Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 53

51K to 54K   out of 156.9K words

a waje da daren nan?,naje gida baki nan,na kirashi yace wajen umma yabarki,kuma kince basai ya dawo ba"
"Eh uzuri nayi masa ne" ajiyar zuciya ya aje
"Ni gaki kin fiddoni,kema kinsan ba yadda za'ayi na iya kwanciya kina waje,fito gani a qofar gida"
"Na fito daga gidan ai"
"Ina kika je?"
"Ina maqota" sai tayi mishi kwatancen gidan yace gashinan,babu jimawa ta fito dauke da wani dan qaramin faranti da aka dora ruwa da lemo,gefe daya dambun nama da meatpie ta aje gabanta
"Ga ruwa kisha" murmushin yaqe ta danyi don har yanzu a darare take,hakanan taji ta kasa sakewa
"Na qoshi wlh anty"
"Da alama dai da gasken shahida baki da kirki" dariya maganar ta bata,saita kuma sakin murmushi sosai
"Ba haka bane anty,kina gani kusan ma tare mukaci abincin"
"Eh...amma ko albarka kyasa" bata sake cewa komai ba ta gutsuri meatpie din kadan,dai dai sanda ta qwalawa yarinyar kira
"Sa'ida me kike ne?,kiyi sauri sauri fa take gida zata wuce"
"Gani nan ummi" tana maganar ne sanda take sakkowa daga saman cikin sassarfa rungume da kayan a qirjinta,a gaban ummin ta zubesu
"Riga daya ce ban gani ba ashe ta shiga cikin wasu kayan
"ok...gasu ki xaba wadanda zasu miki" a nutse take daga dinkunan,duka sun mata hakanan sunyi bala'in kyau,tana son yace xata dauka duka tanajin nauyinta,saita zabi uku daga ciki
"Wadan nan ma sunyi,na gode" tura mata sauran tayi
"Jeki dasu gaba daya,mai yiwuwa telan yaga wanda zaifi miki kyau akan wanda ke kika zaba" haka ta tattara duka kayan ta zuba mata a wata 'yar jaka mai kyau,ta mata sallama ta fito.

Yana tsaye jikin motarsa wayarsa na hannunshi yana danne danne,ganin fitowarta ya sanyashi maida wayar aljihu,ya tarbeta cikin fara'a ya amshi ledar hannun nata sannan ya bude mata gaban mota,dubanshi tayi sosai
"Kaima kariga da kasan qa'idata ko,mu taka zuwa titi ka tsaremin napep" kai ya langwabar mata yana dubanta
"Kar muyi haka dake don Allah,yau dai daya kiyimin wannan alfarmar na kaiki,tunda muke dake shahida ko kara babu baki taba shiga motata kosau daya ba,koda batan hanya" maganar tashi ta bata dariya amma ta maze,ita bata da ra'ayin hakan kwata kwata,ganin yadda yaketa roqarta gashi dare nayi yasa tayi bismillah gami da addu'a ta shiga ya zagaya ya rufe ya tada motar.

Farinciki yau fal zuciyar nuran,haka ya dinga sako mata hira,suna tsaka da tafiya taga ya dauke hanya,idanu a waje zuciyarta na gudu ta kalleshi
"Ina zaka dani malam" dariya yayi
"Karki damu shahida,duk sanda kike tare dani cikin aminci kike,wani waje kawai zamu shiga,ki rakani zanwa mama siyayya"shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya,duk da haka hankalinta bai kwanta ba har sai data ga sunyi parking qofar wajen ta bude murfin motar suka shiga.

