Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   20 / 53

57K to 60K   out of 156.9K words

bakin dan qaramin fridge dinta tana ciro masa ruwa da lemo,saita waiwayo tana dubanshi,murmushi ya qwace mata
"Wani abu makamancin haka bai taba shiga tsakanina dashi ba,kar ka saka komai a ranka,kai kanka shaida ne na wace shahida,abu mai sauqi ne samun hanya zuwa zuciyata kai tsaye har haka?" Maganar tata ta bashi qwarin gwiwa,sai yayi shuru yana nazarinta,harta dawo ta aje masa lemon da ruwan a gabanshi,yayin dashi kuma ya dire mata ledar daya shigo da ita
"Ga abinci nan,inajin kamar kina da buqatarsa shi yasa dana tsaya naci nayo miki naki takeway din,don nasan ko xuwa nayi nace kizo muje muci taren ba zuwa zaki ba" ya fada cikin jefanta da magana,tasan yana jin haushin hakan,ita kuma ra'ayine sam bata dashi,sabida haka tayi murmushi kawai,ko yanzun ma ba zata iya cin abinci yana kallonta ba shina ya sani,amma duk da haka saiya soma bude mata ledar yana cewa
"Kiyi haquri yau dai daya kici a gabana,saimu tattauna abinda ya kawonin,kada lokacin break dinki ya qare na shiga haqqin company",bai gama budewa aka sake bude qofar aka shigo,dukansu suka maida hankali ga qofar,saddam ne hannunshi dauke da ledar gidan abincin dake daura dasu,wanda shahida tafi order abinci acan,fuskarsa cike da murmushi ya nufosu kai tsaye ba tare daya dubi nuradden ba ya iso gabanta,dora abincin yayi saman na nuradden daya bude mata yace
"ga favourite dinki nan", wani abu ne ya takorewa nuradden wuya,ya daga kai ya kalli saddam cikin fushi
"Wanne irin rashin hankaline malam?" Dubansa saddam yayi
"Da akayi me?"
"Ta yaya zaka shigo kai tsaye ba tare daka nemi izni ba,sannan ka samemu zaune zata ci abinci ka dora wata ledar a sama?" A dage saddam yace
"Matarka ce?"
"Koba matata bace ina zaton tare ka ganmu" cikin halin ko in kula yace
"Auto da sauqi abun,kaga kenan allurar cikin ruwa ce,mai rabo ka dauka" ran nuradden saiya kai qololuwar baci,hakan ya sanya shahida ta dubi saddam
"Banason tashin hankali saddam,meye haka?" Baison nuradden ya gane cewa bai taba furta mata kalmar soba bare ya sake samun qwarin gwiwa,hakan ya sanya ya dubeta
"Ba manufata na bata miki rai ba,sai anjima" ya juya ya fice.

Sosai yake jin babu dadi cikin ranshi,saiya dubi shahidan
"Shahida...tsorona da fargabata ta sake daduwa,inajin har cikin raina bani da tabbas idan har baki amsa min cewa ni kikeso ba kuma ni xaki aura ba" gaba daya sai lissafinta ya nemi dagulewa,batason ta dauki alqawarin da zai zame mata ciwo ko nauyin da wuya ta zaiyi wahala ya iya dauka,saboda haka cikin sanyin murya da kwantar dakai tace
"Tsoron meye haka nuradden,ka kwantar da hankalinka don Allah".

