Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 53

81K to 84K   out of 156.9K words

ba kenan zaki fita" agogonta ta kalla sannan ta sauke hannu
"Sauri nake anty"
"Hakan yasanya jiya nace a tasoki ki gani ai" baki ta tabe a fakaice tana tuna haushin da hasina taso tura mata ajiyan da yadda ta matsanta mata,kayan da bataga abinda anwar zai zuba a ciki da zasu burgeta ba
"Idan na dawo na gani,saina dawo anty" ta fada cikin hanzari bayan ta dauki jakarta data aje ta rataya tana ficewa da hanzari,kasa cewa komai anty zubaida tayi sai binta da kallo kawai da tayi harta fice sannan ta girgiza kanta tana tadi ita da zuciyarta,ko ba'a fada ba tasan ganin kayanne bata sonyi.

Kwana uku tana cewa anty zubaidan zata gani amma bata yarda taje inda sukebama bare ta gani,dole ta gaji ta zuba mata idanu,a haka har akaci kwana goma sha biyu,ga tsammanin anty zubaida shahidan zata dauki hutu wajen aiki,saidai taga ko ajikinta bata fasa fita aikin na,sake qara mata kwana biyu tayi taga ko zata dakata da fitar,saidai ranar daya rage biki saura kwana bakwai cif da safe anty zubaida ta sameta a falo tana karyawa ta gama shiryawa tsaf,kallonta sosai take taga da gaske take fita aiki zatayi?,kallon harya sanya shahidan itama yin sak tana kallon anty zubaidan,saidata soma dan tsuke fuska sannan tace
"Ina zaki haka da safe?" Tambayar tadan baiwa shahida mamaki,ko maqota sunsan inda taje zuwa daga safiya zuwa yammaci bare anty zubaidan,don ita bata kawo tambayar tata nada alaqa da aurenta ba
"Office mana anty" ta fada cikin son gamsar da ita,kai anty zubaida ta girgiza
"Bakisan aurenki saura kwanaki bakwai ba ko lissafi ne ya qwace miki?,ko kuma duka kina sane saboda kinha na zuba miki ido ne?"wani abu ya taba zuciyar shahidan,ba zancan data tsana a yanzu irin zancan aurenta,tana sane saura kwanaki bakwai su qullashi to amma ita meye nata a ciki?,me zata zauna gida tayi
" to anty,ni menene nawa a ciki?,me zan zauna nayi a gida?"
"Eh babu komai naki a ciki tunda zubaida ce zatayi aure,so kike duniya ta zagemu ko?,tunda kike kin taba ganin amarya budurwar da aka aurar salin alin?,to banason sakarci,babu ruwana da wani abu daya taba gittawa tsakaninki da anwar ni aikina zanyi kawai,rawata zan taka,saboda haka ki koma ciki daga yau zansa abban huda ya dauka miki excuse,su baki hutun sati uku" kaman ta zunduma ihu haka taji sanda anty zubaida ke maganar,abinda ta dauka wasa ne gashi yana neman tabbata,ba damar musu da ita saboda yadda ta tsare gida sosai,haka shahidan ta soma takawa don komawa dakinta
"Eheennn...jimana" anty zubaida ta sake fada,saita tsaya gami da waiwayowa tana dubanta,sai data kallo agogo sannan tace da ita
"Qarfe sha daya na rana zamu fita dake,ki zauna cikin shirin" kai ta gyada kamar kazar da qwai ya fashewa cikin cikinta,haka ta dinga tafiya harta isa daki,ta watsar da duka kayanta kanta na daukar zafi,me yasa anwar yake son ya soma da nasara da sa'a a kanta?,me yasa anwar ya dawo cikin rayuwarta bayan bata da buqatarsa?,haka ta dinga yiwa kanta tambaya ranta na zafi.

Sha dayan da 'yan mintina suka fita ita da anty zubaidan kawai,bata tambayeta ina zasuje ba har saida suka isa gidan sannan ta fahimci wajen gyaran jiki ta kawota,tamkar wata doluwa haka ta dinga bin anty zubaida da kallo har suka gama gaisawa da matar da gabatar da shahida wajen matar a matsayin amaryar da za'a yiwa bikin
"Kai tubarkalla masha Allah,wannan badon hausawa suna cewa idan kana da kyau ka qara da wanka ba ai bata buqatar komai,saida nasan gyaran ba qaramin hawanta zaiba zubaida" tana jinsu harta gama surutunta ta soma hada kayayyakin gyaran jikin ta buqaci shahida ta sauya wani zani na daban data dauko.mata,fuska ta bata tana duban anty zubaida ranta na baci ta wani gefan,yanzu saboda anwar ne aka kawota nan wajen
"Anty,don Allah abar abunnan,batamin kaya kawai zaiyi" dago idonta tayi daga wayarta da take dannawa ta watsawa shahidan harara,hakanan tana ji tana gani ta sauya zanin aka shiga mata gyaran,bakinta gum tana bin matar da kallo kaman ta mangareta saboda yadda takebin fatarta da kayyakin tana shafeta dasu.