A tsaye yake wajen biyan kudi da yake dab da qofar shiga da fita,yana saka pin dinshi jikin p.o.s machine da ma'aikin wajen ya turo gabanshi,yana gama sawa ya tura musu donsu ciri kudinsu wanda hakan yayi dai dai da ganin gilmawar wata da zuciyarsa hakanan ta afu da sanin wacece,suna miqa masa resit ya karba ya soma takawa don ficewa daga wajen,saiya tuna ya yiwa sa'ida alqawarin turare,tace tana son irin turarenshi randa yaje gidan,yace mata ba lallai a sameshi qasar nan ba,amma zai siya mata copy dinshi,yana da wuya yayi alqawari ya saba banda haka da bazai sake komawa ba,a gajiye ya sake juyawa zuwa ciki ya soma laluben sashen turaruka.

Tunda ya shiga side din daga nesa yake hangowa kamar shahidan,tana tafe yana biye da ita a bayanta kaman wani bodyguard,taku kadan zai qara ya hade tazarar dake tsakaninsu,tana zaban abu tana zubawa a cart din da nuradden ke turawa,ya bata dama ne ta zabarwa maman komai,da fari taso zuqewa yace indai tayi hakan bata dauki maman mamarta ba,dole tayi yadda yakeso.

Sanda ta waiwayo don dawowa daya side din fuskarta ta bayyana fes cikin idanunshi,tana murmushi ne gami da hararar nuradden daya tsokaneta da
"Iyee,ashe madam din tawa an iya siyayya,irin wannan siyayya me aji haka?,gaskiya idan mukayi aure ke xaki dinga min shopping" dauke kanshi yaso yayi tare da aiwatar da abinda ke gabanshi amma sai ya gaza hakan kamar wanda aka haneshi,haka kawai yaji idanunsa na masa yaji yaji,wani abu mai zafi ya sauka a qirjinsa,suna dab da cimmasa ya juya ya soma takawa don barin shagon gaba daya.

Kallon bayanshi kawai ya haifar mata da mummunar faduwar gaba,duk da batasan waye ba bata ga fuskarshi ba,haka kawai ta dinga kallon bayanshi har ya bacewa ganinta nuradden nacan yana zaben zobe,yanayin tafiyarshi da bayanshi kaman anwar
"And so what koda ya kasance anwar dinne?" Zuciyarta ta gaya mata wanda hakan ya sanyata tabe baki da daga kafada.

Tun kafin ya qarasa ya bude motar,yana zuwa ya shiga ya maida murfin ya rufe,saiya samu kansa da kasa tafiya,ya sauke glass din side dinsa gaba daya qasa abinda ba dabi'arsa bace,numfashi yake fitarwa dai dai idanunsa kan qofar fitowa daga wajen,shi kansa baisan zaman me yayi ba me yake jira oho duka bai sani ba,saiya duba agogon hannunshi,tara saura,tara saura fa na dare?,sake maida idanunsa yayi qofar shagon dai ya kafeshi da ido.

Minti goma ya sake duba agogo,tara na dare saura kadan,har yanzu dai shuru?,ya tambayi kansa
"Lafiyanka kuwa anwar?,wai shin ma me kake jira ne?" Ya tambayi kansa da kansa,tuna hakan da yayi yasa ya dage gilasan motar da gaggawa ya zura key zai tasheta,dai dai sanda ya sake duban qofar kanti,sai gasu sun fito fuskokinsu cike da murmushi,yana riqe da ledojin siyayyar,yayin da ita kuma take riqe da iya tata jakar.


*Ga mai buqatar littafin da zan fara bayan kammala alqawarin Allah,ya shiga youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA zaiga an rubuta (subscribe) dajan rubutu,ya danna sau daya zai koma black,yayi screenshoot ya turo zuwa wannan number zanyi adding dinsa a grpup din in sha Allahu 07038670166*

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos*Alqawarin Allah*
2️⃣2️⃣


Fasa kunna motar yayi ya tsaya cak yana dubansu ta cikin gilashin har suka isa bakin motar nuradden din,shi ya bude mata qofar motar ta shiga sannan ya sanya ledar daya a baya,saiya dora dayar saman cinyarta,runtse ido anwar yayi ganin haka yana jin wani abu ya dunqule masa a wuya.

