Author : HUGUMA Category : African Stories & Novels
don tafijin dadin kwanciya,sosai salon labarin ya qayatar da ita shi yasa da an dora sabon shiri a sautin hikima bata missing.
Anty zubaida ce ta turo qofar dakin ta shigo itama da hijab har qasa a jikinta,da alama kayan baccine a jikinta
"Baki kwanta ba?"
"Shirin kwanciyar nake dai,jarrabi nakeson in saurara kafin na kwanta din" murmushi kadan anty zubaida tayi
"Kin ganni nima kundin qaddarata nake saurara,ya zamemin jiki kullum saina saurari sabon episode idan sukayi updating"
"Na koya miki ko anty?" Shahida ta fada tana dariya
"A'ah,ai littafanne idan kika fara saurara baki da zaman lafiya saikinji qarshen kowanne labari"
"Gaskiya kam", zama anty zubaida tayi kan kujerar mudubin shahidan
" dazu mubina tazo tace miki daada tace kije daga ran talata zuwa juma'a shine kika ce ba zakije ba?"yanayin fuskar shahida yadan sauya,sam ita yanzu ko zancan katsjna ma bataso ayi mata
"Anty to me zanje nayi mata kuma?,bayan ta gama tsara duk yadda ranta yakeso?"
"Amma bai kyautu ta kiraki kiqi zuwa bako?,tunda kinsan cewa koma meye daada ba maqiyiyarki bace masoyiyarki ce,kome zata yi zatayishi ne sabida tana sinki ba don ki cutu ba" shuru sukayi gaba daya,anty zubaidan na karantar shahida,yayin da shahidan ta shiga tunanin me zata je ta yiwa daada?,amma tana ganin kuma wannan kamar wata dama ce da zata kaimata nuradden ya gwada sa'arshi ko Allah zaisa haqarsa ya cimma ruwa,kai ta kada
"Shikenan,zanje ran alhamis"
"Yauwa,dadai yafi" ta fadi tana miqewa
"Anty don Allah idan kin fita ki cewa faruqu yayimin transfer din data,data din nan satinta daya da ita nakejin littafin,donma ba cirar data din ake ba ai da tuni ta qare"
"Yana falon uncle,zan masa magana" ta amsa mata tana fita a dakin.
_kuyi manage da wannan_https://youtu.be/_XVqJSBXVPI
*Alqawarin Allah*
2️⃣9️⃣
Da hanzari ta koma jikin wayarta ta cirota,ta koma gefan gado ta rubuta saqo ta tura masa,saita kashe wayar don ta tabbatar ta barta akunne nuradden bazai barta tayi barci ba,tunda damar da yake nema kenan gashi ya samu.
Washegari tana kunna wayartata kuwa kiransa ne abu na farko daya soma shigowa,yadda taji muryarshi ya kasa zaune ya kasa tsaye kaman ance masa an bashi ita dinne,tun a ranar suka shirya yadda tafiyar zata kaya,ya nemi su tafi tare tace sam,ya sameta kawai a can ran alhamis din,murmushi ya saka mai sauti
"Bakison hawa motata kwata kwata shahida,don know why....koda yake babu komai saura qiris in sha Allahu,Allah yakai damo ga harawa dai" murmushi kawai ta saki tana yanke kiran,bazai gane bane,baisan irin illa tabo da masifar da shiga motar wani ta sabbabawa rayuwarta bane,tabon da har yanzu bata daina jin dacinsa ba yana zaga jiki da rayuwarta gaba daya.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Qarfe sha biyu da minti arba'in da biyar tayi sallama falon daada,hasina 'yar gidan qanin abbanta ce zaune ta daga kai cikin mamaki da farinciki ta amsa sallamar
"Mutan kano,yau a gari?,ni har nayi fushi fa,wai shahida kizo har garin nan kwanaki amma ki kasa leqani,gaba daya kin watsar dani kaman wadda ta miki wani mugun laifi?" Murmushi shahida tayi tana zama kan daya daga cikin kujerun gami da cire mayafinta ta aje gefe,iskar fankar da aka qurewa gudu cikin falon tana kadata gami da shigarta tako ina sakamakon zafin da ake zabgawa da kuma uwar rana
"Kiyi haquri hasina,ba'a son raina ba wallahi,wannan tsohuwr ce ta min laifin daya shafeku,amma kiyi haquri zanzo in sha Allahu" cikin murmushi hasina ta tabe baki
