Author : HUGUMA Category : African Stories & Novels
domin Allah,sake fitar da iskar yayi da qarfi tun daga huhunsa,bayaso yasake tafka wani kuskure saboda haka yasake dannar zuciyarsa ya tako a hankali yasauko zuwa qasan,tana zaune a falon tana waya,wanda tana ganinsa ta katse kiran,saita miqe tana dubanshi yadda yazuba mata idanu jikinta bai bata ba,cikin wata kakkausar murya bayan yakauda idonsa daga kallonta yace
"Me yasa kika aikata haka!" Gabanta taji kamar zai yanko ya fado saboda tsananin firgici da tsoro,amma saboda tsoron kada ta bada kanta yasanya tace
"Me nayi?,akanme kake magana?"
"Bakima sani ba?" Ya fada yana dage mata dukka girarsa
"Bansan me na maka ba?" Takuma fada tana gayyato dakiya
"Me shahida dani kaina mukayi miki kika cutar damu har haka?" Tambayar ta bugeta matuqa,har taji wani jiri jiri na shirin kayar da ita,tadan samu ta dafe kujerar da take tsaye daura da ita,gargadi da jan kunne mai girma zuciyarta tayi mata na matuqar bata nutsu ta tsaida hankalinta ba kwabarta zatayi ruwa tsululu ma kuwa,saboda haka ta hade rai tsaf
"Ban gane bafa,me kakeson cewa ne?" Kafeta yayi da idanu bacin ransa na bayyana muraran ganin yadda take nema raina masa wayo,yana ganin yanzu ba lokaci bane da zai kulata,lokaci yana nan zuwa,lokacin daya gama dafata da ruwan jikinta,lokacin da zata fito da bakinta ta bayyana duk wani mugun qullinta,saiya sauke hannayenshi wanda ya nade su ne a qirji yana tsoron kada zuciya ta kaishi aikata abinda baiyi niyya ba,saiya juya ya soma takawa don barin falon,yayin da ita kuma tazuba masa ido,wani dadi na ratsata,tana fatan tafiyar da yayi ya gamsu ne da abinda ta gaya masa,idan kuwa hakane,har fushin qarya zata masa da bore don kada yasake tada magana makamanciyar wannan.
Cikin mintinan da basu gaza talatin ba yashirya dukkan wani abu dake da muhimmanci a wajenshi cikin wata kyakkyawar akwati,yafito da ita,ya kulle dakinsa dana shahida,sannan yasauko ya kulle saman gaba daya,yaja akwatin yafita zuwa harabar gidan,a sannan nafisan na daki tana tsara yadda zata masa boren,kada ma yasameta a falon yasake jefa mata tambayar koya tsammaci wani abu,motarsa guda daya ya bude yasaka akwatin,ya janyo motar yakawota bakin gate,sannan yafito ya nufi wajen malam usman wanda shima yataso da saurin ganin tahowar mai gidan nashi
"Yallabai za'a fita kenan"
"Eh malam usman" ya amsashi yana saka hannu a aljihunsa yaciro kudade masu yawa ya miqa masa
"Duba dakyau kagani,wannan zasu isheka kula da iyalanka da sauran buqatu harna wata uku ba tare da takura ba?" Cikin murna da farinciki yace
"Sosaima yallabai,harma sunyi yawa"
"Babu komai riqe duka,ka koma gida kazauna na baka hutu na wata uku,zanyi tafiya bazan dawo ba sai bayan wannan lokacin,idan kuma nadawo kafin watanni ukun sucika zan nemeka in sha Allah" sosai malam usman yadinga zubawa anwar godiya,ya budewa anwar qofar yafice,sannan shima yakoma cikin dan dakinsa yasoma hada karonshi cikin farinciki.