Duban nafisan yayi fuskarshi a hade" me kikayi haka kenan?,me yasa tun farko baki duba lafiyar atm din naki ba saida kika gama siyayyar?,bayan kinsan accnt din aya samu matsala sai xuwa gobe zai soma aiki?"langabe mishi kai tayi
"Please anwar...don Allah kayi magana da mai kamfanin gaba daya,na tabbatar ka sanshi tunda naji kace bakason yasan ka shigo kamfanin,tunda ka bada rabin kudin yanzu zai amince ka aiko da saura idan ka koma office,Allah wannan sarqar nasha wahala na dade ina nemanta,kuma kanaji suma sukace dsign dinta kadai yayi saura,ba lallai idan na ajeta naje na dawo na sameta" idanunsa ya lumshe kaman bazaice komai ba,haka kawai yakejin kasala tunda ya tashi yau,hakanan zuciyarsa da jikinsa sam babu dadi,baice komai din ba ya fita daga wajen da kanshi ya taka zuwa sashen biyan kudi,suka tarbeshi don tunda ya shigo kamfanin suka gane waye,hakan ya sanya suketa nan nan dashi,daya daga cikin ma'iakatan ya yiwa magana yana son ganin rayyan
"Ranka ya dade,oga bai shigo ba,amma babu damuwa zaka iya ganin rahama" dan shuru ya sake yana fidda wayarsa daga aljihunsa ya duba lokaci,sannan ya lalubo wata number ya kira,bata shiga ba,duka lambobin rayyan din basa tafiya,saiya sake kiran wata number din,ba jimawa aka daga,ya ambaci adadin kudin da yake buqata ya gaya masa inda zai kawo masa
"In sha Allah yallabai ina hanya" daga haka ya maida wayar aljihunsa
"Ai...ranka ya dade basai ka zauna jira ba,rahaman kawai zaka yiwa bayani shikenan zata shigar ne cikin kundin bayanan shiga da fitar kudi na kamfanin" lokaci ya kuma dubawa,shi kansa baison zaman,saboda jiransa da ake,banda ya riga da yayiwa nafisan alqawari kuma baison rashin cika alqawari da baiga abinda zai zaunar dashi har haka ba
"Ba damuwa,bani number din office din"
"To ranka ya dade" ya fada yana gaya mishi cikin sauri kai tsaye ba tare da an sanar da mai office din ba saboda sanin wayeshi baida buqatar sai sun hadashi da mai masa iso,a nutse ya juya ya soma takawa
"Ina zaka?" Nafisa dake addu'ar Allah yasa su gama lafiya su fita lpy karya hutsance mata ta tambaya
"Ki jirani" kawai ya fada yanayin gaba.

Kallon number office din yayi sosai sannan yaja da baya ya kalli qofar,ya dora hannunshi saman handle din ya tura a hankali wanda hakan ya sanya basuji alamun bude qofar ba.*zafafa biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wannan number*

07067124863

*ko kuma*

09032345899


*Alqawarin Allah*
2️⃣4️⃣

"Hankalina bazai taba kwanciya ba idan ba ganinki nayi a gidana a matsayin matata ba...shahida" ya kira sunanta yana miqewa zuwa gabanta,gab da ita ya zauna akwai kusanci sosai tsakaninsu,tanason sake ja baya ta kasa,ya saka hannunshi cikin aljihunsa ya ciro zoben rannan daya siya ya bata tabar masa abinsa cikin mota,ya bude gidan xoben ya ciroshi
"Ki yarda mu qulla wanna yarjejeniyar tsakanina dake yanzu yanzu shahida,ita kadaice zata dan kwantar min da hankalina" bata ankara ba ya kama yatsanta yana ci gaba da roqonta,wani abu anwar yaji ya dakar masa tsakiyar kai,yayu yunqurin juyawa ya fice daga office din salin alin kaman yadda ya shigo,saidai ya gagara haka,ji yayi kaman an kafeshi idanuwanshi a kansu,ya gaza daga qafarshi bare ya juya ya fita din,da hanzari shahida tace
"Sakemin yatsa nuradden...basai ka saka..." Bata qarasa kaiwa ba ya soma zura mata zoben,bansan ya akayi ba,baisan ta yaya ba ya tsinci kanshi da furta
"Stop it!" Cikin tsawa da hargagu,idanuwanshi na sauya kala,wanda yayi sanadiyyar rashin shigar zoben yatsanta,dukkansu waiwayawa sukayi don ganin waye,ga tsammanin nuradden saddam ne ya dawo,amma sai yaga bashi bane,matashin saurayi ne da shekarunsa suka tasamma talatin da biyar,mai kyau kwarjini da cikar zati tsaye yana dubansu,idanunshi qyar kan nuradden din,yayin da idanun shahida ke kanshi,mamaki yaso daskarar da qwaqwalwarta,me yake nan?,me ya kawoshi?,yazo ci mata mutunci ne?,koko yazo tozartata cikin mutane ne kaman yadda yayi mata wancan karon,anya ma shine kuwa?.

Idanunsa har yanzu nakan nuradden suna kallon kallon har zuwa sanda ya soma takowa zuwa cikin office din hannayensa soke a aljihunsa,cikin wata izza da taqama,qarfin gwiwa da qarfin halin da sam baisan yana nunashi ba muraran.

