HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   43 / 53

126K to 129K   out of 158.4K words

ya mishi nauyi ainun, gefen cikinshi ya ri?e mishi sossai amma sanin dalili tunda shi likita ne bai wani damu ba ya haWa mata ruwa mai zafi, ya dawo gadon ya Wauketa kaman 'yar baby.

"Matar Saraki..! Afeefah... Kina ji na? Zan saka ki a ruwa compose yourself kar ki ji zafin a bazata! Am so sorry Ya Saraki bai kyauta ba, Yafam boWWi am"(ki gafarceni kyakyawata)
Da wani irin sloww tune yake maganan a kunnenta kan ya saukar da ita a hankali cikin ruwan, wani irin ?ara ta saki tana rirrikeshi za ta tashi ya shiga ciki ya danneta kawai ta kife kanta kirjinshi tana girgiza wa cikin azaba da kuka mai ratsa zuciya, hautsinannen gashinta da ya gama wargaza wa yake shafawa zuwa bayanta yana hura mata iska a kunnen yana whispering
"sorry, am so Sorry My love."

Sai da suka yi ruwa uku a tare tana li?e bisa kirjinshi idanunta a rufe rufff kan ya sakata tayi niyya suka yi wankan tsarki, a towel fari ?al yayi wrapping Winta ya sake Waukar ta zuwa kan cushion ya ajiye ta, har lokacin bata buWe ido ba kuma bata bar kananun kuka ba shi kuma bai bar lallashi da ban ha?uri ba, gadon yaje ya chanza musu bedsheets.

A gabanta ya tsuguna bayan ya Wauko magani, bata ma san ya zo ba don har bacci ya fara fusgarta na wahala kawai taji hannunshi cikin towel Win ya shafa cikinta ta Wan zabura sbd har lokacin hannunshi da sanyi ta buWe ido sai suka haWa ido tayi saurin rufewa yayi murmushi

"Tashi ki sha magani 'yar albarka..!"
Bata motsa ba shi ya Wago ta zata fara kananun kuka ya sanyata jikinshi ya shiga bata tea din da ya saisaita zafin ta sha sossai kan ta sha maganin, a maimakon tayi shiru ma sai ta sake fara wani kukan.

"Am sorry My love, har yanzu baki ji sassauci ba?"
Ta gyaWa kai tana hawaye don ita kaWai ta san me take ji, shima kuma ya san jarumar mace yake tare da ita tayi matukar ?o?ari, a hannu ya dau?eta bai damu da su sa wani kaya ba suka koma kan gadon ya shimfiWeta bisa kirjinshi
"Sannu Ch?ri am(My darling) in duba in gani ko kina bu?atar stiches?"

Ta ma?e kafada za ta fara kuka yayi murmushi mai sauti kan ya shiga shafa wet gashinta da yayi mishi laushin taSawa saboda bai bushe ba, a kunnenta yayi whispering
"Afeefahh kin san Bugawar zuciya alama ce ta mutum na raye ko? Toh kece bugun Zuciyata wanda hakan ke nufin idan babu ke a zuciyata babu ni zan iya amsa kowace irin tambaya a game dake saidai tambaya daya da ba zan iya amsawa ba ita ce wane irin so na ke miki, wannan tambaya ba zan iya amsata ba domin ni kaina ban san wane irin so nake miki ba abin da kaWai na sani game da yadda nake jinki cikin jinina shine ba zan iya cigaba da rayuwa ba idan har ba'a tare dake ba. Afeefahhh idan har rayuwa ba za ta yiwu babu iska ba haka nima ba zan iya zama mai rai ba tare da ke ba, ke ce rayuwata Gimbiyata"

Duk giyar soyayyarta ya saka yana jin kome ya faWa mata yayi kadan wurin bayyana abin da yake ji, kuka take ba na bakin ciki ko ciwo ba kukan farin ciki take, tana kukan alfahari tana kukan isar ta macen da aka iya macewa a cikin begenta, tana kukan mallakar wannan gwarzo namijin da bakinshi bai yi nauyi ba wurin shimfide mata sirrukan zuciyarshi, rungumeta ya sake yi tsamm yana shafata cikin bege
"Allah ubangiji ya kula min da dukkan lamuranki na rayuwa, yadda kika shayar da ni garWi da za?in zumanki ubangiji ya shayar da ke ruwan alkausara... Thank you so much Habeebty a yanzu you are not just the part of my life you are the owner of my heart, ki yi bacci Habeebty kiyi bacci cikin salama"

