HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   8 / 53

21K to 24K   out of 158.4K words

ya ture ?annenshi ya isa yayi hugging nata
"Oyoyo Mommyna"
"Welcome home my son, idonka kenan?"
Ya sake ta yana Wan shafa kai, ta saki murmushi ta san ya kan shigo cikin Kaduna amma sungulollinshi ba ko yaushe yake bari ya ?araso gida ba, kusan satin shi uku zuwa huWu rabon shi da su sai a waya.

"Wannan kuma wacece yaya? A ina ka samo ta?"
Samha da tun bayan gama murnar su ta ?ure Afeefar kur da idanu tayi tambayar.

"Samha Afeefah sunanta, ki kaita Wakin ki ta yi sallah ki ba ta abinci idan na sau?o bayan isha za mu yi magana"
Babu wanda ya sake tankawa a cikin su har ya haye sama inda nan ne sashen shi, ta du?a ta shiga gaishe su Waya bayan Waya sai ?are mata kallo suke suka amsa ba yabo ba fallasa.

"Mu je"
Samha ta furta mata, ledan ta da samhar salim ya ajiyewa ta Wauka mata ta nuna mata, babu musu ta sa hannu ta Wauka ta bi bayanta. Bayi ta nuna mata ta shige a lokacin har an fara kiraye kirayen Sallar Magrib, Allah ma ya sa ta zauna da Aunty zee da take da 'yan abubuwan zamani Dukda bai kai na gidan ba amma ta iya ta buWe tayi alwala ta fito. Samhar na zaune bakin gado tana latsa waya ganin Fitowar ta ya sa ta nuna mata gabas ba tare da ta bata sallaya ko ta motsa daga inda take zaune ba, sai da Afeefar ta shimfide dankwalinta a saman tiles Win kan Samha ta mi?e ta shige bayin. Afeefah na sallah ta ji samhar na wanke bayin ko da ta idar samhar ta fito ta shimfida sallaya daga chan nesa ta tada Sallar ta, ko motsi Afeefah bata yi ba tana ta Adu'a da ro?on Allah a kan wannan rayuwa da za ta yi a wannan gida, har aka kira isha kan ta mi?e ta gabatar Adu'a ta cigaba da yi a kan kar Allah ya kawo ajalin wani tana cikin gidan, tun bayan Magrib Samha ta fice daga Wakin bata wani jima da idar da Sallar ba tana zaune kawai sai ga samhar ta turo kofa ta shigo.

Plate na shinkafa jollof ne ta ajiye mata da wani karami mai dauke da ruwan leda guda biyu.
"Na gode"
Ta faWa, kai kawai ta gyaWa ba tare da ta buWi baki ta amsa ba ta sake ficewa.

A chan parlor kuwa bayan salim ya shigo daga Sallar isha suka ajiye mishi nashi tray Win dake Wauke da plate na shinkafar da wani an yi wrapping salad da wani saucer mai Wauke da pepper chicken da ke fidda kamshi haWe da zobo jug guda. Bismillah yayi ya shiga ci a natse don ya tara yunwa sossai a cikin nashi, sai da ya gama yayi hamdala hajiyar su da tuntuni idanunta ke kanshi ta ce
"Salim yarinyar chan da ka shigo da ita daga ina haka? Meyasa take a waje har bayan Magrib ba za'a nemeta a gida ba?"

Ya Wan gyara zaman shi
"Wallahi Mommy yarinyar ce rayuwarta abin tausayi, na rasa me yasa mutanen mu suke haka a wannan rayuwa ashe don ajalin bawa yayi ya amsa ?ira sai ya zama lallai lallai wani Wan uwansa mutum ne ya kashe shi? Duk mun manta cewa idan ajali ya zo babu mai jinkirta wa ko da da second guda ne sai ya tafi?"

