Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   46 / 53

135K to 138K   out of 156.9K words

yahuta,yana fatan ba hawan jininsa ne zai tashi ba,don bashi da buqatarsa wannan lokacin,lafiya yake da buqata cikakkiya da zai samu damaryin binciken dayake gabanshi,ya lashi tokobin duk wanda keda saka hannu kan wannan lamarin bazai qyaleshi ba,saiya biya farashin duk wani tashin hankali da suka fuskanta da baqinciki.

A bazata daadan tasake shigowa wannan karon don haka bata samu damar rufe idanun nata ba tashigo dakin
"Karki kuskure,na ganki,tashi muyi magana" kuka keson qwace mata amma ta danneshi,tasan cewa tunda yazo bata da wani sauran goyon baya cewa daadan zatayi ta tashi ta bishi,amma ga mamakinta saitaga ta zauna gab da ita cikin taushi tana cewa
"Muyi magana ta hankali dake mana shahida" sai hankalinta yadan dawo jikinya,nutsuwa kadan ta saukar mata
"Me anwar yayi miki ne?" Sai kuma ta sake dirircewa,daadan tasaki murmushi
"Ki kwantar da hankalinki ki gayamin,wannan karon ina bayanki,don na gaji da ganin wannan kukan naki ace watanni da shekaru masu yawa amma har yanzu basu qare ba?" Ajiyar zuciya tafitar sannan cikin rawar murya tace
"Wallahi daada anwar ba masoyin gaske bane,ya rabu dani tsahon shekaru masu yawa ashe saboda zargin da yakemin da hujja guda daya daya gani da idanunsa wadda hujjar tasa cakude take da qarya da makirci,bayan mun sake haduwa yacigaba da cutar dani da kalamansa,xamana dashi a gidansa duk sanda ta raya masa zai gayamin baqar magana da zata qonamin zuciya,daga qarshe ya auro wadda ya wulqantani ya maida gurbina da ita,ya kwashe abinda bata sani ba ya gaya mata har tana goranta min,alhalin ya gano gaskiya kuma bai gayamin ba saboda sonkai irin nashi,ta yaya zanci gaba da zama dashi daada?" Haba ta kama tana kallonta,itadinma dai bata fadi ko daya daga cikin abinda ya hadasun ba,sai bayani take tana rurrufewa kamar shidin,da sauri daadan tace
"Kai kai kai,amma anwar bai kyauta min ba,yaci amana,ashe azabtar dake yadinga yi bayan nayi ruwa nayi tsaki na aura masa ke?" Da sauri ta dubi daadan,don sai taji kalmar tayi girma da yawa datace azabtarwa,saboda haka tace
"Ni gaba daya banason zama dashi,don Allah daada"
"Kwatar da hankalinki,saki kikeso kenan yanzu?" Gabanta yafadi,amma eh shine amsar da zuciyarta ke bata,saboda haka cikin sanyi ta kada kai sannan tace eh,kanta ta shafa
"Sha kuruminki idan dai wannan ne kin nema kin samu,tashi maza kiyi wanka kici abincinki ki qoshi ki shiga harkokinki,na sake ganin qafarsa cikin gidan nan" mamaki ya kama shahida,baki bude take kallon daada,meya sauyata haka lokaci daya?
"Ko baki yarda bane kika kafeni da ido?,ai dama ko abaya don idanuna sun rufene ina masa kallon na Allah ashe ba haka babe,yanzu kuwa zai gane kurensa,zaisan inasonki,tashi maza kije ga ruwa can mai dumi" murmushi ya subuce shahidan
"Na gode daada,dama nasan shiga yayi kawai tsakaninmu"
"Qwarai kuwa,yanzu kuwa na fiddashi fit" haka ta miqe cikin qwarara jikinta tafice donta sake wanka takuma gasa jikinta,don kwanciyar jiya dayau duka jikinta ciwo yake mata,da kallo daada ta bita sannan tamiqe tabi bayanta.