Tana ganin kawai bata lokaci da bata kudi ne.

A qalla sun kusa kashe awa biyu cur ana abu daya,bin jikin nata take da kallo yadda ya soma wani santsi sulbi da sheqi na musamman,tabe bakinta tayi data tuna saboda me akayi mata,sai taji gyaran sam bai burgeta ba,tana maida kayanta wani qamshi na tashi daga jikinta duk sanda ta motsa,turarukan qarshe da aka murje mata jikinta dasu.

Basu jima ba suka isa gida,a falonta zauna cikinsu huda wadanda ke kallo,faruq ya kalleta
"Anty harkin fara canzawa,kaman bakeba akan dazun da kuka fita'binsa tayi da ido kawai ba tare datace komai ba,kafin ta gama tunanin da take ta jiyo muryar huda
"anty...zamuyi kewarki,tafiya zakiyi yanzu ki barmu?"ta qarasa fada a shagwabe kaman zata saki kuka,nan take ran shahida yaso ya sake baci da tuna hakan da tayu,anty zubaida ce ta katse komai tana tambatar faruq me suka dafa musu,yace white rice ne bazai iya miya ba,hararsa tayi
"Daga kai har haidar din a rasa wanda zaiyi miya?" Huda na gefa na musu dariya,kai ya langabar
"Allah ummi shi yasa nace ki samo mai aiki fa" tsaki taja sai shahida ta miqe
"Bari na hada" tafurta tana yin gaba zuwa kitchen.

Kayan miya ta diba ta soma gyarawa sannan tayi blending,dukka rabin hankalinta da nutsuwarta nakan tunani,data hada miyar saita zauna cikin kitchen din tana duban agogo,tasan zuwa sanda zata gama hudu tayi saita da alwala kawai gaba daya.

Miyar na soyuwa haidar ya shigo yana shaida mata tazo inji anty zubaida,saita rage wutar can qasa yadda ba zata kama ba kafin ta dawo ta fito zuwa falon,a zaune ta sameta da tulin kaya a gaba da alama sabbabi dinkuna ne tana dagawa tana kalla gami da ware wasu gefe
"Kije waje kinyi baqo"gabanta yadan fadi,tadan bata fuska
" waye haka da la'asar din na"
"Ban sani ba nima,idan kinje zaki gani" hakan yadan kwantar mata da hankali jin ba wanda ta tsani ganin bane,nan kan kujera ta dauki mayafinta data dawo dazu dashi ta yafa sannan ta fice.

