Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   52 / 53

153K to 156K   out of 156.9K words

da yakana,bazai iya tuna wani abu daya taba shiga tsakaninsu ba mara dadi banda wanda shaidanu suka qulla,taji tsaiwarsa saboda haka ta daga kai a hankali tana dubanshi,suka hada idanu saita sake masa wani sassanyar murmushi,baiyi qasa a gwiwa ba ya maida mata martani sannan kuma ya qarasa a hankali yazauna dab da ita har jikinsu na gogar juna,hannu yasanya yadauke hannun nata daga saman cikin yana cewa
"Daina malama,don duk wayonki wannan babyn saiyafi sona,sanda na aje abina saboda qauna da soyayya saida na dawo wajen mamarshi,ke kuwa kuka kika dinga yi kina min Allah ya......" Da sauri tasa hannu tarufe masa baki tana turo baki gaba a shagwabe,gefe daya kunya na kamata,tana bala'in jin kunya idan ya tuna mata da first night dinta,wani bahagon first night,dariya yadan saki sannan ya kalli qafarta da a sannan ruwan yazube yana cewa
"Daga ni harke ba wanda ya sake tunawa da ruwan zafi ya zubar miki harke mai qafar,yarinya taji zuma ko?" Ya qarashe da sigar tsokana yana dage mata gira,wata kunya tasake kamata saita dora kanta saman kafadarsa taba diddira qafafu
"To ba fatiha ka tofamin ba,kuma bata tashi ba,ni ban manta da qafata ba kaine dai ka manta saboda an kaika aljannar duniya" itama ta rama tsokanar,murmushi yasaki mai sauti sosai
"Eh na yarda aljannar duniya kika kaini babu musu aini babu jayayya,idanma akwai abinda yafi aljannar duniya kin kaini anshad rahamatullahi,kuma har kwanan gobe kaini kike kamar bazan dawo ba" cacimeshi tayi gaba daya tana boye kanta a jikinsa cikin dariya,hakan ya masa dadi,yasan ko banza yakore yanayin data shiga,a haka ya shashantar da zancan,suka dan zauna na wani lokaci sannan ya dagata suka shige ciki,sai daya taimaka mata ta saka nightgown sannan suka kwanta.


🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Tana zaune gefan gado tana kallonshi cikin mutuwar jiki yana shiryawa cikin yadi ruwan madara,hira yake mata amma sai yaga hankalinshi kamar ba'a kanta yake ba,juyawa yayi ya dubeta sai yaga bashi take kallo ba,ya murxa mata yatsunshi saita daga kai ta kalleshi
"Madam yadai?" Kaita kada tana gyara zamanta
"Babu komai" dan ranqwafowa yayi dab da ita har suna musayar numfashi,ta shaqi nashi numfashin mai dumi daya cakuda da qamshin turarensa har cikin xuciyarta tana lumshe ido gamida sauke ajiyar zuciya
"Wannan kishin fa haka?" Ya fada kamar me rada,da sauri ta bude idanun nata cikin mazewa da basarwa tace
"A ina?"
"A qwayar idanunki" yayi lafazin yana fidda murmushi gamida nuna idanun nata da yatsanshi,kauda kai tayi,harga Allah tanajin kishinsa ba zata boye ba,gani take kamar zance zaije dai,ya lura da gaske basarwa kawai take amma fitar nashin na taba ranta,baice mata qala ba harya kammala shiryawa,saiya kama hannunya yana matsawa gamida kallonta
"Karki damu,babu wanda ya isa ya gutsirar miki mijinki,yadda nafita guda haka zan dawo guda,anwar naki ne ke daya" hannu tazame tana kauda kai sannan tasoma yunqurin tashi tana cewa
"Muje na rakaka"
"A'ah nafa yafe rakiyarnan yau" soma gyara mata shinfidar gadon yayi yana cewa
"Dawo ki kwanta ki huta,ni kaina jiya nasan na wahalar da baby da mamarshi" murmushi ta saki ganin yadda yake qoqarin gyara mata kwanciyarta
"To idan na kwanta yau waye zaimin aikin?"
"Dama ni nake ai tayani kike,to yau na yafe,idan na dawo duka zanyi abina gaba daya" baki takama sanda yake lullubeta da bargo
"Waikai sai yaushe zaka koma office?"
"Sai kin haihu mun gama jego sannan" sosai anwar yabata dariya
"Au to sannu mejego,Allah yaraba lafiya"
"Ameen" ya amsa yana tafe yana turo ciki irin na masi ciki harya fice daga dakin yabarta da guntun dariya,ta lumshe ido takauda dukkan wani tunani dake ranta tagayyato baccin.