Yana tuqin yana tuna yadda dukka al'amuran suka faru har kawo yau,bai tsaya ko inaba sai katafaren gidanshi,wanda ya rayu a cikin kafin yayi aure,dukka ma'aikatan gidan suna nan,don haka gidan fes yake kamar akwai mace a ciki,suka dauka masa kayanshi har zuwa bigiren da suke da iyaka suka aje masa ya qarasa dasu,dakinsa yabude yasanyasu,sannan yazuge akwatin ya fito da envalope din guda biyu wanda yasa musu suna da baqaqen envalope,ya tako yafita zuwa balcony dinsa bayan yadauko ashana,da daya da daya yadinga fito da hotunan yana kallonsu tare da jerasu daya saman daya,nadama danasani mara misaltuwa na sake kamashi,duk sanda zai kalla saiya tuna kalar abinda yayiwa shahidan,bugu da qari kuma tawani fannin mamakin yadda zuciyar wani mutumin take cike fal da sharri,tare da mamakin yadda suka iya zama suka tsara wadan nab abubuwa da yake da yaqinin ba qananun kudi aka sakaba wajen shirya shi kansa plan din,nafisa na qarasa fice masa a rai,zuciyarsa na sake qarfafashi da bashi qwarin gwiwa kan hukuncin da zai yanke mata,shi dayane yafu dacewa da ita,zataCi darajar abu biyu ne a haka,igiyar aurensa da qaddara tasanya aka daura mata,da kuma mutunci da karamcin iyayenta,saida yagama jerasun gaba daya sannan ya qyasta a shanar ya cinna musu,wata takamasu kuwa sosai kaman tasan abinda yake da buri da fata kenan,yana zaune ya zuba musu idanu har suka gamaci suka qone qurmus suka zama toka,yana fatan yadda suka qone dukkan wata matsala dake tsakaninsa da shahidan suma su xama haka.
Miqewa yayi yakoma ciki,ya janyo wata akwatin daban yasoma shirya kayanshi,yau basai gobe ba zai tafi katsina,sam sam ko kadan zuciyarsa ta gaza jurewa,ba shahida a zahiri hakanan babu koda muryarta ne ta waya?.
Yana tsaka da wannan aikin kiran muhsin yashigo masa saiya dakata yadaga kiran yakara a kunnensa.
"Hutu kadaukane mutumina baka sanar da ma'aikatanka ba?" Ajiyar zuciya yasake a fili sannan yace
"Kana ina ne?"
"Ganinan a hanya,yanzu na dawo daga wajen mama"
"Zaka iya biyowa tagida inason ganinka don Allah"
"Babu damuwa,jirani kadan,ina fata amarya ta tanadar mana deliciouse?" Wani tsaki yaja wanda yashiga kunnen muhsin sosai harsai dayace masa meye haka
"Karkaje wannan gidan bana nan,ina gidana na nasarawa" dan jim yayi kadan kafin ya amsa da to,sam shi ya manta ma da cewa duka yau babu abinda yasanya a cikinsa,ko yunwarma bayaji bare akai ga batun cin abinci,a haka muhsin ya taddashi yafito falo ya sameshi.
Binsa da kallo kawai muhsin yake,duba daya yayi masa yasan ba lafiya yake ba,fuskarnan ta sake zama a daure,saida ya shanye coffe cup daya yaji hanjinsa yasoma warewa sannan yadubi muhsin
"Zan ragamar jagorancin office dina a hannunka nawani dan lokaci,akwai wani aiki daya tasomin nakeson na kammalashi da gaggawa" cikin mamaki yake dubansa,anwar da baya wasa da aiki ko zuwa office,koda kuwa bashi da lafiya idan ba tsanani tayi ba zaije akoda a daddafe ne yataba aiki sannan ya dawo gida?
