Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   25 / 53

72K to 75K   out of 156.9K words

kici gashin kanki ba,baki cancanci na barki kiyi zabin da kikaga dama ba,bayan kin cutar da zuciyar da bata cancanci sakamakon da kika bata ba,kin bata rayuwar da alokacin ya kamata ki tattaleta kodon iyaye da qannenki,kin bada jikinki ga wani har yayi ajiya a wajen daba muhallin......" Saiya kasa qarasawa saboda wani dunqulallen abu daya tokare masa maqoshi,ya dinga jin wani turari tun daga zuciyarsa zuwa fuskarsa,bakinsa yaji ya dauki zafi ya fitar da iska zazzafa,yana jin wani irin ciwo da qunci duk lokacin daya tuna da lokacin da kuma abinda ya faru,hotunan dake wajensa da ganin da yayi kaya ido da ido sun kasa gogewa daga qwaqwalwa da zuciyarsa,yana jin wani irin ciwo mara misaltuwa,tabbas da yana da iko daya dawo da lokacin ya goge duk wani abu daya faru ko xai samawa zuciyarsa salama.

Tuni hawaye ya soma wanke mata fuska tana tuna lokacin da abinda ya faru alokacin daya bayan daya,sai a sannan ta dinga tuna kaman ta ganshi,kaman a gabanshi aka sauketa,hakan na nufin ya ganta cikin maye?,ya ganta a lokacin da jini kebin qafafunta?,yaga sanda aka cillo mata pant dinta da kwalabenta?,amma me yasa ya zama mai qaramin tsinkaye?,mai yasa ya zama mai gajeran nazari?,me yasa ya yanke mata wannan danyen hukunci farat daya,haka soyayya take?,haka masoyi yakewa masoyinsa?,sai taji ya sake sireta,daya zama mai dogon nazari da dukka abubuwan da suka faru yanzu basu faru ba
Ranta ya ninka bacin da yayi,hankalinta taji ya tashi,da qyar ta bude baki cikin muryar kuka tace
"Mugu azzalumi,ba ruwanka da kowa sai kanka,ba ruwanka da damuwar wani sai taka,ka tanadi mugun nufi akaina kan abinda baka da cikakkiyar hujja a kai...."
"Wacce huja nake nema baya ga wanda na samu....!" Ya juyo a fusace ya fada idanunshi da suka kada zuwa jaa suna kanta
"Ba hujjar kake nema ba,kanayin komaine don ka wulaqantani dama,ka shirya komai ne donka tozartani,to Allah ya fika,ba zaka taba samun nasara a kaina ba,nuradden kuma idan Allah yaga dama kai baka isa ka rabani dashi ba"itama ta fada cikin tunzura fushi da bacin rai
"kome zaki fada dai dai ne,duk yadda kika fassara lamarin a ranki ko a bakinki kisa a ranki haka ne,any ways ma ni nasan na taimaki rayuwarki ne,ko kina tunanin wancan wawan idan yaji wace ke a baya zaici gaba da haukan da yake a kanki?,kinga 'yammata....koki sawa ranki sauqi ko kar kisa duk uwar ubansu daya" kai take gyadawa bacin rai na cinta,idanunta fes cikin nashi,ji take kaman ta shaqe anwar din,a yanzu babu halittar data ji ta tsana sama dashi
"Zan saka salamar duk da bakayimin fatanta ko burin samunta,amma ka sani....tsugune bata qare ba,don babu abinda zanyi da masoyi irinka nawar!,ka shirya tarbar duk wani abu da zai tunkaroka!" Tayi lafazin da alama wani abu ya motsa ranta qwarai,duk da murta na a raunane amma amma fuskarta da qwayar idanunta na bayyana jarumtarta,wani malalacin murmushi ya saki ya sake matsowa inda take,wannan karon har qamshin turarensan nan data sanshi dashi yana busowa zuwa hancinta,ya kafeta da idanunsa,muryarsa can qasa kamar mai shirin furta kalaman soyayya a gareta yace