Cike da girmamawa yake zaune gaban abban harya kammala dukka bayanansa,ya daga kai a hankali yadubi nafisan yana mamakin zallar rashin kunya,rashin tsoron Allah da kuma rashin adalcin dake danqare a zuciyarta,amma zaiyi maganinta dai dai yake da ita
"To nidai abba bansan meye tsakanina da ita ba,gidana akwai ci akwai sha akwai sutura,amma gatanan abba idan akwai wani abu saita fada din" juyawa abban yayi yana dubanta tare da sake tambayarta akwai wani abu datayi masa tace itadai babu,kai ya jinjina shima yace babun,ganin abban ya soma nasiha na alamun gidan kenan zata koma ba tare da daukan kowanne mataki ba yasa da hanzari cikin firgici tace
"Wallahi abba akwai,fada ne kawai baxaiyi ba ka tambayeshi abba"
"Indai ko laifo kika masa nafi kibude bako ki gayamin me kika masa?" Shuru ya ratsa falon,ta soma dabur dabur,yayin da kowa yazuba mata idanu,abinda yasake daburtata kenan,ta soma kaiwa tana kawowa,ta kasa tsaida magana daya,abinda ya qufula abba kenan da mummy,yayin da mummy takai iya wuya,iya hakan kawai ya tabbatar mata da nafisance bata da gaskiya koda ba'ace komai ba,ita tahaifeta tasan halinta tsaf
"Ki bude baki ki magana ke muke saurara" abban ya fada yana dubanta
"Abba kuskure ne aka samu wanda nayi nadama kuma na bashi haquri,na kuma yarda nayi kuskure amma yaqi yayafemin,ko Allah muna masa laifi ai yayafemana"
"Naji,amma me kika masa ke?" Tirtan tiryan kamar wadda aka matsi bakinta ta kwashe komai kaf ta fada ba tare data rage ba,shuru abba yayi wani irin tashin hankali bacin rai da kunya na dabaibayeshi,duban anwar yayi
"Ka dubi girman Allah ka gayamin kaima dukkan abinda kasani daga naka bangaren" kansa a qasa yana matuqar jin nauyi,don ya sani cewa indai nagartattun iyaye ne babu yadda zasuji dadi ace tsatsonsu ne yashirya wannan baqar muguntar da mugun tuggu,ya hadashi da girman Allah,saboda haka bai boye ba ya gayawa abban dukkan yadda abu ya kasance daga bangarensa dana shahidan da irin yanayin da suka shiga,tuni hawaye yacika idanun mommy,yanxu ita ta haifi wannan?,ita ta haifi halittar data iya hada wannan tuggun?,wanne zunubi ta aikata a duniya?,batasan sanda takaiwa nafisan duka ba tasamu kuwa ta kwada mata mari a fuska,ta bude baki zatayi magana abba ya dakatar da ita don yasan idan tayi fushi bata da dadi,saboda haka ba lallaine abinda zata furta a lokacin yazama alkhairi a rayuwar nafisan ba,idanun abban cikin na nafisan yace
"Kin sanya rayuwarta cikin garari bataji ba bata gani ba,ko gama saninki bata yina,kin rabasu da sunan kina sonshi,ba kuma rabawa ta Allah da annabi ba,kin dasa gaba da qiyayya a tsakaninsu saboda son zuciyarki,kin manta cewa ALKAWARIN ALLAH BAYA TASHI,nafisa.....ke diya tace amma saboda soyayya bazan rufe idanu naqi gaskiya saboda ke ba,bazan cutar da wani diya ba saboda tawa diyar" saiya waiwaya yana duban anwar
"Anwar,idanma na tambayeka kanason ci gaba da zama da shahida ban maka adalci ba,karo biyu kana kara da alkunyar karbar nafisa duk da mun karanci baka ra'ayi,to baza'a sake na uku ba in sha Allahu....anwar,inason ka furtawa nafisa saki yanxun anan gurin ko hakan zai zama izina a gareta" wani wawan ihu tasanya ta dora hannu aka,bacin rai yasa mummy tasake kawo mata duka Allah yakuma bata sa'a ta daki bakinta,saita bar ihun ta kame bakinta daya soma tsatstsafo da jini,sake duban anwar abba yayi ganin yayi shuru
"Anwar,idan na isa dakai yanzun nan nakeso ka saki nafisa" tabbas abun ya masa nauyi,abune mai matuqar nauyi duk yadda kake qin mutum ka furta masa kalmar saki gaban uwa da uba abu wanda dansu shine abu mafi soyuwa a garesu,saidai su boye saboda wani qwaqwaqwaran dalili,karo na uku abban yasake maimaita cewa
"indai ka daukeni uba,kuma na isa dakai ka saki nafisa yanzu anan wajen" cikin jin nauyi kansa a qasa yace
"Na saki nafisa saki daya" wani kuka tasaki tana tumami gamida baiwa abban haquri dashi kansa anwar din,bata taba tsammatar hukuncin da abban xai yanke mata kenan ba,da ko zata mutu ta gwammace tayita zama a gidanta,duk tsiya dai sunanta matar anwar,kuma komai dadewa wataran zai sauko ya haqura,gashi ta kawo kanta inda mahaifanta da kansu suka nemi mafi munin hukunci a kanta.

