Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   35 / 53

102K to 105K   out of 156.9K words

tayi yadda yace ta dawo ta zauna.

Ba'a jima ba sosai ya sake cewa ta dauko mishi ruwa,ta dauko ta aje masa saman table din,saiya daga kansa ya kalleta sannan ya maida kan computer dinsa yaci gaba da aikinsa,awa biyu tsakani yace ta dauko mishi lemo a fridge,idanunta ta juya cikin nuna qosawa,ta sauke numfashi sannan taje ta bude ta dauko masa ta aje
"Ba wannan kalar nakeso ba,ki duba akwai wani daban shi zaki dauko min" hadiyewa tayi ta juya din ta maida ta dauko masa ta aje,saiya dubeta ya kauda kai
"Waishin haka ake bawa mutum abu,a dire masa kaman dutse,baza'a bude masa ba bare a zuba masa?" Hannayenta ta goya a qirjinta ta zuba masa ido
"Wai na tambayeka?,aiki nazo yiwa kamfani ko kai nazo yiwa aiki?" A nutse ya dubeta sannan ya ture cumputer din gefe kadan ya hada yatsunsa cikin na juna
"Bakisan cewa nine kamfanin ba gaba daya?" Ido ta fiddo alamun bata gane ba,girarsa ya daga mata
"Eh,aikin kamfani xakiyi,kuma nine kamfanin gaba daya,babu aikin dayafi nawa aikin,wannan aikin shine aikinki a office dina,zan biyaki albashi kamar kowa albashinma daya fi na kowanne ma'aikaci,ba shikenan ba?" Idanu kawai ta zuba masa tana kallonshi yana fidda qaramin murmushi,tsantsar raina mata wayon da yayi kawai ya isheta bacin rai,saita juya kawai ba tare data tanka masa ba ta nufi qofar fita.

Gabanta yasha ya tsate hanya
"Ina zaki?,lokacin tashi baiyi ba madam"
"Aikinne na fasa bazanyi ba gaba daya" duka kafadunsa ya daga,hakan ya masa shima,don baisan ta yaya zai dinga barin mutane na shiga masa office ba alhali tana ciki
"Fine and good....saiki jira sai lokacin tashi yayi saimu wuce gida" daga haka ya juya zuwa wajen wayarsa da tunda suka fara taqaddamar ta soma ringing,daga wayar yayi yana dubawa,wannan shine kira na dari da biyu daya samu da lambar daga farkon satin xuwa yau,tunda ya daga yaji muryar nafisa bai sake daga wayar ba,don baisan me kuma zata ce masa ba,me yayi saura tsakaninsu?.

Wayar ta wurgar a gefanta ta fada saman kujera tana yamutsa gashinta,sam ta kasa jurewa da rashin anwar kamar yadda mima ta shawarceta ta jira sai zuwa wani lokaci da ita miman ke shirya mata,ta rasa ta yaya zata iya jurewa,daga qarshe dole tabi zabin ranta ta soma neman khalipha baji babu gani,tana neman hanyar da zata gyara kurenta,kullum ranta soyuwa take ta gaza sukuni idan ta tuna yanzu haka fa yana can suna rayuwarsu shida shahidan?,me yasa kishi ya rufe mata ido haka ta tauyi rayuwarta?,ta yaudari kanta akan ba zata iya aurenshi ba?,bayan tasan cewa ka ta kawai ta yiwa qarya,ta ina zata soma gyara wannan babban kuskuren data tagka,tasan cewa abune ba mai sauqi ba musamman idan ta tuna da yadda ta samu soyayyarshi a baya,saidai koma meye tanajin zata jure harsai haqarta ta cimma ruwa,sai taga abinda ya turewa buzu nadi,zata aje mima a gefe wannan karon,zatayi yaqi ta samawa zuciyarta abinda takeso kota yayane ma,idan yaso ta nemi miman daga baya su dora daga inda suka tsaya.

Dirowa tayi daga saman gadonta ta shiga bandaki ta dauraye fuskarta sannan ta yafa qaramin mayafi saman kanta ta fito.

