Author : HUGUMA Category : African Stories & Novels
iya girki saboda rayuwar da yayi tsahon shekaru shi kadai,amma bata da tabbacin iyawar takai har haka.
Waiwayawa tayi sanda aka turo qofa,shine yashigo riqe da cumputer dinsa,idanunsa a kanta,saita dauke kai tayi gaba tashige bandakin kamar ba itace tsaye tana qarewa abincin kallo hadi da sheqar qamshinsa ba.
Kafin tafito ya zuba komai dan dai dai saman plate,ya jawo dan qaramin carfet din dake can gefan gadon ya shirya akai,yana zaune shima akai ya tanqwashe qafafunsa,idanunsa akan qofar sanda ta fito,ta qarasa tadauki wayarta dake tsuwwa tazauna gefan gadon tana amsawa,saiya dauki cokali yasoma ci yana dubanta,itama lokaci lokaci takan faki ido takalleshi,qamshin abincin na saka mata jin yunwa harta kammala wayar
"Kinason kiji yadda mutum yakeji idan an masa rowar abinci ko?" Bata ce masa komai ba harsai da yayi loma kusan uku
"Oya....sauko kici don ni bazan iya hanaki ba" kai ta dauke tana kyabe baki
"Banaci"
"Ko?" Ya tambayeta kaitsaye,saiya aje cokalin nasa ya hade hannunsa yana kallonta
"Option biyu kawai zan baki....na farko" ya furta yana daga yatsanshi
"Ko ki sauko kici da kanki,na biyu....kona tashi na miki dura,na rantse kuma idan bakici ba abinda zan miki kenan" tunda taji ya rantse zai aikata din,hakan yasanyata ta zamo ta qaraso zuwa can carfet din tana hade rai,pillow ya janyo guda biyu yasa mata daya daga bayanta daya daga gefanta cikin tsokana yana cewa
"Bari nasa miki waigi tun kafin ki soma ci,dama na miki alqawari idan baki manta ba shekara shida baya....zan miki girki a lokacin da mukayi aure,duk sanda kika soma ci kunnenki saiya tsinko ya fadi,can u recall?" Ya fada yana dage mata girarsa,sosai jikinta yayi sanyi,ta tuna lokacin,daya daga cikin lokuta masu sanyi da ratsa zuciya cikin tarihin rayuwar soyayyarsu,lokaci cikin lokuta mafi tsada a rayuwarsu,ta tuna lokacin fes,yana daya daga cikin lokutan da sukan zauna kowa na fadin abinda ya tanadarwa dan uwanshi duk lokacin da suka zama mallakin juna,harya tura mata abincin tana cikin tunani,ta miqa hannu ba musun nan ko taurin kai ta soma cin abincin,ya kafeta da idanu yana qoqarin dora murmushi kan fuskarsa,duk da can qasan zuciyarsa wani irin bacin rai da zallar tausayinta ke ratsashi,yaa rabu da ita na tsahon shekaru bayan yasan cewa a daidai lokacin babu wani buri da take dashi sama dashi,bata da wani tunani ko fata sai nashi,ta narka rayuwarta cikin tashi sun narke sun zama abu daya amma ya tsame tashi rayuwar daga cikin tata,saboda wani dalili,saboda zallar mugunta baqin hali da mugun qulli na wasu mutane,mutanen da baisan su waye suba,me suka musu da har suka zabi rabasu ba gaira babu dalili?,qoqarin kauda tunanin yayi saboda a yanzu ba lokacinsa bane,babban burinsa shine ya samu kanta ya sanya daidaito haquri da yafiya cikin ranta,kaman hadin baki suka sake hada ido lokaci daya,ya kashe mata ido daya
"Ya kikaji girkin?" Saita tabe baki donta bashi haushi tana fito dana bakinta wanda batakai ga taunawa ba tana ajewa a gefe
"Ba dadi,gishiri,yaji magi mai duka" baisan sanda ya qyalqyale da dariya ba,abinda bata saniba shine,duk abinda tayi da wata niyya yana karantarta,saidai yakauda kai kawai kamar bai gane ba,yasan cewa dabiyu tayi
"Ko?,to tunda hakane bari kiga" yayi maganar sanda yake juyo da bangaren data fito dana bakinta yasoma dauka kaiwa bakinsa
"Ko babu dadi tunda yashiga bakinki nasan zai zama mai dadi" kallonshi take yadda yakecin abincin hankalinsa kwance.
