mugun ciwo da kanta yake mata,da qyar take iya motsawa bayaga idanunta da suka zama tamkar fulawar da aka zubawa yeast,muryar saddiq taji yana cewa
"Mummy...tana dakinta" a hankali anty zubaida ta turo qofar tana cewa
"Alhmdlh,shahida kin daga mana hankali,ina kika shiga haka ke kuwa don Allah" ta qarashe maganar tana qarasowa kanta,zaro ido anty zubaida tayi ganin irin rawar darin da take yi
"Subhanallahi,ashe bakyajin dadi" ta qaraso gefan gadon shahida ta zauna tana qoqarin yaye rufar da tayi,da qyar da taimakon anty zubaidan ta tashi ta zauna sosai,qarya tayi mata kan tana shiga makaranta zazzabi ya saukar mata shi yasa ta dawo bata kai ga zuwa dakin hutun ba ganin yadda duk suka damu daga anty zubaidan har su saddiq,farouq anty zubaida ta saka ya hada mata ruwan wanka,saddiq ya zubo mata abinci,ita taimaka mata ta shiga bandaki tayi wanka gami da daura alwalar sallar azahar da magariba da duka bata samu yinsu ba,bata bar dakin ba sai data ga taci abinci ta kuma sha magani sannan.

Tana daga kwancen amma hawaye take sharcewa masu dumi,duk yadda taso ga kaucewa anwar da shafe duk wani abu daya shafeshi amma haka yaci tura?,wai sai yaushe?,sai yaushe zaibar rayuwarta zuciyarta da kuma ruhinta ya huta?wunin ranar gaba daya wani irin wahalallen yini tayi,ba shakka anwar ya zamewa rayuwarta babban qalubale,har zuwa dare tana cikin yanayi guda wanda da qyar da sudin goshi ta samu wani wahalallen bacci ya dauketa.

********* **********

A hankali ya daga cup din qarshe na coffe din da yayi saura ya kwankwade wanda shi kansa baisan kofi nawa yasha ba tsahon awannin daya kwashe zaune a wajen,idanunsa jajur suke kai kace an badawa idanunsa yaji ne a ciki,saidai yaqi yarda ko kusa ko alama a kira masa likita ya dubashi,bugu da qari dumin jikinsa ya qaru sosai har kana iya juyo hucinsa idan ya fidda iska daga bakinsa.

Lumshe idanunsa yayi ya dora hannunsa saman sumarshi mai tauri saidai a gyare take matuqa yana yamutsata,buri yake inama ya iya kuka idan yana cikin tashin hankali ko tsanani,inama hawaye zasu fita daga idanunshi ko zai samu sauqin radadin da yake ji?,cikin sauri ya sake bude idanun shi wanda suka sake kadawa fiye da dazu,ko yaya ya runtsesu kwalaben da suka zubo daga jakarta yake gani,hakan yana nuna har yau bata bar dabu'arta ba?,waishin waye ne?,waye ya koya mata wannan dabi'ar?,babu shakka da zaisan waye shida ita duka saiya hadasu ya hukuntasu,dukan teburin gabansa yayi da hannunsa ko zaiji sauqin radadin da zuciyarsa ke masa amma a banza.

Knocking katafariyar qofar falon aka somayi wanda yana ji yayi funfurus,saidai ya cika ya batse saboda koma waye yana son sake birkita masa lissafi ne,bayan kuma ya riga da yaja kunnen duka ma'aikatan gidan na kada wanda ya sake yako doshi sashensa.

Knociking din jinsa yake har qwaqwalwarsa,hakan ya sanya ya miqe a fusace ya isa qofar ya budeta ya kuma bude baki don zazzagewa koma waye masifa,muhsin ne bayanshi likita ne tsaye cikin fararen kayan aiki,dole ya hadiye abinda yaso amayarwa ya saki qofar ya juya zuwa cikin falon ya zabi wata kujerar sabanin wadda ya tashi daga kai ya zube yana maida numfashi,kallo daya muhsin yayi masa baice dashi komai ba ya kalli likitan sannan ya maida idonsa ga anwar din
"Zaka iya aikinka" yace dashi,saiyaka jinjina kai ya soma takawa inda anwar ke zaune ya aje akwatinshi kana ya bude,ya ciro abun gwada B.P ya daura a hannun anwar ya soma gwadawa,cikin sakannin da basu wuce goma ba ya warware abun daga dantsensa ya samu kujerar dake daura dashi ya zauna sosai idanunsa a kanshi
"Yallabai....kasan yadda jininka ya sake hawa kuwa?" Ya tambayeshi kanshi tsaye
"Na sani" shima ya bashi amsa bayan ya sake bude dukka idanunshi akan likitan,cikin mamaki likitan ya maida dubanshi ga muhsin,saiya masa alama daya rubuta magani kawai ya qyaleshi,hakan kuwa akayi ya rubuta maganin ya baiwa muhsin takardar sannan ya tattara kayanshi ya yuwa muhsin din sallama ya wuce.