"Kedai bansan me ya dameki ba,koda yake an auna arziqi da aka samu ma kika ci gaba da zuwa katsinar da kika yiwa yajin aiki wajen shekaru hudu" murmushin da baikai har zuci ba shahida tayi tana cire agogon hannunta
"Yanzun ma mawuyacine idan ban koma muku yajin aikin ba ai" ta qarshe fada wani abu na takore mata wuya idan ta tuna kasassabar dasu daada suka aikata mata,saidai takanji sassauci idan ta tuna tana da hope a yau,qasa qasa da murya hasina tayi
"Hala ta kusa kwatanta miki abinda taso yimin kenan?" Kallonta shahida take ba tare da tace komai ba tana son jin qarin bayani
"Wai in gaya miki matarnan daga zuwa mata hutu shikenan tasa aka mata kiran saurayina qafa da qafa wai ya kamata ya fito hakanan,wannan shekarar ta shirya aurar da jikokinta,wai basai ya dorawa kanshi wata dawainiya ba yayi abinda addini kawai yace masa ya wadatar Allah ya sawa auren albarka" tagumi da haba shahida tayi kawai tana jin wannan bayanin,ita kenan ta mata dakyau ma data amshi kudin aure,amma gwara hasina da ita sau dubu
"Hasina kukan dadi kike,kinsan me daada tayimin?" Kai ta girgixa tana duban shahida
"Kudin aurena da sadakina suka amsa gaba daya ba tare da na sani ba,kuma ba tare da nasan waye zan aura din ba,kawai don bincikensu ya basu managarcine suke ganin ya dace dani" idanu waje hasina ta fito dasu tana duban shahida,kafin tace wani abu suka jiyo maganar daada daga tsakar gida wadda ta fito da wanka ne tana fadin
"Da kika shigo kika bar akwatin naki rana na duka waye zai dauke miki" dole kowanne yaja bakinsa yayi shuru harta iso falon,saita kalli idanunsu na 'yan sakanni kana ta tabe baki
"Magulmatan banza da wofi" daga haka tayi wucewarta daki donta saka kaya,yayin da shahida cikin dacin rai da baqincikin daya taso mata ta fito tsakar gida ta shiga bandaki tayi fitsari sannan ta daura alwala nan bakin famfo ta shigo da akwatin nata.
Qarfe daya da minti ashirin na rana tana tashi daga saman abun sallarta wayarta ta dauki tsuwwa,hasina ta miqo mata ta duba,nuradden ke kira ko bai fada ba tasan ya iso ne,gabanta taji yayi mummunar faduwa ta daga idanunta ta kalli daada data qarawa fura da nono ruwa take sha,saita kalli hasina,suka hada idanu ta mata signa sannan ta fita tsakar gida,ba jimawa ta biyo bayanta,janta tayi bakin kitchen ta gaya mata abinda ke faruwa
"Tabdi,kina tunanin akwai abinda zai sauya dada?,amma arashin tayi akan bar arha,bari na gaya mata baqo zai shigo" ta juya tana komawa,kafin takai ga shiga falon yaro ya tamfatsa sallama yana rangada fadin wai ana sallama da shahida,daada dake zaune a rumfarta tayi katsu tana jiran taji wanda zaiyi magana cikinsu,shuru sukayi ba wadda ta amsa,sai daadan ta kira yaron ya qaraso bakin rumfar
"Waye yake sallama da ita?"
"Wani ne,wai nuradden daga kano"
"Kano?" Ta sake tambayar yaron,saiya kada kai alamun eh,shuru na sakanni sannan tace
"Jeka ce masa ya shigo" juyawa yaron yayi ya fice ita kuma ta kira shahida da hasina gaba daya
"Xauna nan" ta nunawa shahida gefanta,ba musu ta zauna jiki a sanyaye,ta dubi hasina
"Bude firinjin can ki ciro ruwa da lemo" ba musu hasinar tayi yadda tace,dada ta nuna mata shimfidar daddumar data gama salla akai bata kai ga daukewa ba tace ta dora saman nan.
Cikin minti biyu kacal nuradden ya bayyana cikin falon,yaci manyan kaya yanata qamshi,bashi kadai bane shida wani abokinsa ko kuma ince amininsa ne,duk da dan uwanshi ne,cikin girmamawa suka zauna saman shimfidar suna gaida daada,ta amsa musu kadaran kadaham,yayin da idanun nuradden ke kan shahida.