Hajiyar ta gyara zama tana katse mishi hanzari
"Hakane idan har mutum ya mutu ajalin shi ne ya riga yayi amma a komai akwai sanadi"
Ya Wan yi jimmm yana kallonta for seconds kan ya shiga magana
"Mommy Afeefah Marainiya ce! Mahaifinta ya rasu tun tana ciki, mahaifiyarta ta rasu wurin haihuwar ta...."
A hankali ya cigaba da ba su labarin Afeefah kaman zai zub da ?wallah har kawo yanzu, yana sauke aya Samha ta mi?e hannunta duk biyu dafe da ?irji idanu waje ta ce

"Mayya Yaya Salim???"





=???Gureenjoh=???

https://chat.whatsapp.com/Ef0BFnE69VjAhuWCV9Fxbe?mode=ems_copy_t

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Kun ga comments? To ku dage da comments za ku sha mamaki amma idan bakwa yi haka nima zan ke shantakewa. A takaice dai ina ro?on ku da ku ba ni haWin kai mu ga mun gama labarin nan cikin watan nan don kowa ya sanni ya san ba na Littafi mai tsawo*

*011*

Wani irin kallo ya watsawa Samha da ya sa ta koma ta zauna sai kuma ta fara hawaye, juyawa yayi ya kalli hajiyarsu da tunanin za ta yi mata faWa sai ya ga ma kallon shi take da expression na mamaki a fuskanta.

"Mayya fa ka ce Salim? Shi ne za ka tura ta Wakin autana ta fara da ita? Me ya hau kanka da za ka kawo mana cutarwa gida after all faWi tashi da muka sha don mu ga mun inganta rayuwar mu?"
Kasake yayi yana cigaba da kallon mahaifiyar tashi bai taSa tunanin zai fuskanci wani matsala daga Mommy ba, ya zaci ta san zafin Wa kuma Wan wani ma zai iya zama nata musamman idan ta ji cewa Marainiya ce don ta fi kowa danWanar wahalar da maraici ke janyowa.

"Mommy na Wauka Afeefah Abar tausayi ce da muddin na ba ki labarinta za ki karSeta hannu bibbiyu, ki rungumeta tamkar su Samha wallahi mu ma Allah zai dube mu ya ba mu ladar kula da ita"

"Dakata Saleem! Dakata min don Allah! Ka kawo yarinya kana ikirarin danginta sun guje ta saboda Mayya ce da tun tana ciki take cin maita ta ci har uwar da ta haife ta da ubanta ka kuma yi expecting in karSeta? Ta cinye min ku kenan? Ko ni kake so ta cinye maka? To ba da ni ba salim... Ba a gidan nan ba maza maza tun dare bai ba tarkatata ka mayar da ita inda ka Wauko ta tun muna shaida juna je ka fitar min da yarinyar nan a gida ba za mu taSa shiryawa ba..."
Hankali tashe ya Wan kalli kofar Wakin Samha kar Afeefahn ta ji ya matso ya ri?e hannun mommyn.

"Mommy wallahi ba gaskiya ba ne duk fa zargi ne da ?azafi irin na mutanen duniya, wallahi Afeefah is innocent mommy ki tausayawa rayuwarta don Allah. Mu ma fa marayu ne ki saka ta a sawun su Samha idan da Waya daga cikinmu ne ake yiwa wannan kazafi za ki iya jura? Za k...."
A hasale ta katse shi
"Na rantse da Allah zan tsinka maka mari salim ka sake ala?anta yarana da wanchan Abar, eh ku marayu ne amma da ba ku ci naman kowa ba uban wa yayi muku ?azafi? Bari ka ji ba'a taSa yaWa jita-jitar da bashi da kamshin gaskiya ba. Kafin na hasala na haWa da kai ka je ka fitar min da yarinyar nan a gida..."

Samha da har lokacin take hawaye tace
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun ni dai mommy wallahi ba zan iya sake shiga Waki na ba"
Sadiqa tace
"Ni dama daga ganinta na ji har ga Allah bata kwanta min ba, sai nu?u-nu?u take ashe babu gaskiya a lamarin ta"
Sameera ta yi kwafa
"Nan ma ba ki ga idanunta bane, duk abin tso..."
"Kun yi min shiru ko sai na sassaSa muku? Da ku nake magana ne? Ko na kira sunan dayanku anan? Kun ga kun yi kama da waenda zan nemi izininku kafin aiwatar da abin da yake daidai? Duk cikinku akwai wacce ta isa ta hanata zama a gidan nan ne?"
Ya daka musu tsawa Ranshi ya kai ?ololuwar Saci duk mommy ce ta ba su wannan ?ofa amma ya zai yi?