Tanajin ba dadi cikin ranta,amma iya adalcin da zasuma yaron kenan ta dakawa nafisa tsawa kan ta miqe suje,haka tamiqe tana kuka mai sauti tana waiwayen anwar din suka fice.

Bata qyaleta ba saida suka dangana da dakinta,ta tsaya akanta tana dubanta
"Kina tsammanin akwai bawan daya isa ya yiwa Allah dole?,kin aikata abu a sannan Allah yana kallonki ya kuma baki dama don ya nuna miki cewa alqawarinsa tabbatacce ne,kin shiga tsakiyarsu saiya jefaki rayuwa a cikinsu daga qarshe,ke kika rayu cikin qasqanci,ya sanya rabo na haihuwa a tsakaninsu kina kallo,ya kuma barsu tare ke kuma kika sake fita kika barsu,wannan kawai ya isheki izina,Allah shine shaida nayi qoqari matuqa akanki amma bansan yadda akayi kika watsar da duka tarbiyyarmu ba,dama ance duniya ita take maka darasin da mutum bai isa ya makashi ka dauka ba,ki zauna kici gaba da bita wannan kawai ya isheki karatu,kuma indai nina haifeki kin rabu da anwar kenan har abada,kije ki gama yim hankali sannan daga qarshe ki zabi mijin daya dace dake ki aureshi" daga haka tayi ficewarta tabar nafisan.

*BAYAN WATA HUDU*



Tunda ta tashi sau daya fitsari takasa komawa saboda wani azabar ciwon mara da baya dake damunta,sai kwanciyar gadon gaba daya ta gagareta saboda haka ta lallaba tasauko qasa don kada ta tada anwar din da baisamu yin bacci da wuri ba,ya jima zaune yana gadinta saboda tace mishi mararta na daurewa harsai da bacci ya dauketa,saboda haka batasan sadda yasamu ma ya kwanta ba.