Tayin ruwa da lemon tayi musu,Sayyid abokinsa ya bude ya zuzzuba musu a kofi,kusan shi kadai yasha,yana sha suna dan taba jira jifa jifa da daada tana tambayarshi kano,kasancewar ta dauki shekaru masu dama rabonta da ita,tun kafin rasuwar babansu shahida.
Sai da suka kammala tasa hasina ta zuba musu abinci,saidai sunce a qoshe suke,tilas ta rufe ta maida kitchen din,shuru ne ya ratsa na dan wani lokaci sannan sayyid yace
"Am...daada,abinda yake tafe damu dama magana ce game da shahida da kuma abokina nura,duk da nasan bata sanar miki da zuwanmu ba"
"Haka yake" a nutse sayyid ya fayyacewa daada komai,tayi gyaran murya tana dubansu
"Nasan cewa kuna da labarin an bada shahidan harma an karbi sadakinta,idan ma ta boye maka bata gaya maka ba ni ya zama wajibi na gaya maka gaskiyar abinda ake ciki"
"Ta fadama bata boye ba daada"
"Yauwa...an riga da an karbi sadakin yaron,kuma a shekarun da Allah ya bamu bai kamata kuma ace muna magana biyu ba,uwa uba sanin kanka ne cewa haramunne neman aure akan nema,koda ciniki akan ciniki ne haramun ne bare nema kan nema,matar mutum kabarinsa,Allah ya qaddari haka tun farko shi yasa ya hukunta jinkirin zuwanka garemu,saboda haka ina mai yaba maka bisa soyayyar daka nunawa jininmu,ina kuma mai maka fatan samun dacewa da wata matar data fita,sannan ina mai dorawa da baka haquri,kayi haquri,Allah ya sawa zuciyarka dangana" sayyid ne kawai ke amsawa da amin,yayin da gaba daya jikin nuradden ya mutu murus,zufa ta dinga yanko masa tako ina
"Mun gode sosai da karamcin da akayi mana" sayyid ya fada sanda suke miqewa bayan sun ajewa daada kudi
"A'ah yaro...nifa bazan karba ba,zoka dauka ku wuce Allah yayi maka zabi mafi alkhairi" qememe suka qi dauka haka suka fice,daada ta juya ta kalli shahida dake zaune gefanta tana sharbar qwalla
"Saikije ki sallamesu" daga haka ta miqe ta tayi wucewarta daki,sanda ta cimma qofar gidan tuni su nuradden sun wuce,sai tex daya turo mata na anjima zai kirata don yanzu baida nutsuwar tsaiwa,sulalewa tayi ta zauna gefan gadon,tana qoqarin hadiye kukanta.
Shigowar daada dakin ya sanyata daga kai tana kallonta,tana daga tsaye ta soma magana
"Kin kyauta sosai da kika sanyashi yazo kika toxarta mu,daa can kinsan yana sonki baki bashi dama ba har saida muka yanke hukunci a kanki?,ko kina tsammanin mu warware maganar da mukayi kaman qananun mutane?,to idan ma zaki kwantar da hankalinki ki nutsu waje guda shiya fiye miki alkhairi,ki shirya kuma ki dakaci zuwan gobe,mijinki da yardar Allah zaizo kuga juna,idan kinga dama kuma idan yazo din ki watsa mana qasa a idanu" daga haka daadan ta juya tayi ficewarta,sai kawai shahidan ta bita da kallo ranta na quntata,koma meye shi ya janyo mata,kuma shima saiyaji a jikinsa da zuciyarsa yadda ya janyo mata bacin rai tsakar rana ba tare data shiryawa hakan ba.
***** ****** ****** *****
Tunda ta tashi washegarin take kwance abinta kamar ruwa taqi yin komai,saidai daga nan ta koma can,hasina tayi tayi ta tashi tayi wani abun ko taji qwarin jikinta amma ta qeqashe qasa,ko kallo bata ishi daada ba sangar gabanta kawai take,tana daga kwancen tana kallon daada,yadda ta cika fridge dinta da fura da nono mai kyau,lemuka da kuma ruwa,tasa hasina tayi total na kayan fulawa aka siyo komai hasina tayi dan dai dai aka adana komai,baki ta tabe ta dauke kai bacin rai na cinta sanda daada ta fito da sabuwar daddumarta da kawu ummaru ya bata sanda ya dawo daga umara ya fesheta da turare ta baiwa hasina taje ta shimfida a dakin soro.