Da wannan kalamai haWe da tarin lallashinshi mai tsadar gaske bacci ya Wauketa. Ya jima sossai kawai yana kwance in ta motsa sai ya sake shigar da ita jikinshi kaman za'a raba su ne ya yi pecking tsakiyar kanta, sun so su makara don ?arshen ta a gida ya ja su sallah bayan ya kaita tayi alwala, wani ba?in Oman jallabiyarshi mai adon gold ya saka mata sossai ya mata tsawo ya Wauko mata hijab Winta ya saka mata shima ya saka jallabiya ya ja su sallah, suna idarwa ya janyota ta kwanta a kan kafafunshi ya zare hijabin yana shafa gashinta yake musu azkar duk su biyun don da kyar tayi Sallar saboda bacci da zazzabin da bai gama sake ta ba, tuni ta yi baccinta peacefully har ya gama ya dau?eta ya mayar da ita gadon yana kallon pale fuskarta.

Idanu ya lumshe yana sauke numfashi, a duk sadda zai ganta wani sabon ?auna da mararinta yake ji yana kwarara cikin zuciyarshi, hannunta ya ri?o yayi pecking ya sake yi mata peck a Goshi kan ya mi?e ya fito, hadiman da suke share share da goge goge suka zube ?asa suna kwasar gaisuwa, ya Wan shafa kanshi ya ce

"Ammm yau gabaWaya na baku hutu, ina so ku koma sashenku kuyi duk abinda kuke so sai dare ku dawo"

"Godiya muke Yariman Matasa! Godiya muke Ciroman fombina Allah ya kara girma da arziki Allah ya biya bu?atu"
Kai kawai ya gyaWa suka mi?e suka fice shi kuma ya nufi kitchen.

Abeeha da zata fito kenan ta ji yana koran hadimai ta koma ta buga jannah da ke shirin komawa bacci
"Wallahi barin sashen nan ya kama mu Addah jannah... Me afkuwa ta afku ga Ya Rayyan chan kitchen zai dorawa gimbiyarshi breakfast "

Da sauri jannah ta mi?e zaune cike da zumuWi tace
"Keeee Ya Rayyan Win?"
"Shi fa wallahi, hmmm ai na san jiyan nan ba lallai a wanye ?alau ba, bawan Allah Saraki a waje Hadimin Afeefah a gida"
Suka kwashe da dariya jannah na cewa
"Kin ga irin su Yayan nan hmmm ki bar su kawai... Maza shirya bari nima na shirya mu koma sashen Ammi for today mu bar su su ?one in sun ga dama"
Abeeha na dariya ta shiga toilet wanka ji take zuciyarta kal kal, basu fi mintuna talatin ba suka bar sashen abin su.

Shi kam bai ma sani ba yana kitchen, plantain yake frying amma minti minti zai saki murmushi yana tuna moments Winsu na jiya, ji yake ma yana kewanta a jikinshi daga Fitowar shi Wakin zuwa yanzu, sai da ya gama ya haWa mata spicy egg sauce mai Wan yawa, ya yi toasting bread with butter very soft and simple kan ya shirya plate Win with so much love don burin shi kawai ya ga tana murmushi burin shi ya ga ta ji daaWi kuma tayi alfahari, clean tray mai kyau garai-garai ya samu ya ajiye plate Win ya hada da tissue ko za ta bukata wrapped with cutlaries.

Dube dube ya fara har ya samu wani drawer mai dauke da notepads masu yawa da Pen sbd specifying objects, rubutu yayi a jiki ya manna a gefen tray Win ya hada tea mai kauri sossai ya ajiye kan ya Wauka ya nufi Wakin.

