Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 53

3K to 6K   out of 156.9K words

DINπŸ‘‡πŸ‘‡_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layinπŸ‘‡πŸ‘‡
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*πŸ‘‡πŸ‘‡

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuΙ—i gida masoyan asaliπŸ˜‰πŸ˜»πŸ₯°πŸ₯°πŸ˜πŸ˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ‘ŒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»_*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*πŸ™πŸ½

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos


***
0️⃣2️⃣


Qarfe biyu na rana suka shigo gidan ita da huda,a falo suka tadda anty zubaida gabanta plate ne dauke da alala guda uku tana ci
"Wash" kadija ta fada tana zama saman kujerar dake falon,sannan ta zame dankwalin kanta don tasha iska,dogon gashinta da bashi da cika saboda santsi da tsahonsa ya bayyana
"Ina kuka jima haka yau?" Muskutawa shahida tayi,muryarta dauke da alamun gajiya tace
"Kin manta na gaya miki muna shirye shiryen ziyarar da mai makarantarmu zai kawo mana next week?"
"Af,na manta haka ne fa....amma da alama ba qaramin shiri kukewa zuwan nasa ba,ga dalibarku nan ta kasa zaune ta kasa tsaye" inji anty zubaida tana duban huda dake zare safarta tana dariya,yatsina fuska shahida tayi cike da qosawa
"Nima abun duk ya soma ginsata anty,duk sun d'aga hankalinsu duka malaman makarantar.....amma hakan qila baya rasa nasaba da halayyarsa,don a yadda kausar ke gayamin bashi da sauqi sam,kuskure kadan zai gani da bai masa ya dauki mataki,don bai qaunar abinda zai taba students din,last year yazo lokacin ban soma koyarwa a makarantar ba"
"To Allah ya taimaka yayi jagora...kece ma,da kin amshi aikin kamfaninsu abban huda da duk wannan jigilar kin huta da ita,har mota zasu baki kyauta saboda matakin da aka baki aiki akai yakai a bakin" murmushin gefan baki kawai tayi,sannan tayunqura ta miqe tana tattara mayafinta zuwa dankwalinta da jakar makarantarta
"Au....kinga naso na manta...nuraddin ya bada saqo,yayita kiran wayarki wai bai samu ba" cak shahida ta dakata da abinda take ba kuma tare data juyo ba,fitar furucin daga bakin anty zubaida zuwa kunnuwanta jinsu take kamar harbin bindiga
"Waima....ina kika aje wayarki?,nayita kira ni dinma ban sameki ba......anya shahida anya?,sai yaushe zaki saki ki koma dai dai?,saboda nuradden ne kika kashe wayarki?,nuradden kuwa deeja ya cancanci haka kuwa?" Batasan idanunta sun soma fidda hawayen da suka cikasu ba sai data ji saukarsu kan hannunta dake cukuikuye da mayafinta,kasa jure tsaiwa tayi saitayi gaba cikin sassarfa.

Da kallo anty zubaida tabita harta bacewa ganinta sannan ta girgiza kai tana furta
"Allah ya kyauta" bata sake tankawa ba saita maida hankalinta kan alalanta da take ci.

Ganin har huda ta gama komai shahidan bata sake ko leqowa ba,sai anty zubaida ta bawa hudan saqon tace ta shiga ta kai mata,sannan ta gaya mata ta fito taci abinci.

Qarfe hudu na yammaci ta fito a shirye tsaf cikin doguwar riga abaya wadda ta wadatu da adon duwatsu,tayi rolling da wadataccen mayafinta,tayi kyau duk da babu ko digon hoda fuskarta bare akai ga kwalliya,hakanan idanunta tarwai suke babu kwalli ko d'aya a cikinsu.

Ci gaba da kallonta anty zubaida tayi harta kammala tsakurar alalen sannan tace
"Zanje na dubo umma"
"Saikin dawo,Allah ya tsare,bari na baki saqo" ta fada tana miqewa zuwa cikin dakinta,mintina qalilan ta fito da leda ta miqa mata
"Gashi kikai mata" hannu biyu ta saka ta amsa sannan tayi mata sallama ta fice daga gidan,don 'yar rakiyar tata huda yau akwai islamiyya ta riga data wuce kuma,tilas ta wuce ita d'aya.