Sai daya tabbatar da fitar likitan sannan ya miqe riqe da takardar maganin ya qaraso inda anwar din ke zaune,idanu ya zuba masa yana kallonsa wanda hakan ya sanya anwar kau da kai
"Tsahon shekaru kana fama da wannan damuwar,kaqi gayawa kowa dalilinta,kaqi gayawa kowa dalilin faruwarta,duk dai amma bazai wuce akan shahida ba,anya kuwa anwar anya?,me yasa kake shirye shiryen halaka kanka ne babu gaira babu dalili?" Zumbur ya miqe ya soma takawa don barin gurin
"Kar sake cewa dominta ne,na riga dana shafe babinta kamar yadda na shafe babin komai daya faru dani a baya" qara sauri yayi ya wuce zuwa bedroom dinsa yanason baiwa kansa qwarin gwiwa don baison ma anty husaina taji cewa baida lafiya,yanzu dukkan tsofaffin matsaloli zasu taso,magana wata nabin wata har sai yaji kaman kanshi zai tarwatse.

Kwananta goma sha hudu tana qoqarin saisaita kanta da maida kanta cikin yanayin daya dace,yaqi tayi ba dan qarami ba a kwanakin da kanta,ta rame qwarai saboda jinya tasha sosai,bata fita ko ina,hakanan hatta da wayarta ma a kashe take,daga daki sai daki,sam anty zubaida batasan meye ya faru ba,saidai dukkaninsu tattalinta suke har ta soma jin dadin jikinta.

Ranar wata karaba qarfe hudu na yammaci ta fito daga dakinta,gidan yayi mata shuru haka yayi mata fadi,haka take ji duk sanda su huda suka wuce islamiyya saisu barta daga ita sai anty zubaida kawai,hakan ya sanyata tunanin samo islamiyya itama da zata dinga zuwa daukan karatu,don sanda ta fada din anty zubaida dariya ta dinga mata
"Ohni zubaida,shahida bansan inda zakikai wannan son karatun naki ba" murmushi kawai tayi
"Anty karatu fa baya yawa,indai ba mutuwa kayi ba ilimi bai yanke maka ba,ba zaka rasa cin karo da wani abun da baka sanshi ba"
"Gaskiya ne" ta fada cikin nuna gamsuwa.

Sanye take da atampha riga da zani wrapper,sai qaramin mayafi data yane kanta dashi,ta sake haske haka ta fada,a hankali take takawa har zuwa cikin ainihin falon,babu kowa kaman yadda ta zata,sabida haka ta juya ta nufi kitchen don tasan a wannan lokacin anty zubaida tana can.

Da sallama a bakinta ta shiga da dashasshiyar muryarta irin ta marasa lpy,anty zubaida ta juyo tana amsawa fuskarta qunshe da murmushi
"Patient an taso kenan"
"Wallahi anty...na gaji da kwanciyar nan" ta furta tana jan kujera ta zauna akai
"Ai gwara ki tattaka ko zakiji dadin jikinki" sama sama suke hira ita da anty zubaidan,inda tana daga zaune ta amshi wasu ayyukan tana tayata,a haka su faruq suka dawo daga islamiyya suka tarar dasu,zama sukai cikin kitchen din suma,saidai basu bar bakin anty zubaida ya huta ba,wannan ya buda wancan wannan ya buda wannan wai duka yunwa sukeji,sudai tunda anty shahida ta soma lalura kawai gidan sai a slow,waiwayowa anty zubaidan tayi
"Kinga shahida...don Allah debe qannenkin nan ku bani waje na yafe taya aikin wallahi" dariya shahidan ta bushe da ita sannan ta miqe tana duban su huda
"Oya....lets go" ta furta tana kada hannunta,ba musu suka bita a baya suka fice zuwa falon.