Hannu nuradden ya saka cikin aljihun wandonshi ya ciro wani dan qaramin akwati,ya budeshi yana murmushi ya ciro qayataccen zobe a ciki ya miqawa shahida yana murmushin,kallonsa tayi sannan ta kalli zoben
"Da zaki miqo min hannunki na saka miki sai nafison haka,ki saka da hannunki shahida....amma shahida,don Allah zaki aureni?" Maganar ta shiga kunnenta a bazata,daga idanunta tayi ta kalleshi
"Me ya kawo wannan maganar nuradden?"
"Ban cancanci nayi wannan maganar bane shahida?,kina tunanin akwai wani namiji da zai kalleki yaji ba burinsa bane ya mallakeki?,ko tsahon zamanmu tare bai kamata ace na nemi mu zama miji da mata ba?" Bayyananniyar ajiyar zuciya ya saki,gaba daya ya rusa mata lissafi da plan dinta
"Hakane....amma kayi haquri zamuyi wannan maganar daga baya,kaga yanzu dare yayi naga kiran anty xubaida ma"
"Shikenan" ya fada yana maida zoben akwakunsa sannan ya miqa mata,ta saka hannu ta amsa ya zagaya seat dinsa ya shiga ya tayar da motar.

Kashi anwar ya jingina da kujerar da yake kai idanunsa kan motar tasu har suka fice daga wajen,hakanan yaji ya kasa zama shima ya tada motar tasa ya figeta yabi bayansu da hanzari,ba jimawa ya cimmasu,haka ya dinga bin bayan motar har zuwa cikin unguwarsu qofar gidan,gotasu yayi yayi parking din motarsa daga gaban tasu ya kasheta yana kallon abinda ke faruwa,motar ta bude ta fice ta tura gate din gidan ta shige sannan nura ya tashi motarsa ya fice daga layin.

Ya kusa a qalla minti goma a tsaye a wajen
"Wanne abu kake ne haka anwar,kana cikin hayyacinka kuwa?" Yaji maganar daga sama,wani sashe na zuciyarsa na tuhumarsa
"Ya Allah" ya fada shima cikin jin haushin kansa,gami da tuhumar kansa na me ya kaishi aikata haka,saiya kunna motar yana duban agogon dake gaban motar,qarfe tara harda minti goma sha shida,yana jin da qyar idan zai iya zuwa gidana anty usaina yanzu duk da tana can tana jiranshi,kawai saiya wuce gidanshi,zuciyarsa na masa wani irin zafi haka kawai.

Baiyi nisa a tafiyar ba wayarshi ta dauki qara,ya kalli wayar da ido kawai,sa'ida ce ke kiranshi,saiya danna sannan ya maidata handsfree yace
"Ya akayi sa'in(shi yakan kirata dashi wani lokaci)"
"Uncle,zaka zo ne?"
"Me ya faru?"
"Uncle wani abu na gani,wata na gani tazo wajen ummi uncle kasan dawa take kama?" Kai ya kada
"A'ah,dawa take miki kama?"
"Uncle kaman anty shahida nidai haka na gani,amma wannan ta dan fita girma ta kuma dan fita kyau" gabanshi ne yafadi baisan sanda yace
"Yaushe?" Ba
"Dazu dazu suka shigo gida tare da ummi" dan shuru yayi na dan wani lokaci sannan ya sauke boyayyar ajiyar zuciya
"Shikenan...yau bazan samu shigowa ba,amma ki bari gobe idan nazo sai muyi maganar"
"Toh uncle,ka siyomin turaren?"
"Zan kawo miki karki damu,ki gaida ummin naki kice mata wani dan uzuri ya riqeni"
"Toh uncle" daga haka dukkansu suka kashe kiran,tunani ya shiga sosai,sai salon tuqin nasa ya koma slow kaman bazashi gida ba,tunaninta ne ya dawo masa sosai tun farko alaqarsu irin wanda bai taba tsintar kansa a ciki ba.