Kafin ya qaraso shima nuradden din ya miqe tsaye yana dubanshi gami da jiran isowarsa,a qalla kusan minti daya sukayi suna duban juna,taqin dake tsakaninsu kadanne,cikin wata murya dake cike da ginshira isa da bada umarni yace
"Kar ka sake gangancin aikata haka,idan ba haka ba?...."
"Idan ba haka ba me?" Nuradden ya maida masa cikin zafi
"You will regret it!" Ya qarasa cikin tsawa,murmushin baqinciki da kishi nuradden yayi,wai me yasa yayi saken da har yanzu bai mallaki shahida ba?,me yasa yayi bacci har akeson kawo masa farmaki?
"Ina tunanin kana cikin masu sonta ko?" Ya fada yana waiwaya ya dubu shahida dake tsaye tana dubansu kaman wadda ta zama bebiya
"To ka makaro,don kuwa shahida tawa ce,mallakina ce,hakanan baka da wani hurumi na shiga sabgata da ita,idan ma kace zakayi gigin shiga kunyace da nadama a qarshe zata riskeka,yadda ka ganmu haka zaka barmu,kayi kadan ka shiga tsakaninmu,baka da qarfi iko ko izzar rabamu,tarayyata da shahida ba muhallin shigarka bane,bama kaiba,har wani ma dake iqirari ko gigin cewa yana sonta" idanunsa ya lumshe kalaman nuradden na sauka cikin kunne da kwanyarsa,yau shi ake furtawa kalaman nuna iyaka akanta?,wani abu mai nauyi ya sauko saman zuciyarsa,ya bude idanunsa dai dai lokaci da shahida ke cewa
"Please noor,wannan baikai abunda zaka bata ranka akai ba,nida kai mutu ka raba ne,qaramin dalili ko qaramin abu irin wannan yayi kadan ya raba tarayyarmu nida kai" tayi maganar kanta tsaye,direct daga zuciyarta ta hada kalaman,idanunta akanshi,sai ya qarasa bude idanun nashi gaba daya ya watsasu a kanta,ta kauda nata idon da sauri tana baiwa kanta qwarin gwiwa dason yin ramuwar gayya ko sau daya ne kafin wannan damar ta kubce mata,tana son ko sau daya ne yaji ciwon rai ya kwanta yana tuna kalamanta
"Me kakeyi ne anwar?" Yaji tambayar tsakar kansa,kaman an sake doka masa wani abu,yadan runtse idonsa kansa na sarawa daya tuna ainihin abinda ya kawoshi office din
"Assalamu alaikum,ranka ya dade...yallabai din ya shigo,ya nemi ma yin magana dakai" wata murya ta ratsasu duka su ukun,ya waiwaya yana dubanshi,ma'aikacin daya baro dazu ne a daya sashen,sai ya jinjina masa kai ya juya ma'akacin shima cikin girmamawa ya fita.

Kallonshi ya maida kan nuradden ba tare daya dubi shahidan ba,ya murtsa yatsunsa sosai kaman mai neman attention dinsa,ya sakar masa murmushi sannan ya juya cikin wani irin sauri ya bude qofar office din ya fice.

"Wash" shahida ta fada tana dafe kanta tare da duqawa kadan kaman mai ciwon ciki bayan fitar tashi
"Subhanallah" nuradden ya fada da sauri yana nufota,da sauri ta daga masa hannu ta koma da baya ta zauna kan kujera,gabanta ya qaraso ya duqa yana tambayarta,ta nuna mishi kanta
"Sannu,kiyi haquri don Allah,banzo nan da niyyar wani abu mara dadi ba,nazo ne muyi magana dake ta qarshe kuma ta fahimtar juna,bansa ya akayi duka hakan ta faru ba"
"Ba komai,gida nakeson tafiya"
"Muje na kaiki" ya fada cikin nuna kulawa yana miqewa,da gaske kan nata ke mata ciwlo sosai,saboda haka taja wayar office din,ta bada uzurin barin office dinta ba tare da lokacin tashi yayi ba.

Cikin girmamawa rayyan ya tarbeshi,ya bashi hannu suka gaisa sannan yaja masa kujera ya zauna
"Yallabai kai da kanka?,a maimakon kayi tafiyarka kawai saika tsaya bada excuse?" Murmushi anwar ya saki yana shafa kanshi dake masa ciwo
"Doka ce bai kamata ace mune muke karyata ba"
"Kasan yanzu tsarin ya canza,account dinka idan ya zamana kudi na yawan shiga da fita suna saka ido akanshi saboda yadda barayin gwamnati ke bude account kala kala suna aje kudaden al'umma da suka diba,qasarmu saidai addu'a kawai"
"Wallahi yallabai,abubuwan kullum qara dagulewa suke,saidai fatan dacewa" hira suka shiga yi data shafesu,wanda bai jima ba sukayi sallama dash ya fito.