Haidar ne ya soma canza tasha zuwa mbc bollywood faruq yace sam shi mbc action xai kalla,huda kuma ta tubure ita mbc three takeso
"Dalla malama matsa kona kwada miki mari" faruq ya fada yana duban huda gami da zare mata ido
"A'ah wallahi,dalili dame?,bani remote din gaba dayanku na raba gardama
"please anty" faruq ya fada cikin langwabe kai yana miqa mata remote din,ta gane me yake nufi,saita basar tana cewa
"Babu wanda za'a kamo zabinsa,zabina kowa zai kalla" gwalo kowa kema dan uwanshi,tana murmushi ta kamo TVC news kwana biyu tayi missing labarai bata samun kalla,tana jin haidar na gulmarta
"Miss news" ta waiwaya ta kalleshi
"Zamu hadu anjima" da sauri ya dawo ya fasa hawa saman da yake qoqarin yi
"Sorry my aunty kar aji kanmu,niba dake nake ba,Allah kwana biyu dama da baki da lafiyar nan duk sanda ustaz zai karbi hadda fecewa nake kar 'yammatan ajinmu su min dariya...ki taimakeni"
"Saika biya cin hanci"
"Na yarda" ya fadi yana dariya,idnunta a kansu sanda suke wucewa dakunansu don sauya unifoarm dinsu,saida suka bace mata sannan ta janye idanun nata tana sauke ajiyar zuciya,duk sai taji kaman ita kadai keda matsala,takura da quncin zuciya,tana son ta rabu dasu amma ta rasa me yasa qoqarinta ya gaza?.

Ganin cewa suma ba labaran suke ba saita sauya tasha zuwa FASHION TV,sabuwar tasha ce amma tana tashe kuma ta samu karbuwa wajen al'umma sosai,sukan nuna abubuwa kala daban daban,kama daga sutturu na zamani,bukukuwa,birthday,engagment da sauransu,wani lokaci tana son kallon tashar saboda takan debe mata kewa,wasu abubuwan da suke nunawa na burgeta.

Yauma ta tadda suna hira da wata mai gyaran jiki shuwaarab cikin harshen turanci,shirin ya qayatar da ita sosai,ta bada dukkan hankalinta akai,sai suka yanke suka tafi talla,tallan farko da suka sako na engagment din wasu igbo ne,tsaki taja tana gyara zamanta saboda sam bata ji dadin tafiyarsu hutun ba,cikin ranta tana ganin rashin aikinyi ne kawai da zaka tsaya batawa kanka lokaci saboda an maka egage da wani,wai itama soyayyar nan gaba daya meye zaqi ko ribarta?,ta sake jan tsaki sanda aka nunosu suna bayyana yadda suke son juna da farincikinsu da kuma saqon godiya ga duk wadanda suka halacci bikin engage din nasu,remote ta dauka da niyyar sauya channel idan sun gama ta dawo,talla na gaba da suka fara haskowa sai yaja hankalinta matuqa fiye da komai,engage ne na wasu couple da za'ayi musulmai masu cikakken sunan hausawa,hoton farko na amaryar ne tayi kyau cikin shiga ta alfarma,wanda kallon farko idan kayi mata zaka tabbatar ta samu gata,hoto na biyu shi ya sanyata jin wani abu ya tsirga mata,a hankali kanta ya sara,hoton anwar ne a matsayin shine angon da za'a gudanar da bikin engage din nasu kwanaki goma masu zuwa,sosai ya fito tarwai,ya cika screen din tvn tamkar yana tsaye ne a gabanta,sanye da wasu shegun suit,daga sama har qasa shigarsa abar birgewa ce iya kallon mai kallo,miqewa tayi tsaye ba tare data shiryawa hakan ba,wani abu mai nauyi na danne zuciyarta kamar ana shirin riqe numfashinta ne,remote din taji ya mata kadan ta kauda fuskarsa daga screen din tvn,saboda haka bata tsaya ba har sai data dangane da socket din dake jone da kayan kallon ta kasheshi gaba daya,sannan ta juya da sauri don barin falon zuciyarta na wani irin gudu tamkar wadda taga wani abun tsoro.

Sallamar uncle hisham ita ta tsaidata cak,tasan dole ya ganta bai kyautu kuma ta wuce ba tare data yi masa barka da zuwa ba,daidaita yanayinta taketa qoqarin yi,kafin afkuwar haka anty zubaida ta fito daga kitchen din,da sauri ta juya don batason taga fuskarta,ta gwammace ta fuskanci uncle hisham a haka akan anty zubaida,yanzu zata saka ayar tambaya kan sauyawar yanayinta lokaci guda bayan ba haka ta baro kitchen ba.

"Sannu da zuwa abbu" ta fada a sanyaye idanunta na kallon qasa saboda tana ji a jikinta kamar qwayar idanun nata ba dai dai suke ba
"Yauwa rahamatullah(ya kirata da ainihin sunanta),ya jikin naki"
"Da sauqi abbu" ta amsa masa da sauri saboda wani abu dayake qoqarin shaqe mata wuya
"Ma sha Allah" juyawa tayi da zummar barin falon yace
"Shahida" sake juyowa tayi
"Na'am abbu"
"Anjima inason ganinki"
"Toh" ta fada tana sake juyawa zuwa dakinta.

Takai ta kawo

15 / 53