Dai dai lokacin da hankalin nafisa ya kasa kwanciya,takai takawo a falonta yafi a qirga,bai fita daga gidan ba yana nan,amma koda wasa bataga gilmawarsa ba,tayi kawaicin har d'an haqurin nata ya qare,sannan kuma ma gaba daya 'yar qofar da zaka shiga barandar da zata sadaka da falon a qulle take bare tashiga dakinsa tadubashi.
Qarar wayarshi dake aje gefansu ta dauki tsuwwa,a tare idanunsu yakai kan screen din,sunan nafisa ya bayyana saman wayar,saiya miqa hannu zai dauka,batasan ya akayi ba nata hannun yariga nashi isa,tana dauka ta datse kiran sannan ta maida wayar ta aje,sai kuma wani nauyi yakamata ta kasa hada idanu dashi,boyayyen murmushi ya subuce masa,wani sanyi yaji yana ratsa zuciyarsa,ya zuba mata ido sosai yadda ta daburce gaba daya amma ta dake batason ta nuna
"Kishina kike shahida?" Ya ambata murya can qasa yayin daya kafeta da idanunsa da har wani lumshewa tsabar shauqinta da yakeji yana ratsa ko wani sashe na jikinsa,qauna da soyayyar da yayiwa zagon qasa,ya takura 'yan cinta duk da baqar wuya da yakeci,ya hanata ta sakata ta wala,ayau ta samu 'yancin cin gashin kanta,ta samu dama tanata ambaliya iya son ranta,ji yake kaman yanzu yanzu ya soma son shahidan._Abota mai cike da aminci shaquwa da kuma qaunar juna,sadaukarwa da girmama farincikin juna_
_kin karantashi?_
*DANGANTANAR ZUCI*
NA
_SAFIYYA HUGUMA_
_KI KASA KUNNE KI SAURARESHI A TASHAR SAUTIN HIKIMA DAKE DANDALIN YOUTUBE_
*Latsa blue din rubutun nan dake qasa wanda shi zai kaiki ga ainihin inda labarin yake*
https://youtu.be/HJ6p1BihojI
*ALK'AWARIN ALLAH*
49
"Me yasa kake damuwa sai nayi kishinka ne?,kai abun kishi ne wai?" Ta jefa masa tambayar cikin gatse gami da harara,qaramar dariya yasaki yana gyara zamanshi sosai sannan ya kalleta
"Ke za'a tambaya ai,idan na isa abun kishi ko ban isa ba duka kin sani,amma nameye xaki kashemin kiran mata?"saita tasa amsar tambayar,hakan yasa tadanyi jim na wasu lokuta amma tana fakewa dacin abinci harsai data lalubo amsar sannan tace
"Raini ne banaso,ka gaya mata kada tasake kiranka irin haka,idan ba haka ba kar a sake shigomin daki,dama ni na yafe mata kai tuntuni da dadewa,shekara biyar zuwa shida" dariya na taso masa amma mamaki ya kamashi kan furicinta,yaushe tasan nafisa?,a ins kuma?