Matashin saurayine mai kyau da aji tsaye jikin motarsa,sanye yake da shadda riga da wando dinkin tazarce,hankalinsa duka nakan wayarshi a haka ta kusa cimmasa,bata sanshi ba amma sai take ganin tasan fuskar a wani waje daban ko can da dadewa,sallama ta masa ganin baisan da isowarta ba,ya daga kai da hanzari yana amsawa fuskarsa ta fadada da fara'a
"Barkanki da yamma kin wuni lpy"
"Lafiya alhmdlh" ta amsashi a taqaice
"Ya mutanen gidan kowa da kowa lafiya?"
"Lafiya qalau" ta sake amsawa tana mamaki ina ya santa tare da zurfafa tunaninta ko zata iya tuna a inda ta sanshi,murmushi ya saki
"Nasan baki sanni ba,ni sunana muhsin,aboki kuma aminin anwar" lokaci daya maganar ta sauka a zuciyarta,sai yanayin fuskarta ya soma sauyawa,fuskarta ta soma tsukewa,duk da haka tadan dake hadi da qoqarin sassautawa,shima dubanta yake yana karantar sauyawar yanayinta lokaci kadan,bai sake cewa komai ba ya bude murfin motar da yake jingine a jiki ya zura hannu ya ciro wata babbar envalope da qarama ya miqa mata,kallon envalope din tayi sannan ta dawo da kallonta kanshi alamun neman ba'asi
"Katin gayyata ne na dinner ko zaki gayyaci qawayenki,wannan kuma kudine ko zaki buqaci wani abu" kai ta girgiza tana danja baya,a fuska tana ganin mutuncinsa amma baya ga haka so take taci masa mutunci ne shida wanda ya aikoshin,amma duk da haka ba zata kasa bashi saqo ba
"Ka maida masa dukkan kayansa,ka gaya masa aurensa baya buqatar wani shiri tunda a shiryensa aka qulla shi,kudi kuwa baiyi kudin bani ba a yanzu har zuwa nan gaba,ka gaida na gode" daga haka ta juya zuwa cikin gidan tana takawa a nutse,da kallo ya bita qwaqwalwarsa cunkushe da tunani da mamaki,kullum kwanan duniya sake mamaki yake kan meye haka mai girma daya raba kwanunansu ya tarwatsasu haka zuwa pieces suka kasa kuma daidaita tsahon shekarun?,amsar daya kasa samunta kenan haryau daga wajen anwar duk da sanda rabuwar ta afku shine mutum na farko daya sha wuya da anwar din kafin rayuwarshi ta daidaita,saiya xagaya ya bude murfin motar tasa ya shiga yana tuna yadda sukayi da anwar sanda zai ya shirya kudin da katin yace zai kaimata da sunanshi,har kusan haurawa sukayi kan koda zaikai din yakai amma bada sunanshi ba.

Iska ya furzar daga bakinsa lokacin da muhsin ke zaune kan daya daga cikin kujerun office din yana sake tambayarsa wanne laifi ya aikatawa shahida haka?,ya dubi envalope din daya fita dasu ya dawo dasu kamar yadda suke,hakan na nufin bata karba ba kenan
"Bata karbi kayan daka kai din ba kenan?" Anwar ya tambayi muhsin kai tsaye yana dubanshi,kai ya kada
"Ni duk ba wannan na tambayeka ba,inason gyara wannan barakar ne shi yafi damuna,banason alaqar taci gaba da tafiya a haka"
"Me ta gaya maka sanda kaje?" Ya sake jeho masa tambaya ba tare daya damu da nashi bayanan ba
"Batace komai ba" murmushin yaqe ya saki,takowa yayi kusa dashi kujerar dake fuskantarsa ya zauna
"Ta fadi maganganu a kaina,takuma ce ba zata karba bata buqata right?" Idanunsa cikin na muhsin ya fada,kauda idonsa muhsin yayi saboda shi kansa wasu lokutan anwar na masa kwarjini da yawa
"Kaga malam nidai bance maka haka ba,banason tone tone" miqewa yayi yana jijjiga kai
"Ta fada,na santa kamar yunwar cikina" gaban envalope din ya qarasa,ya farke dayar ya cire kudaden ciki ya janyo locker din office din nasa ya zubasu ciki,sannan ya janyo daya locker ya ciro wasu ya musanyasu dasu ya maidata ya manne muhsin na kallonsa,ya kwashesu duka ya aje masa key saman teburinsa
"Idan ka gama ka rufe ko ina" daga haka ya juya yana takawa sannu sannu zai fice daga office din
"Wait mana malam,ina zaka je?" Murmushi ya jefa masa ya fita ba tare daya amsashi ba.

Gidansa ya soma isa ya bude sashensa ya shiga,ya aje kayan hannunsa,bandaki ya shiga ya tara ruwan wanka mai dumi ya sake wanka sannan ya nemi abinci yaci ya qoshi,wardrobe dinsa ya bude ya zabi kayan da yaje gani sun dace da irin wannan lokacin ya sanya,ya tsaya gaban mudubi yana taje kansa gami da kallon kansa yadda kayan suka amsheshi,tuna abinda ya faru tsakaninta da muhsin yayi,saki yaja,wato ita mai taurin kai ko?,har yau bata kallon laifinta sai wani take dorawa alhakin faruwar komai ba tare data duba nata laifin ba,aikawa yaso yi direct inda dole ta karba saqon,amma hkanan yaji yana son yaje yaga hawayenta ya takaleta ya kuma tsone zuciyarta,saiya aje cumb din yana daura agogon fata sannan ya zauna ya daura takalmansa ya feshe jikinsa da turare ya dauki key din motarsa ya fito.

