Author : HUGUMA Category : African Stories & Novels
qararta ba,kuma bance tamin wani abu ba" shuru anty usaina tayi tana nazari,ba shakka tasan halin anwar ciki dabai,kaifi dayane,hakanan qarya bata cikin tsarinsa ko za'a kasheshi kuwa,to amma duk da haka yau da gobe sai Allah,kuma batason nuna masa wani abu mai kama da goyon baya bare yasamu mafaka,saboda haka rufe idonta ta masa fada sosai tace zata kuma nemi nafisan taji meya faru,shidai qarshen magana yace idan ta gaya mata koma meya faru zata iya nemansa,takumayi masa duk fadan da taga dama.
Yana aje wayar suka hada idanu da shahida,ta langabe wuya ta bude baki zatayi magana ya dora yatsanshi saman lebbansa yace
"Shshshshsh!!" Sannan ya mata nuni da hannu kan ta taho,ba musu ta aje abun hannunta,ta taho a hankali ta fada jikinsa,tanason saka baki amma qiri qiri ya hanata cewa komai,lullubeta yayi cikin jikinsa yayi kissing goshinta a tausashe sannan yace
"Shuru nake buqata,na yafe hirarma" hakance kuwa ta kasance,sukaci gaba da zama shurun a haka har barci ya sacesu.
_zaku jini shuru gobe,zan taho muku da sauran pages dinku,nidai a nunan kara aci gaba da sauraron littafaina a SAUTIN HIKIMA dake youtube_🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️55
*_ina ma'abota karatun tsararrun labari masu dauke da tarin darussan rayuwa?,maza garzaya ka nemi littafin 'YA'YA NA,na haziqa fasihiyar marubuciya NABILANCY LUV,littafin 'YA'YA NA,labari ne daya qunshi soyayya mai ban tausayi,soyayyar wa da qanwarsa ba tare da yasan ciki daya suka fito ba,garzaya ki sayi naki kan farashi mai sauqi,sannan ku saurari littattafan marubuciyar a tasharta ta DA BAZARKU NOVELS dake dandalin youtube,karki sake a baki labari_* 🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️
Aqalla saida suka kwashi cikakkun watanni biyu suna hutawa sannan soma suka shirin dawowa qasarsu,har sannan anty usaina tana masa mitar nafisa,amma yace shi bazai sauraraba,yayi alqawarin zama ayi maganar duk sanda tagaya mata abinda ta aikata masa,amma tunda bashi yakawo qara ba bayanin me zaiyi.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Cikin fushi tasake cire rigar karo na hudu tajefar da ita itama,ranta na suya kamar zata fashe,anwar dake zaune gefe dariya tanacinsa kamar ya mutu amma haka ya cinye kayarsa
"Wannan ce ta biyar,idan taqi shiga itama saidai a haqura da fitar"
"Yi bismillah dai ki gwada,in sha Allahu za'a dace" ya qarashe maganar yana wayancewa da tari saboda dariyar data ciyoshi,tun rannan suke musu,yace mata tazama 'yar lukuta amma sam taqiya tace yafita yin qiba.
Kuka kawai yaji ta fashe dashi bayan ta wurgar da rigar ta samu waje ta zauna,da hanzari yatashi yana cinye dariyarsa ya isa inda take yajawota jikinsa yana lallashi
"Haba anshad dina.....yanzu meye abun kuka a ciki?"
"Wallahi qibar nan ta isheni,duk bakai ka jawo ba,kayita bani zaqi da maiqo kace naci babu komai?,duba fa tumbina don Allah" ta fada tana jawo hannunsa saman cikinta ta dora,saiyadan fiddo ido,shi kansa yayi mamakin yadda cikin nata ya daga fiye da jiya,don ko a jiya bai daga haka ba
"Yanzu kiyi shuru bari nasake lalubo miki wata rigar ki saka saimu fita,daganan saimu biya asibiti su baki maganin rage qibar da tumbin" ya fada yana miqewa yanufi ma'ajiyar kayansu yafidda mata wata doguwar riga free size,Allah ya taimaketa tana sakawa tayi mata,hakanan tashirya suka fice.