A gefen bedside ya ajiye ya yaye mata duvet Win har lokacin riganshi ne jikinta, ganin tana baccinta peacefully ya shafa fuskarta motsi ta fara a hankali har dai ta buWe idanunta da suke kumbure ta sauke bisa kanshi ya sakar mata kyakyawar murmushi
"Good Morning My Queen, My greatest blessing and the reason i believe in love..."

Duk yadda bata so murmusawa ba sai da yayi escaping ta tsinci zuciyarta da dumbin farin ciki wane takarda.

Mi?ewa tayi zaune tana sau?e kanta ?asa haWe da fara wasa da hannunta tace
"Good Morning"
Bai matsa mata ba ya san kunya ke Wawainiya da ita shi ko a jikinshi ya Wauko tray Win ya ajiye mata a kan cinya zai yi magana wayanshi ya shiga ?ira ganin mai martaba ne da kanshi ya sa yayi picking yana fita daga Wakin don dole zuwa parlor.

Note Win da yayi rubutun ta Wauka ta shiga karantawa.
"Na shirya miki wannan karin kumallon ne da tarin soyayya, kina da muhimmanci sossai a rayuwar Ryan. Allah ya albarkaceki da farin ciki da lafiya kullum, Ina ?aunar ki!"

Zuciyarta ta sa hannu ta dafe, kaunar ya mata yawa ji take ta ma rasa me zata yi sai sake karantawa take tana murmushi. Adanawa tayi ta dauki fork ta fara cin abincin da ya shirya mata da hannayenshi, loma biyu tayi sai gashi ya dawo yana zama gefen ta
"Afuwan mai martaba ne ya kira ni ko yau zan samu fita ran gadi da shi"

Kai ta gyaWa tana sakar mishi cokalin bata ce komai ba don ya riga ya sanya hannu cikin nata ya karSa ya cigaba da bata cike da kulawa yace
"Kin san me na ce mishi?"
Kai ta girgiza
"Ce mishi nayi yau yini na, magana na da duk wata kulawa tawa naki ne ke kaWai saboda kin bani abu mafi daraja a rayuwarki..."
Da sauri ta kalleshi tana zaro idanunta waje gabaWaya ya saki murmushi mai kyau har hakwaranshi na bayyana tace kaman za ta saki kuka
"Da gaske haka ka faWa mishi?"

Hancinta ya lakace
"Gashi na saka ki kallona da waennan idanun da suke kashe ni, kuma na ji wannan murya taki mai kaman sarewa..."
Bata san tayi murmushi ba shima ya cigaba da yi har ya gama bata.

"Mu je in miki wanka..!"
Ta zaro ido
"Zan iya wlh"
Tayi saurin faWa a ShagwaSe ya kalleta
"Ya daina zafi? Kin tabbatar za ki iya tafiya?"
Kai ta gyaWa ya dage tray Win ta sau?o tana Mi?ewa tsaye ta ri?o shi jin tana shirin faWuwa wani Sharp pain na shigarta, ya ajiye tray Win yana saSarta

Duk rigima da ShagwaSar da tayi ta mishi dole suka yi wankan ta lura ita ce ke mutuwa da kunya shi ko a gyalen shi tattalin ta yake wane ?wai, shi ya dubo mata wani kaya ta saka Dukda ma ba masu nauyi ba a parlor ya ajiye ta ya kunna mata Tv wai tayi kallo bari ya zo, har ya tafi ya koma yaje ya Wauko mata popcorn ya zo ya bata yayi pecking goshinta kan ya koma Wakin nashi ta bi bayanshi da kallon ?auna tana murmushi cike da tarin farin ciki....






