Author : HUGUMA Category : African Stories & Novels
gida ne,ita kanta daadan ma bata sani ba,inaga basai anje anata kaiwa da kawowa ba,ayi komai kawai a gama lokaci guda"
"Kana ganin babu wata damuwa ko matsala?"
"Haba shehu,kaine fa,babu wata damuwa wallahi,dama meye burinmu banda muga yaranmu sunata aurensu".
A ranar gaba daya kawu ummaru suka amshi kudin auren shahida harda sadaki,aka kuma tsaida lokacin biki ko ince daurin aure a wajen maza watanni uku masu zuww,wanda yayi dai dai da watannin da aka tsaida a farko na daurin aurenshi da nafisa.
Yana tsaye jikin motarshi qafafunshi amatuqar sanyaye,irin wannan lokaci ya jima yana mafarkin zuwanshi shekara shida baya,ya qiyasta yanayin farinciki da zai samu kansa a duk sanda Allah ya tabbatar masa a wancan lokaci har baisan sau naya ya qiyasta din ba,sai gashi abun yazo a bahagon yanayi,yanayin daya kasa tantance wani iri ne,farinciki ne ko baqinciki?,kansa ya daga a hankali sanda ya soma jiyo muryoyin su kawu dahiru da alama suna sallama ne dasu kawu ummaru.
Ranar kasa shiga yayi wajen daada duk da yaso suyi sallama,haka ya sake dibansu kawu shehu ya sauke kowanne a gidansa sannan suka wuce wajen inna shida kawu modu.
Murmushi ne kawai ke fita a fuskar daada sanda 'ya'yan nata ke gaya mata yadda komai ya kasance
"haba,ba banza ba nutsuwar yaron ta yimin,naji ya shiga raina sosai,ashe jinin gidan malam usman ne(sunyi zama na maqotaka ne tun iyayensu da kakanni,zaman da sukaji dadinsa,kunsan mutanen daa akwai riqo da zumunci da kuma girmama alaqa da dangantaka komai qanqantarta),na godewa Allah,Allah yasa albarka ya kuma tabbatar da alkhairi"
"Amin daada" dukkansu suka amsa suna jin dadin hadin
"Yanzu daada za'a sanar dasu kenan?"kai ta girgiza
"qwarai kuwa,ka shaida ma ita uwartata,sannan kuma ka kira can gidan hishamun a shaida musu,duk da cewa shi ya sani amma sai a gaya masa an karba harda kudin auren da sadaki,gobe idan ka dawo kai ummaru ka kiramin rahamar ka hadani da ita"
"To shikenan daada" ya fada yana lalubar wayarshi dake aljihun rigarsa.
*_GUDUN QADDARA guzurin taddata....._*
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wadda ta fito tun daga zuciyarta,ta sauke idanunta kan tafin hannunta tana bitar maganganun nuradden daya gama furta mata ayanzu,dauta dauko na anty zubaida data gama gaya mata jiya,kusan maganganun nasu sunyi kamanceceniya da juna,a yanzu bata da wata mafita bata da wani uzuri kaman yadda anty zubaida tace mata,imma dai ta baiwa nuradden dama wa imma ta sallameshi hakanan ya daina wahala,ko ga ummanta madai wannan karon ta matsa qwarai kan ya kamata ta tsaida manemi tayi aure,tunda dai abinda ya farun da ita bawai qarshen rayuwarta ya kawo ba,saima sabon babin rayuwa daya sake bude mata,idan ta sallami nuradden bata jin akwai wani qwaya daya cikin samari dama masu auren dake kara kaina akanta da zata iya kwatanta rayuwarta ta wanzu tare da tashi
"Na amince nuradden....Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi" hannayensa gaba daya ya hada ya rungume a qirjinsa yana lumshe idanunsa,wani farinciki da baisan a wanne mizani zai dorashi ba ya shiga dawainiya dashi,sai kawai ya zame saman gwiwoyinsa a gabanta
"Shahida,ki fadamin me kikeso na baki ladan wannan kyakkyawan albishir din naki?" Kai ta kada kawai qwalla na taruwa a idanunta,murmushi mai cakude da alamun son yin kuka na kubcewa saman fuskarta
"Babu abinda zaka bani face nace kayi qoqari karka sa na sake yin nadama da dana sani a rayuwata karo na biyu"
"Koda baki roqi haka ba wannan duty na ne" da ido kawai ta dinga bishi yadda ya rasa inda zai tsoma ranshi ya dinga bata mamaki,harta daina mamaki ma abun ya soma bata dariya,sai daya tabbatar ta dan saki ranta sannan yace
"Yanzu yaushe za'a kai maganata katsina?,shine abu daya da zai sake sawa in samu nutsuwa a raina,in kuma tabbatar na yiwa duk wani dake da buri ko hanqoran mallakarki na masa fintikau din da dole ya haqura" murmushi ya qwace mata,tasan cewa burinsu daada kenan,tana da tabbacin indai nuradden ya isa katsina to magana ta qare,don ba wani lokaci zasu ja ba ba tare da sun bashi ita ba
"Karka damu duka abun bana sauri bane,next month za'a dauki azumi,sai kayi haquri mu barwa salla" fuska yadan bata
"Gaskiya yayimin nisa,saidai idan har kin yarda ne ni zan kaiki,qafarki qafata"hannu ta daga tana murmushi
"Shikenan naji,sai kuma me?"