A reception ya tadda nafisa yana kai kawo,tana ganinshi ta qaraso inda yake
"Inata neman inda ka shiga...."bai amsata ba ya ciro waya da aljihunsa yayi kira yana buqatar qarin mota guda daya,sai daya kammala sannan ya dubeta
"Zasu zo su daukeki,ni xan wuce inda da baqi,ki tafi da duka kayan da kika zaba babu matsala"
Da ido ta bishi sanda yake takawa don ficewa daga katafaren wajen,tana mamakin sauyawarshi lokaci guda,iyaka tunaninta ka gaza ganowa,tilas ta samu waje ta zauna,lokaci lokaci tana duba lokaci gami da bin jama'ar dake kai kawo a wajen da kallo.

Gefanta ta kalla kamar wadda aka baiwa umarni,take idanunta suka sauka a kanta tana takowa a hankali cikin nutsuwa nuradden na binta a baya,cak ta miqe tsaye tana ci gaba da kallonta har zuwa sanda ta fice daga ginin gaba daya,duk data ganta da wani amma sam hankalinta da zuciyarta sun kasa kwanciya,yanayin anwar daya sauya lokaci daya shi ya fado mata a rai,ko ita ya gani?,gabanta ya sake faduwa hankalinta ya tashi,itakam ta shiga uku,bata qaunar duk wani abu da zai hada anwar da shahida koda na bacin raine bare na mutunci,lallai tana buqatar qarin bayani,hakan ya sanya ta taka har zuwa reception
"Sannu malam" ta fadi tana duban daya daga cikin receptionist din
"Yauwa,kina da buqatar taimako ne?" Ya fada yana karantarta a nutse ganin kaman hankalinta bai jikinta,yaga kuma da wanda sukazo din tun dazun
"Eh...don Allah tambaya gareni"kai ya gyada
"yi tambayarki" duban hanyar da shahida tabi ta wuce tayi kaman har yanzu tana wajen sannan ta maida dubanta gareshi
"Don Allah malam wannan matar data fita yanzun nan ita da wani,ma'aikaciyarku ce?" Shima qofar ya kalla sannan ya kalleta
"Eh" yace yana gyada kai
"Yauwa,don Allah ina take?,sannan tana da aure ne ko tayi aure?"
"Kiyi haquri madam,gaskiya bama bada imformation haka kai tsaye game da duk wani ma'aikacin wannan kamfanin,idan kana buqatar ganinsa ne ka iya samunshi a nan"gyara tsaiwarta tayi,tana son sanin wani abu game da rayuwar shahidan,zataso qwarai ace a shekarun nan tayi aure kodon tabar mata anwar din ta samu nutsuwa ita kanta,ta daina fargaba kullum dare game da ita ko dawowarta rayuwarsu
"Kaga ba wani abu bane,childhood friend dina ce,na jima ina nemanta ban samu ganinta ba sai yau,kuma nayi qoqarin na tareta muyi magana amma ta kubcemin bansan ina tayi ba"
"Kiyi haquri doka ce ta kamfani" ba yadda batayi ba amma bata samu komai akanta ba,hakanan ta juya a sanyaye tana jaddadawa ranta dole ta sake nemo mima,tana shirin zama driban da anwar ya turo ya qaraso yayi mata magana kan ta taso su wuce,haka ta fita daga kamfanin jiki babu qwari tana danasanin rakiyar data roqi anwar yayi mata.

*12:45 pm*


Idanunsa qyar bisa rubutun dake kan screen din computer dinsa,ya gama tsara duk wata yarjejeniya ta kwangilar da zasu amsa,amma ya kasa fahimtar meye gyara meye daidai cikin rubutun bare ya tura,dogon tsaki yaja wanda kana ji kasan akwai abinda ke tafasa zuciya da tunzurashi,maimakon ya tura sai kawai yayi serving dinsa a draft,ya rufe cumputer da qarfi har screen din ya bada qass da alamu ya masa lahani.

Miqewa yayi yakai ya kawo sau biyu tsakiyar dakin nashi,sannan ya sake juyawa ya isa bakin window din daki,ya zuge labulen gami da budesu gaba daya,iska mai sanyi irin ya daren daya soma nisa,darenma na damina ta soma shigowa,ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yana kallon sama da yau tayi fresh da taurari tare da fatan zafin da yake ji cikin zuciyarsa zai samu ya ragu,runtse idanunsa yayi karo na barkatai

_ina tunanin kana cikin masu sonta ko,to ka makaro,don kuwa shahida tawace,mallakina ce,hakanan baka da wani hurumi na shiga sabgata da ita,idan ma kace zakayi gigin shiga kunya ce da nadama a qarshe zata riskeka,yadda ka ganmu haka zaka barmu,kayi kadan ka shiga tsakaninmu,baka da qarfi ko iko ko izzar rabamu,tarayyata da shahida ba muhallin shigarka bane,bama kaiba,har wani ma dake iqirarin ko gigin cewa yana sonta_