A hankali take takawa zuwa bakin titi,jikinta a mace yake kamar yadda take jin zuciyarta sam babu wani qwarin gwiwa ko karsashi tattare da ita,tun daga can nesa ta hango shigowar motar,kallo d'aya tayi mata ta gane motar kota wace,hakan yasa ta sake tsananta d'aure girarta gami da kau da fuskarta tamkar bata ga motar ba.

Ilai kuwa yana zuwa dab da ita ya rage saurin motar,saidai yadda ta dauke kai tare da qara saurin tafiyarshi ya hanashi damar ce mata komai,tana jinsa ya qara yin gaba,hakan ya nuna mata reverse zaije yayi ya dawo,don haka ta qara sauri,cikin sa'a ta cimma titi kafin ya juyo ta samu abun hawa ta shige ko waiwayenshi ma batayi ba bare ta san ya iso ko bai iso ba.

Tsam tayi da ranta cikin abun hawan lokacin da yake sake kusantata da ainihin unguwarsu,wadda anan komai na rayuwarta ya samo asali,a nan duk wani babu na quncinta ya bude,anan komai ya wanzu ya kuma wakana cikin shafukan rayuwarta.

Tafiyar mintina talatin suka iso,ya gangara da ita cikin layinsu kamar yadda ta saba aduk lokacin da tazo unguwar tasu bata sauka a titi saita dangana da qofar gidansu,kanta ta dauke gefe guda lokacin da sukazo gifta wani katafaren gida,bata maida kanta ga kallon gabanta ba har sai da suka isa qofar gidansu,sauka tayi ta sallami mai motar tana cusa kai cikin gidan gami da yin sallama.

Fakadeden tsakar gidan nasu wanda ada can zamanin quruciya takejin babu wajen daya kaishi dadin xama da dadin yin wasa,kafin wasu murd'addun al'amura su zama silar da zaman tsakar gidan ya zame mata tamkar zama kusa da ramin maciji,babu kowa a tsakar gidan saidai a share yake sarai fes cikin tsafta da kulawa,batayi mamakin ganin babu kowa din ba don tasan a irin wannan lokacin saura qannenta na islamiyya.

Daga falonta ta amsa mata sallama,shahida taci gaba da takawa har zuwa qofar falon ta sabule takalmanta ta shiga tana sake maimaita sallamarta.

Cikin sanyi ta amsa mata kamar kowanne lokutta,wanda hakan kusan ya zame musu jiki ita da umman tata
"Yanzu kike tafe?" Umman tata ta fada cikin jin nauyin d'iyartata wanda har yau ya kasa barinta
"Wallahi umma,na manta yaune ranar da nake zuwa sai wajen uku na rana na tuna"
"Da kin bari sai gobe ai,tunda yamma tayi.....mubina ma ta riga da tayi wankin harsun bushe ta shanya,tunda taga rana ta soma baki zoba tace wataqila yau yaya ba zata samu zuwa ba"
"Me yasa?,da ta jirani ai ina kan hanya" gaida ummantata tayi ta amsa tana tambayarta anty zubaida huda da mai gidan,ta miqa mata saqon da anty zubaidan ta bata wanda itama batasan meye a ciki ba,bayan umma ta gama godiyarta ne kuma shuru ya biyo baya,shahida ce ta dinga qoqarin sako hira jefi jefi,ko kusa a yanzu batason yadda umman take qin sakewa da ita,kaman ba ummanta ba?,komai ya canza tsakaninsu tun shekarun baya da suka shude.

Qarfe biyar ta shiga kitchen ta soma dorawa ummantata abincin dare da taga tana niyyar daurawa,ita kuma tana daga tsakar gida zaune kan tabarmar da suka shimfida,duk wani motsin rahama na kan idanunta,itama rahaman ta ankara da hakan saidai ta nuna bata kula ba,irin wannan kallon umman tata ta saba binta dashi da dadewa,kallon tausayi,kallon nadama,kallon kaicon biyewa son rai da son zuciya da sukayi ita da mahaifin rahama shekarun baya da suka shude,har hakan yaso jefa diyar tasu cikin hallaka,da tuni yanzu bayan shudewar mai gidan ita daya zata ci gaba da kurbar baqinciki da bacin ran abinda suka aikatawa rayuwar rahaman.