Har yayi sallar magariba yana dakin hotel din daya kama,bacci da hutawar dayaso yi duka basu samu ba,lokaci daya yaji hankalinsa kuma yayi gida,ya kamata yaje yaji me ake ciki kam bincikensa,don lokaci yayi daya kamata ace ya matsa lamba,saiya tattare dukkan wani dake mallakinsa a hotel din yafito.

Tunda safen ta fuskanci dagashi har shahidan basa gidan gaba daya,sai ita qwallin qwal,maimakon taji hankalinta yakwanta amma saitaji akasin haka,don ragewa kanta damuwa ta zari muqullin motarta taje gida ta dawo amma babu abinda ya ragu,saita ciro wayarta ganin har sanda ta dawo din babu anwar babu dalilinsa tasoma kiransa,harta qaraci burarinta ta katse ba'a daga ba,haka ta dinga kiransa a jejjere amma is'nt answering,daga qarshe ma idan ta kira saita katse bata tafiya,haka ta wuni har gab da magariba sannan tawuce kitchen ta dora abinci,wanda girkin nata dama baya wuce shinkafa da miya da dafaduka,suta iya.

Sanda taji ana knocking qofar falon ta zaci anwar ne yadawo,farinciki ya kamata,Allah yasa shi daya ne ba tare da shahida ba,kai Allah yasama gagarumin fada sukayi tanemi saki,tunda ta goranta mata kan abinda take tunanin cewa ita nafisan bata sani ba,abinda zata tsammata kawai amwar ne yazauna ya kwashe ya gaya mata,tuna wannan yasa murmushi ya qwace mata
"Ashe dai nima ba baya bace na iya hada tuggu" tayi furucin a sarari tana sake feffesa turare yadda zata burge anwar,cikin ranta tana lissafin saura sati biyar komai ya daidaita,maganinta yagama aiki,ita kanta batasan budurin da za'a kwasa ba ranar,qila ma saitasashi ya baiwa mai gadi hutu donsu baje kolinsu dakyau,da wannan tunanin tasake fitowa tanufi qofar falon kana tabude.

Wadda tagani tsaye bakin qofar tayi masifar daga mata hankalinta,yarinyar da tuni suka jima dayin handing over da ita?,ta gama mata aikinta ta kuma sallameta?,to kuma meye ya dawo da ita?.

Fiddausi ta ratse nafisan tashigo kai tsaye cikin falon tana qarewa daular falon kallo,lallai mima tayi gaskiya,ita tana can tana fama da ciwo babu kudin aiki bare na magani na nafisa na morar aikin data mata?,lallai da sake kuwa wai an baiwa mai kaza kai.