"Dama kin santa ne?" Ya tambayeta yana dariya dariya,saita qi bashi hankalinta,don jin tambayar take kaman ta rainin hankali,kamar da biyu yake mata tambayar,ita zai tambaya ma wai tasan nafisa ko bata santa ba?,saita shareshi taqi amsashi
"Uhmmm,kenan dama bincike kike akaina ko?" Ya sake tambayarta yana dage mata girarsa
"Ka isa ma?" Ta fada da sauri tana tsareshi da ido don kada ya zaci ta damu dashine har take bibiyarsa
"Ohhhh....hakane fa" saiya miqe tsaye yana ci gaba da boye dariyarshi,yadauki wayarsa ya juya ya bude dakin yafice,saita saki ajiyar zuciya,me yasa bata iya shareshi ne?,me yasa take biye masa?,ta tambayi kanta,ta sake sauke numfashi tadan jingina da filon daya sanya mata tana tuna irin maganar da sukayin a yanzu da amsar data ringa bashi,saita dan dafe bakinta kadan,taji wani abu yadan sosa ranta,kaman tana amfani da kalmomi masu tsauri da bada negative answers da basu kamata ba,data tuna kuma dalilin daya janyo haka saita share kawai,batason yadawo suyita maimaitawa don haka tamiqe ta isa bakin qofar,ta saka muqulli tarufe,dawowa tayi tazauna ta sake jingina da filon tana lumshe ido,a hankali darensu najiya ya soma dawo mata,saitayi zumbur tazauna tana kwabar kanta,duka abun kunya yake bata,shi yasa shi kansa anwar din batason dawowarsa,jinta take duka a takure,wani banbarakwai,sake gyarawa tayi takoma ta sake kwanciya.
Bayan yabude madaidaiciyar qofar yasoma sauka qasan,tana nan tsaye jikin makarin benan tanajin taku ta daga kai tazuba masa idanu tana kallonshi,fuskarta kwance da bacin rai kamar yadda ta tsammaci ganin tashi fuskar,saidai ga mamakinta wani irin annuri nutsuwa da kwanciyar hankali take gani kwance saman tashi fuskar,babu bacin rai ko qwayar zarra,sai hakan yasake baqanta mata,wato kwanan farinciki sukayi kenan shida matarshi?,ita taga duhu?
"wannan wanne irin tsantsar rashin adalci ne ?,ka dauki kwanana ka kaiwa wata?" Ta fada kamar xata saki kuka,dubanta yake sosai cikin mamaki,anya bata da jinnu yarinyar?
"Ashe harkin manta lokacin da kikacemin naje kenan?" Shuru kuma tayi bata da sauran wani abun qorafi kuma,idan ma za'a daga nata lefin ya ninnika nashi,to amma bai kamata tayi faduwar haka warwas ba
"Kuma saika tafin?"
"Ina da maslahar data wuce haka ne?" Ya jefe mata tambayar yana tsareta da kallonshi,wanda yakarya duk wani karsashi da shiri nata,dole tasauya akalar maganar
"Ga breakfast can" daga kai yayi ya dubi sashen sannan yakalli agogon dake maqale a saman wajen,ba tare da yayi magana ba ta fuskanci me yake nufi,saboda haka bata sake cewa komai ba
"Uhmmm,akwai wani abune?" Kai ta kada tana matsawa daga wajen,itakam gaskiya wannan maganin banda mima ta gaya mata haukane qarshen sakamakon rashin kammalashi da babu abinda zai sata qarasashi,haqura zatayi,soma tsinewa shahida tayi,a duniya bata da maqiyiya sama da ita,waima me yasa qaddara bata fara hadata da anwar ba?,lallai dada ita ya soma haduwa duk yadda zatayi ta toshe ganinsa daga kan duk wata diya mace sai tayi,saiya qarasa saukowa shima yasamu daya daga cikin kujerun ya zauna
"Zonan" yayi kiranta,ta tako a hankali ta zauna kujerar dake daura dashi,kallonta yayi na tsahon wasu mintuna wanda hakan yayi mata nauyi,kwarjininsa yacikata,yanayin fuskarsa kawai ya gaya mata dagaske zaiyi dukkan wata magana da zata fito daga bakinsa
"Me yake damunki?,meye matsalarki?,lafiya ce baki da ita ko kuwa?" Ya jefa mata tambayar data zo mata a bazata,tadaga kai ta kalleshi ta maida qasa da sauri,saboda kwarjininsa na iya sawa ta fadi sirrin cikinta
"Babu komai,lafiyata qalau"
"Kin tabbatar?"