Sai da suka gama duk uzurorinsu sannan yaduba wani asibiti ta internet wanda suka qware kan duk wani abu daya shafi mata,yabi map wanda ya nuna mishi hanya har asibitin.
Dukkansu suna zaune gaban likitan bayan sun gama masa bayani,yayi rubuce rubuce sannan yace zata shiga wani abu wanda zaiyi scanning jikinta duka,zai nauyinta,tsaho da maganin daya dace da ita.
Cikin mamaki baturen likitan yake kallan anwar idanunsa a waje yana cewa shahida maza tasauko cikin yaren turanci
"Yallabai?,ka taba ganin an baiwa mai ciki maganin rage qiba?"
"Wacce mai cikin?" Saiya nuna shahida
"Matarka mana,tana da ciki ta yaya za'a bata maganin rage qiba?" Idanu shima ya fiddo duka suka kalli juna lokaci daya shida shahida,ta dubi likitan
"Bani da wani ciki,bani da komai"
"Bata da ciki dr"
"Taya zaku qaryatani bayan gashi na gani da idona,idan baku yarda ba muje dakin scan".
Dukkansu idanunsu na kan allon computer din scanning din sanda yasoma yawo da abun gwajin saman cikin shahidan,Allahu akhbar,saiga baby nan wanda yasoma girma halittarsa soma sauyawa zuwa ta mutum,daga anwar har shahida qamewa sukayi kawai,anwar yanajin kansa yana zagayawa cikin duniyar farincikin da yakejin babu irinta,yayin da shahida wani abu me sanyi yashiga ratsa ranta,yau itace dauke da cikin anwar dinta?,yau itace cikin qudura da hikimar ubangiji xata samawa anwar da ko 'ya?,likitanne ya katse kowa cikinsu yana cewa
"Hala madam batayi ciwo bane shi yasa bakusan da shigar cikin ba?" Hannu anwar yasa yadauke siraran hawayen da suka ziraro masa ta gefan idanunsa yana baiwa likitan amsa
"Ko kadan,ba wanda yakawo ciki gareta"
"Haihuwar fako ce?" Kai ya kada masa yana miqa hannunsa zuwa ga shahida,ta saka nata a ciki ya matse gam yana kallon qwayar idanunta,wata qaunarta da soyayyarta nasake tasiri a ranshi,yanajin duk duniya babu wani abu daya isa ya shiga tsakaninsu yanxu,ko mutuwa tayi yanajin zai iya binta
"Saiku kula da kyau daga yanzu tunda kun sani,gashinan baby ne sati goma sha biyar" ido ya sake fitarwa yana girmama lamarin ubangiji,wata uku harda wani kwanaki akai amma cikinsu ba wanda yakawo cikin ranshi?,anan likitan yarubuta mata 'yan magunguna na qarin lafiya,sannan sukayi xaman dirshan aka samu nurse dake kula da masu ciki tamusu lacture na yadda mace zata kula da kanta da babyn cikinta,wuni guda ana abu daya,matar tasha tambaya,saidai dariya kawai da take sam bata gaji dasu ba,don ita abun ya qayatar da ita sosai sun burgeta,tasha jin ana cewa baqaqen fata musamman hausawa basu iya soyayya ba ashe qarya ne,ta qaryata hakan akan anwar da shahida,sai yamma sosai sannan suka dawo gida,nanfa sabon fi'ili yatashi,bata da katabus anwar ya sanyata a gaba,ko sanda sukazo kwanciya ya cuso kanshi saman cinyarta gaban cikinta,ta zaro idanu
"A'ah,yaaa anwar karfa ka bugeni" ta fada a shagwabe,baki ya kama
"Ni na isa,inason in cewa babyna gudnyt ne" dariya yabata,tace