Qarfe shida qannenta nata suka shigo,ta bisu da kallo sanda suke shigowar cikin jin dadi tare da musu addu'a cikin ranta,koda yaushe tana jin dadi har cikin ranta na yadda rayuwarsu ta banbanta da tata rayuwar a sanda take da shekaru kamar nasu,kallo daya zakayi musu kasan suna samun kulawa da tarbiyyar data dace,mubina ke bin rahama(shahida),sai khadija,faruq,sajid sai qaraminsu nasir.

Dukkansu fuskarsu qunshe da walwala suka iskota,ta jima cikinsu yayin da mubina ta amshi aikin girkin,tana yi suna hira da yayarta da sauran qannunta.

A nan kan qatuwar tabarmar suka ci gaba da zama,suka gabatar da sallar magariba,sannan mubina ta zuba abinci cikin babban tray.

Gaba dayansu kowanne ya sanya hannunshi suka soma ci,suna hira lokaci lokaci,har cikin ranta tana jin dadin kasancewa cikin 'yan uwanta,saidai wannan kallo da duba da umma ke mata tana qaunar ya gushe daga idanunta,ta manta da faruwar komai,ya zama tarihi kamar ma bai taba faruwa ba.

Sallamar usman d'an maqotansu shi ya katse hirar tasu,ya gaida ummansu sannan yace
"Ana sallama da anty shahida" hada idanu sukayi da umman,yayin da kowa abinda ke yawo a zuciyarsa ya tashi daban da na d'an uwanshi,qas da kanta shahida tayi tana kokawar hadiye lomar tuwon data riga ta saka abakinta,batakai ga hadiyewa ba saqon usman ya shiga kunnenta,sai taji gaba daya abincin bai mata dadi a bakinta,ya kuma gagara wucewar,hakan ya sanya ta miqe tsam ta isa bakin rariyarsu ta zubda tuwon sannan ta wuce dakin umman ba tare data bi takan aiken da akayo mata ba.

Suya kawai qirjinta yake,waye wannan yakeson mata kutse ne cikin rayuwarta a sanda bata shiryawa hakan ba?,waye shi da zai tunkari rayuwarta a sanda bata da dukkan wani tsari akan kowanne d'a namiji?.

Shigowar umma dakin shiya katse mata tunaninta,ta yunqura ta miqe ta zauna sosai daga kasalalliyar kwanciyar da tayi,wani mummunan tashin hankali ya ziyarceta sanda ta dubi idanun umman taga hawaye na biyo kuncinta,cikin matuqar rudewa da gigita tace
"Um....umma...hawaye fa kike umma meya sameki?,don Allah kibar kukan,kiyi shuru kice wani abu"
"Dole nayi kuka shahida....bazan daina kuka ba harsai sanda abinda yake damuna ya gushe,tashin hankalin da kika shiga kadai sanda aka aiko kiranki ya tabbatarmin akwai sauran rina akaba,kuma hakan ke nunamin cewa dafin da muka zuba a zuciyarki har yau bai gama wankewa ba" zamowa tayi daga saman kujerar tayi gurfane a gaban umman tata itama hawaye na sakko mata cikin tashin hankali
"Ko kad'an umma,kufa iyayena ne,kune kukayi silar zuwana duniya,umma....ba tun yauba na gayamiki ki goge duk wani abu daya faru daga ranki,ki daina alaqanta duk wani yanayi da zaki gani tattare dani da cewa laifinku ne"
"Indai kinason hakan ta faru shahida ki koma yadda kike....ki amshi wani cikin masu sonki kiyi aure,anwar bashi kadai bane namiji da don ya miki wani abu zai zama silar da zaki maida kanki wata aba daban ba,indai ina ci gaba da ganinki a haka baki sauraren kowa bare akai ga batun aure bazan daina zargar kaina ba har na koma ga mahaliccina,kamar yadda mahaifinki bai daina zargin kanshi ba har ya koma ga mahaliccin......" Maganar tata saita riqe,kuka sosai ya qwace mata,tana tuna abubuwa marasa dadi da suka faru a rayuwarsu,tana tuna komai tar cikin kwanyarta,qaruwar kukanta ya qara dasa tashin hankali a zuciyar shahida,wadda ta miqe ta figi mayafinta cikin rawar murya tace
"Zanje,zan fita umma indai hakan shi zai sanya farinciki da walwala a cikin zuciyarki" bata qara second guda ba tayi waje,kai tsaye kuma ba tare da saurarar komai ba ta wuce zuwa qofar gidansu.*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGπŸ™πŸ½*
πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos



0️⃣3️⃣

Jingine yake jikin motarsa ya qurawa qofar gidan idanu,ji yake kaman ya shiga ya fito da ita,ganin fitowarta ya sanyashi kasa tsaiwa jikin motarsa kamar yadda yake tsaye a dazun,sai ya tsaya qyam yana dubanta,ji yake tamkar an masa rahama,shi kadai yasan yadda yake jinta cikin jiki da ruhinsa,wani irin so yakewa shahidan,kamar ya rufe ido ya bude ya ganta cikin gidansa,ta zama matarsa kuma mallakinsa.

"Barka da fitowa,Allah yasa ban takura ki ba" ya fada yana sakin murmushi,duk da ya fuskanci kamar bata cikin ainihin nutsuwarta,kai kawai ta iya gyadawa
"Kiyi haquri idan na takurakin,na kasa jurewa ne,na kira wayarki yafi sau nawa bakya picking,naje gida nemanki na bada saqo amma banga respond ba" ya fada yana tsagaitawa da maganar don ya bata damar cewa wani abu,duk da bashi da yaqinin zata amsa din,tsahon zamanshi da shahida duk daba wani dogon lokaci can suka dauka ba,zai iya qayyade adadin kalmomin bakinta daya ji,ko dama can tun asalin shahida mutum ce mai qaranta magana qwarai,bata da yawan surutu,tafi ganewa zaman shuru da kad'aita.

Ason ranshi ta shiga gaban motarshi ta zauna suyi hira sosai da ita,saidai yasan hakan bamai yiwuwa bane,ko a yanzu daya zo yayi shahadar quda ne kawai,don bai tsammaci fitowar tata ba
"Ko zamu qarasa can ki samu ki xauna karki qosa da tsaiwar" yayi qarfin halin fada yana nuna wani dakali dake qofar gidan nasu gab da qofar shiga zaurensu,a nutse ta daga jigatattun idanunta ta kalli bigiren da yake nunawar,kasancewar akwai wadatar hasken wutar lantarki taga wajen sosai,idanunta ta lumshe wani abu na takore mata wuya,kallon wajen a koda yaushe yakan tuna mata dashi,abinda bata da muradi ko kadan,kai ta girgiza cikin qarfin hali tace
"Nan ma ya isa,don ina saurine zan wuce gida dare yana yi" cikin zumudin da yake yunqurin boyewa ya muskuta kad'an
"To idan babu damuwa me zai hana ki shigo saina saukeki?" Hannunta saman wuyanta kamar wadda ke taba yanayin zafin jikinta,duk da tana jin kamar zazzabin ne ke shirin kamata tace
"Babu buqatar hakan.....zan iya komawa ciki?" Kafin yakai ga bata amsa tuni har ta soma tattaki,kasa cewa komai yayi yana kallonta harta shige cikin gidan.

Sit din driver ya koma ya zauna cikin matuqar kasala da mutuwar jiki,zazzafar ajiyar zuciya ya saki gami da furzo iska mai zafi daga bakinsa,kallon kansa ya shiga yi a madubi,haryau bai gano wani naqasu tattare dashi ba ko makusa daya sanya shahida ta kasa sakewa dashi,iya kyau Allah ya baiwa noraddeen kyau,kudi aji da nasaba,baisan wacce hanya zaya bi ya shawo kan shahida ba,da yana da masaniya kan hanyar da babu shakka yabi ko don ya mallaketa zuciyarsa ta huta da abinda take ji,sai daya kusa a qalla mintuna goma kafin ya iya miqa hannu yaja murfin motar ya rufe ya tadata yabar layin.

Bakwai taso barin gidan,amma ba ita ta tafi ba sai qarfe tara,sai data tabbatar ta kwantarwa da ummantata hankali duk da tata duniyar a rude take,haka ta shirya tayi sallama da qannenta ta wuce gida.

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Sannu a hankali yake takowa cikin gidan saman shinfidadden marbles daya malale ilahirin gidan,hannunshi d'aya soke a aljihun wandonsa yayin da daya yake riqe da wayarshi da yake amsa kiran daya shigo masa,ya jima tsaye tsakiyar qawataccen falon yana amsa wayar kafin daga bisani yayi sallama da wanda suke wayar ya soma qoqarin shiga akwatin tura saqonni.