Sai daya kashe wasu mintoci kafin ya isa gida,a gajiye ya isa falonshi ya fada saman kujera yana lumshe idanunshi kafin ya budesu,yanason manta komai amma abubuwan nata zarya bisa qwaqwalwarsa,sai kawai ya miqe zuwa bedroom dinshi,ya cire kayanshi ya daura towel ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan sanyi sosai.

Ya jima zaune gefan gadonshi yana neman bacci ya sureshi amma abun yaci tura,saiya miqe zuwa wani safe na musamman dake dakin,ya saka lambobin sirri ya budeshi,envalope din daya tsani gani yau da kanshi ya daukota,ya bude abubuwan dake ciki gaba daya,hotunan ciki suka bayyana,take kanshi ya soma daukan zafi,idanunsa suka kada jazur dasu,saiya kasa ci gaba da kalla ya soma tattaresu yana tuhumar shahida cikin ranshi
"Me yasa shahida me yasa?,me yasa za kiyi haka,me yasa kika tarwatsani,me yasa kika tarwatsa duk wani buri da fata na?" Ya qarashe maganar yana cilla envalope din cikin abun ya maida ya rufe,saiya fada saman gadonshi yana maida numfashi gami da ambatar
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil"


*WASHEGARI*



Qarfe goma da minti arba'in ya isa gidan cikin dinkin shadda wadda tayi masifar masa kyau da fito da kyawunshi.

Dukkansu suna falo suna karyawa
"Uncle sannu da zuwa,ina kwana" suka dinga fada daya bayan daya,fuska a sake yake amsa musu yana tambayar lafiyar kowa suna amsa mishi
"Ina ummin taku?"
"Tana sama tana wanka" sa'ida ta bashi amsa bakinta fal da zance,turarenta ya ciro ya miqa mata tasa hannu biyu ta amsa cikin Murna
"Uncle na gode,na gode"
"Yauwa" ya amsa yana duban tashar da suke kallo,hijra tv waqoqi suke sanyowa na mawaqa daban,sa'ida ce ta tashi daga cin abincin da take ta dawo kan kujerar da anwar yake kai
"Uncle" ta fada qasa qasa,waiwayo yayi yana kallonta
"Uhmmm"
"Maganarmu ta jiya...." Shuru tayi ta ganin saukowar anty usaina,suna hada ido tahau rarraba idanu,miqewa tayi tsaye kafin ta iso,ta jefa mata harara
"Ku kwashe farantan nan kukai kitchen,munaya ki hadasu ki wanke,ke kuma uwar zance ki bita ki daura abincin rana,kafin ki gama laqaqin naki kin gama" duka suka miqe falon ya zama daga ita saishi,ta zauna tana dubanshi
"Jiya sai kuma na jika shuru,sa'ida tace ba zaka samu shigowa ba" yana shafa kanshi yace
"Wallahi,jiyan na taho wani uzuri ya tsaidani"
"To Allah ya rufa asiri" a mutunce ya gaisheta ta amsa masa cikin kulawa sannan daga bisani tace
"Ko a hado maka abincin kari?"
"Eh to...amma bada wani yawa ba" dauke idanunta tayi daga kanshi ta mayar qofar kitchen din ta kira sa'ida tace ta hado mishi.