"Aikin gama min komai nikam,yau nafi kowanne namiji dake fadin duniyar nan sa'a" yayi furucin a sanda yake kallon sararin samaniya cikin madaukakin farinciki.
Qarfe tara ta shiga gida don bata wuce hakan a waje,duk da dama ba fita take wajen kowa ba,kusan nuradden din ne kawaima yaci qwallo da har take fita ta saurareshi,ga mamakinta saita tadda anty zubaida zaune saman kujerar falon hannunta daya tallafe da kanta,gwiwar hannunta saman hannun kujera,ba kowa falon sai ita kadai,kallon wani series da suke haskowa a mbc take,sallamar shahidan ya sakata dagowa da sauri tana dubanta
"Anty,yau yana sameki a nan?" Qoqarin daidaita kanta tayi
"To ya zanyi,uncle dinki yace lallai lallai naga shigowarki na tura masa ke" murmushi tayi tana zama hannun daya kujerar dake daura da anty xubaidan
"Hala anty kinkai masa qarata ne kan nuradden?,to kisha kuruminki,na riga na baiwa nuradden dama,zuwa nan da qaramar sallah xai isa gasu daada in sha Allahu" ta qarashe tana duban anty zubaida,don tasan ta gama mata abinda ranta keso kenan,sai taga ta murmusa kadan
"Ya za'ayi nakai qararki?,koda nakai dinma ai Allah abinda ya hukunta dole shi zai faru ko?,yanzu dai kije yana falonshi yana jiranki" sai data miqe sannan tace
"Anty muje tare mana don Allah"
"Ba ruwan zubaida" ta fada da hanzari,dariya ta baiwa shahidan yadda tayi maganar kamar wata baquwar uncle hisham din,saita juya ta wuce tana cewa
"Ai shikenan anty".
"barka da dare uncle"shahida ta furta sanda ta nutsu a gaban uncle hisham,ya sauke takardar da yake dubawa ya kalleta
"barka kadai shahida,sai yaushene zakuyi hutun naku kamfanin?"
"Eh to uncle gaskiya ina zaton sai sai dab da sallah,saboda wannan season ne na yawaita da kuma cunkoson custumers" kai ya jinjina sannan ya danyi shuru kamar mai nazari kafin daga bisani yace
"Daada ce keda buqatar kije,to ban sani ba ko xaki samu ko weekend ne kije kiji kiran nata na meye?"
"Shikenan uncle babu damuwa,yau alhamis ranar juma'a tunda da wuri muke barin kamfani saina shirya naje,idan yaso ran lahadi da yamma saina dawo"
"Hakan yayi,shikenan dama kiran"
"To uncle saida safe" ta fada tana miqewa
"Allah ya bamu alkhairi".
A inda tabar anty xubaida nan ta taras da ita,saita daga kai tana kallon shahidan,ganin babu sauyin fuska tattare da ita ya tabbatar mata uncle din bai gaya mata komai ba,zai turata ne kaman yadda dada ta buqata,sallama anty zubaidan tayi mata ta wuce wajen uncle din,tabar shahidan na sake sabon xaman ganin maimaicin wani shiri,tana mitar baccin wuri da yau su faruqu sukayi suka barta ita daya,don bata jin dadin zaman falon ita kadai.
A nutse yake murza motarsa tamkar wanda baison barin titin har zuwa sanda ya isa unguwarsu anty usaina,cikin nutsuwa ya faka motar sannan ya kasheta ya fito,cikin wani irin karsashi yake takawa zuwa cikin gidan,haka kawai yake jinsa kaman mai yawo cikin farin gajimare wanda shi kansa baisan dalilin haka ba,yana shirin saka qafarsa kan step qwaya daya da zai sadashi da falon gidan ya jiyo muryar sa'ida na kiranshi,a nutse ya waiwaya,sai ya tsaya hannayensa zube a aljihun wandonsa yana dakon qarasowarta.