"Meyake faruwa?,Allah yasa lafiya" a nutse ya warware masa komai kamar yadda yayiwa daada ba tare daya gaya mishi ainihin meye matsalar ba,yarufe da cewa
"Dole na tafi katsina,saboda daada da nake da hope akanta naga kamar wannan karon bani da wannan goyan bayan,wallahi muhsin ku fitar darai dani wannan karon idan narasa shahida,bazan iya jurewa ba,wancan lokacin hawan jini kawai nasamu,wannan karon kuwa zuciyata ce zata buga" yaga gaskiyar haka qarara saman fuskar anwar din,tausayinsa yakamashi,cikin qarfafa gwiwa ya daki kafadarsa
"Be a man mana,haba ba haka nasan anwar dina ba,nasan zaka iya u can do it,kaje,inada yaqinin soyayyar da shahida ke maka kamar yadda nake da yaqini kan taka soyayyar a gareta,ina maka fatan alkhairi,zakaci nasara,kayi qoqarin hada duk wani courage naka Bravery" kalaman muhsin sun kwantar masa da hankali,shine mutum nabiyu dama dayake tsammatar samun qwarin gwiwa daga garesa,sai anty usaina,wadda ya gaza fuskantarta ya bayyana nata komai,baisan da fuska dakuma sigar da zaiyi amfaniba ta fahimceshi ba tare da an samu wata barakar da qarin damuwar ba.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Tana zaune rumfar daadan ta tasa kwadon zogale a gaba tana masa cin qoshi kamar wadda tasamu shinkafa,yayin da daada ta zuba mata idanu tana kallon ikon Allah,dukkan wani alamu name yaron ciki yagama bayyana tattare da ita,amma har yanzu bataji komai daga bakin shahidan ba tattare da wani abu dazai nuna tasan da zaman cikin,kasa shuru tayi ganin yadda take hannu baka hannu qwarya
"Ohni habiba na shiga uku,wannan anya ba nomau zaki haife mana ba?,wannan ci haka kamar gara?" Idanunta ta wurga tsakar gida waidon taga koda wani take magana?,don sam koda wasa bata gane da ita take ba,don maganar batayi kama da tata ba,saida ta gama dube dubenta sannan tace
"Nifa dadina dake wani lokaci saikiya hira ke kadai,yanzu dawa kike?" Harararta tayi sannan tace
"Sabon kamu ce,gidan nan bayan ni akwai watane?,konice nake da juna biyu?"
"Juna biyu kuma?" Shahidan ta tambayeta tana dubanta
"Ciki mana"
"Wainice mai cikin?" Ta sake tambayarta tana maida lomar data dauko cikin kwananon
"Ah ah nice don gyatumarki" saita narke fuska tana duban daadan
"Allah ni bani da komai,kawai don hankalina ya kwanta inacin abinci yadda yakamata saikice wani ciki ne dani?" Idanu kawai ta zuba mata,ta tabbatar da gaske bata sani ba,a qadamin da ake kaima yanzu sai taga shurun yafi alkhairi,don haka ba abunda tace illa
"Hakane,Allah yakyuata" tasaka a ranta kawai zata lura da ita tasa mata idanu,har zuwa sanda zata fahimci haka.
Haka kawai taji zogalen yafita daga ranta,saita ture gefe tana niyyar tashi
"Ahaa,ya haka"
"Na qoshi" tafada tana ficewa bakin famfo tasoma wanke hannu.
Sallamar anwar data ji ya sanyata kwasowa da gudu daha bakin famfon zuwa rumfar daadan,tasaki salati tana kallonta
"Ahir dinki wallahi karna kuma gani kina gudu,idanba haka ba zan cire hannuna daga lamarin naki"
"To daada me yazoyi don Allah?"
"Ina ruwanki dashi,ki barshi mana yashigo yagamu dani ai,yi wucewarki kawai" saita wuce uwar dakan daadan,tahaye saman gado ta qudundune abinta tana kasa kunne sosai don taji ya zata kaya.
A nutse yasake sallama yashigo,yayi kyau cikin shadda wadsa ta amsheshi matuqa,ta qara masa kyau da kwarjini sosai,,daada dake xaune daga dakin nata amsa mishi,ya qaraso yana cire sau cikinsa,tun jiya yashigo garin cikin dare,daqyar ya taushi kansa ya iya bari zuwa safiya.