Zama tayi hankali kwance kan daya daga cikin kujerun,yayin da nafisa ke tsaye cikin rudewa tana kallonta
"Fiddausi?,meya kawoki gidana bayan kinsan nawar yasanki,dama ba'a ta batun shahida,bamuyi haka dake bafa"
"Zauns malama nafisa meye abun tashin hankali?,maganace 'yar qalilan takawoni muyi mu gamata nawuce nima ba dadin jikina nakeji ba,kawai tasowa nayi"
"Fadi abinda ke tafe take,duk da nasan babu wata sauran alaqa sata rage tsakanina dake" baki fiddausi ta kama sannan ta watsa mata harara
"Hakafa,kaza ci ki goge bakinki,to zuwa nayi in shaida miki inada buqatar wasu kudade da ga wajenki,don hantata tasamu matsala sakamakon shan kayan maye dana dinga yi" dukka qugunta ta kama da hannayenta,tana ganin tsantsar rainin wayo irin na fiddausin
"Kimin aiki tsahon shekara shida baya sannan yanzu kawai don taki taciyoki saikizo neman kudi gurina,ce miki akayi banki ce ni?,waishinma in tambayeki?,nina aikeki shan kayan maye?" Idanu fiddausin ta zuba mata kafin tadaga mata hannu
"Kinga malama,zaki bani ko bazaki bani ba?"
"Bazan bayarba aiba ajiya kika bani ba,ko kuma ki danneni ki qwata idan kina da qarfi" dariya fiddausin ta fashe da ita har tana dafe cikinta inda yake mata ciwo saboda amsawar sa wajen yake
"Sanda kika bani aikinki aina dambe mukayi ba,hakama wannan,na qyaleki,amma ki tuna ina daya daga cikin matakan nasararki,kuma bazan rabu dakeba,kisa haka a ranki" fiddausin ta miqe tasoma ficewa daga falon,sai tsoro yakama nafisa,tayi kamar tabita ta kirata su sasanta amma taji wani girman kai yazo mata,wata zuciyar na gaya mata
"Qyaleta,kada ki bita,idan kikayi haka kin nuna tsoronki a fili,sannan gobema dawowa zasuyi,iyaka koma meye duk inda za'aje a dawo kice baki santa ba qawar shahida ce,kinga kota nan kin qarawa wuta fetur,kin qarawa shahidan baqin fentk,wannan shawarar takarbu sosai a ranta,saboda haka tasaki ranta tazauna taci gaba da kallonta.

Wani irin tuqi yake cike da gajiya da tunanuka barkatai,kamar bazaikai kanshi gidan ba,tafiyar awa biyu da rabi saida takaishi awa uku da rabi cur kamin ya isa garin kano.

Sanda me gadi yabude masa qofar taba shirin fita itama daga gidan,haske fitilar motarsa ta dallareta,saiya samu kanshi da zuba mata idanu sosai,kaman fiddausi,kaman itace,tome ya kawota gidan?,me tazoyi?.

Saida ya aje motar tashi sannan yafito yadawo wajen maigadin,cikin girmamawa ya rusuna
"malam usman waccae yarinyar wacece?"
"Wai wadda tafita yallabai?"kai.ya kada masa don baison yawan magana ma saboda yadda kanshi ke sarawa
" eh ita"
"Ai qawar hajiya amarya ce,tacemin qawarta ce wajenta tazo,to Allah da ikonsama sainaga hajiyan tabude mata qofar falo da kanta"
"Ohkey" anwar yafada yana juyawa zuwa cikin gidan.

A duburbuce tamiqe tana masa sannu da zuwa cikin fargaba tana addu'ar Allah yasa baiga fiddausi ba,don fitarta daga falon da shigowarsa idan ba shegen sauri tayi ba mawuyacine idan bai ga ta din ba,idanu kawai ya zuba mata yana fata da addu'ar Allah yasa bata cikin wannan lamarin kodon girma da mutuncin iyayenta dayake gani,saiya amsata sama sama yana hayewa sama,ta biyoshi tana masa zancan abinci zai fara ci ko wanka,waiwayowa yayi yana dakatar da ita
"Idan ina da buqata zan sanar dake,yanzu hutu nake buqata tukunna" haka ta juya takoma qasan,abu duka yabi ya dagule mata,abu goma da shirin,haka tazauna nan ta rafka tagumi tana jiran sanda zaiyi maganar yace takawo masa,saidai har sha daya nadare shuru babushi ba dalilinsa,alissafin kwana dama ba nata bane bare tabishi tayi qorafi,girkinma tayine kawai donta fake da taga shahida bata nan,haka tagaji ta haqura tattara tawuce dakinta tana saqa yadda zatayi da fiddausi tun bata zame mata gagarumar matsala,ta yanke cewa zuwa gobe da safe zata nemi mima suyi magana,zata shaqa mata kudi yadda aiki zaifi tafiya daidai.

Cikin dare gaba daya tunanin yadda suka hadu da nafisa yake da yadda tafara sonshi,daya kasa samun nutsuwa saiya tashi yayi sallah da addu'o'i sosai,wani irin zargi a kanta mai qarfi yadinga shiga zuciyarsa,ya dade yana wassafa abubuwa iri iri kafin yasamu bacci ya debeshi.