Aladabce ta rusuna tana gaidashi ya amsa yana dubanta
"Daga ina kike?" Sai data dan waiwaya sannan ta dawo da dubanta wajensa
"Uncle....gidansu anty shahida,ummi ta aikeni na amso mata saqo?,kasan me uncle?" Kai ya girgiza yana dubanta
"Na ganta mafa tazo wajen mamansu,uncle kaganta kuwa kaman ba ita ba...."takun data jiyo ya sanyata tsuke bakinta,cikin minti daya anty usaina ta bayyana,akwai 'yar tazara tsakaninsu kadan,ya juya ya dubi sa'idan
"Wuce kafin tazo ta fara miki jajayen idanuwa" maganar ta baiwa sa'ida dariya har sai data qyalqyale da dariya sannan ta soma takawa don wucewa ciki
"Wato kin dawo shine kika samu waje kika tsaya kina masa wannan dan banzan surutun naki ko?"kai ta gyada
" a'ah ummi,nima fa yanzu na shigo"harararta tayi cikin ranta tana qissima lallai ya zama dole ta kwabi sa'ida,donta fuskanci kanta yana rawa tanason ta lalata mata plan
"Wuce,saura kuma naga qafarki a wajen" da hanzari sa'idan ta wuce,anty usaina ta bita da kallo harsai data shige sannan ta dauke idanunta,dai dai sanda anwar yake tsaye daga inda yake,a nutse yana karantar duk wani motsi na anty usaina,murmushi ya kubce masa,ya gama ganeta tsaf,ya gama karantar tsoronta,ya kuma gane me take boye masa,saidai baisan nata shirin ba,koma meye nata shirin shi zai mata ba zatan da bata tsammata ba,idonta ta sauke a kanshi,tana tsaye har ya isketa
"Yaushe kai kuma ka dawo?,daga wuni daya sai kwana har biyu?"
"Tun jiya na dawo,wasu sabgogi ne suka riqeni,duk yadda naso in shigo baiyiwu ba" bata ce komai ba ta bude qofar falon ta shiga yabi bayanta.
Bayan sun gama gaisawa suka shiga hirar mutanen garin daya baro ya gaya mata kowa lafiya sannan yace
"Kin tambayeni lafiya na tashi zuwa katsina ba yadda na saba ba" ya fada yana duban anty usainan dake yankan farcenta
"Eh ai dole,koma waye daya sanka yadda kaqi jinin zuwa katsina dole yayi mamakin tafiyar taka"
"Neman aure naje,na nema kuma sun bani" saita dakata da abinda take tana kallonshi sosai,saidai bata ga alamun wasa tattare dashi ba,hakan ya sanya ta gyara zamanta
"Auren wa kuma anwar"
"Shahida" ya fada kai tsaye kuma a taqaice,wani abu taji ya tsarga mata gaba daya ilahirin jikinta,saita aje rezar gefanta ta zauna sosai tana kallon anwar,tana jin wani farinciki na ratsata,da gaske ko mafarki take,shahidan da take tayi masa farautarta?,sun shirya kansu ne koko yaya abun ya faru?abinda ya shiga tsakaninsun dama baiyi girman da zasu kasa daidaita tsakaninsu ba amma har ya zama silar rabuwarsu na tsahon shekaru?,ya zama silar lalacewar soyayyar da kowa yake sha'awa,duka cikin lokaci kadan ya karanci tarin tambayoyin dake yawo a idanunta,qaramin murmushi yayi yana jin wani ciwo cikin ranshi,inama ace yadda kowa ya kalli lamarin hakan yake
"Karki damu anty,na rage miki aikin da kiketa yunqurin yine" ya qarasa fada yana son ganin yanayin fuskarta,ajiyar zuciya ta sauke ta zauna sosai zaman dake nuna ta soma samun nutsuwa
"Zuciyata ta kasa karbar rabuwarka da ita ne anwar,inaji a jikina bai cancanci ku rabu ba"
"Shikenan ai....yanzu dai anty abinda nakeso kici gaba da zama a yadda ta sanki har zuwa lokacin da komai zai daidaita" sai yanayin fuskarta ya sauya
"Komai zai daidaita kamar yaya?,kana nufin baku daidaita ba ka nemi aurenta a haka?" Kai ya gyada mata
"Eh kusan hakanne"
"Me hakan ke nufi anwar?"
"Babu komai,kema hakan kikeso mu kasance tare fa?"