Dakin mahaifiyarta ta wuce,ta sameta zaune tana waya,saita samu waje tana jiranta garta kammala,kusan tunda abun ya faru ta sake dauke mata wuta,a baya ta sani amma ta nuna kamar abin bai dameta ba,tunda tana tsammanin abinda ta aikata shine dai dai
"Mommy,zuwa nayi na baki haquri" dubanta tayi sannan tace
"Akanme?" Shuru tadanyi sannan daga bisani kanta a qasa tace
"Nasan na bata muku kan qin auren anwar da nayi,amma a sannan idanuna ya rufe,don Allah momy kuyi haquri,ki tayani baiwa daddy haquri" tabe baki mommyn tayi tana miqewa
"Aike za'a baiwa haquri,name zaki bamu haquri tunda kin aikata dai dai,rayuwarkice fa kuma kika zaba mata abinda kike ganin yafi davewa da ita" daga haka mummyn ta bude qofar dakin nata ta fice,da kallo ta bita kafin daga bisani ta janye idanunta tana sauke ajiyar zuciya,lallai aikine ba qaramiba a gananta kafin ta soma shan kan iyayenta,wanda sune tsaninta na nasararta Wajen anwar,saita miqe kawai tabi bayan mummyn,sai inda qarfinta ya qare kam.

Lokacin sallar azahar taga ya sanya rigarshi ya fita,hakanan ta miqe itama ta shiga bandakinsa dake nan cikin office din ta shiga tayi alwala tazo ta tada sallah kan abun sallarsa dake cikin office din.

Bai wani jima ba da yawa ya dawo dauke da takeaway,ya aje mata nata ya bude nashi ya wanke hannunsa ya soma ci,ta gefan ido take satar kallonsa,wato har yau halinshi nacin abinci da hannu dai yana nan.

Ranar haka suka wuni har lokacin tashi,yana aikinsa tana zaune waje daya,saidai sam taqi zama saitin da zata ga fuskarshi koshi yaga tata,tayi danasanin karbar tayin aikinsa da biyoshi kamfanin datayi yafi sau shurin masaki,kome za'ayi kam ba zata taba iya aiki dashi ba,ta gwammace tayita zaman gidan akan zamansu qarqashin inuwa daya,suna musayar numfashi daya kusa da juna sosai har kamar haka,ta saurari muryarsa data wulaqantata wulaqancin da har yau yaqi gushewa yabar zuciyarta,duk sanda ta nutsa duniyar tunani saita tuna kalamansa da har yau bataji kalaman da suka yiwa kunnuwanta muni kamarsu ba.


🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Qarfe shida da minti ashirin da biyar na yammaci ya shigo gidan.

,yana zaune a falon yana sauke gajiyar daya tarawa kansa yau,ji yake kaman bazai iya hawa samanshi ba,da ido yake bin kowanne sashe na falon da kallo,ko ina fes yake ba alamun datti ko qura,hakanan yana fitar da sassanyan qamshi mai ratsa zuciya,amma saika rantse ba wani dan adam cikin gidan,sai qarar na'urori kawai dake fita kadan kadan,ya janye idanunshi kenan yana shirin miqewa yaganta tana fitowa,sanye take da doguwar rigar atamfa mai gajeran hannu,wadda tafitar da shape dinta sosai,kama dafa damammen cikinta,qirjinta da yake das cikakku,zuwa mazaunanta da suka dace da qirar jikinta,kanta babu kallabi sai gashinta dake daure waje daya,tayi kyau kamar wata 'yar tsana,fatarta ta sake fresh na zama waje daya,da alama ta fito daukan wani abune,suna hada idanu tayi turus kamar zata juya,sai kuma ta maze taci gaba da takowa,dab da zata giftashi tace
"Sannu da zuwa" ciki ciki kamar wadda aka turawa tsumma a baki,wanda banda kunnuwansa dake dukka wajen ba bazai iya jin me tace ba,hakanan yaji yana da sha'awar ya takaleta,kwana biyu da bai ganta ba saiyaga kaman ya jima bai ganta din ba,saboda haka ya hade rai qyam sannan yace
"Zonan" yadda ya kirata cikin gadara da bata haushi,amma saita tuna koma meye itace a qasanshi,saboda haka ta sassauta ranta ta tako inda yake zaune ta tsaya gefanshi,saiya daga kai yana kallonta
"Me haka?,zaki samin ciwon kai rage tsahonki" dubansa tayi sosai kaman zata tanka saita shareshi,ta zauna hannun kujerar da take daura dashi,samun kanshi yayi da qare mata kallo,idanunsa suka tsaya kan qirjinta kamar wani mayen qarfe ke janshi,idanu ta zaro data fuskanci inda yake kalla,saita goye hannayenta a wajen abinda ya fargar dashi cewa kallonshi ya zarme da yawa,saiya maze yana sake hada rai
"Haka kike zama dama idan bana nan?" Ya jeho mata tambayar,mamaki ya kamata,ta kasa gane me yake cewa?
"Kamar yaya?,ban gane ba?" Ta tambayeshi itama tana kallonshi bayan ta kalli kanta
"Wannan shigar gaskiya bata dace ba" mamaki ya sake kamata
"Waini da waye cikin gidan?"ya gane sam maganarsa bata da makama saboda haka yace
"tunda haka kika zaba shikenan,bani ruwa nasha tunda baki iyaba har sai mutum ya roqa" ta gane sarai neman abun fada yake,saboda haka ta miqe kawai ba tare datace masa komai ba ta wuce kitchen din,saiya waiwaya ya bita da kallo,karon farko da yaji wani abu yana ratsashi tun daga tsakiyar kansa zuwa tafin qafafunsa,ya lumshe ido yana ambaton sunan Allah,baqon feelings yakeji sosai wanda har yaso danne gajiyar da yakeji.