A hankali yake tafiyar kaman bazaije ba,karon farko da zai fara zuwa gidan anty zubaida kenan,yadan yi nauyi a hanya hakan yasa bai isa ba sai qarfe shida mintina hamsin suka rage kenan a yi sallar magarib.

Maigadin gidan anty zubaida ne ya iso ya bashi hannu don suyi musabaha,cikin tantama yadanyi jim don yana ganin bai kamata suyi hannu da hannu ba
"Mu gaisa mana abokina,bakason ladar ne" da sauri ya miqa masa suka gaisa
"Inason magana da wata yarinya shahida a gidan nan ne" cikin washe baki yace
"Au,kaddai kaine angon?" Murmushi kawai yayi sannan ya sake cewa
"Idan ka shiga matar gidan zaka sanarwa zuwa na,sannan ka turomin faruqu ko haidar"
"Toh...toh" ya fada yana juyawa zuwa ciki.

Sanda saqon kiran ya sameta tana daki tana shiryawa bayan ta gama mitar wankan turaren da anty zubaida ta kafa nata dokarshi,turaren na nata dadi da qamshi amma tuna dalilin yinsa ke qona mata rai da dagula mata lissafi,tsaki taja sanda huda ta gaya mata ana kiranta,ta shiga mita
"Wai wanne irin kirane da baqi haka tun dazu ba za'a bar mutum ya huta ba?,haka kawai kana zaman zamanka daada ta tada zaune tsaye cak,ni wallahi na gaji da wadan nan abubuwan,daga wannan sai wancan?" A haka ta shirya ta zari hijabi ta fito
"Baqon na waje ai" anty zubaida tace da ita sanda taga ta tsaya ta mata turus,haka ta juya ta fita kaman zata fashe.

Faruq ta soma hangowa cikin dakin saukar baqi na gidan baki na motsi da alama hira yake zubawa,harara ta zabga masa duk da bai ganta ba,a haka ta isa ta yaye labulen,tare idanunsu suka sauka cikin na juna,yawun bakinta ya tsaya kowannensu na kallon dan uwanshi ba tare daya dauke ido ba,gani yayi kamar ba ita,fatarta ta sake sauyawa kyanta kaman an matso shi,qamshinta ya soma cika wajen,shima kwarjini taga yayi mata,shigar ta amsheshi,yayi kyau ya sake zama cikakken mutum da hankali da ilimi suka ratsashi,ita ta soma janye idanunta,ranta a hade tsaf ta taka zuwa ciki tana duban faruq,saiya miqe,anwar yace
"Zan nemeka kafin na wuce kada kayi nisa"
"To yaya" ya fada yana ficewa,sai da taga fitarsa sannan ta zauna hannun kujerar dake a dab da bakin qofar fita,tanason tsareshi da ido donta karanci me ya kawoshi amma batasan me yasa takejin rashin qwarin gwiwa ba,ta maida idanunta kan tafin hannunta tana murzawa ba tare data ce masa uffan ba,hakan ya bashi damar kafeta da ido,ya soma kallonta tun daga yatsan qafarta zuwa saman kanta,yana jin wasu tagwayen abubuwa na fada cikin zuciyarsa,daya nason yaqar daya gami da rinjayarsa,inda daga qarshe dayan yayi galaba,saiya runtse idanunsa yabar kallonta saboda wani bacin rai dakeson shaqeshi,kullum kwanan duniya yana son sasautawa kanshi,yana son ya daina ganin baqinta da baqin abinda ta aikata,yana son abinda idanunsa suka gane masa da hotunan daya gani su bace daga idanunsa ko zai samu salama da rangwame amma hakan ya faskara,sai komai yayi kaman zai goge saiya sake dawowa sabo fil a ransa.

Walwalar da yake jin kaman zata samu a ruhinsa ta dusashe,sauran faragar fuskarsa ta bace bat.

