HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   26 / 53

75K to 78K   out of 158.4K words

kar bata yi ba ya zama laifi da kyar ta ce a rarrabe

"S..sannu da d..dawowa"
Yadda tayi maganan ya sa ya Wago slowly ya kalleta kan ya mayar da kanshi yana kai fork na karshe baki bayan ya haWiye ya Wauki ruwa daga fari kal Win glass cup dake gefenshi ya sha kan ya mi?e ya bar wurin, a tare suka sauke ajiyar zuciya Afeefah tace

"Adda Abee Meyasa da ya dawo da mu kika sa muka zauna?"
Tayi murmushi tana cin shinkafar tace
"Har yanzu baki san Yaya Rayyan ba, ai ya tsani saboda shi ka ?i yin abinda ke gaban ka yanzu da za mu tafi bayan ya kiramu ya kuma san me za mu yi anan muddin muka tafi haka zai titseyemu ya tsare gida ya ce sai mun faWa mishi dodo ne shi da muke avoiding Winshi..."

"Shi dai komai kayi baka burgeshi?"
"Aikam bana tunanin akwai abinda yake burgeshi muddin ba abinda ya shafi Mammi bane"
Ajiye hirar shi suka fi suka cigaba da cin abinci don hanyar lafiya a bita da shekara dazu sun tsira gaba basu san me zai faru ba.

Bayan sun gama wurin Mammi suka yi suka samu ma tana waya ne da wata cousin Winta akan boxes da ake haWa mata na auren, ita dai Afeefah a kunyace ta zauna don yanzu sai take jin kunyar Mammin na rufeta, bayan Mammin ta gama waya ta dube ta

"Afeefah yaushe ne kuke gama exams ne? Bana so kina yawo cikin rana ana wannan gyaran jikin"

"Mammi wednesday za mu ?are"
Ta mayar mata da amsa.

"Da sau?i, saturday ne Waurin auren Abeeha ya zancen telan?"

Sai da gaban Afeefah ya faWi ita ta kasa sabo da zancen auren sam, ji take kaman ana daddaureta ne in aka yi maganar sai ta ga kaman ba gaske ba ita ce zata yi aure, auren ma Rayyan za ta aura? Ya subhallah wani chill take ji yana running over her spine.

"Mammi kin san telan Jannah ne zan ?irata na ji ko ya gama haWawa ko ni sai in je in karSo"

Hira suka cigaba da yi akan bikin da za'a yi shi ne a yini guda, Waurin aure, yini, walima da mi?a amarya Waki in ji mutanen garinmu suka ce Jollof, ba ana yinshi bane saboda talauci ko wani abin, ana yin hakan ne saboda sau?aka zirga-zirga expecially a irin situation na Mammi da bata bukatar stress ko kadan.

Ranar Juma'a ana yi mata lalle sai ga su Fa'iza da fauziyya har da Ummusalma matar Sulaiman da ta sake da ita sossai a yanzu, ga Abeeha da Jannah sai suka zama kaman bridemaids suka cike Wakin da hirarraki ana yi ana dariya, Mammi kuwa sai sawa take ana turo musu abubuwan taSawa sossai hakan yayiwa Afeefah daaWi sai take jin nishadi a ranta na taruwansu ko ba komai Allah ya haWa ta da tarin mutanen kirki, wani irin kyau lallen nata yayi ba?i da ja ya karSi hannu da kafafunta duk suma 'yan matan sun yi. Mammi ma tayi ja a yatsun hannu.

Sai dare suka tafi har Jannah akan sai gobe da sassafe za su dawo.

Rana bata ?arya sai dai uwar Wiya ta ji kunya, yau aka wayi garin Asabar kuma a yau ne ake shirin ?ulla wani babban al'amari mai tarin nauyi tsakanin Afeefah da Rayyan, da misalin karfe takwas ya shigo Wakin Mammin don ta kalli kayan da ita ta bashi ya saka a ranar don rana ce ta musamman a gareta da ma shi baki Waya.