=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*52*

https://chat.whatsapp.com/HUJI7tg9TOU941grP60r4S?mode=ems_copy_c

Kinaneman group din dazaki ringa sarinkayan kitchen cikin farashin sari...tayadda koda kinje kasuwa bazakisamu kasa d farashinmuba snn zaki iyazuwa har hargida kisayi dukkan kayan dakike bukata cikin kwanciyar hankali kokisaya ayimaki delivery zuwa dukkan inda kike afadin Nigeria da dama makotan kasashenmu kikarbi kayanki cikin farinciki da aminci!!!.....kiyi joining a mai nono kitchen utensils and household........gaskiya d amana sune takenmu!!!=?O?
*****

Ga mamakinta bai fita Win ba ya tabbatar mata da gaske yake ya cewa Abeey bata da lafiya ba zai iya yin nesa da ita ba, kunya ya rufe ta amma shi ko a gyalen shi da kanshi ya gyare Wakin tsaff ya wanke beddings da suka Sata kan ya dawo yayi joining Winta a parlor hannunshi da mug yana sipping tea, da kanta ta kai kwance jikinshi ya mayar da hannunshi Waya bayanta ya rungumeta suna kallon a tare hasken parlorn a kashe Dukda hantsi ce amma yadda curtains suke rufe kirib rip hasken duk a kashe sai ya ba da wani yanayi kaman cinema.

Film din ya ?are amma bata sani ba saboda ta yi nisa cikin tunani, hawaye kuma na bin fuskarta har take ji kaman zazzabinta zai dawo sabo, kula da hakan da yayi ya Waga mishi hankali ya Wago fuskarta yana kallon ruwan hawayen da take yi
"Afeefah lafiya? Me yasa kike kuka haka?"

Yana maganan ne yana Wauke hawayen da palms Win shi wasu na gangarowa, a hankali tace
"Twins na cikin film din nan sun tuna min da Suhail da Suhaila ne, ko ya suke? Na san yanzu sun girma, ko suna maraicin uwa kaman yadda nayi? Ko suna samun farin ciki duk ban sani ba..."
Fuskarta ya saka cikin tafukan hannunshi guda biyu ya matso sossai har suna shakar numfashin juna chan ?asa cikin Muryar rarrashi yace
"Ba kin rabu da su ba kenan har Abada Bebe..! Za mu koma in shaa Allahu za mu je mu gansu a tare ki daina zubar da hawayen nan, they are priceless to me..."
Yana kai nan yayi leaning tare da fara Wauke hawayen da harshen shi cikin wani salo da ya sa ta sake ?an?ameshi, daga nan ya sau?ar da lips dinshi a kan nata da baya gajiya da su, sai da ta ga yana ?o?arin Waukar wani hanyar ta zame tare da kwanciya kan jikinshi ya rungumeta suna sau?e numfashi a tare.

"I love you...!"
Ya raWa mata a kunne, ta Wan yi murmushi bata ce komai ba.
"Na jima ina son na baki ha?uri kan wani laifi da na miki"
Ta Wan Wago kanta tana kan jikinshin
"Me kayi min Ya Saraki?"
Ya kai hannunshi Waya yana wasa da gashinta da ya ki yarda ta saka hula idanunshi na a kan fuskarta yace
"Ranar da kika fara gani na i scared you alot da har na kan yi sensing tsoron ki a duk sadda kika ganni ko kika ji muryata, that time i was very upset sai nake ganin kaman idan da akwai wanda ya fi cancanta da kashe kanshi ni ne but why you? ?ar karama dake da wannan Wanyen hukuncin? Raina ya Saci da na yi kwanaki da takaicin da ban san na menene ba, i wanted to go back to the hospital ko in kira Saleem amma na danne kawai ban yi hakan ba, daga baya i saw you at saleem's place da yake ba ni labari i was shocked sai dai sanar da ni da yayi yana sonki ya sa na miki murna a lokacin bcs na san shi mutumin kirki ne ?warai sai kuma matsalar mommy ya yi striking"

Ta Wan yi murmushi har lokacin tana kallon fuskanshi yadda yake magana da ma yadda yake wasa da gashinta na kara dulmiyar da ita a kaunarshi tace
"Dukda na ji tsoro sossai da reaction Winka to tell the truth shine yayi sanadiyar gane kuskurena, reaction Winka ya fahimtar da ni ba karamin kuskure nayi ba a yunkurin kashe kaina da nayi... A lokacin bani da yadda zan yi Afeefah Mayya ce kuma annoba ce ba Afeefar yanzu ba"
Yayi murmushi da yayi mishi kyau sossai
"Har yanzu ma ai ke mayyar ce!"
Ido ta zaro, ya kai hannu ya lalace mata hanci
"Eh mana! Gashi kin lashe min zuciya"
Bata san ta saki murmushi mai sauti ba tana Wan hararanshi yayi pecking idanun yana sake rungumeta.

