HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   14 / 53

39K to 42K   out of 158.4K words

sun tsorata basu taSa tunanin za ta iya kai hannunta jikinsu ba don ita Allah yayi ta da tsananin son yaranta, hawaye take yi ta sake cewa saleem ya maimaita
"Mommy... Mommy da gaske zuciyata ta kamu da Soyayyar Afeefah da ba na tunanin ko wani hukunci za'a yi min zai sa ta fita daga ciki, mommy kila sai kin cire zuciyar gabaWaya daga kirjina za ki daina jin harshena na furta kalmar ?auna zuwa gareta..."

Wani irin kuka Sameerah ta fashe da shi, a yanzu ta yarda ta yarda ba wani asiri don tabbas abin da take ji a kan Sulaiman shi ke azabtar da Saleem tunda har zai iya mayarwa mommy magana sau uku, Mommy ta sake Waga hannu zata mareshi sadiqa ta ri?e hannun tana hawaye
"Mommy ba shi za ki daka ba ga Mayyar da ya kamata ki kassara chan, wallahi Afeefah sai kin bar gidan nan ba za ki tarwatsa mana gida ba"

Afeefah dai ta rasa yanayin da take ciki, wani irin ?auna da tausayin saleem ne suka sake mamaye zuciyarta ko tunanin inda za ta nufa in sun kore ta bata yi, damuwarta saleem idan suka raba su basu mishi adalci ba, shi ya cancanci bautar ta na aure har mutuwa.

"Saleem!"
Mommy ta kira shi karo na ba adadi muryarta har yanzu da wani irin mamaki, idanunshi da suka sauya ainun ya Wago ya kalleta tamkar ba soja ba wani irin rauni ya bayyana karara a fuska da idanun nashi.

"Saleem!!"
Ya amsa a hankali
"Saleem!! Sau nawa na kira ka?"
A hankali yace
"Uku"
"Wannan ba aikin hankali bane na asiri ne, amma ko da asirin ai ka san matsayi na a wurin ka ko? Ka san ni wacece ko?"
"Mommy ke mahaifiyata ce kina da darajar da babu wanda yake dashi a wurina duk faWin duniyar nan. Kin isa da ni kuma na san za ki so farin cikina! Mommy a yanzu ba na jin ina da wani buri da zai haifar min da farin ciki kaman Afeefah, ban san sadda sonta yayi min wannan kamu ba don ba ya shawara kan ya shiga wallahi ina sonta! Ba zan iya rarrashin zuciyata ba don so bai san rarrashi ba..."

"Afeefah Allah ya isa tsakanina da ke! Allah ya isa"
Mommy ta faWa tana kuka. A lokacin hawayen da saleem ke danne wa suka gangaro ya Wago ya kalli mommyn zai yi magana ta daka mishi tsawa a kan ya mata shiru
"Aure kake so zan Waura maka aure da yar Wan uwana Sabreena da take sonka tun bata san kanta ba, amma soyayya, magana ko zancen aure tsakaninka da wannan yarinya saleem har Abada, ko bayan raina ne Allah ya isa ban yafe ba! Wallahi wallahi sai na iya tsine maka ka sake shiga huldar yarinyar nan ko a hanya kuka haWu ban yafe ba ka mata ko da sannu ne... In har ni na haif...haifeka Saleem sai dai in kana da wata uwar za ka iya"

A razane yake kallonta, ta share fuskanta ta dubi Samha
"Je Wakina ki Waukomin akwatin da ya fi kowanne girma"
Da sauri ta tafi, Sameera zuciyarta ne ke tsitsinkewa a yanzu tsoro ne ya rufeta, wlh tana iya jin irin abin da saleem da idanunshi ke runtse yake ji a yanzu, gabaWaya jijiyoyin kanshi sun mimmi?e girgiza kai take yi
"Mommy don Allah ki dakata! Ki tsaya kar azabar yayi mana yawa... Ki barta don Allah ko bai aureta ba ta z..."
Sadiqa ce ta kai mata duka
"Kema asirce ki tayi don ?aniyarki? Wallahi ta gama zaman gidan nan"
A lokacin Samha ta shigo da wani cream trolley.