?an uban sun Men lace ne fari kal mai shegen tsada ?ar ciki da babban riga ya wani zauna mishi sak kaman don shi aka halicci yadin, hula da takalminshi bakake ne haka agogo tsadadde dake Waure tsintsiyar hannunshi zuwa azurfa mai ba?in dutse da ke ?ar yatsar shi, fasalta irin fita a angon da yayi ma Sata lokaci ne sai kamshi kam kaman an yi barin turare, fuskar Mammi ya zubawa ido kawai don bai taSa ganinta cikin nishadin da ya ganta a ranar ba sai ya ji wani abu mai sanyi na sau?a cikin zuciyarshi, matsowa tayi ta kama hannunshi tana murmushi tace

"Za ka tafi a saurayi ka dawo matsayin magidanci Saraki, ba zan ce komai ba illah Allah ubangiji ya tsare muku hanya daga zuwanku har dawowanku"

Yayi murmushi ya juya zai fita tace
"Saraki...!"
Ya waigo ta Wauko turarenta ta sake fesa mishi ya fita ranshi fess Dukda wani abu da yake ta ji na tsungulinshi akan auren.

Ga dumbin mamakin shi yana fita ya tarar da motoci sun fi sha biyar dauke da tarin ma'aikatan asibiti da ma 'yan uwanshi sojoji, a hankali ya juya ya kalli Sulaiman da ke mishi murmushi sai yaji wani abu na mishi yawo a jiki, bai taba zaton za'a mishi irin wannan karan ba duba da gaisuwa ce kawai ke hada shi da kowa, wani iri yake ji a sadda ya shiga gaban motan Sulaiman suka fara barin unguwar babu saleem, ya nemi saleem a waya har ya gaji baya samunshi ko da ya dawo gidan ya je mai gadi ya tambaya ya tabbatar mishi sun yi tafiya da madam, ya tambayi su mommy yace basa nan suma. Ko jiya sai da ya koma amma bai same shi ba akan basu dawo ba bai ji daaWi ba sam da hakan ta kasance.

Bai gama shan mamaki ba sai da ya kalli tarin dangin Mammi, iyalai da jikokin uncle Winta motoci kusan nawa har da abokanan arziki don a matsayin auren jikan Uncle Win za'a yi, kan su tafi Mammi ta ro?i uncle Musa akan duk runtsi a dawo da sadakin Afeefah wanda Saraki zai bayar in ya so ko wani abu ne a bashi daban amma sadaki na Afeefah ne.

Mutanen Dutsen-wai suna zaune kawai suka fara ganin lafiyayyu kuma tsararrun motoci suna shigowa one after the other, babban masallacin garin da bashi da wani girma sai haraba suka yi wa tsinke tuni dama Uncle Mansur ya aiko da masu canopies an kafa dayawa a harabar don masallacin ba zai Wauki mutanen ba, an shimfida carpets-carpets anan suka yi masauki, Kawu an nemo na ?asan akwati don ma?on shi ma bai barshi yayi sabon Winki cikin dubu hamsin din chan ba bai tashi jin kunya ba sai da ya ga mutanen alfarmar da suka taru a wurin, kowa mamaki yake yara sai leke suke wasu matan ma na ma?ale saman katangu ana kallon ikon Allah, kowa Allah Allah yake a ce wannan shine mijin Afeefah Annoba su kare mishi kallo...

Fara haramar Waurin aure ake, a hankali Rayyan ya kalli Sulaiman
"Nawa ake bayarwa?"
Sulaiman ya Wan juya hannu alamar mene kenan?
"Sadakin?"

"Duk abinda kake dashi hawa hawa ne amma last da na duba a masallaci ?arancin sadaki yana dubu Wari da tamanin da uku ne"
A lokacin aka fara ambatan sunayensu a hankali ya karkata ya zaro bandir Win dubu-dubu guda biyar ya mi?awa Uncle Sanusi aka mi?awa liman an Waura auren Afeefah Kamal da Rayyan Moh'd Khamis akan sadaki naira Dubu Wari biyar lakadan ba ajalan ba, wani irin yanayi ne yake ratsa shi da ya kasa fahimta, idanunshi da suka sauya ya runtse yana ji ana ta rabon goro da dabino da sweets.