Tun tana jin ciwon zata iya daurewa harta soma fidda numfashi cikin ciwo gumi na karyo mata,bata jima da farawa ba ya farka a firgice,idanunsa suka sauka a kanta yasauko da hanzari har yana tuntube yana tambayarta
"Shahida....lafiya?,me yake miki ciwo" daqyar ta iya cewa
"Marataaaa"
"Bari na kira dada" kamar zai kifa haka yabude dakin yafito,kai tsaye ya doshi dakin da aka baiwa daadan sukutum take zaune tana jiran zuwan haihuwar shahidan,don anwar din qemagadas ya murje idanunsa yace ba inda zata,ga daadansu ta ishesu,zai samo wata mai aikin da zata dinga zuwa tana tafiya.

Abun mamaki saiya sameta saman abun sallah,ta daga kai tana dubanshi
"Shahida ce ko?" Ta soma tambayarsa tana miqewa daga saman abun sallar,cikin hanzari yagyada kai
"Wallahi farkawa kawai nayi na taddata ta tana murgususu"
"Tun dazu na lura kamar batajin dadi,dauriya ce kawai irin tata,muje" ta fada tanayin gaba.

Sanda daadan ta isa dakin haihuwa ta taso gadan gadan,ta hada gumi sharkaf duk da sanyin acn dake dakin
"Kai anwaru,maza kaje mabusar sanyin can karta haifa mana yaro cikin sanyi,daga nan kafita kaja mana qofar" ya kashe dai na'urar yadda tace,amma sam yaqi matsawa ko nan da can,tausayin shahidan ya kamashi matuqa,idanunsa suka kada sukayi jazur,tausayin mata da qimarsu yasake yawa a idanunsa,dama haka suke shan gumurzu kafin zuwan kowanne yaro ko yarinya duniya?,amma a haka yara suke butulcewa iyayensu?,a haka suke qin jin qansu?,yana tsaka da wannan tunanin tayi wani gauron numfashi daya sanyashi dawowa cikin hayyacinsa,kukan baby ya karade dakin cikin 'yan sakanni hade da hamdalar daada,babu yadda ta iya shita miqawa yaron tana ta shahidan da mahifa bata kai ga fadowa ba,kamar suna rige rigen amsar dan da wani haka ya karbeshi daga hannu daada ya qura masa idanu,yarone namiji masha Allah,sai qwalla tacika idanunsa yasoma kissing yaron ba tare daya damu da yanayin jikin yaron ba,daga qarshe dai da anwar din aka kammale komai,ya amshi duk wani kaya da aka bata ya zagaya bayan gidan da kanshi ya wankesu fes da dettol ya shanya,yabar daada tana gasawa shahida jikinta.

Kafin wani lokaci gidan yasoma cika da 'yan barka tako ina,dangi da yan uwan shahida harma dana anwar din,dole tasa yashirya yafita daga gidan badon sonshi ba.

Bashi ya sake samun damar ganinsu ba saidaya dawo gidan wajen qarfe tara na dare,dukkansu suna falon harda mejegon,saboda baqi 'yan barka basu jima da tafiya ba,daga daada,sai mubina sai shahidan da baby dake hannun mubina,tunda yashigo idanunsa nakan shahidan,wadda take fes cikin atamfa riga da zani,da alama tasoma huce gajiyar naquda,suka gama gaisawa dasu ya yiwa daada sannu sannan ya miqe zuwa dakinsa,yanason kiran shahidan yanajin nauyi,haka ya haqura yashiga.

