HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   49 / 53

144K to 147K   out of 158.4K words

murmushi tace
"Ka fa san wacce nake nufi ko baka san sunanta ba?"

"What name? Afeefahhh ita kaWai na sani, Afeefah kamal Its the only name i learned nd i call.." Yayi maganan yana lakace hancinta idanunshi na tabbatar mata da sunanta kaWai shi ya sani a duniyarshi.
Za Ta sake magana ya haWe bakinsu sai da ya tabbatar ta manta da maganan wata zarah kan ya zare bakin yana rungume da ita suka yi bacci cikin natsuwa da tarin ?auna.

Washegari da safe shi yayi mata breakfast don da asuba ma bai barta ba duk jikinta ya mata laushi, bayan ta karya yayi wanka ya shirya cikin wasu fararen kaya da suka amshe shi ?warai da gaske ga mamakin ta ta ga ya Wauko wani alkyabba silver ya saka da yayi mugun yi mishi kyau, baki ta saki tana kallonshi sai ya Wauko wani takalmi shima silver da ya fi yanayi da na saurata ya saka ya saka hula kan ya zauna ya naWa rawani.

"Tabarakallah Masha Allah!"
Ta ambata tana sau?e numfashi idan ba Allah ba waye? Waye ya isa kera irin wannan jarumi, santalale kuma kyakyawar namiji haka mai zati da kwarjini? Bayan nan kuma ya Wauka ya bata matsayin miji! Alhamdulillah ta sake ambata bata san ya iso ba sai hura mata iska da ta ji yayi a fuska ta lumshe idanu tana sake buWewa a kanshi hannu ta Waga a dunkule ta shiga furta mishi kirari.

"Ado da kanshi ya sara maka Wawisu...Barden maza in ka fito ya?i ya kare, mari babban kifi maganin hadamammu...bangon duniya sun yi iya yinsu sun kasa Huda ka, Allah ya bar mini kai jarumin jarumaina...!
Mai sarauta da halin girma.
Tauraron sarakai jigon Afeefah
Saraki kai gaba kai musu nisa kamo ka sam sam ba su iyawa sarakai duk suna a bayan ka..! Allah ya ja da zamanin Ciroman duk duniya Yariman matasan Fombina...kare ka angon Afeefah"
Sossai yake murmushin da ya sake tafiya da ita ya du?a yayi pecking goshinta yace
"Duka wannan kirari nawa ni kaWai Matar masu sarauta?"
"Duk kirarin da zan ma ka wuce nan Sarakina! Allah ya bar mini kai har aljannah"
Ya shafa fuskarta yana kallonta har lokacin cikin towel take ya shafa idanunta da suka sake haske da sheki zuwa lips Winta da ya mayar da su cherry Red tsabar yadda ya fitine su ya furta

"Zan fita, ki kula min da kanki har zuwa dawowata kar kuma ki manta da cewa Saraki na ?aunar ki... Your eyes, your voice, your smile kai komai da komai i just love everything about you"
Ta sau?o tana gyara towel Win ta Wauko turare ta sake fesa mishi tana murmushi tace
"I love you more takecare, sai ka dawo"
Kaman kar ya tafi haka ya fice ta koma ta zauna tana murmushi.

Yana fita kai tsaye Fada yayi fuskarshi a haWe ya shiga dogarai suka fara mishi kirarin isowa, karon farko da ya zo fadan tun naWinshi shi karan kanshi Abeey ya ji mamakin ganinshi haka, a gaban mai martaba ya du?a
"Barka da safiya Your majesty..."
Sarkin dogarai zai amsa sarki ya Waga mishi hannu
"Barka dai Ciroma, ina Fatan lafiya don da ganinka akwai magana fal a bakinka"
"kwarai kuwa Adalin sarki, na zo ne zuwa na musamman a yau... Na zo ne in shigar da ?ara ina kuma fata wannan sarki mai adalci zai yi mana hukunci daidai da tsarin addini bisa adalci irin nashi"
Gaban mai martaba ne ya faWi, ya riga ya san binciken da Sameer ke yi amma baya so ko ma menene a kawo shi gaban fada shi kuma Saraki Yana so ne duniya ta shaida ta yadda kunyar duniya da mutanen cikinsa kaWai ya ishe su kan su gamu da na lahira, yana sane yayi hakan kar ma Mai martaba yayi tunanin Afuwa saboda zumunci ko wani abu...