Sai hannu ake bashi ana mishi murna da kyar yake iya kawo murmushi fuskarshi don yanayin da yake ji baya misaltuwa mishi, kawu sai kallonshi yake baki galala yana ayyana lallai wannan zai iya zama maye tunda gashinan irin mazan da yake kallone idan yara suna kallon India, a fina-finan ma wannan ko ya aka yi kuWinshi daban ne, limami ne yake rike da kuWin sadakin kawu yaje ya fara kokarin karSa sai uncle Musa yayi interrupting Winsu

"Kun dai san sadaki hakkin mallakar matar ce ko?"
Limamin ya gyaWa kai
"Toh zan tafi da wannan tunda ita yarinyar na gabana zan bata"
Yana kai nan ya nuna Mansur shi kuwa ya karSi kudin gabaWaya wani irin kullutun bakin ciki ne ya tasowa kawun har wuya, uncle Musa ya murmusa ya fiddo dubu hamsin ya ba kawun Dukda haka bai huce ba sai kumburi yake, anan aka yi reception 'yan kauyen sun ga abinci da kaji iya gani, yana ta mamakin ya aka yi Mammi ta shirya waennan abubuwan with her condition, duk kauyen babu gidan da ba'a ci shinkafa da kajin auren Afeefah ba don enough aka yi shi.

Karfe goma sha Waya suka fara barin garin, kawu ya tafi zai shiga mota Uncle Musa ya janyo shi
"Malam Labaran na ga kana kokarin shiga mota?"

"Eh wai dama in je ne in kalli inda 'yar tawa za ta zauna"
"Ah ai ba'a yi haka ba, ba yanzu ba zaka bari sai ta kwana biyu da kaina zan zo in kai ka yanzu ka ga mutanen da ka tara dole ka tsaya ka ga sun tafi cikin salama"
Yana maganan ne yana tuna zancen Mammi da tace duk rintsi kar su dawo da kowa, tana so ta dasa musu wani bakin ciki ne a rai gashi dai wacce suka kora sun haWa ta da ?addarar ta rabonta shine ya kawo ta har cikin Kaduna, sannan gashi sun gani kuma sun shaida a yanzu ta shallake wa tunanin su kuma babu yadda za su yi babu abin da suka iya. Kwalelen biri da hantar kura.
Shi dai bai gamsu ba amma haka uncle Mansur yayi ta mishi za?in baki har motocin suka watse illa Sulaiman da Rayyan wanda yake jingine jikin mota ya harde hannayenshi a kirji yana mamakin ikon Allah wai yau shi ne da aure. Ko sha'awar kallon kawun baya yi don ko da kawun ya zo yana washe mishi baki tattare girarshi yayi ya haWe fuskarshi ta koma ainihin shi mai tarin kwarjini dole kawun ya kyale shi.

Su ne karshen barin garin sai masu canopies, sai cece kuce ake to Annobar ya saki Afeefah ne ko an mata maganin mayun ne? Kap kauyen babu yarinyar da aka Waura mata aure kwatankwacin na Afeefah, sadakinta kaWai yayi sadakin mata ashirin a kauyen kaf... Inna Larai na zaune da suntumemen kafa da kullum kara hauhawa yake tana jin komai tana hawayen bakin ciki, inna Asabe ma sai uhmm uhmm take tayi abin duniya ya taru ya masu yawa barin ma da aka aiko kulolin abinci wai na gidan kawun, ko da Afeefah ke mata abincin sayarwa wannan yayi jarinsu sau goma don daga ganin shinkafar ka san ba na yara bane ga kaji baja baja.

Suna gani Afeefah ta haye? Garin yaya duk basu sani ba. Ni kam na ce Allah take dashi.