"A shirye nake,kece zan gayawa ki shirya zama dani idanma ba'a shirye kike ba,yaushe kikeso wasan ya fara?" Ya fadi cikin halin ko in kula,ganin kallon da yake mata bacin rai ya sanya ta fashewa da kuka sosai ta zube saman kujerar tana rufe fuskarta da tafin hannunta,saiya tabe baki yana isa inda hularsa take yasa hannu ya dauka yana cewa
"Ashe raguwa ce ta gaske,tun yanzu?,wasan namu kuwa zaiyi iri qarkon da nakeso?" Ya dora hularshi saman kansa sanda ya qarashe maganar,saiya sanya hannunsa cikin aljihunsa ya ciro kudade sabbabi masu dan yawa ya aje hannun kujerar da take kai yana cewa
"Ga kudin zance nan,kuma bance a sayi abunda za'a bugu da kudina na,idan aka siya Allah ya isa na" sosai maganar ta doketa,tana niyyar daga kai ta dubeshi ta fuskanci ya juya zai fita ne,har yakai bakin qofa sai yasake cewa
"Ammmm..." Yana dawowa da baya,kanta yazo ya tsaya hannunsa daya a aljihun wandonsa dayan kuma yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa
"Karki manta da sadakina akanki,shaidu kawai za'a tara a daura,ban lamince ki kula kowanne dan iska ba,ciki harda wannan looser din,idan kuma kikayi hakan shima Allah ya isa ban yafe ba" saiya sassauta murya ya sauko da kansa qasa qasa gab da ita
"Ina fata har yanzu wasu daga halayen anwar basu bace miki ba daga kanki,mutum ne mai kishi,ina da kishi kan mace koba wadda ban biya sadakinta ba bare wadda na cire halalina sa nasha wahalar nema zafi da sanyi nabiya" a fusace ta bude fuskarta saboda yadda maganganunshi suka isheta,saita ganshi dab da fuskarta,cikin bacin rai da muryar kuka take cewa
"Sadakinka din banza da wofi,idan kana son nunan kudinka wata tsiya ce kaje ka karbi sadakinka idan har ka isa cikakken namiji" tsaf ya karanci bacin ran dake kwance muraran saman fuskarta,saidai yadda yake jin quna yana tunanin bata jin haka,duk sanda zai kalli fuskarta yana tuna sanda aka sauketa ne a gabanshi,cikin maye,cikin jini,pant dinta a gabanshi aka cilloshi,wani ya riqe zuwa jikinsa gaban idanunsa,saiya runtse idanunsa kana ya bata baya ya soma takawa
"Idan kin isa ke kije ki karbo kin kiga idan ban amsa ba,dama taimako nayi kuma na fuskanci ke bakiga hakan ba" daga haka ya qarasa ficewa daga dakin,sake rushewa da kuka tayi,ta tsani kalmar taimakon nan,wannan wanne irin cutace?,ita zai taimaka.

Cikin gida ya qarasa,daada na rumfarta a zaune ita da hasina,saiya cire takalmansa ya zauna saman tabarmar dake shimfide qasan inuwar bishiyar dake tsakar gidan,daadan tayi tayi dashi ya shigo amma yace wucewa zaiyi,dole ta fito ta zauna daga gefan tabarmar itama
"Zan wuce daada,ina tunanin rana ita yau za'a kawo lefe,to bansan inda za'a kai ba,can wajen umma,ko nan garin ko kuma gidan uncle hisham?"
"Babu damuwa akai can hidan hashimun tunda acan za'a yi duka bikin,muma can zamu tattara ai mu tafi"
"To daada,Allah ya saka da alkhairi ya qara girma" ya furta yana dan sadda kanshi qasa alamun girmamawa
"Ina kuma ta shiga?" Daada ta tambaya,ya fuskanci shahida take magana,saiya saki murmushin daya qwata fuskarshi duk da baikai masa qasan ranshi ba
"Tana daki tana kukan bata sona can na barota" kama baki daada tayi tana salati harta baiwa anwar dariya,harya miqe ya aje mata kudi ma sam bata kula ba tana ta jajjabi tare da sillewa shahidan hasina na dariya,sai daya sanya takalmansa sannan ya kalli hasina
"Taimaka kije ki fito da ita daga dakin karta rube" dariya hasina ta saki sosai,abun saiya qayatar da ita,ya yiwa daada sallama suka fice zuwa soron gidan shida hasina.