"Yau kuma?,babyn da ba'asan dashi ba saiyau shine duk za'a soma matsantamin" wani tsalle yayi yadawo yazauna dirshan saman gadon yana dubanta
"Inji wa?,kinsan na dade inaji a jikina ciki ne dake?,kawai na qyalekine don naga kamar tsoronshi kikeji,kumama kinsan me?" Kaita girgiza murmushi mai kyau yana fita a fuskarta,saida yamatso sosai yadora kanshi kafadarta saitin kunnenta sannan yace
"Idan ban manta ba,lissafina yayi dai dai da randa nake tunanin nayi ajiyata fa,kin tuna ranar?,randa nace ki taimakeni mutuwa zanyi,ashe kuwa da baki taimakeni ba shahida mutuwar zanyi alhalin datai a jikina,daga sanda nafisa tazama uwar yarana aina mutum,duk dadai ko banza nasha yakushi da cizo da duka ma duka,ranar nasha wuya ba kadan ba" ya fada yana mata cakulculi wanda ya sanyata curewa waje daya kunya na kamata tana dariya qasa qasa,ajiyar zuciya yasaki wanda tashiga kunnenta ta tada mata tsigar jiki
"Alhamdulillah,Allah ya taimakeni ya kadoni daga dakin nafisa yasanyani nayi ajiyata a kyakkyawan muhalli,bigiren daya dace,jikin uwa tagari,na godewa Allah da wannan karamcin daya yimin,na godewa Allah daya cikamin burina yasanyaki zaki zama uwar 'ya'yana abinda naketa buri tun bansan alfanun haka ba" luf tayi tana sauraren yadda yake kodata,tana godewa Allah bisa dacen miji datayi,ajiyar zuciya itama tasauke
"Amma haskena....ya kamata ka waiwayi nafis...." Yatsanshi ya dora saman lips dinta wanda hakan ya sanyata kasa qarasa maganar
"Nafisa babu abinda zan mata,bazan iyaci gaba da zama da ita ba,duk wanda yace nazauna da ita amatsayin matar aurena ba shakka ya zalu ceni zalunci mai yawa,hakan kuma na nufin ta haifamin yara daga jikinta?,Allah ya tsareni,bakisan haqiqanin wace ita ba,yarinyar da har yanzu nina mata lefi ba ita tayi kefi ba nare ta saduda tanuna nadama,abu dayane zai hana na bata takardarta direct hannu da hannu na maidata gida,girma da qima da darajar alhj abba,amma duk randa ta gaji da zama da kanta zata bayyana abinda ta aikata kota nemi saki,wannan shine sakamakonta,mu rufe wannan caftar karmu bata darenmu,matso kidan sanmin" ya fada yana cukuikuyeta,tunda yafadi hakan tasan me yake nufu,alhmdlh bata da matsalar rashin lafiya ko kuma lalura,don haka bataga abinda zaisa ta nesanta kanta da mijinta ba,cikinta lafiyayye ne,irin lafiyar da ita kanta tayi mamaki,duba da yadda mata ke fuskantar qalubale daga wannan zuwa wancan daga sanda suka samu ciki harsu haifeshi.
Cikin nasara farinciki nutsuwa da kwanciyar hankali suka koma nigeria,suka tadda kowa lafiyar Allah,sun sage zaga wadanda suka dace sujewa,a sannan ciki dai yasoma bayyana kanshi,murna wajen anty usaina kamar tayi me?,ranar saidata dafa abinci mai azabar yawa tayi sadaka,burinta zai cika,burinta na taga dan anwar a duniya,jikokin iyayensu xasu qaru,bata fasa masa fada kan nafisa ba nashi kawai murmushi,sai washegari yashriya zuwa gidan don yanason yasake debo musu wasu kaya.