Washegari yana idar da sallar asuba yakira marwan donjin ya ake ciki,tun da dare yaga miscal dinsa amma bazai iya kiranshi ba a sannan saboda yadda qwaqwalwarsa ke a cunkushe,
"Sir,mun samu nasarar kama wani saurayi,mun soma masa tambayoyi amma bamukai ga kammalawa ba,zuwanka muke jira"
"On my way" ya fada a taqaice ya aje wayar,yana aje wayar marwan ya lalubi shahida,a sannan ta gama sallarta da addu'o'inta tana niyyar komawa takwanta,saboda yadda takejin wani sabon bacci na dibarta,ji take kamar ma batayi bacci ba gaba daya,wayar ta kalla,ta gane number din ta anwar ce,saitayi rejecting kiran kana ta maida haqarqarinta takwanta.

Wayar ya daga sanda suke gaya masa busy da alama kashewar akayi kenan,saiya sake qoqarin kira amma aka gaya masa a kashe take,yasaki wata ajiyar zuciya sannan ya aje wayar yatashi yashiga wanka.

Sanda yakammala yasauko batako tashi a bacci ba,ya bude qofar yafice,saidaya tada motar taji qarar motar,ta tashi a firgice ta leqa,daga yadda taga ya shirya tabbas bada wuri zai dawoba kenan,saita saki labulenta tana tabe baki gamida komawa cikin bargo ta nannade cikin zuciyarta tana cewa
"Zakazo hannu me,wato saboda waccar gantalalliyar da bansan ma ina taje ba bata nan shine kaketa wannan ciccikar,to in sha Allahu tama tafi kenan" ta qarasa fada tanayin rub da ciki gamida rungume fillo taci gaba da dibar baccinta.

Ba ita ta farka ba sai sha goma nasafe,wanka tasoma shiga tayi kafin tagama shiryawa taji cikinta nakiran ciroma,saboda haka tagama shiryawa a gaggauce ta fito tayi kitchen,kayan break ta hada sosai don jiya bata wani tsaya taci abinci sosai ba ta kwanta,ta dauko ruwa da drink ta dawo falo ta zauna ta baje tana cin abincinta hankalinta akwance,don kullum gari ya waye hankalinta sake kwanciya yake,tana ganin nasara na kusantota,kwanakinta na sake raguwa na zuwan ranar da takewa mugun tanadi,donko jiya saida tayi order din wasu matsiyatan rigunan bacci,inda za'a mata lalle da gyaran jiki kuwa da gyaran gashi tuni tayi booking tama biyasu,dukka zannuwan gadonta ta bayar tayi order wasu shegun upcoming design 2020,wayarta na hannunta tana neman number mima don suyi zancan fiddausi da yadda za'ayi da ita sai kawai taji sallamar miman.