Eh...amma zanso ace hakan ta faru ne a lokacin da duk wani sabani dakw tsakaninku ya zama babu shi"
"Karki damu anty" shuru tayi tana nazari,yayin da zuciyarta taji ta mata sanyi sosao,ta dinga jin farinciki na shigarta,tana ji babu shakka abune mawuyaci anwar ya samu soyayya irinta shahidan,abune mai wahalar gaske yaso wata kwatankwacin nata son koda shi yana qaryata hakan tasan wani dalili ne nashi na daban daya rufe masa idanu har yake qaryata hakan
"Nafisa fa?" Ta sako mishi zancan da take ganin kamar ya manta ne
"Ba abinda ya sauya tsakanina da ita"
"Tasan da wannan maganar?"
"Zata sani anty,zata sani idan lokacin daya dace ta sani yayi"
"Shikenan,Allah ya shige gaba ya kauda dukkan abunqi"mai makon ya amsa saiya soko wani zancan
"cikin satin nan ne tafiyata,ina ganin ki lissafa duk abinda kuke da buqata don bazan dawo ba saina gama wata biyun gaba daya,aiki ne mai muhimmanci a gabana"
"Babu wata matsala,don bana tunanin zamu buqaci komai harka dawo din"
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Ranar juma'a qarfe biyu na rana suma gama shirin tafiya katsina,ga mamakinta sai uncle hisham ya hadasu ita da haidar da faruqu,ganin haka huda itama ta turje saita je,hakan yasa ta hada kayanta duka suka bar gidan sai anty zubaida kawai.
Tafiyar tayi mata dadi sosai saboda su faruq,har Allah Allah ta dinga yi su isa,basu jima sosai saman hanya ba suka isa katsina.
Sosai daada tayi farincikin ganinsu su duka,ta rasa inda zata sanyasu,kowannensu haba haba takeyi dashi,saida suka ci suka sha suka nutsu qarfe uku na yammaci,a lokacin su faruqu sun fita kewaya 'yan uwa dake nesa,shahida tace ta gaji ba zata iya fita ba sai gobe,jin haka yasanya huda itama cewa bazata bisu,nan tayi kwanciyarta saman cinyar daada suna hira abinsu.
Duban shahida daadan tayi bayan ta maida nutsuwarta sosai
"Rahama" ta kirayi ainihin sunanta,saita daga kai daga danna wayar da take ta dubi daada
"Yau kuma sunan nawa kike sha'awar kira" maimakon ta maida mata yadda suka saba sai tace
"Maida hankalinki jikinki ki aje wannan wayar" jin hakan yasa ta sauke wayar saman cinyarta tana kallon daadan
"Abinda yasa nace a turomin ke,inason gaya miki cewa mun bada ke kuma mun karbi kudin aurenki"
*KIYI SUBSCRIBING,KI TURA WANNAN NUMBER DON SAMUN DAMAR SHIGA GROUP DIN SABON LITTAFINA DA ZAN SOMA RUBUTAWA BAYAN ALQAWARIN ALLAH IN SHA ALLAH*
07038670166
SAUTIN HIKIMA
https://youtu.be/H7M7h6l6wNM*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata zata tuntubi wadan nan numbers din*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*Alqawarin Allah*
2️⃣7️⃣
Murmushi shahida tayi tana kada kai
"Haba tsohuwa,wai gajiyar da kukayi dani yasa har kin soma min irin wannan wasan?,toki kwantar da hankalinki idan ma bugun cikina kike,ana gama azumi aka sallace zan kawomiki dandasheshen angona"
"Ni banga miji ba kamar anwar" daada ta fada cikin ranta,amma a sarari saita sake hade fuskarta sosai,ta yadda shahidan zata fuskanci bada wasa take mata ba
"Ki dakatar dashi,don hatta sadakinki yana hannu,kuma watanni uku ya rage daurin aurenki" cak ta tsaya ta nutsu sosai tana son karantar maganar daadan,ta fidda gaskiyar dake cikin maganar
"Sadakina fa daada kike cewa kun karba?"