Mommy ta karSa ta jefa mata
"Na tsani ganin ko inuwar ta ne, ku gaya mata ta tattari duk taeukucenta ba na son ganin ko ?yallenta a gidan nan kar ma ta dawo cikin dare ta kama wani biya... Har Abada ko magana ta yi wa dana sai na tabbatar ta kare rayuwarta a gidan yari"

Ko gwada ro?on su bata yi ba don ta san ko sama zai haWu da kasa a yanzu mommy ba zata amince da hakurin ta ba, kuka mai sauti take yi jikin saleem ne ya fara rawa, ba zai cigaba da sauraron kukanta ba ba zai iya ganin tafiyar ta ba, zuciyarshi tamkar zai fashe saboda tsoro da fargaba in ta fita ina za ta je? Wa ta sani a duk faWin Kaduna? A hankali ya mi?e jiri na kwasar shi a dafe da gini ya cigaba da tafiya har ya bar Wakin zuwa lokacin da gaske yake hawaye, hukuncin Mommy tamkar zare mishi farin ciki tayi a wannan rayuwa, tamkar ta kulle shi ne a magar?amar da ya fi kowani magar?ama duhu da azaba.

Afeefah ta haWa komai nata, wayar da saleem ya saya mata kawai ne ke ri?e hannun mommy kan suka tasa ta gaba har wajen gate, ta jima tsugune a wurin tana kuka kan ta mi?e ta share fuskarta ta ja akwatin ta fara tafiya.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel...! Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Abin da take ta nanatawa kenan tana share hawaye ta yi tafiyan da bata san adadi ba har ta fito wani babban hanya dake dauke da ababen hawa fiye da cikin unguwar da ta bari, nan ma mi?awa kawai tayi ta cigaba da tafiya ko biyar babu a hannunta, ta fi awa biyu tana tafiya janye da trolley Win lokaci lokaci ta kan share hawaye masu zafi dake zuba mata, a daidai wani wurin ba da hannu ta tsaya ta Waga kai ta kalli garin, mutane ne ke ta hada hada kowa harkar gabanshi yake yi, daidai wutan ya nuna ja motoci suka tsatsaya wani daga gaba yayi kokarin kin bin doka sai hatsari ya faru a wurin tuni go slow ya wani irin haWuwa.

Tana tsaye har lokacin rike da akwatinta kamkam sam bata san me za ta yanke ba, bata san ya za tayi ba kaman an ce ta Waga kai sai idanunta da suka zama wasu iri tsabar kuka suka shige cikin nashi daidai yana sau?e glass, kallon seconds biyar suka yi wa juna ya Wauke kanshi ya mayar gaba yana tsaki, ita kam bata dauke kai ba sai take jin kaman ta je ta ro?e shi ya taimaka mata ko da ya haWa ta da Sulaiman ne, amma kuma Sulaiman ai bai san wacece ita ba idan su ma suka kore ta fa? Innalillahi wainna ilaihi rajiun ta sake faWa hawaye na silalo mata daidai ya sake kallonta idanunshi suka sau?a kan hawayen a lokacin suka samu hanya ya ja motar ya bar wurin.

Juyawa tayi ta cigaba da jan trolley Win dama ta sani bashi da kirkin saleem, babu mai kirkin saleem ma a duniyarta shi kaWai ta sani mai kirki, daidai ta zo gaban galaxy mall da ta gani rubuce sama za ta wuce sai tayi karo da wata mata, baya baya matar tayi za ta faWi Afeefar tayi hanzarin sake akwatin ta ri?e ta
"Subhallah! Ki yi ha?uri"
Ta faWa cikin dasasshiyar muryarta, sai ta ga matar ta kasa tsayuwa numfashinta na ta kai komo ga ta dai cikin shiga na alfarma har da jaka a hannunta
"Lafiya Aunty? Ko baki da lafiya ne?"
Take ta tambayar cike da damuwa matar ta kasa magana.