Idanunsa ya bude sanda take aje masa ruwan,idanunsa kuwa sukayi kyakkyawan gani,saiyaji kaman yakai hannunsa kamar ana janshi ne,ya samu da qyar yayi controlling kansa sanda qamshin turarenta ya soma rarraba mishi hankali,yana kallon tasoma takawa don barin wajen ya kasa magana sai binta da idanu,da qyar yasamu cewa
"Nace ki tafi ne?" Waiwayowa tayi tana kallonshi fuska a turbune
"Zo nan" ya sake fada,ba yadda ta iya don batason ta saba da dabi'ar musu da gardama data soma masa ya zame mata jiki
"Zubamin" ya fada yana nuna mata ruwan,haka ta sake duqawa tana zuba masa,ta gama ya amsa yana nuna mata wata leda daya shigo da ita
"Kaimin dakina" ya dora qafarsa daya kan daya ya soma shan ruwan,baki take turowa ciki ciki,ya soma kaita bango,ta dauki jakar ta soma hawa saman,nan ma da kallo ya bita yadda mazaunanta ke juyawa kai kace tana sane takeyin hakan,ajiyar zuciya ya sauke bayan ta bacewa ganinsa,ya dire cup din da hanzari ya miqe ya rufa mata baya.*Alqawarin Allah*
41

_ku ziyarci tasharmu ta youtube don sauraren tsofaffi dama sabbabin littafanmu,da sababbin ma da bakusan dasu ba wadanda zasu fara zuwa muku ta tashar nan gaba kadan da ixinin ubangiji_

https://youtu.be/-tPtW9YtNpU


Tana shirin fita yana shirin shigowa sukayi kacibus,tadanja da baya tana neman hanyar wucewa
"Waye ya miki karatun yadda ake zama da mijine?" Yayi tambayar yana dubanta,dagowa tayi cikin mamaki ta kalleshi,saiya dage mata gira guda daya
"Eh,gaskiya bata iya komai ba kaman yadda na lura,saboda bangani a qasa ba" ya fada yana takowa zuwa inda take tsaye,yanajin bazai iya barinta yadda ta rikitashi taci bulus ba ba tare da shima yau yadan taba koda fatarta ba yaji yadda akeji,baya ta soma ja tana kallonshi,bata fahimci me yake shirin aikatawa ba saida ya kusa qureta jikin madubin dakin,idanunta cike fal da tsoron da takeson boyewa tace
"Meye haka kakeyi?"
"Abinda kika gani" ya bata amsa bai fasa nufota ba,cikin dan tsoro tace
"Karka tabani" cak ya tsaya yana kallonta
"Tunda kwartone ni?" Ya amsa mata ta sigar tambaya,bai kuma bi ta kanta ba yaci gaba da nufarta,don baijin zai iya haqura din shima bai d'aana ba,ko ina ta kalla ya riga daya kangeta,a haka ya hade gap din dake tsakaninsu,ya zagaya hannunsa ta qugunta ya janyota sosai cikin jikinsa,fuskarsa ya sauko da ita dokin wuyanta yana kai hancinsa,ta soma juye juye tana son ta qwace daga hannunshi
"Banaso,meye haka,ka sakeni"
"Ni kuma inaso" ya fada yana fidda numfashi saboda yadda abun ya soma masa dadi,wayarsa dake saman mudubin ta dauki haske da qara,wanda hakan yaja hankalinsu gaba dayansu,a tare idanunsu ya sauka a tare kan screen din wayar,sunan NAFISA ya bayyana saman screen din,dauke idanunshi yayi yaci gaba da abinda yake,hakanan taji wani abu yadan sosa mata rai kadan,amma saita dauka yadda ya tarfata ne yake yadda yaso da ita,sosai yake shinshinar kowanne lungu da saqo na jikinta yana fitar da numfashi,ko ina jikin shahidan rawa yake itama,karon farko da irin hakan ya soma faruwa da ita a rayuwarta,tsoro da haushin anwar din ya cikata ganin da gaske yake yau ba wasa bane,kaman wanda aka tsikara ya saketa da sauri gami da turata baya shima yaja baya da hanzari yana zama gefan gado ya dafe kanshi dayaji ya sara masa lokaci daya
"Ya Allah" ya furta yana ci gaba da dafe kan nashi,hanqota kawai yayi sanda take rungume jikin wani,bayaso ire iren wadan nan tunanukan su dinga dawo masa kwanya,saboda haka saiya dinga maimaita
"Hasbunallahu wani'imal wakil" tana zuge zif din rigarta tana mamakin yadda lokaci guda yasaketa haka,yanayin da taga ya shiga din,saidai itama ba'a nutse take ba saboda haka tana gama jan zip din nata ta soma tattaki cikin hanzari zata fice
"Dawo nan!" Ya fada cikin kakkausar murya,ba musu tadawo din ta tsaya cak saidai bata dubeshi ba,fuskarshi a dinke take tsaf babu fara'a ta sisin kwabo
"Shiga ki hadamin ruwan wanka" jikinta a mace take takawa zuwa bandakin,ta hada mishin ta fito ta shaida masa,saiya miqe kawai ya zari towel
"Karki tafi saina fito" ya fada yana shigewa cikin bandakin,tsayawa tayi cak,ta jingina da madubi tanajin yadda qafafunta suka mutu,jikinta babu qwari sam,ta soma tuna yadda taji daxun da yadda abun ya kasance,saita lumshe idanunta tana tuns komai,qamshin jikinsa daya goga mata yana zarya cikin hancinta har zuwa qwaqwalwarta,kasala na sake saukar mata,qarar da wayar tashi ta sakeyi ita ta katse mata duk tunaninta ta sanyata bude ido,bata tabata ba sai dubanta data kai kan wayar,sunan nafisa ne dai again,saita ci gaba da kallon wayar harta katse,tana shirin dauke idanun nata wani kiran ya sake shigowa.