"Idan baki yarda ba tunda ni sa'ar wasanki ce,saiki jirayi wadanda kike yadda da nasu zancan anjima suzo su shaida miki" tana kaiwa nan ta yunqura ta miqe ta nufi qofar fita,hakan yasa shahida ta miqe zumbur cikin tashin hankali harta manta da wayarta dake seaman cinya ta cimma dadan ta ruqo hannunta,muryarta na rawa tace
"Daada....wa kuka baiwa ni?,nidai nasan ba wanda na bawa dama,da nura mukayi magana shi kuma sai bayan sallah mukayi dashi zaizo" juyowa tayi ta kalleta
"Mai rabo muka bawa,zama zamuyi mu zuba miki ido sai sanda kika ga damar aure sannan kiyi?,to sakalcina baikai nan ba...idan zaki nutsu ki fahimceni ki nutsu idan ba zaki nutsu ba kuma kici gaba da shiriritar saina qyaleki cikin duhu" dakiya da dukkan juriya ta gayyato,ta soma kokawar maida qwalla da abinda ya tare mata maqoshi tana cewa
"Na nutsu,ki gayamin don Allah" komawa tayi ta zauna inda ta tashi,itama shahidan ta koma ta zauna idanunta qyarr kan daadan,kamar ta fiddo zuciyar daadan ta karanta komai haka takeji
"Yazo yana neman aurenki,dan mutunci ne yaro da mai mutunci kirki da karamci,bashi da wani aibu ko abun qi,hakan ha sanya ya turo magabatansa,kawunki ummaru ya sanshi kawun nashi gaba da baya,hakanan muma din akwai wata 'yar alaqa tsakaninmu duk da bamai qarfi bace,babu wata matsala hakan yasa aka amshi harda sadakinsa,karki damu karki daga hankalinki zaki sanshi zaizo ya sameki kuga juna,ke kanki kinsan shekarunki a yanzu sun isa ace kina gidanki harda albarkar zuri'a ma,idan baki aure ba shahida yanzu sai yaushe?" Kuka ta fashe sosai dashi,don tana ganin itace hanya guda daya da zata iya samun mafita da ita
"Don shekaruna sun soma tafiya wanda har yau basu rufa ashirin da biyar ba kawai daada saiku amshi kudin aure harda sadakin wanda ban sanshi ba?,bansan daga inda yake ba?,bani na turoshi ba?,ba soyayya ko sabo tsakaninmu?,wallahi wannan zubarmin da mutunci kawai da ajina kukayi" ta qarashe cikin kuka wanda yasa huda ta tsaya sak tana kallon shahidan,daquwa daada ta watsa mata
"Kinci qaniyarki,makaranta muka zubar miki ba aji ba,wanne aji kike nema bayan na gidan aure?,ba gata muka yi miki ba?" Haushi ya ciyota,saita sake saka kuka
"Wanne irin gata daada haka ake gata tsakani da Allah?,kaman na rasa mashinshini?,kawai sai mutum yazo muku sama taka ku karbeshi?"
"To yanzu aisai ki hadamu ki zanemu uwarmu,mun miki laifi ko?" Ta fadi tana fiddo idanu tana kallon shahida,wani tashin hankali takeji da bacin rai qwarai,idan taci gaba da magana batasan me zai fito daga bakinta ba,daboda haka ta gwammace ta barwa daada falon kawai,haka ta miqe ko gabanta bata gani ta shige dakin.
Wani irin tashin hankali ta tsinci kanta ciki,saitakejin kaman da wasa daadan ke mata zata dawo tace tsokanarta take,saidai har akayi magariba su faruqu suka dawo shuru daadan bata bi ta kanta ba,sanda suka dawo suma suka leqo dakin da take,dukkansu tambayarta suke me ya sameta da suka sameta a kwance,saidai ba wanda ta baiwa amsa,tana jiyo muryar daada daga falo tana cewa su fito suzo ita ta basu amsa,haka suka juya suka fita,faga haka basu sake dawowa dakin ba suma.
Har qarfe goma na dare tana kwance ita daya cikin dakin cikin wani yanayi,nuradden ya jirata yafi a qirga ta kasa dagawa saboda tashin hankalin da take ji cikin zuciyarta,saida goma ta gota daadan ta shigo dakin da kanta ta taddata,ta aje kwanon abincin hannunta sannan ta samu gefan gadon da shahidan ke kai ta zauna
"Tashi ki dauki abincinki kici" shuru tayi mata kaman bata ji me take cewa ba,ta sani sarai taji din,tsohon halinta keson motsawa saboda an mata zancan an bada ita
"Saboda an hadaki da miji nagari za'a miki aure shine kika yiwa abinci yajin aiki?,kusan ni natsaya tsayin daka kan maganarnan saboda ganin nagartar da yaron yake dashi,sannan kuma ina da yaqinin cewa bamuyi miki zaben tumun dare ba,uwa uba nasan ko ba dade koba jima sai kinyi dariya kin godemin da irin mijin dana zaba miki" tana ganin daadan tazo gabar da zatayi magana saboda haka ta miqe ta zauna sosai tana gyara rigarta data sabule
"Duk naji dada na fahimceki,amma daada ina ake irin wannan auren?,ban sanshi ba bansan waye ba,bance ina sonshi ba bani na aikoshi ba kawai sai a daukeni a bashi ni?,ta yaya