Fuskarta cike da murmushi ta daga kai tana duban miman tace
"Kice nayi serving credit dina 'yar halak kina kan hanya" tayi furucin tana duban miman,ganin shigarta tayau ta musammance,ga wani shegen baqin gilashi data manna a fuskarta tana taunar chewing gum
"Ai kuwa dai" ta qaraso kusa da nafisan tazauna tana jan farantin gabanta,ta dauki tsoka daya na kazar da nafisan keci takai bakinta tasoma taunawa sannan tace
"Kina sha'aninki,kinfa samu yadda kikeso"
"Wallahi,saima komai ya daidaita"
"Ko?" Miman tafada cikin gatse
"Aikinfi kowa sani,qawa zan jiqaki fiye da yadda kike zato"
"Zamu jiqe tarai daiko?"
Saita waiwaya tana duban miman cikin rashin fahimtar lafazinta,saita maza tana cire hannunta daga abincin,dama taqoshi takai geji
"Eh mana,magana nazo muyi dake"
"To inajinki" ta fada tana tattara dukkan hankalinta ga miman
"Nifa gaskiya magana ta Allah nagaji aure nakeso,saidai dukka mazan gaba dayansu ba'yan goyo bane ba 'yan mutunci ba,gashidai tare aka sha sha'anin amma duk wanda kasoma masa zancan aure mai mutuncin cikinsu nema kawai zaimaka kame kame,mara mutunci kuwa ga da ga zai gayamaka bazai aureka ba 'yar mutunci yakeso,wadda zai bareta a leda yakoya mata komai kamar an gaya musu ana yiwa Allah wayo ne,to duka dai yanzu ba wannan ba,kinga dai anwar gaba daya tare mukasha wahalar nemansa,Allah kuma da taimakonsa da tawa dabarar yasa aka sameshi,saboda haka yadda muka sha wahala tare yanzu ya kamata mu raba dadin tare" wani shashashan kallo takenin miman dashi harta kammala,kaita girgiza tana yatsina fuska
"Amma gaskiya bansan nayi saken da kika rainani da yawa ba mima sai yanzu,mijin nawa kike maganar mu hada dake?,kin gama bin kwalta shine kikeso na hada miji dake?,to bari kiji,kinfi kowa sanin bazan hada anwar dakowacce mace ba,ba abinda bazan iyaba don na mallakeshi ni kadai,yadda nayiwa shahida kawai ya isheki shaida,saboda haka idan wasama kike ki daina" shu'umin murmushi Mima tasaki tana kallon nafisa kai tsaye
"Ko banza bin kwaltata da kike magana akai ya miki rana,shahida kuma tun daga shaye shaye da aka jefata,wurgota gaban anwar cikin jinin period da sunan abortion tayi zuwa hotunan qarya da aka turawa anwar duka idea dita ce,naki kawai shine biyan kudi amma qwaqwalwarki babu wani motsai da take"
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" cewar anwar dake niyyar shigowa falon kunnuwansa sukaci karo da munanan lafuxan da suka kusa tarwatsa zuciyarsa,da hanzari yadafe qarfen valcony din sannan ya daddafa yasamu ya tsaya da qyar don gujewa aikata ba dai dai ba,ya nutsu ya tattara hankalinsa wajen daya
"Idanma akwai inda qwaqwalwarki ta motsa tobai wuce inda kikaci gaba da tafi da anwar ba tare da munana masa shahida cikin tunaninsa a fakaice,hatta da hotunan da aka aika mata saboda dodewar basira tunaninki bai kawo ayi haka ba saida nayi magana,to bari kiji....inma dai ki bani qofa ayi mu taru mu rufawa juna asiri,imma kuma ayi uwar watsi kowa ya rasa wallahi,abun boye kuma yafito fili" cikin hargagi masifa da tashin hankali nafisa tace
"Ke qaramar 'yar iska qaramar qwaruwa,kinyi kadan wallahi,yaushe akayi daren bare garin ya waye?,ko shahida dana gansu tare inakan bakana na rabasu balle ke da kika ganmu gaba daya sama taka?,duk matar data rabi anwar wallahi ba zata tsira ba,ita kanta shahidan sainasa ta dandani guba mafi daci a rayuwarta fiye da wadda na dandana mata a baya,saboda haka kicire kanki daga wannan rikicin ba gurin shigarki bane,sannan idan ke kika turomin fiddausi ma yarinyar da tunda tagama baiwa shahida kayan maye na sallameta ta gama aikinta,bata tashi dawomin ba sai yanzu,kuma ina kyautata zaton plan dinku ne toki gaya mata ta jaye jiki daga rayuwata,don ina da wasu ma'aikatan bayan ke,wuyarta na fidda kudi zan samu wadanda suka fiki komai da komai" dariya mima ta sheqe da ita
"Haka kikace?"
"Qwarai kuwa" yatsunta ta murza suka bada sautin d'as d'as sannan tace
"Mu zuba nida ke,shege ka fasa" daga haka ta juya tana neman hanyar fita.