Yana gama parking mota ya tunkari gidan,ya tura qofar saiya sameta a bude,tun kafin ya qarasa falon yasoma jin tashin hayaniya da zage zage,dab dazai qarasa din tafito da sauri kamar zata fadi suka kusa cin karo da anwar,yaja da baya yana dubanta,fiddausi ce,tabbas itace,saiya koma da baya ya saka muqulli ya datse gate din gidan sannan ya daga waya yayi kira na 'yan mintuna sannan yakashe,sanda yadawo dukkansu suna tsaye cirko cirko itada fiddausin,jikin fiddausi rawa kawai yake don tasan komai,ba shakka da tasan haka zata faru ba zata taba yarda tazo gidan ba,yayin da nafisa ko ina na jikinta yake rawa,yau kuma shikenan duk wata sauran hujja data riqr ta ruguje,tunda ga fiddausi mai kankat ya sake samunta a gidan,ba jimawa aka soma knocking ya bude,police ne mata biyu maza biyu,suka gaidashi cikin girmamawa ya amsa,suka durfafi nafisa da fiddausi,saiya dakatar dasu ya nuna fiddausi kawai
"Iya wannan ce" nan suka cakumeta tana hurwa da neman afuwa amma baiko kalleta ba,saida suka fice da ita sannan yadawo da kallonshi kan nafisa,baice mata qala ba yawuceta yashige zuwa cikin gidan.
Da hanzari tabi bayansa,yana hawa sama tasha gabansa,fuskarta cike da hawaye tana qwalla tace
"Kome na aikata nayine saboda kai,saboda ina sonka,saboda banason ganin kowacce mace ta rabeka bayan ni,ka yafemin" ta fada tana hada hannayenta waje guda,donta gaji zuwa yanzu tasoma sarewa da zaman da sukeyi,watannin maganinta sun cika harma sun wuce amma ace bata mori wahalarta ba,wani kallo kawai ya watsa mata ya gewayeta ya wuce abinsa,sai daya tattara abinda yasan zasu sake buqata yazo yawuceta yabar mata gidan.
********************
Cikin wata iriyar soyayya nasara da taimakon ubangiji take rainon cikinta hankali kwance,ta sake kyau tayi bul bul gwanin sha'awa,tsakanin anty zubaida anty usaina ummanta da daada babu wanda bai farinciki da daidaituwar lamura a tsakaninsu,kowa sha'awarsu yake gami da son barka.
Zuwa sannan sun sake yarda sun kuma amince dacewa dukkaninsu babu wanda zai iya rayuwa babu daya,gaba dayansu son junansu cikin jininsu yake yawo,hakan yasanya bai iya zuwa konan da can idan bada shahidansa ba,ta zame masa kamar wata jakar hannu,kome nisa ko gajarta tafiya da abarsa yake,tun anty usaina na fada harta tattara ta xuba musu ido,wai ita tana ganin ya kamata ace ya qyale shahidan haka ta huta,ashe aikin banza take,saita fuskanci duk koko ne yake dukan kunun zaqi,itama batason bacin ran anwar din ko kuma yayi nisa da ita,dole ta tattara ta zuba musu ido.
Sau biyu suna zuwan gidan dauko kaya shida ita,da fari tace yaje shi daya,daga baya tilas taje da kanta don za'a kwashe mata dukka kayanta da sukayi saura ne daga gidan.
Sanda tashiga nafisan na falo a zaune,ta sake tsukewa ta rame kamar ba ita ba,abu na farko data soma gani cikin shahida daya soma fitowa sosai,wanda kamar ma yagirmi watanninsa,wani tashin hankali yarufto mata,gumi ya karyo mata,ta girgixa ba kadan ba,anwar din na biye da ita,kamar uban gida damai gadinsa,tashin hankali da ba'a saka masa rana,saita kasa dauke idanunta daga kanta,yau shahida ce da cikin anwar a jikinta?,yau shahida itace ta karbe anwar daga hannunta,shahidan itace ta xama haka?,tazama babbar mace abun alfahari wa mijinta?,ita kuwa zaman me take da bazataje inda za'a karbo mata haqqinta ba?,wannan wanne irin gashin quma ne ta yarda tazauna a cikinsa?,ta kalli kanta saita ganta a wani bushe kamar ba ita ba,tana zaune suka sake saukowa daga saman yana riqe da wasu kayan nata,saida yazo daidai ita yaciro kudi a aljihunsa ya aje mata ba tare daya dubeta ba yabi sahun shahida suka fice,da sauri tamiqe ta isa bakin window,ta dage labulen ta yadda zata iya hangosu harsu fice.