"Eh" ta amsa mishi gabanta na faduwa
"To me yasa kike duk abinda kikeyi din?" Tsoro ya kamata taqi dubanshi,tsahon minti biyu kafin tace
"Babu komai" cike da mamaki yake dubanta
"Babu komai?" Kaita sake gyada masa,shima shurun yayi yana jinjina kai tsahon wasu daqiqu sannan ya sake kada kai
"Is okey,yayi kyau" daga haka saiya miqe ya soma takawa zai fice daga falon,binsa tayi da kallo harya qarasa ficewar sannan yaja qwafa tana maida kallonta saman benan,tanajin kamar tahau ta jawo shahidan ta sauko da ita tama fiddata daga gidan gaba daya,gashi kwata kwata bata kulata,babu fuska ma tattare da ita bare ko fadi in fada suyi ta samu caccaba mata maganan da zata tsaya mata a ranta,don taci alwashin saita sa mata baqinciki da takaici a ranta tabbas kuwa,koba dade ko bajima.
Qarfe uku na rana ba zato saiga mima ta kawo mata ziyara,ta dinga kallon inda suke zaunen bayan ta gama zagaya gidan tana qissima ranar shigowarta,tanajin ba zata iya haqura takai har lokacin datake hasashe din ba,gwara tashigo kota yayane itama a dama da ita,mai rabo ka dauka,ya kamata tasoma yiwa nafisan jirwaye da kamar wanka,ta maida kanta kan nafisan dake aje mata kayan qwalam
"Kuwai komai da kanku kuke ko irin mai aikin nan baki da ita?" Baki ta tabe tana neman wurin zama
"Shifa mutumin nan duk inda na zaceshi ya zarce nan,ra'ayinsa komai nashi daban yake da sauran maza,baya ra'ayin me aiki idan ba iyali matarsa ta tara suka mata yawa ba,anan dinma yace saiya zabo dattijuwar daya yarda da ita mai asali da mutunci" kai ta jinjina cikin zuciyarta tana cewa bari dai tashigo saita gyara zaman kowa.
"Gidankun nan yayi min kyau" miman ta fada tan kurbar lemo idanunta akan nafisa tanason taga yanayinta,saitayi murmushi
"Donma qaraminne bakiga babban ba" idanu tadan fiddo
"Oh,yana da wanda yafi wannan ne?" Kai ta jinjina
"Sosaima,ainishi naso ya sakani yace a'ah dukka anan xamu zauna"
"Allah yasamu a danshinku"
"Ameen" ta fada cikin alfahari,haushi ya kama mima ganin nafisan bata shinshino komai ba,saita rabe baki,badon tanason dorata akeken bera kada tagano da wuri ba ai dayau kam zata fada mata abinda ke ranta
"Nifa mima,matar nan ta soma shigemin hanci qwarai,kawai so nake na fatota"
"Kaman yaya fa?,banace miki kibar mata shiba nadan lokacine aiko?,kinga nafisa ki rufawa kanki asiri karki xo kiyi abinda zai dameki ki bata rawarki da tsalle,wannan banzan kishin fa dole ki taka masa burki zuwa na wani dan lokaci" nan mima ta fitittike mata saida ta tabbatar nafisan tahau ta zauna daram sannan tasamu sukuni,zuwa sanda komai zai qare zatasan yadda zatayi dasu gaba daya.
Daya fita gidan anty usaina yaje wanda yayi wajen kwana biyar bai samun zuwa,tunda yaje kowa zancan shahidan yake masa,ita kanta antyn ita take tambaya,a hanyar dawowa ne ya tsaya ya kira wani yaronshi marwan,ya masa bayanin binciken da yakeso ayi masa,ya dauki hoton fiddausi,suna da unguwarsu,sannan yadauki fuskar matashin duka ya tura masa,sai daya tsaya ya yayi musu takeaway na abinci duka su ukun sannan yakoma,a lokacin biyar da rabi na yamma.