Ci gaba tayi da kallon wayar har kiran ya sake katsewa,duk kiran daya shigo din kan idanunta ya dinga shigowa yana katsewa,wanda a qalla kafin ya fito din an kira yakai sau goma sha biyar,kuma ba'a fasa kiran ba,bata dauke idonta ba itama saida taji ya soma qoqarin bude qofar bandakin sannan ta kauda kai tana tunanin wace wannan haka?,meye ya faru take jero kira haka ba qaqqautawa?,bakin mudubin ya tako saita matsa gefe tana sake dauke kanta wani sashen,towel ne daure a jikinsa iya qugu,sai wani daya ratayo wanda duka duka bai gama rufe jikinsa ba gaba daya,wani nauyi da bata taba jin irinsa ba ya saukar mata,gabanta ya dunga faduwa sosai,ta sake dauke kanta yadda ko inuwarsa ba zata gani ba,baice mata komai ba ya daga wayar ya duba mai kiran,duka nafisan ce,cikin zuciyarsa yaja tsaki yana tambayar kanshi me zata masa?,ya aje wayar yana cewa
"Kije ki shirya,zamuje duba anty usaina batajin dadi" waiwayowa tayi cikin faduwar gaba da fargaba,bala'in kunya da nauyin anty usainan takeji,yanzu kuma zai kaita gidanta?,saidai a kamatance ma bai kamata ta musa masa ba kodon karamci irin na anty usainan da qaunar da take gwada mata.

Tana shiryawa amma kiran wayar ya tsaya mata arai,ta rasa dalili,kiran sai takega kamar yayi yawa,a haka ta gama shiryawa tsaf cikin wani lace,ta yane kanta da yalwataccen mayafin daya dace da shigar tata,saidata dubawa anty usainan abinda zata kai mata ta saka cikin jakar hannunta sannan ta fito,a falon qasa suka hadu,saita tsinci kanta da satar kallonsa duk da bata shiryawa hakan ba,anwar badai wanka ba,tunda can tun lokacin da bashi da komai mutum ne mai tsafta da kwalliya ma gaba daya,yayi kyau cikin yadin kufta na maza,dubanta yayi sosai wannan karon kanshi tsaye babu boye boye
"Wannan qamshin yayi yawa" yana takowa zuwa gabanta,tuna abin daxu daya mata tayi saitayi hanzarin jaa da baya kada ya maimaita,don har yanzu jikinta a mace yake,tsayawa yayi cak saiyayi murmushi cikin ranshi,ya gane me take gujewa,itakam ba wani turare ta saka ba bayan na jikinta,juyawa yayi ya fice ta mara masa baya.