Sai data soma shiga motar bayan ya bude mata,yarufe ha zagaya sit dinshi yashiga,yana shirin tada motar ya waiwayo suka hada idanu,ta zuba masa ido shi take kallo,yatsanshi ya sanya ya lakaci hancinta yana cewa
"Wanann kallon fa?,kinason jefani wata duniyako?,idan kuma nace adan sanmin yanzu sai a narke ace za'amin kuka" narkewar kuwa tayi sosai tace
"Hubbie"
"Anshad" ya amsata yana kallonta
"Wannan fa ina ganin ba dai dai bane ka......" Yatsanshi yadora saman lebanta yana cewa
"Karkice komai,kome zan mata ba zata tabajin irin dacin dana jiba tsahin shekara shida,karki manta hawan jini gareni yanzu haka,itafa?,ba zata taba samun hawan jini ba" dole tadauke kanra tayi shuru saboda yadda ta fuskanci bacin rai na shirin motsawa kan fuskarsa
Kudin ta kalla saita dauke kai da sauri tayi cikin daki tana sakin kuka,kayanta tasoma hadawa,saidata hada kayanta tsaf sannan ta dauki mayafi da muqullin motar data manta rabonta da hawanta tafita farfajiyar gidan,saidata nemi taimakon wani saurayi dayazo wucewa yabude mata qofar tafitar da motar yarufe mata,sannan ta kulle gidan ta harba motar titi.
Mommy na xaune falo,hannunta daya riqe da remote,daya hannun kuma wayace take latsata jifa jifa nafisan tashigo falon kamar wadda aka jeho cikin kuka,a firgice momyn ta aje wayar hannunta ta tari isowarta,kan cinyarta ta fada tana sakin kukan
"Ke nafi,lafiya?,lafiya kike?meya faru?,lafiya?" Da qyar ta dago kanta
"Momy anwar ne,anwar baya sona mommy,anwar ya wulaqantani ya wulaqanta rayuwata tunda aka kaini" cikin hargagi momyn tace
"Ke dakata banason shirme,ki bude bakinki ki gayamin abinda yafaru,banason kuma qarya ko shirme" daqyar tashare hawayen nata sannan tasoma magana
"Tun farko nayi kuskure mommy,saboda na takura anwar ya aureni ashe zan karbi sakamakona,anwar mommy tunda na aureshi bai taba hada shimfida dani ba,sai gashi yanzu haka matarsa ciki gareta,bayaga haka ya sauya gida ya dauke matarsa sun barni ni kadai cikin gidan,yahanani fita ya hana kowa zuwa,baya zuwa baya kwana a gidan,nabashi haquri nayi nayi ya gayamin me namasa yaqi gayamin,mommy azabtar dani kawai yake" shuru take tana nazari cike da mamakin anwar dinne zai aikata haka?,to idanma ya aikatq din meye dalilinsa?,tasan halin nafisa hakanan tasan halin shahida,ba shakka ruwa baya tsami banza
"Kin tabbatar da cewa iya abinda ya faru kenan ke baki masa wani laifi daya sanya yake aikata miki hakan ba?"
"Niba abinda nasan nayi masa,kuma nabashi haquri ma amma yaqi saurarata,nidai mommy na gaji da irin wannan zaman" ta qarashe fadar tana sake fashewa da kuka,jinjina kai mommy take kawai tana nazari,tsahon wasu mintuna kafin tadubeta
"Kukan ya isa,tashi kije ki huta kafin abbanki yadawo" daga haka nafisa ta miqe tahaye dakin mommyn tana goge fuska.