Dubanshi daada tayi sanda suka gama gaisawa,ta lura yadanyi rama kadan
"Yanzu kake tafe?" Kai ya girgiza
"A'ah,tun jiya da daddare"
"Aikin kuma fa anwaru?" Cikin kalar tausayi ya karyar da murya
"Wanne aiki daada bayan babu shahida?,akwai wani abu daya kaimin ita muhimmanci ne?" Nauyi yadan kamata,sam anwar din kamar wani me sambatu,zarar magana yake kanshi tsaye,'yar kunyar dake tsakaninsu ma ya manta da ita
"Don Allah daada,Allah yasani dake na dogara,dukkan wani buri da fatana yana kanki" ko banza tasan iya kwanakin kawai shima ya dandana,tana sane itace ta amshi wayar shahida ta tayata kashewa,shi yasa daga bisani koya kirama bata shiga
"Anwar,nayi niyyar horaka ne kuma alhmdlh dukkan wata gaba ka tsallaketa,zanyi wani aiki da nake fata shizai daidaitaka da shahida,abinda yasa tunda farko ban goyi bayanka kai tsaye ba tare dana horaka ba shine,akan samu matsala tsakanin miji da mata,amma babban cikas da koma bayan da ake samu shine,dangin mata sukan rufe ido,suqi tsayawa su saurari qorafin diyarsu bare subi diddigin matsalar abi mata haqqinta,kawai koma meye yafaru sai ace taje tazauna taci gaba da haquri,saboda suna tsoro kada yarinyarsu tazama bazawara ko aurenta yamutu,bayan hakan ba aibi bane,babban abinda ke sake bazama surukai ya qara musu qaimin azabtar da matarsu shine irin wannan,data kawo matsala wasu kota bakinta baza'a saurara ba za'ace tashi ki koma kiyi haquri,komai girman matsala kuwa,kumashi babu mai tsawatar masa koya nemi yadaina,saiyayita cin karensa babu babbaka,duk da alhmdlh kaidin baka cikinsu,kuma dukkan wata alama dake nuna nadama da danasani na ganta tattare dakai,zan shiga lamarin ammafa ta bayan fage,sai kuma ka yadda da shardan dazan gindaya maka" da sauri ya gyara zamanshi cikin zumudi yafurta
"Kowanne irin sharadine indai har shahidana zata dawomin zan iya daukeshi" kai tajinjina tana murmushi
"Nafarko kasa haquri aranka ka kula da aikinka,nabiyu banason ka yawaita zuwa gidan nan,koda zakazo din a qalla yazamana sau daya idan yayi tsamari sau biyu a sati,na ukun kuma jigo shine,bazan taba nunawa shahida cewa ina bayanka ba,zan nuna mata a bayanta nak,nasan halinta sarai wannan shine kawai hanyar da zan dawo da ita hanya,na sani ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba cewa akwai soyayyarka cikin zuciyarta amma daskararriya,zanyi qoqarin farkar da wannan qauna da tausayin da tun asali take maka,wanda shine hanya daya tilo,sabida haka zaka jure kyara kora baqar magana daga wajena ka fahimta?" Kai ya gyada cike da gamsuwa,duk da sharadin rashin ganin shahida yafi kowanne yi masa tsauri,amma dole yadaure
"Na fahimta daada,kuma nagode Allah yaqara girma,amma daada,wayarta fa,batashiga koda nakira"
"Karka damu,tana wajena,zan bata,amma sai lokacin da hakan ya dace" godiya yasake mata wanda daga bisani daadan tamiqe cikin daga murya
"Saika tashi ka koma inda kafito,don jikata babu inda zata koma tunda kai bakasan darajar aure ba,bakasan darajar matarka ba,ka wulaqanta mana diya,karna sake ganin qafarka idan ba takaradarta ka kawo mata ba" tun shahida na kwance tana saurare tana sakin ajiyar zuciya harta miqe tazauna tana sauraren yadda daada ke babbaka fada kaman zata ari baki,yayin da nawar ke faman roqo da namen yafiya,daga bisani taji dif alamun yatafi kenan,saita koma takwanta tana tuna irin kalaman da daadan take.