"Na zo ne in shigar da ?arar Makama, Madaki da Fulani Adama bisa laifin zamba cikin aminci, yaudarar masarauta, cin amana, zalunci da kuma kisan kai... Sun cutar da wannan masarauta kuma sun cutar da sarki tsawon shekaru a yanzu kuma sun cutar da abinda bai kamata su cutar ba... A Yanzu kan shari'a tayi nisa nake shaida cewa na yanke alkawarin aure dake tsakaninmu da zuri'arsu don zuri'arsu basu da nagartar amsa sunan sarauta har abada"

Kallon kallo aka shiga yi cike da dumbin mamaki yayinda Makama da Madaki zufa ya shiga yi musu wanka, gabansu ke faWuwa amma Makama ya dake ya ce
"Wani irin zance kake yi Ciroma? Kar fa ka manta waenda kake zargi da waennan muggan ayyukan ba tsaranka bane kuma iyaye muke a gareka... Daga dawowarka zuwa yanzu har ka isa shiga lamuran da baka sani ba? Ka kiyaye don ba za mu yafe sharri ba ko daga waye kuwa.."

Yayi murmushi ya ce
"Sanin kun taka matsayin iyayen nawa shi yasa na kawo zancen inda za'a yanke hukunci da wasu ne chan. Hmmmm...."
Mai martaba ya katse shi
"Mecece hujjarka na wannan zargi Ciroma?"

"Ina da tarin hujjoji amma kan nan ina so a gurfanar da Fulani Adama gaban fada a kuma gayyaci duka matan LaamiWo don duk ya shafe su"
Sarkin gida Mai martaba ya kalla tuni ya fice, duk fadan ana zaune shiru kowa da abin da yake sa?awa yayinda su Makama ke zare idanu suna kuma haWa gumi da tsoron abinda wannan karamin alhakin zai iya yi musu.

"Kaman yadda kuka sani gabaWaya bana Waga kafa a zalunci kuma ko wanene muddin na same shi da zalunci na kan hukunta shi ne daidai da laifin da ya aikata ban cire kowa ba, Ciroma ya shigar da karar Makama, Madaki da kuma Fulani Adama bisa zargin cutar da iyayenshi da matar shi za mu so jin hujjojinshi don yin hukunci daidai da laifukansu idan kuma muka same shi da son bata suna ko wasa da hankalin wannan fada shima za mu yanke mishi hukunci daidai da laifinshi. Muna sauraronka Ciroma"

GaabWo ya kalla sai ya mi?e da sauri ya fita, idanu Fulani Adama ta zuba mishi tana jin wani irin tashin hankali na rufe ta, da alama kallon biri take yi mishi shi kuma yana mata kallon Ayaba, a zaton ta ta toshe duk wani hanyar da zai iya sunce mata zani a kasuwa sai ya ke kokarin nuna mata shi Win mai zamani ne dole ta kiyaye shi. bata gama tsurewa ba sai da ta ga wasu sojoji mata biyu sun shigo da rahane da aka chanza mata kamanni ko tsayuwa bata iya yi suka gurfanar da ita, zabura tayi sai kuma ta koma yaraf ganin An sake shigo da wani mutumi an yi mishi Waurin huhun goro Dukda shekarunshi, azaba duk ya ishe shi ko motsi baya iya yi mai kyau....

"Kai!!!"
Rayyan ya daka wa tsohon tsawa da sauri ya zube ?asa yana ro?on yafiya cikin kuka.