Hankalin Afeefah ya tashi, kar ta mutu yanzu ma a ce ita, ya zata yi? Ba Za Ta iya barin ta a nan ba a haka yadda take duk ta fice hayyacinta ta jike jagwaf da gumi Dukda sanyi ake. Wani tunani ne ya faWo wa Afeefah ta yi hanzarin karbar jakar matar tana cewa
"Aunty taimakon ki zan yi ba sata zan miki ba bani da ko biyar da ba zan taSa jakanki ba"
BuWewa tayi ta samu Wari biyar bata tsaya tunani ba ta tari abin hawa ta sanya matar a ciki itama ta shiga mai machine Win ne ya dauka mata akwatinta tana ce mishi
"Asibitin dake kusa don Allah"
"Sannu, Sannu"
Take ta maimaitawa matar gwanin tausayi sai taji tana yi wa Allah godiya da ya barta da lafiyanta ko ba komai ta tsira da shi, a haka suka isa wani private hospital ya shiga da su har ciki aka dau?eta emergency zuwa lokacin bata numfashi.




=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*018*

Sai da ya bar gida da motar ya fahimci gas din Ac Win shi ya ?are, hakan ya Sata mishi rai don baya son buWe glass na mota yana tu?i, a haka ya tafi Asibiti yayi abin da zai yi a ranar wuraren sha biyu ya bar asibitin ya nufi gida, a daidai babban titin da zai Wauki hanyar cikin unguwar su na Barnawa hold up ya ri?e shi, a dole ya sau?e glass saboda zafin da yake ji.
Karon farko da idanunshi suka sau?a a kanta bai gane ta ba sai da ya Wan yi focusing na seconds kan ya gane ta, wannan yarinya ce da ya taSa ceta from poison, wannan yarinya da saleem ke so, sam bai yi tunanin wani abu ne ya tsayar da ita a wurin ba sai a karo na biyu da ya mayar da idanunshi wurin suka sau?a a kan trolley dake gabanta, idanunta ya sake mayar da ido sai ya fahimci ta yi kuka sossai, horn ake ta danna mishi hakan ya sa ya ja motar yayi gaba wayanshi ya zaro ya shiga neman Layin salim sai dai har 2missed calls ya mishi bai Waga ba shi da ya tsani kira sau biyu ya kan ce ai duk uzurin da mutum ke yi in ya zo ya ga na farko zai bi ba sai ka ta jera kira kaman marar aikin yi ba, a kira na uku saleem ya Waga sai dai ya kasa magana.

"Saleem are you Okay? Whats wrong with ur voice?"
Saleem ya kasa magana don shi kaWai ya san me yake ji, Ryan bai taSa jin Muryar abokin nashi a haka ba, dole ya nemi wuri yayi parking
"Saleem Mommy ce?"
Yayi uttering
"Uhmm Ryan Mommy ta kori Afeefah ban san wani irin hali za ta faWa ba, mommy tayi alkawarin tsine min na sake ko da magana da Afeefah ne bare yunkurin taimako aure ko soyayya, she's too young Ryan she's too young! Na san tana chan all alone, scared and disturbed idan wani abu ya same ta fa? Its all my fault da na fara son ta Its my fault..."
Hawayen da yake yi ne ya sa ya datse lips Win shi da ?arfi sai kawai ya katse wayan.

Kunna motar rayann yayi yana jin wani abu a ?asan ranshi, tausayin Saleem ya rufe shi haWe da damuwan jin halin da yake ciki bai taSa jin abokin shin haka ba, saleem da ko haWe rai baya yi. Fuskarta yake gani a idanunshi ashe kallon taimako take mishi, steering ya Wan buga da tafin hannunshi yana zagayowa inda ya barta sai dai neman duniya bai ganta ba, har parking yayi ya sau?a yana takawa da kafa ya zazzaga bata nan. Bakinshi ya Wan taSe kaWan yana shirin juyawa wayanshi yayi ringing.

Zarowa yayi sai ya ga Driver Win Mamminshi ne, dagawa yayi
"Ado ya aka yi?"
Ya fitar da maganan yana lumshe ido sam ba zaka san yana da damuwa ba ko hankalinshi ya Wan tashi don fuskar bai nuna ba ko da wasa.
"Oga akwai matsala ne, Hajiya ce!"
Tuni ya ware idanun a take suka sauya ya fara nufar motanshi yana ji Ado na mishi bayani wai ya kaita sayayya kuma yayi ta jira bata fito ba ya shiga ciki kuma yayi neman duniya bai sameta ba.
"A ina ne?"
"Galaxy mall"
Yana kusa da wurin ?arasa wa kawai yayi
"Ka ?irata?"
Ya jefawa Ado tambayar Ado yayi saurin du?ar da kanshi don ya san fushin Rayyan a take sai ya haukace, idanunshi sun yi mishi kwarjinin da ba zai iya kallon cikinsu ba
"Ban fito da waya ba"
Wani irin kallo ya watsa mishi lip Win shi ma sun yi nauyin buduwa bare su sake furta ko da kalmar A.