Bakin qofar dakin ya coge ya yaye labulen bayan hasina ta shiga dakin,ta isa inda take dunqule tana gursheqen kuka
"Saikace yau akace za'a kaiki?,taso da Allah karki tara mana jama'a" hannun hasina ta buge tana jin takaici yana cikata,duk maganganunsu da daada tana jinsa,tamkar ma ya raina mata wayo ne,ko yana tunanin 'yar qaramar shahida daya sani a baya ce wannan?
"Matsa hasina barta,bari na rage miki aikin na dauketa zuwa qofar soro saiki qarasa shiga da ita ciki,da sauri ta bude fuskarta,idanunta da sukayi jawur zuwa fuskarta ta kalleshi dasu
"wallahi wallahi ka sake ka tabani sai kayi dana sani!" Ta fada a kausashe
"Meye hakane shahida?" Hasina ta tambayeta tana dubanta cikin mamakin kausasa lafazin da tayi,dubanta yake sosai,yana son yace shine farau?,amma idanun hasina yasa ya maida amsarsa
"Wallahi wallahi kinji nima na rantse matsawar baki tashi kin shige ba ko abinda yafi danasani zanyi saina dangana dake har rumfar daada" saiya maida dubansa ga hasina dake tsaye tana kallon dramer
"Ina cikin mota a qofar gida,minti biyar na bata idan ta dara hakan bata tashi ba ki fito ki gayamin" kai ta gyada ya saki labulen ya taka a sannu ya fice daga soron.

Bata buqatar duk wani abu da zai kawo wani kusanci tsakaninta dashi,so take ya tafi yabar gidan saboda haka ta miqe tana hada hanya,hasina ta dauki kudin dake aje inda ta tashi ta bita dasu a baya,ko kallon dada dake tsakar gida tana mita batayi ba ta shige rumfar daadan ta zube saman kujera,saita dora hannu aka ta fashe da ihun kuka ko zataji salamar radadin da take ji cikin ranta,hasina kallonta take idanu a waje cikin rudewa tace
"Meyw haka ne shahida kike kamar wata 'yar shekara goma,ya zaki tara mana jama'a?" Takai qarshan maganar sanda daada ta runtumo cikin dakin tana tambayar ba'asi
"Au ihu kike?"
"Wallahi daada bana sonshi,shima daada ba sona yake ba bazai gaya muku gaskiya bane kawai" baki ta tabe tana mata duban sakarya
"Au Allah ko?,ashe tun farkon saninmu dashi mu muka jajibo miki shi ko?,ashe qiyayya ce ta hadaku a baya ba soyayya ba?"
"Daada baya sona yanzu bana sonshi!" Ta sake fada cikin kuka
"Eh naga alama,shi yasa bai bar kakarki ba yaci gaba dayi mata aike a boye bai bari nasan wayeshi ba,kuma qiyayyar ce tasa ya tasl qafa da qafa ya nemi aurenki hannun iyayenki"
"Wallahi daada kinji na ra ntse miki da manufa a lamarinsa"
"Dama akwai auren da babu manufa?,shirme kenan" ganin duka taqi fahimtarta saita sauko gwiwoyinta qasa tana kallonta
"Daada,don girman Allah ku maida masa kudinsa,ko bazaku bani nuradden ba na amince ko zabamin ko waye a lokacin da kuka saka na bikin nawa ayi dashi" nazarinta daadan tayi na wani dan lokaci sannan ta kamata ta miqar da ita tsaye
"Naji,zauna muyi magana" sanyi taji yana ratsa zuciyarta,ta soma jin qamshin nasara,saita miqe din kamar yadda daada ta buqata suka koma saman kujera suka zauna.