Gaban mommyn ya koma ya kama hannunta idanunshi kaman garwashi don saura kiris ya fara yi mata kuka a yadda yake jin zuciyarshi ya ce
"Don girman Allah mommy kar ki koreta, ba zan iya bari ta tafi ba mommy in ta fita a gidan nan ina za ta je? Musulma ce fa 'yar uwarmu kuma mace, ko don aikina na kare lafiyar al'umma mommy ba zan iya tura Afeefah waje ba, Don Allah mommy ba don ni ba ki sake nazari akan hukuncin ki kar ki saka ni yin abin da zai yi hunting Wina for life please mommy"

Ganin zai kai gwiwar shi ?asa yana cigaba da ro?on ta ya sa ta ri?e hannunshi suka koma zaune, wuri guda ta tsurawa idanu sama da mintuna biyu ta sake kallonshi duk ya marairaice yana ro?onta, Salim a yaranta yana da ha?uri yana kuma da kawaici don da wuya ya ro?e ta abu ko ya tambayeta ko da kuwa yana matu?ar bukata ko da kuwa bu?atar kuWi ne, yana tausayinta ?warai gani yake har yanzu bata huta da Wawainiya ba alhali, gidan gadon su ma 'yan haya ne ciki bai san ya suke kashe kudin ba a haka shi yake daukar Wawainiyar karatun ?annenshi da cin su, tufafin su da ma sauran hidima na rashin lafiya bai taSa gazawa ba tun da ya ri?e ?asa to Meyasa za ta kasa yi mishi wannan alfarma guda? Amma kuma idan yarinyar ta kashe mata shi fa? Numfashi mai matu?ar nauyi ta sau?e ta ji ana cewa Mayu sun fi cinye kurwan wanda ya taimaka musu ya ji tausayinsu kenan muddin yarinyar za ta zauna gidan sai ta cire wa salim tausayinta? Amma ta yaya?

Ta sake jan ajiyar zuciya cikin gamsuwa da shawarar zuciyarta
"Shikenan Salim na amince ta zauna amma fa ina da sharuWWa, sharrudan da zan gindaya maka wanda matu?ar ka tsallake Allah ya isa ban yafe maka ba"

A firgice yake kallonta, zuciyarshi kaman zai fito waje jikinshi har yana wani rawa don ba ya wasa da Abin da ya shafe ta, me yayi zafi da Allah ya isa? Da kyar ya iya buWe bakinshi da yayi masa nauyi ya furta
"Allah ya isa mommy? Ni??"

Ta gyaWa kai cikin alamun tabbatarwa tana kawar da idanunta daga kallonshi kar ma ya bata tausayi kuma ta san muddin ya amince ba zai taSa tsallakewa umarnin ta ba.
"SharuWWan su ne babu ruwanka da abin da ya shafe ta, za ta zauna zan bata abinci sau uku kaman kowa, za ta yi aikin da ya kamata a ce kowacce mace na yi saidai duk wani abu da ka ga na yanke a kanta babu ruwanka, do not question me a kan duk abin da ya shafe ta i repeat! Magana ta fatar baki tsakanin ku in har ya wuce minti Waya ban yafe maka ba, ni zan duba in ga cancantar saka ta makaranta ko akasin hakan idan zaman ba na Wore bane dole za ta bar gidannan ka kuma yanke kowace alaqa tsakanin ku, ko da ko sannu ne"

Ya yi jimmm kanshi ?asa duk ya damu kan ya sau?e numfashi
"Shikenan mommy in shaa Allahu zan kiyaye umarnin ki"
Yana kai nan ya mi?e ya bar musu parlorn Ranshi na ?una, da yana da mata babu abin da zai hana shi ri?e Afeefah tamkar 'yar sarki ya ba ta ingantacciyar rayuwa, a yanzu ma bai fidda tsammani ba ya amincewa mommy ne da tunanin with time za ta sassauto daga kudurinta.