Bayan abban ya kammala cin abincin dare mummy tayi masa duk bayanin da nafisan tayi mata,yayi shuru yaba jinjina kai cikin tunani kana yace takira masa ita,sanda tazo yadda ta gayawa mummy haka ta maimaita,saima sake kambama laifin anwar din tayi donta samu haqqinta dawuri,shuru alhj abba yayi kafin daga bisani yace
"Kin tabbatar yadda kika fada haka abun yafaru?" Kai ta jinjina
"Eh abba"
"Nafisa,kinfi kowa sanin halayyata,idan har na binciki ba haka bane,kona samu kece baki da gaskiya toki kuka dakanki" gabanta yayanke ya fadi,gumi ya karyo mata,hankalinta yatashi sosai,amma duk da haka saita gyada kai
"Na yadda abba"
"Tashi kije" ya fada yana ci gaba da tunani,sai data fice sannan yadubi mummy
"Bilki,tsakanin anwar da nafisa babu wanda bakusan halinsa ba,amma ba'a yanke hukunci ba tare da an tuntubi kowanne sashe anji ta bakinsa ba,zan nemeshi naji yadda ake ciki tukunna,amma tabbas ina tantamar cewa haka siddan anwar ya aikata hakan,na sanshi ba sanin shanu ba,akwai abinda ke faruwa,yana da alkunya kara da kawaici qwarai" itama kai take gyadawa
"Nima dai haka abba,abun ya dauremin kai" wayarsa yajanyo yasoma neman layin anwar din.
Dai dai lokacin da shahida ke zaune daura dashi saitin gwiwarsa,sanye da gajeran skert da qaramar riga wadda tayi mata kyau dukda cikin dake gabanta,kanta babu dankwali ta miqe qafafunta saman na anwar din yana matsa mata saboda yadda suka riqe,qorafi yake danyi mata da qunaquni qasa qasa tana danne dariyar dake cinta,wai lallai shi saidai a gobe ta rakashi abuja,ita kuma wannan karon tace a'ah,saboda jikinta saya soma nauyi zuwa yanzu,kiran alhj abba yashigo,wayar tafi kusa da ita saita dauko tamiqa masa,gabanta yafadi hakanan saboda taga sunan dake kan wayar,ta kuma san wayeshi,saita soma yunqurin tashi tun baikai ga daga wayar ba,don a gaskiya tana bala'in kishin anwar din,batajin zata iya jure abinda tajure abaya akanshi,tsaf zuciyarta zata samu matsala,bai tsaidata ba yabita da kallo sanda yake daga wayar ita kuma tana ficewa zuwa harabar dake gaban falon mai shuke shuke kafin kakai ga ficewa farfajiyar gidan gaba daya.
Cikin girmamawa da dattijantaka suka gaisa sannan daga bisani alhj abban yace
"Nadawo gida na tadda nafisa a gida,idan babu damuwa duk sanda kasamu lokaci inason ganinka,daga yau zuwa gobe dai ina hutu ina gida" a ladabce yace
"Toh abba in sha Allahu ina tafe"
"Yauwa" ya fada suna datse kiran duka lokaci daya,aje wayar yayi yana sauke ajiyar zuciya,yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta qoqi,takuma shafawa kanta lafiya data kai kanta gida,hakanma shima ya sauqaqe masa,tunawa yayi da shahida,saiya miqe da sauri yabi bayanta.
Tana zaune kan daga cikin kujerun hutuwar dake wajen,hannunta daya saman cikinta,ta tsurawa wata tukunyar fulawa dake wajen idanu,ko ba'a gaya maka ba kasan tunani take,idanu yazuba mata,tausayinta na ratsashi,tunda halin shahida dabanne a rayuwa,daya daga cikin abinda ke qara masa soyayyarta a zuciyarsa kenan,tana da kawaici,tana da kara