Kalaman nuradden suka dawo masa fes kamar ma a sannan yake furta masa su,kalaman da yau wuni sur su suka dinga qona mishi rai,suka hanashi dukkan wani sukuni da walwala,baya tunanin tsahon rayuwarsa bayan labarin mutuwar mahaifansa akwai kalaman da wani ya gaya masa da suka hanashi sukuni irin wannan,bai tabajin anci mutuncinsa ko anci masa fuska ba kamar haka
"Shashasha,zaka ganne koni waye,zaka ganne qarfina isata da kuma izzata"ya fada afili zuciyarsa na yanke masa shawarar abinda ya kamata yayi.

_please noor,wannan baikai abunda zaka bata ranka akai ba,ni da kai mutu ka raba ne,qaramin dalili ko qaramin abu irin wannan yayi kadan ya raba tarayyarmu nida kai_

Girgiza kansa sosai yayi zuwa hagu da dama,kalaman shahida na sake amsa kuwwa cikin kunnensa,ware idanunsa yayi murmushi ya subuce masa shi kadai
"Zaki fahimci cewa nidin ba qaramin dalili bane keda shashashan masoyinki"ya furta sanda yake qoqarin rufe windows din dakin jin yayyafi ya soma sauka,yanajin bai kamata ya qyale nuradden ya furta masa wadan nan kalaman ba ya kuma ci bulus,bai kamata ya qyale shahida taci gaba da rayuwarta yadda taga dama ba,yadda ta tsaida duk wani aiki na zuciyarsa ya kamata itama tata zuciyar ta tsaya,bai kamata ace zuciyarta taci gaba da aikin da har xata karbi wani a matsayin masoyi ba bayan ta quntata tashi,ta kuma barta a rufe ruf,ta sanyata ganin baqi da baiken soyayya.

A nutse ya hada abincinsa yaci sosai,don ya gama yankewa kanshi shawara,kuma shawarar ta karbu dari bisa dari cikin ransa,hakanan yaji duk wani nauyi dake qirjinsa ya sauka,walwalarshi ta soma dawowa,hakan kuma yana jin bai rasa nasaba da nunawa nuradden kurensa da illar lafazin da yayi a gareshi da zaiyi.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Kofin kunun hannunshi ya aje yana duban anty usaina
"katsina zan wuce,ko kina da wani saqo wajensu inna?" Cikin mamaki take kallonshi
"Katsina kuma anwar?" Kai ya gyada yana murmushi
"Mamaki kikayi anty irin wannan kallo haka?"
"Ai dole nayi mamaki,idan zaka katsina ba haka muka saba yi dakai ba,hasalima saina tursasaka kafin kaje,wani lokaci ma saika zabi lokaci da kanka,baka taba cemin zaka katsina haka katsaham ba sai yau,kodai wani abu ya faru acan ne kake boyemin?" Sai ta bashi dariya ganin yadda duka ta damu,har yanzu bata daina damuwa dashi da lamuransa ba
"Anty na,babu wani daya faru,shikenan Allah baya shiryar da bayinsa duk sanda yaga dama,da da nake qin zuwa yanzu Allah ya shiryeni shikenan?" Kai ta kada
"Allah yasa"
"Yasa ma" ya amsa yana murmushi
"Atamfofi ne kawai zan baka ka kaiwa innan kayan sallarsu dana saba basu,sai kuma sannu da jiki da zakace ina yiwa basira"
"Gsky banjin zan samu zuwa gidansu basiran,saboda ayau nakeso na dawo"
"Shikenan,mayi waya" ta fadi tana miqewa don shiga ciki ta debo masa saqon.

Zuwa qarfe sha biyu na rana ya gama duk wata siyayya da yakanyi musu a sanda zaije katsinan waje kakanninsa wadda ta haifi mahaifinsa,kasancewarsu masu qaramin qarfi sosai,daya na raina ya dauki hanya,ya saki ajiyar zuciya yana qissima yadda abubuwan zasu kaya idan ya isa can.*zafafa biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqatar siya zaki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899


*Alqawarin Allah*
2️⃣5️⃣

Tafiyar awa biyu cif ta shigar dashi garin katsina,tuqi yayi lafiyayye cike da nutsuwa da kuma tunani kala kala,kai tsaye unguwar kakanninsa ya nufa.

Yana qoqarin parking motarsa kawunshi modu ya fito da alama masallaci zashi saboda yadda yake dan hanzari,bai ganshi ba

20 / 53