Ko da suka iso Kaduna shi kadai ya nufi babban parlorn akwai mutane ciki sossai don yan uwa Mammi duk suna nan ga su Umma duk sun zo yara ana ta ciye ciye ana wasa, kai tsaye karamin parlorn Mammi ya le?a sai ya ga wata cousin Winta tace mishi
"Tana sashen ka Rayyan"
Bai amsa ba don duk ana ta ango ango kanshi kasa da kyar yake dan murmusawa don kanshi sara mishi yake.

A parlorn shi kuwa ya samu Mammin da wasu, tsayuwa yayi kawai yana kallonta ta ci wanka cikin leshi blue doguwar riga ta Wora gyalen da ya shiga da leshin a kanta da aka yi wa dauri mai kyau, daga wuyanta kunnenta zuwa hannayenta da yan yatsunta gwalagwalai ne da suka kawata adonta ta mishi kyau ainun har bai san ya fadada murmushin shi ba ya shigo ciki. Ta tako a hankali ta kama hannunshi sai hawaye suka shiga zubo mata

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana, Allah na gode kwarai da ka ba ni lafiyar kasancewa da Wana a rana mafi muhimmanci cikin rayuwarshi, Allah ka dube su ka basu zaman lafiya Allah ka sanya musu tausayi, jin kai, bege da kaunar junansu ka bashi ikon bata kariya da sau?e duk wani hakki nashi na aure... Rayyan..."
Sai ta kasa magana sai hawaye, kaman zai yi kukan shima yana jin adu'o'in nata har a cikin zuciyarshi ya sa hannu yana dauke mata hawaye, jan shi tayi suka zauna ta zaro wayanta ta kira Abeeha

"Ku zo da ita"

Daga haka ta kashe.

A gefen Mammin ya zauna yana gyara mata gyalenta nan masu hoto suka shiga aikinsu, sossai suke yin kyau don shine yake ba ta kulawa bayan ya gama gyara mata gyalen ya sake share mata fuska kan ya kalleta yana murmushi duk ana Waukar su, suka kalli cameran suka murmusa a tare ba karamin kyau suka yi ba, zai yi magana suka yi sallama suka shigo ganin murmushin Mammi yayi yawa ya sa ya kai idanunshi inda take kallo.

Afeefah ce ke tahowa a hankali kaman wacce ke tafiya a kan ?aya, tayi masifar kyau cikin wani exlusive luxery lace da aka yi wa Winki na amare, ko ina na jikinta a rufe ne ruf banda hannu da fuskarta makeup da aka mata ya matu?ar amsarta ko don shine karo na farko a rayuwarta ne bata sani ba, amma kam tayi kyau Tabarakallah.

Mammi ta mi?e ta tarbota
"Masha Allah, Tabarakallah Wiyata you made a beautiful bride"
Shi kam kallon seconds biyu yayi mata ya janye idanun har suka zo suka zauna Mammi tana tsakiya Afeefah na gefenta na hagu yana zaune a gefenta na dama, idanunshi ya Wan tsayar akan yatsun Afeefar da suka yi kyau ainun har yanzu mamaki yake, Mammi ce ta kama hannun shi ta kamo na Afeefah ta haWe a tare suka Wago sai zuruf idanunsu suka faWa cikin na juna, idanunta da suka sake haske suka yi mai saboda kwallin da aka saka mata ya tsayar da kwayar nashi a kai, ba zata iya jurar kallon ba sai ta du?ar da kanta daidai Mammi ta Wora nata hannun a kan nasu camera man yayi musu magana suka kalleshi aka shiga Waukar hotuna.