Yana karyawan suna taba hiran,a hankali shurunsa yafi maganarsa yawa,hankalinsa ya karkata kan hijra tv da suka sako waqar jarumar mata,saita dinga taba ranshi kadan kadan,tana tuna mishi wani lokaci can baya,a nutse ya dauki remote din dake aje kusa dashi ya sauya tasha,dai dai sanda anty usaina tace
"Anwar....ya kamata fa ace ka soma shiri,biki saura sati hudu amma banga alamun hakan tattare dakai ba"sai daya hadiye abincin bakinsa sannan yace
"to me zanyi anty bayan wanda nayi"
"Kamar ya me zakayi?,haka zaka aurar musu diya babu maganar lefe babu komai?" Aje cokalin hannunsa yayu sannan yace
"Nifa anty,da zaki yadda da maganata ayi haquri a qara min wasu watanni"
"Saboda baka da gidan sakata ko baka da kudin yi mata lefan?,ko sadaki ne baka dashi?" Murmushi ne ya subuce masa ba tare daya shirya ba
"Au dariya ma nake baka ko anwar?"kai ya girgixa dariyar na kubce masa
"ni na isa antyna,kawai dai....naga kina yin nafisa ne da yawa" zamanta ta gyara sosai,alamun maganar da zata masa nada muhimmanci
"Ba haka bane anwar,ka fahimceni,mutanen nan suna da kawaici da dauke kai,basu da son zuciya ko tilasta mutum,da wasu ne su yadda suke ganin sun isa dakai dinnan kawai zasu baka umarnin ka auri diyarsu ne,su saka kuma ranar biki da komai baka data cewa,uwa uba ina gudun halayyarku ta maza kafa kazo ka murje ido kace ka fasa ka barmu da kunya" murmushi yayi yana kallon qasa,shikam dama bayajin zai dauki irin wadan nan abubuwan,dalili kenan da tun farko ya zabi yaci gashin kansa,bai qasan wani bare ya tilastashi koya tauyeshi,rama halacci dai wannan yasan abune mai kyau,kuma shine hujja daya,dalili daya da zai sakashi ya haqura ya auri nafisa
"Anty kiyimin kyakkyawan zato,ba abinda zai faru da yardar Allah indai daga bangarena ne,abinda kawai yasa na buqaci qarin shine,akwai wata 'yar tafiya da zanyi ta wata uku,kinga zaifi kyau naje na dawo,hankalina ya hadu waje guda,duk abinda za'ayin ma sai ayin,zan baki kudin da zai isa a hada lefan kafin wucewata da sauran abubuwan da aka sabayi na al'ada" ajiyar zuciya ta saki
"Shikenan,yanzu ya za'ayi ka shaida musu?"
"Wannan duk ba damuwa bace,zan samu alhj da kaina,baida matsala,yasan da tafiyar tawa dama"
"Shikenan,Allah yayi mana jagora ya bada sa'a"
"Amin anty" daga haka suka shiga hirar data shafesu,sai wajejen shabiyu na rana ya baro gidan shima ganin haduwar hadarine,bayan ya tambayesu ya tabbatar basu da wata damuwa.


🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Cikin harabar gidan yake zaune cikin motarsa,murfin motar side din da yake a bude yake,hakanan ya ziro qafarsa daya waje,iska mai dadi dake kadawa tana shigowa har inda yake,iskar na masa dadi qwarai,,dalilin kenan daya sanya idanunsa lumshewa yana shaqarta har tsakiyar kanshi,knocking glass din motar yaji anyi,ya ware idanunsa a hankali suka sauka kan fuskar nafisa dake tsaye cikin kwalliya tana dubanshi daga sama har qasa,duk da fuskarta qawace take da kwalliya amma annurin cikinta kadan ne,shigarsa take kallo,yayi kyau cikin qananun kaya baqaqe qafarshi saye cikin wani booth mai bala'in kyau,quruciyarshi da kyanshi muraran suka bayyana,sai taji sonshi na sake shigarta,baqinciki da bacin ran daga bikinsu ya sake mamayeta har hakan ya bayyana kan fuskarta
"Whats wrong with you" ya tambayeta idanunsa qyar a kanta,saitayi narai narai da idanu,qwayar idonta cike da qwalla,,da alama gab take da sakin kuka,shuru tayi ba tare data amsa ba,fitowa yayi gaba daya daga motar ya rufe sannan ya jingina da ita hannayensa shima harde a qirji
"Me ya sameki kuma?"
"Au..baka ma sani ba zaka cemin?" Hannayensa ya watsa yana harde qafafunsa sannan ya soka hannayensa a aljihun wandonsa
"Eh to,xai iya yiwuwa ni abinda nake tunanin shi zai saki kuka ke a wajenki bashi bane"
"Me yasa anwar me yasa har qarin watanni uku bayan wata gudan dake gabanmu" girarshi biyun ya dage yana murmushi
"Au,kice ke kukan aure kike,to saurin na meye?,wata hudu kawai saiya zama damuwa?" Langabe kai tayi tana dubanshi
"Ni sai ya zama damuwa mana a wajena idan har wajenka bai zama damuwa ba,dama ni na damu dakai ai na sani" murmushi ya kuma saki,yadan tafa hannunshi kadan
"Abinda ya faru ya riga ya faru,sai a jira zuwan lokaci"
"Ai shikenan,yana iya"agogo ya kalla sannan yace
"Zan wuce" idanu ta zaro
"Duka duka yaushe kazo?,haba ya anwar mana don Allah,hajiyama fa tace ka shigo kaci abinci"
"Sauri nake nafisa,amma idan na samu chance anjima zan dawo,idan ban dawo ba kuma sai gobe" ya qarashe maganar yana bude motar,sai daya shiga sannan ta mayar masa da murfin ta rufe ta daga masa hannu
"Allah ya kiyaye" shima hannu yadan daga mata,har zai tada motar tayi hanzarin tsaidashi
"Sorry...don Allah ka yimin alfarma mana"
"Allah yasa batafi qarfina ba" murmushi tayi
"Bata fiba,saidai idan ba za'a min ba" dan qaramin murmushi yayi
"Fadi muji"sai data danyi shuru na sakanni sannan tace
"Kamfani triple R Gem nakeso ka rakani don Allah" shuru yayi yana dubanta
"Me zakiyi a can" hannu ta yarfar
"Kai ya anwar,da banso gaya maka ba Allah,amma..."
"A'ah,riqe cikinki" yayi maganar sanda ya tada motar,da sauri ta zaburo
"Bafa wani abu bane,wasu sarqoqi nakeson saya a can" kallonta kawai yake,burin nafisa yayi girma da yawa,duk sarqoqin garin nan amma sai taje har triple R ta saya?,iya saninshi wajene dake da babu abun qaramin kudi a can,dutse ne masu daraja da tsada suke sarrfasu,wanda ba kowa ke iya siyan abun kwalliya ba acan,bayason ya fiya gwasaleta har taji kaman ya tozartata,sai ya gyada kai
"Alright..amma gaskiya bani da lokaci cikin satin nan gaba daya,saidai ko zuwa next week"
"Well,yayi indai zaka rakani din" da haka sukayi sallama ya fice daga gidan yabarta tsaye awajen sonshi na shawagi da ita,sai kuma ta tuna yau akwai partyn da zata saboda haka da sauri ta juya zuwa cikin gida.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍


Qarfe biyar ta fito daga kamfanin kaman yadda qa'idar lokacin tashinsu yake,saidai gaba daya hankalinta ba'a kwance yake ba saboda baqin hadarin daya hado yake kwance a sama yana shirin zub da ruwa.

Kusan mutum uku ne sukayi mata tayin sauketa a gida amma ta doje don kare mutunci da qimarta,ciki harda alhajin dake nacinta wanda ta lallaba ta fito abinta ta baroshi a office din rayyan mai kamfanin gaba daya suna lissafin wasu sarqoqi da sukayi masa,haka ta fito cikin ranta tana addu'a Allah yasa ta isa gida lafiya qalau.

Titin babu wadatar motoci sai jifa jifa,ko dama

18 / 53