"Menene ala?arka da waenchan???"
Ya Waga kai ya kalli su Fulani Adama ya ce

"Tsawon shekaru arba'in kenan ina yi musu aiki ba na asiri bane, ina ba su wani magani ne da ya shafi lalata mahaifa, hana Waukar ciki da ma zubar da shi idan ya samu... Sai G...gu..ba. A gafarceni Ranka ya daWe da farko ban so aikatawa ba suka min barazana da 'ya'yana daga baya son zuciya da kudin da suke cika min ya ja ni har na zalunci Sarkin mu mai adalci.... Don Allah a yi min aikin gafara na tuba na bi Allah na bi ku ku yafe min..."
Tsaki Rayyan ya ja ya kalli Rahane
"FaWi bayanin da kika yi min..."

Cikin kuka da tarin nadama marar amfani ta shiga cewa
"Sunana Rahane, ni ce amintacciyar Fulani Adama tun da jimawa amma ba ni na fara yi mata wannan aiki ba mahaifiyata ce da Allah ya yiwa rasuwa, ta bani labari kan rasuwar ta irin son mulki da izza irin na fulani Adama, ta tabbatar min akan mulki babu abinda Adama ba zata yi ba, ta iya makirci kala kala kuma bata bar kowa ba har mai martaba, da fari bayan aurenta da mai martaba ta zaci zata haihu plan Win ta kuma tana haihuwa za ta yi sanadiyar mutuwar shi danta ya zama mai jiran gado sai Allah bai kawo haihuwar ba har ya auri Fulani Aminatou anan ta yanke hukuncin muddin bata haihu ba babu mai haihuwa a wannan masarauta har mai martaba kuwa don haka ta yanke hukuncin yin mai gabaWaya Wai Haihuwa da hanji da taimakon yayanta da ?aninta suka samu wannan mai maganin sadidan yake bata maganin hana Waukar ciki..

A kowani sashe na matan sarki tana da amintacciyar baiwa da take biyan su makudan kudi suke yi mata aikin zuba maganin nan a abinci kowace mace da mai martaba ya aura, tun Fulani Aminatou bata shekara uku ba ta gama da mahaifarta yayinda a fili take nuna tausayi da neman taimako ga mai martaba wanda hakan ya bata matsayi mai girma a idanunshi, Shigowar Fulani FaWimatu ya zame mata barazana don bata yarda hadimai su mata girki ba kuma idan tana yi bata nisa da bakin murhunta hakan yake bata damar Waukar ciki tunda duk abinda ta girkawa mai martaba ma babu maganin, duk ta Wauka Fulani Adama kan san yadda tayi ta sha wannan magani da take karSo wa cikin ya Sare. ko da ta samu cikin farko na yarima Aliyu ta gudu Mambila babu yadda basu yi ba su sayi hadimarta mai rasuwa Hanne ta zuba musu maganin ta ?i har alkawarin kasheta suka yi amma ta ?i amincewa bayan sun dawo masarauta suka samu nasarar ba wa yarima Aliyu guba ya ci ya mutu fahimtar za ta iya tona musu asiri itama suka yi ajalin ta.

Cikin Ciroma Sameer ne ya zo musu bazata don ita kanta mahaifiyar bata san da ciki ba sai da ya girma, sun yi duk yadda za su yi sai dai Zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzuru ana shaho sai yayi dole ya zo duniya, sun so kashe shi yadda suka yi wa Yarima Aliyu amma shi Win murucin kan dutse ne bai fita ba sai da ya shirya ya zame musu kabewar kan ?abari bakin cikin mai taushe, daga karshe dole suka sa mahaifiyarshi ta rabu dashi ala dole don babu yadda ta iya tana so wa danta rayuwa.