Sanda yashiga baisamu nafisan ba tana bandaki,ya aje mata ledar nan cikin dakinta sannan yawuce saman,sanda yamurda qofar shahidan sai yajita akulle,yasan dai saboda shine,murmushi yasaki ya sauka qasa dakin karatunsa,inda yake aje muqullan gidan duka ya laluba yaciro spare ya dawo ya zira ya bude,a hankali ya tura qofar,duka dakin yayi duhu sakamakon qwan lantarki da aka kashe sannan kuma dukka labulayen dakin a sauke kuma a zuge,duk da haka yana iya hangota kwance tsakiyar gadon tana baccinta hankali kwance da tunanin babu wanda zai shigo mata daki,murmushi yasake saki cikin zuciyarshi yana cewa
"Wannan fa shine bonono din rufin qofa da barawo" aje mata ledar itama yayi ya rufe mata qofar yadda yaganta yajuya ya fice.
Wanka yasake sannan yazauna sosai ya soma cin nashi abincin ,yanaci yana nazari gamida shirya yadda abubuwan zasu kasance,wayarsa ya dauko dake gefe ya lalubo number muhsin yakira,bata wani jima tana ruri ba yadaga,suka gaisa kana suka dan taba hira,irin hirar da suka saba sannan ya jeho masa tambayar
"Amm da Allah nace zaka iya tuna fuska ko wanda ya baka envalope din nan daka kawomin shekara shida baya?"
"Wace envalope fa?" Kwatanta masa lokacin yayi,muhsin yasaki dariya
"Kai mutumina,da alama an baka alawa irin tada shine ka tuno da lokacin ko?"murmushi ya kubce masa,saidai bai bari muhsin ya fahimta ba
"am seriouse inason nasani ne muhsin"
"Gaskiya ban sashi ba,infact ma ban taba ganinsa ba,har yauma ban sake ganin fuskar ba"
"Oh god,try to recall mana muhsin"
"I can't recall anything....da gaske nake maka namanta anwar,shekarunfa da yawa"
"Alright,shikenan,amma inason indan rage ayyukan office dina zuwa naka,saboda akwai muhimmin abinda zanyi,wanda maybe ya dinga jamin lokaci ya hanani aiwatar da duka ayyukana"
"Baka da case,aikai yanzu sai an maka uzuri,ka zama mai gida biyu" murmushi kawai yayi masa,sannan ya masa godiya katse kiran.
*10:30 pm*
A tsorace ta daga kai ta dubi bakin qofar,dama tun daxu data farka taga abinci jikinta yabata anwar ne ya bude qofar,to amma ta ina yasamu key dinta?,tambayar data dinga yiwa kanta kenan,idan tace bata tsorata da anwar ajiya ba ba shakka tayiwa kanta qarya,hakan yasa yau din gaba daya ta kasa sakewa cikin dakin nata,dukda ta gama shirin kwanciya amma tana zaune daga gefan gadon.
Yakaranci abinda ke idanunta amma saiya basar ya isa saman gadon ya aje butar shayi da cup din dayashigo dashi gamida wayoyinsa da qaramin littafin addu'o'insa,saita sauya wajen zama kan kujerar dake kallon gadon,bai tanka mata ba kaman yadda itama haka har ya gama komai ya haye saman gadon,yazauna sosai ya jingina da fuskar gadon yamiqe qafafunsa bayan ya rufe qafafunsa zuwa qugunsa da duvet,idanunsa cikin nata yace
"Taho ki kwanta" saita maqale kafada,idanunta na shirin raina fata
"Bakiji ba?" Ya tambayeta yana daga girarsa,saitayi shuru ba tare data amsa masa ba
"Ba abinda zan miki ki taho ki kwanta" ya fada yana daga hannunsa sama kaman wanda yayi surrender
"Mema ya kawoka dakina?" Ta tambayeshi cikin tsoron da takeson boyewa,ya danne dariyarsa ya amsa mata
"Abinda ya kawoni jiya" yankewa gabanta yayi yafadi,idanunta suka hada qwalla tanason shanyesu don kada yagani,ya zuba mata ido yana karantarta dariya tana cinsa
"Duk jarumtarki da iya maida magana?....tsokanarki nake to taso ki kwanta,idan kika musamin kuma zanyi abinda bakiso" hakanan ta taso cikin mutuwar jiki da tsoron da bata taba zaton zatayiwa anwar din shi ba.