Daidai lokacin da tuni anwar yakira police dake maqota dasu,suna tsaye a qofar gidan,ya riga ya basu umarnin budurwar da zata fito yanzun su kame ta,sukumaje su aje masa ita harsai lokacin daya buqata.

Tana fitowa sukaci karo dashi,yana tsaye jingine da qofar shiga falon,tsoro da firgici yadan shigeta nako yaji abinda suke fada?,saidai kafin tagama kowanne tunani yabi ta gefanta ba tare daya kalleta ba yashige cikin falon,da kallo tabishi tana sake yaba anwar din,tare dajin haushin kanta natunda farko ta tsaya taya wata yaqin nemanshi,bayan itama macace kamar waccar kuma tana da buqatarsa,saita saki ajiyar zuciya taci gaba da takawa don ficewa daga gidan tare da bawa kanta qwarin gwiwar mallakarsa kota halin qaqa.

Tsaye tamiqe sanda anwar yashigo falon,gabanta yayi wani mummunan faduwa sanda suka hada idanu,shi daya yasan me yakeji a lokacin,tabbas banda yayi dogon yaqi da dogon nazari ba ya afko sanda suke tsaka da zancan daga mima har nafisa saidai su tsinci kansu gadon asibiti,duka jijiyoyin kansa sun tashi rudu rudu,wani irin bala'i yakejin yana cinsa tako ina,amma yadanne zuciyarsa saboda abubuwan da zuciyartasa ta shirya masa aiwatarwa cikin dan qramin lokaci,bayan yayi qoqarin dannar kansa da kiran sunayen Allah,kauda kansa yayi ya nufi saman,yasoma takawa cikin sauri sauri,yayin data bishi da kallo cikin kokwanto,tanason yi masa sannu da zuwa amma ta kasa,tunaninta yakasu kashi biyu,ko yaji abinda suke fada?,ko mima ce ta gaya masa wani abu?,a'ah baijiba,don da yaji batajin girman abinda yajidin zai iya barinsa yawuce ba tare dayace komai ba,da wannan tunanin tasamu waje tazauna tana dakon saukowarshi,donta lura bai fiyason tana hawa saman zuwa dakinsa ba,abun yana bata haushi.52

Yakai ya kawo ya kawo cikin dakin nashi yafi sau shurin masaki,idanunsa sun kada jazur haka zuciyarsa quna kawai take,ji yake kaman yasauka ya kama nafisa yayi mata mafi munin hukunci zuciyarsa na tausarsa,wayarsa yadauka yayi kiran daya daga cikin jami'an tsaron daya damqa case din a hannunsa,ya shaida masa aje a karbi mima su hada da saurayin,ya jaddada masa lallai lallai yanason su karbi hukunci mafi tsananin kafin ma akai ga tafiya kotu,bayason abar kowa yagansu koyasan inda suke bare ma akai ga zancan beli,don babu shakka bazai qyale daya daga cikinsu ba.

Kashe wayar yayi yana furxar da iska mai zafi daga bakinsa,yana tunanin yadda zaiyi da nafisa,bayajin ko kusa ko alama zai iyaci gaba da tarayya da ita a rayuwarsa,yadda tayi dukkan abinda tayin donta rabashi da shahida yaci alwashin ba zata taba samunsa ba a rayuwa,burinta bazai taba cika ba,inama ace wannan abun ya bayyana ne kadin yakai ga aurenta?,yaso ace hakan tafaru ne a sannan,bazaiyiwu yaci gaba da kallonta qarqashin inuwa guda shida ita ba,donta cutar dashi cutarwa mai yaw,uwa uba tasa ya cutar da rai mafi soyuwa a gareshi,randa take masa soyayya daya tsaftatacciya ta

46 / 53