Fulani Adama ta fi tsanar Fulani FaWimatu akan duka matan sarki don Cikin lokaci kankani ta lalata wa Fulani Salimah ma mahaifarta ita ce ta zame mata gagara badau bisa kariyar Allah, a farkon aikinta babu asiri babu tsubbu don duk ta fi gane kirsa da makirci amma Makama da ya fi kowa son mulkin yana ganin kaman ko ba jima Ciroma Sameer zai dawo sai ya je yayi mishi asirin da zai saka ya manta komai da kowa, ya mishi asirin da zai ji ko sunan iyayenshi ba zai iya ambata akan harshenshi ba, ya saka mishi tsanar masarauta da sarautar gabaWaya, Kwatsam sai ga shi ya Sullo kaman huduwar rana tafin hannu yayi kaWan ya kare shi sun shiga tashin hankali don basu taba zato ko tsammanin bayyanuwar shi ba tunda an tabbatar wa Makama cewa asirin ba mai karyewa bane don kogi aka jefa aka ba wa tsuntsu wani ya fire sai gashi ya dawo kuma da wata mace.

Anan suka yanke hukuncin aura mishi zarah da haWin Bakinta na daga ta aure shi sarki yayi murabus za su kashe shi su kashe sarkin sai su karbi sarautar har dan Zarah ya girma, kwatsam ta fahimci Fulani Afeefah na da juna biyu, hankalinta ya tashi ta aikeni wurin mai maganinsu inda ya bani magani na kawo sai dai duk abinda aka bata bata ci har sai da Fulani ta yi mata wasu maganganu da suka raunata zuciyarta ta sha fura, a cewar mai maganin sai bayan sati ma zata yi Sari kar ma a zarge ta tunda da wayon ta ba zata bari a lokaci Waya ta zubar da cikin ba dayake Allah ba azzalumin bawan shi ba akwai rabon kamatan dumu dumu bisa laifukanta sai cikin ya Sare a ranar dole aka san me ta ci kuma a ina ta ci inda daga ranar Ciroma Sameer bai bar su sun shaki iska ba.

Ya kama ni aka dinga min horo iri iri bai bar ni ba sai da na faWi komai na kuma kaishi wurin mai maganin aka kama shi... Ku yafemin don Allah ku yafe min na tuba wallahi umarni kawai nake bi don tsira da rayuwata"

Cikin kuka mai tsuma zuciya ta ?arasa.
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..! Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Abinda ke tashi kenan a fadar duka matan sarki kuka suke yi mai tada hankali yayinda mai martaba ya runtse ido yana jin hawaye na sulmiyo mishi, ashe kashe mishi yaro suke niyyar yi shiyasa take kanainaye shi da kissa da komai take cusa mishi son auren Zarah da Sameer? Ya gode Allah da ba'a yi auren ba da ba zai yafe wa kanshi ba.

"Wallahi na yi nadama tun ba yanzu ba amma tsoron hukuncin Fulani Adama ya sa na kasa daina basu magani, yarana sun mutu duk a gobara na auri mata sama da biyar duk suna gudu su bar ni don na kasa basu haihuwa, tun mutuwar yarana na yi nadama amma ban san yadda zan yi ba a gafarceni"
Tsohon ke fada. Fulani Aminatou tace

"Allah ya isa! Allah ya isa tsanina da ku duka wallahi Allah ko da ni kaWai ce zan yafe muku ku shiga aljannah ba zan taSa yafe wa ba"
Fulani Salima ma Allah ya isa take jerawa cikin kuka mai ciwo, mai martaba hawaye kawai yake yi haka Ammi dake jin mutuwar yaronta ya dawo mata sabo.

"Babu aure tsakaninka da Zarah har Abada Ciroma, ku kuma wannan kaWai ya ishe ku tsoron Allah, wannan kaWai ya kamata ya ishe ku ishara.... A tube musu duk wani rawanin zuri'arsu ku kuma shaida na yanke igiyar aurena da Adama a dibe su a kaisu kurkuru mafi azabtarwa na wannan masarauta kan a yanke musu hukuncinsu.... A tabbatar basu samu natsuwa ko kwanciyar hankali ba"
"An gama ranka ya dade"
Sarkin dogarai ya zube ya amsa kan wasu majiya karfin suka shigo suka saSesu ko damar magana ba'a basu ba, kunya da dana sani marar amfani na rufe Adama komai ya kare mata a lokacin da bata yi tsammani ba.