Saidata bata 'yan mintuna ta nutsu tukunna sannan tace
"Komai da kika gani a rayuwa yana da dalili,inason ki gayamin dalilinki na duka wadan nan maganganun da tsallen badaken qin auren mutumin da kowa ya shaida kuma yana da labarin soyayyarku" shuru tayi kawai tana qiyasta ta yadda zata gayawa daadan komai bayan basusan komai ba akan rayuwar data fada a baya,sannan uwa uba shi kansa anwar din ta fahimci ba wanda ya taba gayawa ko bashi labarin komai,idan ta aikata hakan kamar ta dabawa cikinta wuqa,kamar ta yaye mayafin asirin da Allah ya rufa mata kenan?,ganin tayi shuru sai daada tayi tsammanin ko batason magana ne a gaban hasina,saboda haka ta korata waje
"Ki gayamin dalilinki,indai matuqar na gamsu,toba shakka a yau basai gobe ba zamu maida masa komai nashi" tofa ga qoshi ga kwanan yunwa,ta ina zata fara ya zatayi?,batason tona komai,batason kowa yaji komai,tana ganin kamar ba muhallin kowa bane ba hurumin kowa bane
Kai ta kada
"Daada baya sona ne,nima yanzu na daina sonshi,kinga babu amfanin aurenmu" murmushi ta saki tana kada kai
"Banda abinki shahida ta yaya masoya haka siddan zasu daina son junansu?,ai ruwa baya tsami banza" cikin nuna dagiya da qarfin hali tace
"Hakanan nidai daada muka daina son junanmu,don Allah karku qulla auren qiyayya" hawaye ta siraro daga idanunta muryarta ta soma rawa,saita sake murmushi tana kallonta
"Shahida,anyi auren hadin da baki taba ganinsa ba bai taba ganinki ba sai hadi kuma an zauna lafiya harma yafi na soyayyar qarko,kin ganni nan gani da ran Allah?,to sanda na auri kakanku sai randa ya shiga dakina nasan shi na aura,saboda haka indai rashin soyayya ne hujjar fasa aurenki da anwar indai kikaga an fasa to la shakka mutuwa nayi bana raye,ko bana raye zanbar wasiyyar a tabbatar an daura,don anwar din ya cika dukkan siffa da kamalar da annabi yace a baiwa mutum aure" daga haka sai daadan ta miqe ta qyaleta,tashin hankalin data ji a sannan yasa taji zuciyarta ta bushe gaba daya,hawayen idanunta sun bushe tas,saita miqe itama ta shige daki tayi rub da ciki tana sakin ajiyar zuciya ko zataji sanyin tuquqin da ranta yake.

Ta shafe a qalla minti talatin a haka kafin daga bisani ta janyo wayarta,ta lalubo number nuradden ta kira,bugu daya tak ya daga,ajiyar zuciya ya soma saukewa da alamu hankalinsa shima ba'a kwance yake ba,duk sai taji bacin rai ya sake shigarta,shi ya janyo komai,shine silar komai
"Ka dawo ka sake neman aurena karo na biyu nuradden,bazan iya aurensa ba" ta fada kai tsaye ba tare da tayi sallama ba ko tace komai,kafin taji yace wani abu taji an karbe wayar,da sauri ta daga kai don ganin waye,daada ce,bata ce komai ba ta kara wayar a kunnenta
"Nura kana jina?" Ta fadi sanda take ficewa daga dakin,saita miqe ta zauna sosai saman katifar tana bin qofar da kallo.