Zaman kurame ne yaci gaba da wanzuwa tsakaninsu harna tsahon wasu mintuna,sai daya gama zamanshi don kanshi sannan ya miqe,cikin wani taku ya isa dab da ita ya tsaya akanta,kana ya ranqwafa gefanta har tana iya jiyo qamshin ya aje envalope din hannunshi,ba tare daya dago ba yace mata
"Baki iya gaisuwa ba saikace a gidan mashaya inda kowa yake ogan kanshi,karki tsammaci xaki gidana da wannan dabi'ar ki tsira,ga saqon da muhsin ya kawo miki daxu kika maidashi nina dawo dashi,idan kin isa karkiyi amfani dashi yadda ya dace kiga yadda zata kaya mana nidake,tunda na fahimci cikin halayen da kika koyo kala daban daban harda taurin kai ko?,good....inason wannan sabon halin naki,idan kin tashi gayyatarki karki sake ki kwaso min tarkacen 'yan maye,ko tarkacen qazaman tsaffin samarinki" daga haka ya dago yana shirin wucewa zuciyarta taje iya wuya,ta kasa daurewa
"Idan ba haka bafa?,me zakayi?" Ta fada a tsiwace cikin fushi da fusata,saiya sake dawowa gabanta ya tsaya,ya dubeta na wasu mintuna sannan ya saki murmushi
"Ki aikata din sai kiga sakamakon" miqewa tsaye tana masa kallon tara saura kwata sannan tace dashi cikin salo na masifa dake cin zuciyarta
"Baka isa ka sakani abinda banyi niyya ba,baka isa komai ba idan ma kana tunin ka isa" murmushi ya sake saki wannan karon mai sauti,yadan buga qafarsa sannan yace
"Ko a haka aka tsaya ai inga irin tawa isar ko?,hukuncin da zan miki ba isata kawai zai nuna miki ba,izzar aure da izzar anwar namiji"
"Namiji shine zai tsaya takara da abokan adawarshi ya kuma samu nasara,ba wanda zai wafta koya biyo ta bayan gida ba,koya taka wani tsani don kaiwa wannan bigiren,ka daina batawa kanka lokaci wajen kiran kanka da namiji,ba namiji bane kai saidai mata maza" idanunsa ya qura mata qir sanda take maganar cikin dakiya da rashin nuna tsoro,hakanan bilhaqqi da gaske,ganin takai aya saiya soma takowa inda take tsaye,ta tsaya cak don ganin iya gudun ruwanshi,saidai harya iso gab da ita bai daina takowa ba,hakan na nufin zai hade gap din dake tsakaninsu kenan,don haka ta soma ja baya ga zatonta zai tsaya amma ina,bai barta ba sai daya tabbatar ya hada bayanta da bango,qafarshi dake saye da takalmi saman tata qafar wanda yana iya jin zafi zafi na tudun takalminsa daya take mata qafa,kusancin dake tsakaninsu yayi yawa,tana iya ganin fuskarsa tarwai wadda kyau ya cikata gamida iya gyara,idanunsa sai suke juye mata irin na anwar dinta na wancan lokacin sak,janye qwayar idanunta tayi gabanta na bugawa da sauri da sauri,tsoro da fargabar me zaiyi mata na shigarta,saitaga ya daga hannu kaman yana shirin marinta,ta runtse idonta da sauri tana wassafa me zata masa ita bayan ya gama marin nata,ji tayi yaja baya da sauri cikin kaushi yace
"Sai na saki kinyi nadamar lafazinki,tsautsayi kuma yasa bakiyi yadda nace miki ba" daga haka ya juya da sauri sauri ya fice daga dakin,cikin hanzari ta daga murya
"Idan ka isa ka tsaya mana ka dakenin kaga yadda akeyinta" gab da zai fice ya waiwayo yace
"Aiba a gidan syrup muke ba" kalmar ta tsaya tana fassarawa,take wani abu ya cushe mata maqoshi,cikin qanqanin lokaci hawaye ya ballewa idanunta,tana jin zafi a zuciyarta duk sanda yayi wani lafazi dazai iya tuna mata da abinda ta aikata a baya,sulalewa tayi ta zauna a wajen,ba shakka ba'a bari a kwashe duka,shaye shaye ashe wani tabone da tambarinsa bai barin jikin maishi?,koda kowa ya manta ba'a rasa burbushi,ta jima a wajen tana jin ciwo kala kala kafin ta miqe ta fice daga dakin,ko kallo envalope din basu isheta ba bare ta dauka.

A falo anty zubaida tace ta tsaya ta duba dinkunanta na biki wanda ita batasan ankai bama,don ko kayan har yau bata kalla ba bare ta gane me takeso a ciki har tayi tunanin kaiwa dinki?,bata cikin yanayin da zata iya zama cikinsu saboda haka tabawa anty zubaidan uzurin kanta na ciwo zata duba zuwa safiya da haka ta wuce dakinta.

Washegari sun fito da anty zubaida zata koma gidan gyaran jiki tanata kumbure kumburenta

28 / 53