Rayyan ya dubi Afeefah dake kuka ya girgiza mata kai a hankali yace
"Na gode Afeefah. Na gode kwarai ta sanadiyarki asirinsu ya karye idan baki manta ba duk ayoyin da kike yi wa Saleem a tare muke sha Dukda ban san da zaman wani asiri a jikina ba, Kin ba ni babban dama ta sanadiyarki na samu faWa wa Mammi abinda ta jima tana son ji na wanene ni kafin mutuwarta. Ba zan taSa manta wannan taimako naki ba na gode"
Ammi ta rungumeta tana kuka. A haka aka watse zaman fadan mai martaba sai ri?e shi aka yi zuwa sashenshi tuni Rayyan ya ma?ala mishi ruwa don ba karamin hawa jinin shi yayi ba.





=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*58*

Alhamdulillah komai ya cigaba da tafiya normal bayan nan, ta cigaba da lectures Winta cikin kwanciyar hankali kuma tana samun duk wani kyautatawa daga zuri'ar na mijin nata kaman yadda shima yake kara samun kusanci da iyayenshi, Mai martaba ya sha jinya kan ya warke ya tara matan yayi ta basu ha?uri a ganinshi komai ya faru ne sanadin aurenshi da suka yi, sun nuna haka ?addarar su take sai dai Fatan Allah yayi musu sakayya akan Adama, Zarah da bata san komai ba sai da aka warware daga farko ji tayi duniyar yayi mata zafi damuwa yayi mata yawa ta tattara ta koma wurin mahaifiyarta da dukkansu har yan uwanta kunyar abinda mahaifinsu ya aikata ya sa ba sa iya ko fitowa, Ammi bata neme ta ba haka Aisha don tunda har ta yi niyyar auren Rayyan ne don ta cutar dashi su ma suka ji ba za su iya cigaba da hulda da ita ba amma Aisha tayi kuka kaman ta mutu, ta Wauki zarah kaman 'yan biyunta ne bata zaci hakan daga gareta ba.

Maganan yanke hukunci sai da suka yi wata biyu suna cikin na uku gar?ame cikin azabtarwa kan aka yankewa Fulani Adama hukuncin kisa ta hanyar rataya, Makama da asirinshi ya dawo mishi ya haukace damuwarshi kawai a barshi yayi ta tafiya ji yake kaman kwakwalwarshi zai fashe idan bai shiga duniya ba dukan da yake yiwa Madaki yasa aka raba musu Waki, shi Madaki da sauran hadiman an yanke musu life imprisoment iyalan su sun yi kuka kaman ba gobe amma bahaushe ya ce tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan yi wa dukan tsiya.

Soyayya tsakanin Saleem da Aisha yayi nisa don har ya turo mai martaba yace za su yi fixing rana sai a haWa da na Ameer da ya kasa komawa da Abeeha dake shirin gama makaranta, Jiddah dai da tayi mugun kewan su sai dai a haWu a yi ta waya. Yau ya kama ana ya gobe Afeefah za ta gama First semester examination Winta kuma Rayyan ya tabbatar mata a satin za su fara shirin tafiya Kaduna don ta matsa mishi sossai akan komawa ga su Suhail da kuma su kawu Dukda shi ba?in cikin kawun bai taSa wankuwa mishi a rai ba sai dai bai hanata ba don haka mai lalle ta nema Ammie ta turo mata har sashenta.

Tana zaune da dogon wando da wani shirt Black na ma Rayyan Win ne daga ganin girman da yayi mata amma ta fi jinta comfortable ciki, ta Waura Black dan kwali a kanta an gama lallen kafa da hannun duk an saka leda su Aisha na gefe suna ta hirar su da ta shafi rayuwa har jan ya kama aka cire mata sai aka zana mata ba?i a bayan hannun don ta ce jan kawai ya isa a kafafun yarinyar kwararriya ce kuma lallen ya mugun kamawa yayi maroon sharrr kaman ka sace kafafun in ka gani, Rayyan ne yayi sallama ya shigo duk suka mishi sannu da dawowa daidai an gama ba?in kenan ya tsaya yana kallon hannun kan ya ce

"Wai tunda

49 / 53