Zata shiga baya kamar yadda ta saba masa taji qofar taqi buduwa,haka tayita qoqarinta na budewar amma taqi da alama lock ya saka,dole ta dawo gaba ta bude ta shiga.

Horn biyu maigadin ya dage masa gate din ya saka motar,ya qaraso suka gaisa da anwar din sanda yake fitowa daga motar,suka soma takawa zuwa cikin gidan,suna gab da valcony din da zata sadasu da qofar falon tana fitowa cikin doguwar riga da yalolon mayafi,hada idanu sukayi da anwar,saita kasa dauke idanunta daga kanshi,gabanta na faduwa qaunarshi na sake ratsa zuciyarta fiye dada,sai taga kaman an qara masa kyau da haske,ga wani kwarjini na musamman da gake fitarwa,shi ya soma janye nashi idanun ya soma yin gaba,suka hada idanu da shahida dake bayanshi,kowacce nata idon cikin na 'yar uwarta,sake kallon shahidan nafisa take sama da qasa,kishinta na ratsata,ta sake kyau da aji fiye da daa,duk da cewa ba zata taba mance fuskarba,duk da cewa ta ganeta amma saita janye idonta daga kanta ta rufawa anwar baya,tana jin wani abu na sukar zuciyarta,da kallo tabi bayan shahidan har suka wuce,sannan taja qwafa ta wuce,tanajin a zuciyarta wannan karan kam ba zatabi shawarar mima ba,zuciyarta takai maqurar da bazata iya jurewa ba.

Yana gaba tana binsa a baya cike da kunya har cikin babban falon anty usaina,gaba daya yaran suke miqe suna musu sannu da zuwa,sa'ida ta soma tare shahida ta rungumeta
"Oyoyo anty,uncle,amma bakacemin zakuzo da anty ba yau"
"To ai gata kin ganmu" ya bata amsa yana zama saman daya daga cikin kujerun,yayin da maibin sa'idan ta haura sama donta shaidawa anty usainan zuwan sun tana cewa
"Yanxu ma tahau saman,anty nafisa ce tazo dubata" cikin shi da shahidan ba wanda yace komai ba,itakam nunawa ma tayi kaman bata santa ba bare ta ganeta,sunata taba hira da sa'idan,yayin da shi kuma ya shiga tunanin me nafisan tazoyi gidan anty usainan?.

Dawowa tayi ta shaida musu tace su hau saman,shine dai a gaba tana binsa a baya har suka bayyana wani falon dake daman,anty usainan na zaune qasan carfet suka shiga da sallama,fuskar anty usaina wadace da fara'a takewa shahidan lale kota anwar ma bata biba,a kunyace ta zauna gefan anty usainan tana jin anwar na tambayar antyn fitilun harabar gidan da wasu suka mutu
"Ka qyalesu hakanan tunda dai gidan da haske ai shikenan" saita sake maida kanta ga shahida wanda kanta ke sunkuye a qasa,gaidata tayi a kunyace anty usainan ta amsa cikin kulawa,Shahidan ta mata sannu da jiki ta amsata
"Aina warware alhmdlh,shine sai daya tattagoki" qaramin murmushi ta saki kanta a qasa cike da jin kunya da nauyinta,daidai lokacin sa'ida ta shigo dauke da tray wanda ta cikashi da kayan ciye ciye,kai tsaye ta aje gaban shahidan,ta durqusa tana zuba mata duk abinda ke cikin farantin,qasa qasa shahidan ke kallonta tana dariya idanu a waje yadda su anty usaina bazasujiba tace
"Sa'idah,wannan duka?,aisai cikin antyn taki ya fashe"
"A'ah anty kici wallahi,yauke baquwarmuce ta musamman"
"Mu kuma aisai a koramu ko?,yauni aka yiwa danwaken zagaye saboda kin ganta ko?" Tana dariya sa'idan ta daga kai daga shiryawa shahida cake da take cikin plate ta kalleshi cikin dariya
"Ba haka bane uncle nina isa?,kawaidai nasan ka gayamin cewa kaida anty abu guda ne,kaga idan na bata kamar kai na baiwa" murmushi yayi yana daga mata hannu yana satar kallon shahidan,shi sam ya mance daya gaya mata hakan,ya fada ne a gaban anty usaina don sake kwantar mata da hankali da amintar mata tunaninta,saidai ya manta

35 / 53