Ko da za'a musu su biyu Mammi bata tafi ba don ta san in ta bar wurin shima sai ya bari, ta mi?e ta mishi umarnin komawa mazauninta ya koma Win amma har lokacin da space tsakanin shi da Afeefah mai hoton ya kalleta yace
"Amarya ki Wan matsa kadan sai ki sa kan ki akan kafadarshi"
Irin bugawar da zuciyarta ke yi tunani take kila saura kiris ya fashe ta mutu, kamshinshi presence dinshi a kusa kusa da ita haka sai ya nemi ruda ta, yana so ya tashi don ya gaji hakan ya sa ya Wan matsa kaWan Jannah da duk tsoronta ta zo ta kama hannun su ta haWe sai suka kalli juna don duk sadda jikinsu ya haWu su suka san abinda suke ji, kallon ya ba da wani ma'ana na daban nan aka shiga daukar hotuna. Sossai yake a takure na tsaye aka ce shine last Mammi dai bata yi magana ba amma idanunta ne ya hana shi barin wurin wallahi.

Bayanta ya koma, ya matso sossai har tana jin kirjinshi na taSa bayan nata babu zato ta ji hannunayenshi duk biyu ya zagaye cikinta, a Wan razane ta Wora nata biyu a kan nashi
"Kin natsu ko sai na karyaki biyu? Baki san mutum ya gaji bane??"
Da Wan faWa yayi maganan a kausashe amma wanda suke tare za su dauka wani abin arzikin yake rada mata aka daddauka ya zame ya bar wurin su ma suka fice.

An yi yini an ci an sha an yi hidima har la'asar kan aka sake wanka aka fito harabar gidan walima, amarya na sanye da wani tsadaddiyar Abaya da yanayinshi kaWai ya bayyana tsadar shi canopies da kujeru aka shirya sossai aka yi walima aka ci aka sha kan mutane suka fara watsewa don bayan isha aunties Win su Jannah za su kaita part dinshi dake cikin gidan, Mammi bata mishi maganan wani gida ba saboda ta sani ne ba zai taSa tafiya ya kyaleta a gidan ba, kuma parts dake gidan kenan don a tsare aka yi ginin Allah ma ya sa dakuna biyu ne a nashi part Win da kitchen da store sai parlor da dining section kaman flat ne mai zaman kanshi.

Aiko kan bayan isha mutane kadan ne a gidan masu aiki sai aikin tattare gidan suke, Afeefah tayi sallah aka shirya ta again cikin atampha aka Wora mata lafaya aka mi?a ta wurin Mammi, sossai ta yi mata nasiha tana hawaye itama kuka take don bata da bakin godiya ga Mammi, ta yi mata abubuwan da godiya sun yi kadan ta cika mata burinta na ganin ta auru, ta rungumeta ta zame mata uwa da uba ta bata duk wani gata da take tunanin ta rasa to da me zata saka mata in ba da zama lafiya da kuma zuciya Waya jal da Wan ta mafi soyuwa a gareta ba? Sossai take kuka tana tuna mamanta da Aunty zee ina ma Aunty zee na nan ta ga wai Afeefah ce a Wakin miji? A haka aka kaita Wakinta da Adu'a a Bakinta.

Mammi waya ta Waga ta kira shi, ba'a yi mintuna biyu ba ya shigo sanye da kananun kaya ash har da hoodie don zazzabi yake ji tsabar hayaniyar da yake ji ya mishi yawa ya saukar mishi da ciwon kai sossai.

"RAYYAN...."





=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*33*

"Rayyan a yau Allah ya nufa ka sake samun wani nauyi a kanka bayan nawa da na ?annenka, na san ba wai ka ganta bane ka ji kana so har aka yi muku aure Allah SWT ka ba zaSi shi kuma ya zaSa maka abinda ya fi dacewa da kai da kuma rayuwarka, idan har ka ci amanar ta ko ka ha'inceta ba ita ka yi wa ba Allahn da ya baka shi ka yi wa, kar ka kalleta domin ni, kar ka so ta domin ni, kar ka yi mata wani abu na alfarma domin ni duk abin da zaka yi mata ka yi saboda Allah, idan ka so ta ka so ta saboda Allah don Allah ba don ni ba ka ba marar Wa kunya. Ka zame mata gatan da ta rasa, ka zama uwa, uba kuma jigo a rayuwarta, ka zama majingina a gareta ka tallafi rayuwarta daga cikin duhuwa zuwa haske madawwami"

A hankali ya Wan Wora

26 / 53