*muna muku fatan alkhairi tare da fatan zaku gudanar da bukukuwan sallarku lafiya cikin amincin ubangiji,Allah ya karba mana ibadunmu,ya gafarta mana zunubanmu,yaji qanmu ya jiqan mamatanmu,yasa mu cikin 'yantattun bayinsa amin umma amin,ZAFAFA BIYAR na muku fatan alkhairi*

*_karku manta,ku kasance da tashar SAUTIN HIKIMA TV don sauraren littattafan da zasu debe muku kewa yayin ayyukan sallah a gida*

*kundin qaddarata*
*daurin boye*
*mutuncin mace*

Duka wadanda na rubuta
*fatan alkhairi a gareku*
#zafafa biyar
#sautin hikima tv
#team anwar
#team shahida
#team nafisa 🏃🏾‍♀️

_ma'assalam_🤝🏽🤝🏽🤝🏽_ziyarci tasharmu ta youtube don sauraren tsaffin litattafanmu dama sababbi da zamu fara dorawa nan gaba kadan in sha Allah_

https://youtu.be/H7M7h6l6wNM


*Alqawarin Allah*
3️⃣1️⃣


Minti goma kyawawa daadan ta dawo,ta miqa mata wayartata tana dubanta,sannan ta miqa mata kudin da anwar ya bata tana cewa
"Tunda kin zabi zubar mana da qima rahama mu zuba nida ke" daga haka ta juya ta fice,a sannan ji shahidan take kamar ta dora hannu aka tayita zunduma ihu ko xata ji sanyi cikin zuciyarta,me yasa ba zasu fahimceta su bata uzuri ba?,me yasa ba zasu haqura ba?,wai da anwar da itama wa sukafiso ne?,waye nasu a ciki?,kira ne ya sake shigowa wayarta,ta daga ta duba da sauri sai taga nuradden ne,muryarsa kadai ta gaya mata cewa ya karaya bashi da wani sauran fata
"Shahida,na rasaki shahida,ta ina zan iya jurewa rashinki?,zan iya tsira daga hukunci da horon rasaki da zuciyata zata yimin?,ki tayani addu'a bansan ya zata kayamin ba" daga haka ya yanke kiran,me daada ta gayawa nuradden?,shikenan ta rabata dashi?,dole ta zauna da mutumin da sam bata ra'ayinsa ne wai?,irin wannan masoyin zata rabata dashi?,kalamansa kawai sun tabbatar da tsantsar qauna da soyayyar da yake mata,saita kifa kawai rubda ciki tana lalube da binciken meye abunyi a qwaqwalwarta,mecece mafita?duk wata dabararta ta qare,wayonta duka ya qure,daada ta yanke komai.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe bakwai da rabi ne na daren ranar,yana zaune a harabar gidan saman daya daga cikin fararen kujerun roba dake wajen,shi ya zabi zama a wajen saboda yadda iskar damina mai sanyi ke busawa gabas da yamma,hakanan qwayayen lantarkin dake harabar gidan sun haske ko ina harda korayen tsirran dake harabar wajen,sai yake jin zuciyarsa wasai,hakanan babu nauyi qunci ko wani abu da yakejin ya dameshi a yanzu,shaqar iskar yake sosai yana fesarwa har cikin huhunshi qamshin iskar da sanyinta na sake sa zuciyarsa cikin wani shauqi da walwala,fuskarsa fes take a washe.

A hankali take takowa cikin gayunta,tayi kyau don ba qaramar kwalliya ta dauka ba,don yau din na daya daga cikin ranakunta na musamman,saboda bako da yaushe take samun dama irin wannan ba,ace yau anwar din yazo zance takanas saboda ita,zata iya irga sau nawa hakan ya taba faruwa a tarayyarsu,shi yasa duk ransa zaizo din ba qaramin tanadi takewa ranar ba.