Yana kashe wutar dakin taji caraf ya rungumota ta baya,a tsorace tace
"Kayi alqaw...."
"Ban manta ba..." Yayi saurin tararta gami da bata amsa,sosai ya sanya shahidan cikin jikinsa yanajin duminta,lumshe idanunsa yayi yanajin wani madaukakin farinciki na yawo dashi,yanajin kamar duk duniya babu wata halitta data kaishi farinciki a irin wannan lokacin,tun suna sauraren bugun zuciyar juna har bacci yayi awon gaba da kowannensu.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Cikin kwanakin duk yadda taso kauce masa yaqiya,duk yadda taso nesanta kanta dashi kamar yadda suka saba yaqi bata wannan damar,ya shanye yacinye ya kuma jure duk wani qalubale daga gareta,ta sashe guda kuma lokaci zuwa lokaci tana mamaki dason sanin meye ya sauya dukkan wani tsauri nashi zuwa laushi sanyi taushi da zallar qauna?,ta kasa samo amsa ko fahimtar komai,haka ta kasance cikin wannan tunanin na tsahon lokaci.
Gefe guda nafisa nata lissafin kwanakin da suke gabanta,saidai kowacce rana cike take da shahida,bata ishi shahidan kallon ba bare ta tanka ta kota samu abun fada,sautari koda hanya ta hadasu da shahidan kallo daya shahidan take mata ta kauda kanta kamar batasanma Allah yayi tsiron nafisan ba,duk yadda ta tsammaci shahidan saita taddata ta wuce nan,wani irin aji ne da ita,kamun kai da jan mutunci,qasanma takan iya jera kwana biyu batako leqo shiba bare tasauko.
Hakan yana yiwa nafisan ciwo,ba haka takeso ba,duk da haka tayi lamfo tanason ko sau daya ne ta tanka ta amma bata kula ba.
Ranar data soma janta shahidan ta sauko qasa a backyard dinsu ta wanke undies dinta ta shanyasu anan saboda bandakinta rana bata shigowa,ita kuma tafiso rana ta dakesu su bushe saboda.zafin ranar yakan kashe qwayoyin cuta idan akwaisu a jikin undies.
Da yammaci ta sauko zata debe,tunda ta sauko daga sama ta tadda nafisan zaune cikin falon,bata ko kalli gefanya ba amma taji a jikinta irin kallon da take mata,ta wuce abinta zuwa inda tayi shanyar,saidai abin mamaki babuko abu daya a shanye,data duba wajen dakyau saita gansu cikin wani kwando da ake zuba sharar flowers da ake yayyankewa na gidan,tayi mamakin meya kaisu ciki?,saidai bata kawo kowa a ranta ba ta juya don komawa ciki,tana shiga falon ta soma jin dariyar nafisan,bata sani ba waya take koba waya takeba oho don bata dubi sashen ba,amma ta tsinto muryarta tana cewa
"Wallahi kadanma mutum yagani,ba abinda mutum ya aje sai shegen jin kan bayan ba kowan kowa bane,da bamusan asalin balbela ba da sai muce daga masar tazo saboda tsabar fari" ta gane ta kuma fahimci sarai cewa da ita take,ranta yabaci sosai