"Ka san kuma da gaske na ri?e ka? Har ma sunanka marar kirki a zuciyata.."
Ya Wago ta ta zauna yana kallon fuskarta
"Seriously??"
Ta gyaWa kai
"Na fahimceka ne a sadda Mammi ta sanar da ni wanene kai!"
Shiru yayi, ta sa hannunta ta ri?e nashi biyu
"I hope yadda komai ya wuce a tawa rayuwar kaima za ka bar komai ya zama tarihi Ya Saraki!"
Shiru yayi bai ce komai ba, ta san halin kayanta bata so tayi zurfi a maganan ranshi ya Saci amma ta fahimci yar tsamar da yake yi da mahaifiyarshi kuma rayuwa ba zai taSa tafiya a haka ba, dole ne zai bar komai ya wuce kaman ba'a yi ba ta sani ba at once zai chanza ba amma a hankali dole zai wuce Win...

Baya baya tayi ta jingina bayanta da jikin hannun kujerar bayan ta saka pillow sai ta wara mishi hannu, a hankali ya kai kwance kanshi na sauka a kan kirjinta ta saka hannayenta biyu tana shafa kanshi zuwa bayan wuyanshi shi kuwa ya lumshe ido yana ji kaman ya Wauketa su koma Waki don kunna shi take ba tare da ta sani ba.

Sun jima sossai a haka kan ya ce
"Kin san mene?"
Ta ce
"uhm uhm"
Tana cigaba da wasa da gashin keyarshi
"I love hugging you, a duk sadda kika rungumeni sai na ji kaman mu dawwama a haka a tare, I just wanna lay here on your chest forever"
Sake rungumeshi tayi tana jin kalamanshi masu tsada na sake samun matsuguni a ranta, ita kanta tana mamakin kanta amma an ce komai wuri yake samu a yanzu da yake nuna mata so da kauna sai taji she can go any extent don ganin ta faranta mishi itama, tsoron da take mishi ya kau sai taga kaman ba shine ke bata tsoron nan ba, kaman ba shine take shakkar ko tari a gangarshi ba.

Suna parlorn har azahar ya fice masallaci ita kuma taje Waki tayi Sallarta, bata so ya dawo yace zai yi girki don haka ta wuce kitchen kawai daga Wakin bata cire hijabinta ba don rigar jikinta wani iri yake sakata ji bashi da maraba da babu, har lokacin ba wai ta dawo daidai bane amma tana ga responsibilty Winta ne samar masa abinda zai ci.
Mai ta Wora a wuta ta kawo ?oda da ta yanka 'yan daidai ta zuba, suna cikin soyuwa ta fara yanka sausage suma bayan ta kwashe kodar da ya soyu ta zuba sausage Win shima sai da yayi ta kwashe ta zuba shrimps da ta wanke tsaf ta soya su ta kwashe, ta kawo tomato patse ta zuba cikin man ta fara soyawa a gefe tana markada kayan miya da suke a frigde a gyare already sai da tomato din ya fara za?i kan ta juye kayan miyan a kai ta fara seasoning da su curry, chicken seasoning da dai duk abinda zata bu?ata kan ta kawo soye soyenta na Wazu ta zuba cikin sauce Win ta juya tare da rufewa ta nufi basmati Rice dake kitchen Win kofi biyu ta diba ta tafi bakin sink tana cikin zuba ruwa don wanke shinkafar ya shigo.

"Kin yi laifi!"
Ya faWa yana nufarta, ta kalleshi ta saki murmushi
"Tuba nake Ciroman duk duniya!"
Hijabin ya zare mata ya koma ta bayanta yayi hugging Winta hannunshi Waya na zagaye kwankwasonta
"Meyasa kike girki a yau? Ba ki san na haramta ba?"
"Ba wani abu mai wuya

43 / 53