Gabansa ta tsaya sannan tayi sallama tana kallon yadda yayi masifar kyau cikin qananun kaya sai kace wanda ya dawo daga europe,ya daga kai yana dubanta sannan ya amsa,cikin shagwaba shigarsa da yadda yayi kyau yana dada burgeta tace
"Ya bakaci komai ba dear?" Ta qarashe fada tana jan kujerar dake kallonsa ta zauna,duban tulin kayan ciye ciyen dake gabanshi yayi sannan ya kalleta,shi sam a ra'ayinsa ba mutum bane mai yawan son ciye ciye,kusan ma babu cimarshi ciki sai kadan,kafada ya daga
"Karki damu,duka basu da muhimmanci,zuwankin da ganinki ya fisu muhimmanci" wani farinciki data jima bataji kamarsa ba ya tsirga mata,ta lumshe ido tana sakin murmushi,ta jima bata ji kalmar data mata dadi matuqa daga anwar din ba irin wannan,sannan ta budesu idanun nata a kanshi
"Ya gida yasu momy"
"Kowa lafiya suna ma gaidaka" ta fada tana zuba masa lemo sannan ta tura masa,bai musa ba yaja yadan kurba tana binsa da kallo,batasan wane irin qauna takewa anwar din ba,jifa jifa take sako hura yana tayata kana ta sako masa zancan bikinsu,lissafin events da zatayi da sauran abubuwa,yana kurba yana saurarenta sai daya shanye sannan yace mata
"Next week za'a kawo lefen idan Allah ya kaimu....saidai kuma kafin sannan inason nayi wata muhimmiyar magana dake,duk da na riga na shaidawa su momy amma naga kece yafi cancanta ki sani,kuma ni yafi dacewa na sanar miki da kaina" dukka hankalinta ta bashi ganin yadda ya tara shima nutsuwarshi waje guda gamida soke yatsunsa cikin na juna yana dubanta sosai
"Uhmm,ina jinka"
"Komai da kika gani a duniya muqaddarine daga Allah,hakanan ba wanda ya isa sauya tsarin Allah,yadda ya tsarawa bawa haka zai karba,naka kawai ka gode masa,zaka iya tsarawa rayuwarka abu amma idan baiyi dai dai da tsarin Allah ba zai sauya maka ne da wanda yake ganin shine daidai da rayuwarka kuma shine mafi alkhairi,to...ina tunanin ku biyu za'a daura mana aure dasu lokaci guda,na nemi aure watanni biyu baya da suka wuce Allah ya qaddara kuma an bani,yanzu haka cikin satin da za'a kawo naki kefen suma za'a kai,lokacin daurin aurenma kusan daya ne,rana ce kawai aka bambanta,kinga ya kamata ace kin sani saboda kina da haqqin ki sani din,nasan mai yiwuwa hakan zai bata miki rai saboda halin kishi irin na mata,saboda haka ina mai baki haquri tare da shaida miki haka Allah ya qaddara dama tun fil'azal shi yasa ya hukunta faruwar hakan,ina fata hakan bazai dameki ba don kowacce cikinku matsayinta daban" wani irin abu taji yana mata yawo tsakiyar kaa kamar ana yamutsa qwaqwalwarta,wannan wacce iriyar mummunar rana ce?,wanne irin mummunan labari kunnuwanta suke dauko mata?,saita cije lebanta da kyau ga zatonta mafarki take ko zata farka,saita fuskanci da gaske ne,wani abu ke niyyar toshe mata numfashi,ta fahimci idan bata bari tayi kuka ba wani mummunan abu na iya faruwa da ita,saboda haka kawai ta saki hawayen da take qoqarin tarewa suka soma zuba
"Wanne irin abu kake gayamin haka anwar?,kana gayaminne fa kishiya zaka yimin tun ban shiga gidanka ba,anwar kana

25 / 53