Mubina ita takai masa abincinsa,yace ta tura masa shahidan,yana zaune yana dakon jiranta tashigo,ya miqe da hanzari ya amshi yaron dake hannunta,sannan ya jayota zuwa jikinsa ya rungumesu gaba daya yanajin wani farinciki,nutsuwa da kwanciyar hankali na ratsashi,sai daya zaunar da ita sannan shima yasamu waje yazauna yana furta alhmdlh,sannan yabude fuskar babyn,baccinsa yake bawan Allah,ya qurawa yaron ido yanason tantance dawa yake kama
"Kamarku daya,haka anty zubaida tace sanda kana yaro" yaji shahidan ta furta,ya dago yana murmushi yadubeta
"Na sani,amma naso anshad dina ya yiwa kara,kinga dana morewa kallon cute face din nan taki koda baki kusa dani" hannu tasa tashafi fuskarta zuwa hancinta daya dan tasa sakamakon ciki tana murmushi
"Cute face ta sauya zuwa ugly" idanu yazaro yana kada harshe alamun alamun la la la
"Inji wa?,bana tunanin akwai wani yanayi ko zamani da zaizo na daina ganin kyanki shahida,don dama ba kyanki nakeso ba,shahidan dai,shahidana ni ita nakeso" ko bai fada ba tasani,anwar dinta na daban ne,kamar yadda soyayyarsu take ta musamman,bai barta ba sai data tayashi zaman cin abincin,yanayi yana kallon fuskar babyn sannan tayi haramar tafiya,sai data isa bakin qofa yana biye da ita yamiqa mata yaron
"Wanne suna kikeso a saka masa?" Ta karbeshi tana murmushi
"Ai dakai da kaya duk mallakar wuyane,na baka dama ka zaba masa"
"Allah ya raya mana abba usman" da sauri tadaga kai tana dubanshi,cikin rawar baki tace
"Abba na?,na zaci sunan naka abban zaka saka ai,shima ya rasu yariga abbana rasuwa" murmushi na fita saman fuskarsa yana karantar tsantsar farincikin dake saman tata fuskar wanda hakan yake sake saka ranshi jin farinciki,a rayuwa yana jin dadi idan ya farantawa shahidan,ta faranta masa a sanda baida abun faranta mata,ta sadaukar masa da abubuwa da yawa a rayuwarta tun bata mallaki wani abun azo a gani ba,ta fifitashi ta kuma fifita farincikinsa fiye da nata,taqi duk abinda takeso saboda shi,hakanan taso abinda bataso saboda shidin,a rayuwa me zaice mata?,banda Allah yaci gaba da bashi dama daduk wata qofa da zai faranta mata
"Abba usman nakeso a sanya masa" hawaye fal idanunta tabuda baki zatayi magana yasa tafin hannunsa ya rufe mata bakin
"Banaso kice komai....Allah yabamu alkhairi,yau zanyi kewarki,bansan ta yaya zanyi bacci ba" ya qarasa fada yana sakar mata murmushi,itama saita maida masa hawaye na gangaro mata
"Allah ya faranta maka sama da yadda kake farantamin,yasa mahaifanka na tare a aljannatul firdaus" daga haka tasoma takawa tana barin wajen,idanunsa alumshe ta amsa yanajin gardin addu'ar data masa har cikin qoqon ranshi.

Daada ce ta taryeta sanda tashigo falon tana zubda qwalla
"A'ah lafiya?,ko ciwon ciki kike?" Kaita girgixa
"Koda yaushe fifita buqatarsa kan tawa yake,koda yaushe fifita farincikina yake akan nashi,daada sunan abbana yasaka masa" ta fada tana zama kusa da daadan kuka na subuce mata,ita kanta daadan taji dadi qwarai matuqa,ya maida mata sunan yaronta,yaronta da take qauna
"Anwar ba mijin yardawa bane,anwar ba gama garin miji bane,irin mijin dake da wahalar samu kenan,abinda yasa nayi tsaiwar daka sai dana tabbatar komai ya gyaru tsakaninku,kici gaba da godewa Allah daya baki miji kamarsa" da haka daada ta samu ta lallasheta,harsai data koma normal sannan kuma ta dora da tsokanarta
"Yar nema,oh yau ga anwar din da ake wani cewa ni daada bana sonshi harda d'a,ko yaushe aka fara sonshi har aka haihu dashi oho,ahhhhh,ni habi naga ikon Allah" kunya saita kama shahidan,ta aje mata usman ta juya mata baya taba qunquni da mita,mubina tace
"Ya shahida me za'a dinga kiransa?"
"Duk yadda yayi muku"
"Hamdan yayi?"
"Allah yasa saura su iya kira,idan basu iyaba sa kirashi da nurain dinshi ai" cewar daada.