Tuni suka cika parlorn da hayaniya bayan barin shi suna uzzurawa mommyn akan me yasa ta amince da zaman yarinyar gidan?
"ku yi shiru ku bar ni da shi, ai in bata ga wurin zama ba da kanta za ta fitar da kanta daga gidan ba sai wani ya kore ta ba."
Ta mi?e ta nufi Wakin Samha tana jin abin da zuciyarta ke gayamata daidai ne, duk suka rufa mata baya wane sarauniya da fadawarta.
Suka sameta zaune inda take tun bayan idar da Sallar ta idanunta suna zube a farantin abincin da ko loma uku bata yi ba saboda tunani da ya ci karfin kwakwalwanta, tsoro ne sossai da fargaba suka danne yunwar da take ji don rabonta da abinci tun da suka karya da Baaba da safen a asibiti.

"Ya ma Sunanki?"
Mommyn ta tambaya tana sake ?are mata kallo.
"Afeefah" ta amsa a hankali.
"Ban san wani kalar tsafin kika yi wa Saleem ba da har karo na farko ya zaSi bijirewa umarni na a kanki, amma bari mu ga ko ke kin san hallaci? Zan ja miki federal warning akan yarana don ni karan kaina ban san abin da zan iya aikatawa ba a kansu, hawainiyarki ta kiyayi ramata idan kina cin ?asa to fa ki kiyayi na shuri wallahi ko da wasa 'ya'ya na suka yi ko da ciwon kai ne hmmmm"

Ta kara hmm Win da wani irin siga na razanarwa,
"ana magana ba za ki amsa ba?"
Sadiqa tayi maganan tana hankada ta da kafar ta
A Wan razane ta gyaWa kai.
"Tashi in kai ki inda za ki zauna, ki Wauki farantin nan don daga yau a ciki za'a na baki abinci har Allah ya raba mu da ke, kuma ba ki isa a saka miki abinci ki bar mana ba don a nan ba ma almubazzaranci da gumi muke nema don haka dole duk abin da aka saka miki haka za ki cinye. Shara, mopping da wanke-wanke su ne aikinki. Am I clear?"

Sameera tace
"Kai mommy ke ma ina wannan ina jin turanci? aka ce kin fahimta?"
"Eh na fahimta"
Ta amsa cikin rawar murya.
"Tashi mana ni ki bar min Waki, ko za mu tsaya muna jiran ki ne?"
Dole ta mi?e da sauri ta Wauki kayanta da plates Win ta bi bayansu, ta kofan baya suka fita suka mi?a har Boys quaters jin hayaniya da hira haWe da dariya kuma Muryar maza ya sa ta sake tsorata, isan su varender Win Hajiya ta shiga buga cikin aihinin main building Win Waya daga cikin su ne ya le?o ganinta ya sa ya koma da gudu ya ?ira sauran suka fito su uku. Ba manya bane chan matasa ne duka masu jini a jika da fafutukar neman halal, Ishaq shi ne ke musu wanki da guga sai iliya da shi ne driver sai mudi mai gadi, ganin duk maza ya sake tsorata Afeefah me hajiyar take nufi? A sama ta ji muryarta tana cewa

"ke! Ga Wakin ki nan"
Tq nuna mata wani single room dake kan varender Win. Da gaske a waennan garadan za ta haWa ta, ganin yadda suke kallonta kaman kura ya ga nama ya sa hawaye Salle mata a take tana ji hajiyar na cewa
"Mudi wannan itace mai wanke-wanke da share share za ta zauna a Wakin nan kar in ji kar in gani"
"To! To hajjaju in shaa Allah za mu kiyaye"
Suka juya suka tafi suka barta nan tsaye kyam.

"Sannu kyakyawa"
Bata tanka ba sai shige wa Wakin da aka kira da nata da tayi da gudu ta datse kofan tare da zamewa a jikin kofan tana fashewa da kuka sossai.