"Ka iso kenan?" Cewar wata farar mace data fito daga daya daga cikin qofofin dake jere a falon,shekarunta na haihuwa a qalla zasu doshi arba'in da biyar,tana sanye da atamfa wadda tayi matuqar yi mata kyau,a kallon farko idan kayi mata zaka ga kama ta zahiri tsakaninta da anwar,saidai banbancin launin fata,wanda shi tashi fatar choculet colour ce wato wankan tarwada mai kyau,yayin da tata fatar ta kasance fara ce duk da ba irin farin nan can can ba,anty usaina kenan 'yar uwa daya tak data ragewa anwar a duniya,kanshi ya daga ya dubeta sannan ya maida kan wayar yana amsa mata da eh,lokaci guda kuma shima yana yiwa kanshi gurin xama kan daya daga cikin kujerun.

Second goma ya qara ya aje wayar gefanshi sannan ya dago yana gaidata,ta amsa tana tambayarsa yanayin aikin da iyalin gidan alhj sambo,ya amsa mata da duk lafiya kowa yake
"Ina duka yaran?,suna makaranta ko?"
"Eh ai yau tun bakwai suka wuce,saboda anata shirye shiryen zuwanka,duk sai murna suke suce malaman sun shirya abubuwa da yawa" murmushi kawai ya saki,donshi karan kansa yakanji dadi a duk sanda ya tsinci kansa cikin daya daga cikin makarantun daya gina da kansu yaran al'umma kuma ke amfana da hakan,goshinsa yadan shafa kadan sannan yace
"Naji kince nazo anty,Allah yasa dai lafiya" zamanta ta dan gyara sannan tace
"Lafiya lau,kan maganarka ce da nafisa.....naji kayi shuru,yarinyar ta qagu,kuma nima ina kuma tsoron halayyarku ta maza,musamman kai da ludayinka ke kan dawo,kada ya zamana wani abu da zai sauya ra'ayinka ya gitta,ina tsoron faruwar hakan kodan halaccin mahaifinta a gareka" shuru ya ratsa na wani dan lokaci kafin daga bisani yace
"Kawai dai ta kasa sama ranta nutsuwa ne,kishinta yayi yawa,kinfi kowa sanin halayyata anty,so banga abun d'aga hankali ba,komai na rayuwa idan aka bishi da tsari saiyafi bada ma'ana,ina sane kuma sauran wasu 'yan lokuta kadan akai gabar data dace nayi magana" kai take jinjinawa,tunba yauba tafi kowa sanin halin qannin nata,idan yace yes wuya ko rintsi basa sauyashi,hakanan idan yace no to ya bari kenan har abada,bata taba ganin abinda yace A'ah ba daga baya kuma yazo yayi accepting dinsa
"Shikenan,zan mata bayani,Allah ya dafa mana" bai amsa ba ya shigar da wata tambayar
"Zuwa tayi ta sameki?" Ya tambayi anty usaina yana dubanta,tasan halayyarshi tasan meye baiso da wanda yakeso saboda haka ta kada kai
"Wannan ba abinda ya shafeka bane.....ga abun kari can ko zaka karya kafin ka wuce,tunda baka aje mai maka ba" siririn murmushi ya saki kawai yana shafa kansa,sannan ya miqe suka jera da antin zuwa dining suna hirarsu ta zumunci.

"Har yau baku manta baya ba,gargajiyarku tana tare daku" anwar ya fada yana kallom coolers din abincin dake saman dining din,duk da baisan meye a ciki ba amma ya sani cima ce irinta bahaushe ba kayan ciye ciye na bature ba,murmushi anty usaina tayi
"Laifin abbansu,yace manta baua butulci ne" murmushi kawai yayi yana kada kai,ko shi dinma ya fada ne kawai don ya tsokaneta,amma bashi da cima data wuce irin tasu wadda aka gada kaka da kakanni,sam ciye ciye zamani ba kasafai suke burgeshi ba,yakan ci lokaci zuwa lokaci amma ba komai da komai ba.

Tunda ta fara zuba abincin hankalinsa yaji yayi matuqar tashi,duk lokaci haka duk a inda yaga wannan cimar saiya tuna da ita,cimar da a baya bashi da sama da ita musamman da

2 / 53