Saida komai ya kammala hasina ta isketa kwance cikin kujera tana saqa da warwara ta zauna gefanta
"Ya kamata ki tashi ko ruwa ko watsa kyaji dadin jikinki?" Idanunta da suka sake girma saboda kwana biyu data yi bata saka musu kwalli ba ta watsawa hasina cikin salon tambaya
"Me kikeson cewa?,kice kawai na tashi na yi masa kwalliya saboda zaizo,mutuncina ya qara zuba a idanunsa ko?" Murmushi hasina ta saki tana kada kai
"Niba haka nake nufi ba,kawai nasan yadda kikeson wanka wuni guda kuma ace tun safe ga azahar ta shiga baki watsa ruwa ba bare kici wani abun ai babu dadi,a qalla kodon tsaftar jikinki ko?" Saita maida kanta ta kwantar gami da rufe ido sannan ta amsa mata
"Share kawai" dubanta hasinan tayi na wasu mintunan sannan ta miqe tana cewa
"Allah ya kyauta,ya kamata dai ki sawa ranki salama,tunda kinsan cewa aikin gama ya gama,kada madai azo gaba kina jin kunya yazo kiga ya miki ki kamu da sonshi,kinsan wallahi daada ba raga miki zatayi ba"da sauri ta sake bude idon ta dubi hasina
"So,bakisan nayi bikin binneshi ba?" Dariya ta qwacewa hasina ta kama baki tana kallonta
"Shi kuma wannan da kika kawo fa?,mutunci kuke kenan?"
"Nuradden?..inason in rama halaccin da yayi minne shekaru kusan hudu"
"Tabdi,kice gwara da Allah yasa daada ta zaba miki miji,ashema ba soyayya kuke ba kenan" kofin dake gefanta shahida ta wafto ta jefi hasina dashi Allah yasa ta kauce bai sameta ba,har ga Allah taso ta sametan don bata da bakinma ce mata ta fita saboda wani abu dake takore da wuyanta
"Na rantse da Allah na tashi hasina saidai daada ta fiddaki daga gidan nan" cikin dariya ta fice tana cewa
"A'ah,a'ah,bani nakar zomon ba,ratayarma kuma ba'a bani ba".
Qarfe uku na rana da 'yan mintina daada ta shigo ta sameta
"Tashi kiyi wanka ko yanzu nasa akaimin ke bandaki na sabeki" ta furta tana nuna da gaske take,saida ta gama taurin kanta ganin da gaske daadan take sannan ta shiga bandaki tayi wankan.
Sanda ta fito mai kawai ta shafa sai turarenta oily data gogawa fatarta,tasaka wasu riga da skert na atamfa ta zura dogon hijabinta daya sauka har saman qafafunta ta soma da nafila kafin ta gabatar da farillar sallar la'asar.
sanda ta kammala saman abun sallar ta zauna tana jan hasbunallahu wani'imal wakil,saboda faduwar da gabanta yaketa yi wanda batasan dalili ba.Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka tazo ta ratsa falon,hasina da daada suka bita da kallo,hasina baki bude ta dubi daada saboda ganin yadda shahidan zata fita ba kwalliya babu komai sai zabgegen hijabi,qwafa dadan ta saka sannan tace
"Rabu da ita ja'iarar kawai shashasha" sarai ta jiyo dadan,haka ta dinga takawa har zuwa dakin soron,ta saka hannu ta yaye labulen ta shiga.
Babu kowa cikin dakin sai kayan ciye ciyen dake jere a tsare,daga saman daya daga cikin kujerun kuma hula ce mai azabar kyau da daukar ido da alama ta baqon ce,to ina ya shiga?,shuru dakin sai uban qamshi daya cika dakin na turaren baqon,wanda qamshin turaren yaso daukar hankalinta,saita samu hannun daya daga cikin kujerun ta zauna tana qarewa dakin kallo da idanu kamar yau ta soma ganinsa,ta dinga qoqarin rage faduwar gabar da takeji tana saisaita kanta da nutsuwarta.
Kamar a mafarki kamar a wasa ta dinga jiyo murya kamar ta anwar tana doso dakin,saita ware idanunta ta zubesu duka bakin qofar,yayin da zuciyarta ta soma qara gudu daga gudun da take yi a dazu,a nutse ya yaye labulen yana sauke wayar dake kunnenshi,cikin sakan daya idanunsu suka sarqafe cikin na juna,a nutse ya janye nashi idanun tamkar ba ita ya gani ba,yayin da shahidan ta miqe zumbyr kamar wadda aka tsikarawa wani abu idanunta dukka a waje saman fuskar anwar wanda ya jingina bayanshi da bango daura da qofar fita,tafin qafarsa guda daya ya tokare bangon da ita ta baya dayar kuma yana tsaye a kanta.