Dariya suka sheke da shi don tayi mugun basu dariya suna shiga Waki kuma suka fara gulman kyaunta, kaman daga sama suka ga an turo kofa da ?arfin gaske duk razana suka yi sai kuma a take suka wani irin zubewa ?asan ganin Saleem ri?e da bindiga muraran, fuskan nan yayi Red babu wanda zai iya cewa ya taSa ganinshi cikin wannan yanayin a take jikinsu ya tsume cikinsu ya shiga ba da ?arar tsoro suna tunanin me suka yi?

Iliya ke ta maimaita
"Yau mun shiga uku mun lalace allurar ce wallahi ta tashi a kanmu ya Allah ga mu gareka.."
Kuuuuu haka kowa cikinshi ke ba da sauti ganin ya sake haWe fuskan nan tamau, ya samu hannun kujera ya zauna tare da Wora kafan shi daya kan kujerar ya sa bindigar ya Wan sosa goshinshi yadda za su sake gani da kyau su tabbatar, ya sau?ar yayi kooking ta ba da sauti tuni suka ma?ale juna suna kakkarwa kaman kadangarun da suka faWa wuta sai salati suke.

Ya ce cikin dakakkiyar murya
"Menene wannan a hannu na?"
Mudi da yake jin yana shiru saleem zai iya fashe kanshi don an sha ce musu idan allurar sojojin ta tashi bata da hankali ana Sata wa sojan rai sai kisa yayi carab ya ce murya na rawa

"Abin kashe mutane"
"sunanta na tambaya!!"
Ya faWa a hasale da kuma gaske a mugun hasalen yake, Ishaq yayi saurin cewa
"Sunanta bindiga wallahi bindiga sunanta"
"Kun dai san ni soja ne, kuma ina da lasisin harbata ko?"
Sai kai suke gyaWawa kaman kadangaru
"BuWe baki za kuyi ku amsa ni malamai"
Tuni suka cika Wakin da
"Eh, tabbas! Ha?i?a hakane!"
"To ku buWe kunnuwanku da kyau ku ji ni, wannan yarinya da Hajiya ta kawo ta nan ko kallon da ya wuce na seconds kuka yi mata bare magana ta fatar baki ba tare da kwakwaran dalili baaaa..."

Ya mi?e tsaye ya isa inda suke ya WodWora bindigar kan kowannen su yace da ?arfi
"Toh tabbas sai ya kwana a lahira!!! Ina Fatan kuna ji na da kyau??"
Suna zare numfarfashin tsoro da kaWuwa suke amsawa a tare
"Mun gane wallahi mun gane, ba za mu kuskure ba ranka ya dade yallabai"
Ya Wan matsa baya.
"Kar ku ga kaman ban cika zama ba, gidannan ko ta wani Sangare ina da abin Waukar video a Soye waninku ya gwada saSa doka ta ya gani..."

Yana kai nan ya juya ya fice bayan ya sake nunnuna musu bindigar a Goshi ai da gudu iliya da mudi suka fara rige-rigen isa bayi sai zawo...! Ko magana cikinsu babu wanda ya sake yi a haka baccin dole ya kwashe su dukunkukune da juna.

Ya Wan jima tsaye yana kallon kofan Wakin nata bayan fitanshi kan ya wuce, yana tsaye a balcony Win shi na sama ya ga isar mommy da ita wurin abin ya matu?ar damun shi, ta ya mommy za ta haWa mace da maza har uku waenda ba muharammanta ba? Tsoro ne ya mamaye zuciyarshi ba zama yake ba yana matukar tsoron wani abu ya sameta ba zai iya yafewa kanshi ba, wayanshi ya fitar ya kira Rayyan.

Ringing na ?arshe ya Waga da sallama
"Ya aka yi ne man?"
"I need your advice, ni ne na kawo lu'u lu'u mai tsananin daraja da ?ima sai na rasa inda zan killace hakan ya sa dole na ajiye a inda ba ni da tabbacin za ta samu tsaro da kular da ta dace da darajar ta, ban gama nazari ba sai na kyalla ido na hango wasu kananun Sarayi da basu kai ko da shakar

8 / 53