Duk da cewa sunyi da daada zuwa biyu zai dingayi a sati amma saiya gaza hakan,yakanzo sau uku ko hudu,wanda daadan kanyi lamfo tadinga zabga masa fada da sababi,barinma idan idanun shahidan biyu,tana boye cikin dakin daadan ta fuskanci tana jinsu,duka wannan ba damuwarsa bane,duk zuwan da zaiyi saiyayi addu'a,Allah yasa yasamu ganin koda giftawar shahidan ne,akwai sanda yaqi tafuya da wuri,amma haka yaqaraci zamansa yatafi bata yarda koda labule ta daga ba bare tafito.
Bangaren nafisa kuwa duk inda tashin hankali yake nata yakai nan,daga sanda ta fuskanci cewa anwar ya qauracewa gidan ne gaba daya,babu wani abu daya raga mata wanda idan yana nan akeyi,komai akwai cikin gidan kai kace yana nan,saidai kuma tun ranar daya saka qafarsa yabar gidan bata sake ganinsa ba,sanda ta kirashi kiran yashiga saidai ba'a daga ba,sai bayan wasu lokuta aka biyo kiran,kuka tafashe masa dashi waiko zuciyarsa xatayi laushi,abinda batasaniba shine haushin kukan nata dayakeji ya zarce misali
"Dakata malama,karki cikamin kunne ya akayi." Ya dakatar da ita,wanda kakkausar muryarsa ta dauke mata kukan cak
"Ta yaya zaka barni a gida a jingine?,me nayi maka da zaka qauracewa gida,baka nemana,idanma shahidan ce ta janye maka hankali ko gida ka raba mana ai a qa'idar addini raba kwana ake ko?" Idanunsa a lumshe yana kwance rigingine sanda take wannan maganar,ambatar sunan sunan shahida da tayi saiya zama kamar wani fami ne tayi masa,qyamar nafisan tasake cika masa rai,yadinga tuno maganganu da labarin boyayyun halayen nafisan dayau saurayin da yasa aka kame masa wanda shiya watsar da shahida qofar gidansu yake bashi,tun yanaji har ya kasa zama ya saurara ya miqe yafice ba tare daya gama ji ba,yadinga jin cewa tacuci mahaifanta mutanen arziqi,ta yaudaresu taci amanarsu,donya tabbatar suma basu da labarin duka wannan badaqalar,ta yaya zasu zaci tana zuwa club har idan ta kama takwana a can,bude idanunshi yayu tarwai yana kallon dakin nasa da yake ciki sannan yasoma magana cikin izza
"Abu nafarko da zan gargadeki dashi shine,sunanta yafita daga bakinki,abu nabiyu kuwa matsayin da kike ciki shine yadace dake,abinda nabaki kuma shine akwai abinda kike da buqata,gargadin dazan miki shine,karki kuma kirana" ya maimaita har sau uku sannan yadora
"Idan kika sake kuma kika tako gidan da nake ciki,bama gidan da nake ciki ba,idan kika sake kika aikata haka a bakin aurenki,ban yarda naga qafarki a waje ba,hakanan ban yarda naga qafar wani cikin gidana ba koshi waye,ki kiyaye" daga haka bai sake saurararta ba ya kashe wayar.