"Ki nutsu shahida ki fuskanci komai yadda ya kamata" shawarar farko da zuciyarta ta soma bata kenan bayan qwaqwalwarta ta dawo daga aiki bayan daukewar da tunaninta yayi na wucin gadi.
Shuru ya ratsa dakin na tsahon minti biyu tana jira taga shin anwar dinne da kansa ko wani ya rako?,wajenta yazo ko batan kai yayi?
"Lafiya malam me kake a gidan mutane?" Idanunta a kansa fuskarta na nuna zallar bacin rai
"Ina cewa kin fito ne don ki gana da wanda ya nemi aurenki?" Ya qarashe maganar da sigar tambaya fuskarsa a dinke yana dage girarsa qwaya daya idanunshi cikin nata,cikin tsananin razana da firgici ta fiddo duka idanunta waje.
👑https://youtu.be/H7M7h6l6wNM
*xafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki sharing,ga mai buqatar siya zai tuntubi wadan nan numbers din*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*Alqawarin Allah*
3️⃣0️⃣
"Kana nufin kaine mutumin daya kawo sadakina da mudin airena ba tare da sani ko yardata ba?" Ta furta wani bala'i na cinta,maimakon ya bata amsa da baki saiya daga mata dukka girarsa biyun yana dubanta kai tsaye ya kafeta da idanunshi,wani tashin hankali taji ya rufto mata irin wanda bata taba jin irinsa ba tunda maganar aurenta ta bullo,tashin hankali da ba'a saka masa rana,ko zata yarda da kowa ba zata yarda da anwar ba,ko zata amince da auren kowa ba zata taba amincewa da auren anwar ba koda su biyu kadai suka rage a duniyar,murmushin takaici ta saki wanda qasan zuciyarta ji take kaman zata fashe
"Kaima kasan ka dauko abinda bazai taba yiwuwa ba har abada,tamkar wanda ya mutu ya dawo ne,kai bakaji kunya ba anwar?,kana tunanin akwai abinda yayi saura?,kana tsammani akwai wani sauran abinda ya rage tsakanina dakai?,to bari kaji na gaya maka,ba zaka taba samun yardata ba,ba zaka sake samun soyayyata ba,har abada aure tsakanina dakai,har abada...." Qawataccen murmushi ya saki,da alamun kwanciyar hankali kwance kan fuskarshi,sai daya sauke qafarsa ya sauya jinginar da daya sannan ya rungume hannunsa daya dayan kuma yana shafar sajensa idanunshi a kanta,fara'ar fuskarshi ta bace bata
"Hajiya shahida....dukka tunaninki bai baki dai dai ba,baije inda ya kamata yaje ba" sauke qafarsa yayi ya soma takowa inda take tsaye,sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sosai sannan ya tsaya ya soke hannayensa cikin aljihun rigarsa
"Kina tunani ko tsammanin soyayya ce tasa na nemi aurenki?,ko kina tunanin neman yardarki nake kafin na aureki?"sai ya sake takowa gab da ita kamar zai hadeta da jikinsa,ya nunata da yatsa
"Zan aureki don na nunawa wancan wawan cewa nidin na girmi qaramin dalili babban dalili ne ni,sannan nayi isar da zan yanke guntuwar soyayyar da yake taqama da ita,soyayyar da bai iyata ba,bai gama saninta bama bare ya iya,baisan kanta ba baisan mece ita ba!" Ya qarasa fada yana dan daga muryarsa gami da nuna qofa da yatsa kai kace nuradden ne ke tsaye a wajen,saiya sauke hannun nashi yana maidashi aljihunsa kana yaja baya kadan har yanzu bai dauke idonsa daga kanta ba
"Yana tunanin ya sanki?,yana tunanin yafi kowa saninki koya riga kowa saninki?,ya gayamin magana yayi tunanin yaci bulus?,inaso yaji ciwo ya kuma ci gaba da jin ciwo a ransa duk sa'a daya da zata wuce da tunanin wani mai suna anwar ya haramta masa auren wadda yake iqirarin yanaso,wadda yake iqirarin ba wanda ya isa ya shiga tsakaninsu" yana kaiwa nan ya juya mata baya,yana jin kamar ana yankar zuciyarsa
"Baki cancanci na qyaleki