****** ****** *******


Cikin wani tsadajjen lace take takowa zuwa dakin anwar din safiyar ranar suna,ado tayi na gami na fada,duk wani abu na ado ta maqalashi a jikinta cikin salon daya dace,hakanan hamdan na nannade cikin tattausan abun daukar yara mai azabar kyau wanda ya dace da tsaddadar rigar jikinsa,ba abinda ke tashi a jikinsu sai qamshi,yanayin adonta saika rantse da Allah amarya ce.

A nutse ta tura qofar dakin bakinta dauke da sallama,tunda yaji muryarta ya tsaya da duk abinda yake ya zuba idanu yana dakon qarasowarsu,kallon kallo ake a tsakaninsu,ita tana kallon irin shigar daya xuba ta shadda dinkin babbar riga da tasha aiki aska tara kai kace wani angone da ake daurin aurensa,yayin da shima yadda ta sauya lokaci daya wani irin kyau ke tashi daga jikinta ita da yaronta,saiya bude mata hannayenta,batayi qasa a gwiwa ba ta tako a hankali cikin wata tafiya data jaa ra'ayinsa,ya hadasu gaba daya ya rungume yana sauke ajiyar zuciya
"Kin zama wata sarauniya"
"Kamar yadda ka zama yarima ba" tare suka saki dariya ya amshe hamdan yana masa wasa,duk da baccinsa kawai yake baisanma me ake ba,sai da suka gama gaisawa ya tambayeta ya tabbatar da babu wata matsala,sukan dan taba hira,dubansa tayi
"Ina da wata shawara mana aboo hamdan idan babu damuwa"
"Fadi duk abinda kikeso ummu hamdan" dariya tasaki cikin nishadi
"Niko me zai hana kasaka a saki qawar nafisa fiddausi dama wancan namijin da aka kama?" Shuru yayi yana dubanta kamar yadda ta tsareshi da idanu tana fatan ya karbi zancanta,ga mamakinta sai taji ya saki ajiyar zuciya
"Na jima ina wannan tunanin sanda zuciyata ta huce,amma sai wata zuciyar take gayamin ban giwa rayuwarki adalci ba idan na sakesu,shahida.....tun daga randa Allah ya mallakamin hamdan na yafewa dukkan wani wanda ya taba batamin rai...."
"Ko yaushe tunaninmu daya hubby....daga randa Allah yamin kyautar hamdan ya kuma bani mahaifinsa naji duk wani wanda ya tabamin wani abu bansan dashibama a duniyata,daga hamdan sai mahaifinsa mahaifiyata da 'yan uwana kausanta,yafe musu kadai ya isa ya sauya halayensu"
"Haka yake,bako da yaushe daukan fansa yake xama dalilin shiriya wa mutum ba,abunda kawai akeso koda yaushe bawa ya fahimci kuskurensa yakuma gyara yanemi yafuyar wanda ya batawa,kamarni....kinga ya zamemin izina kan illar saurin fushi da yanke hukunci ba tare da cikakke kuma qwaqwaran bincike ba........"
"Kamar yadda yaxamemin aya kan illar qin miqawa Allah dukka wata damuwa da kake ciki ba tare da kayi biye biye ba,naga illar kayan maye,ina maiwa Allah godiya daya

52 / 53