Bin wayar take da kallo baki a sake,wannan wanne irin tashin hankali ne yake shirin tunkarota?,tayiwa kanta tambayar da bata da amsarta.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Duqe take gaban famfon dake tsakar gidan sanye da riga da skert na wani yadi mai rawa wanda yazauna mata das a jikinta,ka ta babu dankwali sai kalba manya da daada tayi mata,jelolin kitson suka biyota saboda duqawar datayi,kayan sawarsu take daurayewa ita da daada,Allah Allah take tagama ta je tadauki alalen gwanwgwani na manja daadan tayi musu yau,don sam kasa yi tayi ita tayi niyya,saboda idan tayi da kanta saita kasa ci tarasa dalili.
A nutse yayi parking din sabuwar farar motarshi dayau yasoma hawanta,wani kyau na musamman yaudin yayi,yana sanye da wani yadi na maza mai taushi da rashin kauri,wanda har kana iya hango fara qal din vest dinsa taciki,dinkin da kadan yawuce gwiwarsa,haka hannun gajere ne iya gwiwar hannu,idanunsa glass ne mai garai garai wanda ka iya ganin qwayar idanunsa,baqin sau ciki da baqin agogon hannu na fata na maza,sosai yake qamshi kamar yadda yasaba a al'adarsa,a nutse yashiga soron gidan,yana addu'a tare da fatar yasamu yau ya ganta.
Sallama biyu yayi babu amsa,saboda haka yadan leqa tsakar gidan don yaduba koba kowa a gidanne,idanunsa suka hango mishi ita,wani abune ya tsirga masa tun daga kansa har qafa,ya kafa maya idanu yana kallon qugunta daya sake budewa,saiyaji kaman ana jansa zuwa gareta,yataka zuwa bayanta ya tsaya yana qare ma lungu da saqo na jikinta kallo.
Ko kusa bataji sallamarsa ba ko tsaiwarsa,saidata gama matse kayan ta dago sannan ta juyo cikin gaggawa da niyyar shanyawa a igiyar dake bayanta,karan taci karo da mutum kana ta fada jikinsa,baiyi sanya ba ko daga mata qafa yasa hannayensa gaba daya ya lullubeta tsam cikin jikinsa yana maida numfashi,saita soma kiciniyar qwace kanta
"Lafiya malam,meye haka?,me kakeyi?"
"Kewarki nake shahida,wallahi na azabtu sosai,don Allah shahida please,ki tsaya ki saurareni" dukka qarfinta ta sanya ta tureshi sannan tasoma yunqurin shigewa dakin bayan tasaki kayan shanyar hannunta,caraf ya damqo hannunta,saita waiwayo suka shiga kallon kallon,kyau da qyalli gami da taushi da fatarta ta dadi yi yanason gigitashi,fuskarta tayi wani fresh tana fidda annuri,qirjinta yaciko kaman yadda hips dinta suka fito,idanunsa taga yana mata wani haske da kwarjini,yaci gaba da kafeta da kallonshi yanason kallon yabi duk wata jijiya da jini na jikinta ya karya lagonta,ganin kamar yasoma samun dama yasanyashi zare gilashin idon nasa yaci gaba da jefa mata guba a kallonsa,yarrr taji jikinta yayi,wanda yasanyata cikin gaggawa tasake tureshi da sauri ta afka dakin nasu.
A tsorace daada dakejin redio wadda batasan dukka abinda ke faruwa ba ta tashi daga kashingidar da tayi tana tambayarta lafiya?,bata iya tsaiwa amsa mata ba tafada dakin gadonta jikinta na rawa,saita zubawa qofa ido ta daga murya tana cewa
"Waye?"
"Nine daada" ya amsa mata lokacin dayake kwashe kayan data zubari din yasoma shanyawa a igiya.
Bai shigo ba saidaya gama,tasan cewa lallai shahidan najinsu,saboda haka ta dinga surfa masa bala'i,yana zaune yana murmushi gamida addu'ar plan din daadan yaci,ta masa nuni daya tafi ya dawo gobe yayin da asarari ta masa kora sosai,ya miqe ya mata sallama yafice,ko iya haka yau yaci ribar zuwan nashi,cikin nishadi yadinga tuqi don zuwa gidan inna,yanajin qamshin