Wayanshi kawai yake dannawa ya shiga ?iran layinta sai dai ringing na duniya ba'a Waga ba, tracker ya shiga na Find my Iphone tuni ya ga location da take, a maimakon hankalinshi ya kwanta sai hankalinshi ya sake tashi ba za ka sani ba amma in ka ?ura mishi ido zaka ga hannayenshi har rawa suke idan kuma ka taSa za ka ji sun yi sanyi tamkar ?an?ara to baya cikin lafiya kenan.

Mota kawai ya shiga ya ja tafiyar mintuna goma ya isar da shi asibitin yayi rough parking ya sau?a ya nufi ciki, a gaban nurses station ya tsaya
"An kawo wata elderly woman yanzu! Where is she?"
Da Wan karfi yayi maganan don ya ga mace Waya ce kawai ta mayar da hankali kanshi tsawar da yayi ya sa duk suka juyo, kofan emergency kawai ta nuna mishi ya nufi wurin kawai ya tura ya shiga.

"Excuse you! Baka san ba'a shiga nan bane?"
Id card Win shi ya fitar ya nuna musu idanunshi na kan Mammi da suke ta ?o?ari wurin ganin sun ceceta ya furta a hankali
"The patient is experiencing end-stage renal disease(ESRD) nd she's diabetic i hope ba ku yi kuskuren komai a kanta ba"
Ja da baya wanda ke rike da drip yayi don ba ruwan masu sugar bane, Id card Winshi kuma ya tabbatar musu da waye shi. A tare da shi aka cigaba da ?o?arin ceton Mammin kusan awa Waya da wani abu kan suka fara fitowa aka barshi shi kaWai.

A kan kujera ya zauna ya sa hannu ya ri?e nata Waya ya gimtse a duka hannunshi biyu ya Wora goshinshi a kai yana jin jininshi na cigaba da tsitstsinkewa rauni mai girma ne da ba zaka Wauka irin shi mai dakakkiyar zuciya zai nuna ba bayyane a fuskar shi da ma idanunshi, ?iran sallah ne ya sa ya Wago a hankali ya zuba mata idanu sama da mintuna uku kan ya mayar da hannun a hankali ya ajiye mata ya mi?e ya fito Fuskarnan babu Wigon walwala, a kan trolley idanunshi suka fara sau?a ya Wan kalli Ado da ke ma?ure gefe kaWan kaman zai yi magana kuma sai ya fasa yayi gaba, sallah yaje yayi bayan ya idar ya dawo yana shigowa reception Win tana Wagowa suka haWa idanu, handbag Win hannunta ya Wan kalla kan ya nufeta.

Yana matsowa dukar zuciyarta na ?aruwa gabanta sai dukan uku uku yake tamkar za ta rasa numfashinta take ji don bai daina kallonta ba kuma bai daina nufarta ba kamshinshi ya riga shi isa, ko kan ya iso aka ?ira shi
"Sir the patient, ta farka"
Numfashi kaWan ya sau?e ya juya ya nufi Wakin, bata san ta kama numfashi ba sai da ya Sace mata taji tana kokarin mutuwa ta sake shi da ?arfi tana dafe kirjinta, Allah ya gani tsoron shi take bata sani ba ko tun ihun da yayi mata ne tayi developing wannan tsoro ko yaya amma muddin ya sau?e ido a kanta sai ta ji wani tension na building inside her.

Idanu kawai ya zuba mata ta Wago ido ta kalleshi cikin ?arfin hali ta sakar mishi murmushi tare da mi?a mishi hannunta, ya taka a hankali yaje ya kama yana zama
"Mammi..."
Sai yayi shiru ta sake yin murmushi mai kyau
"Saraki na ji sau?i ka kwantar da hankalinka, sannan am sorry na ji ina son Wan shan iska ne ya sa na fita not knowing hakan zai faru am sorry na Waga maka hankali"
"Mimmi stop it please, am sorry i wasn't there to take you out myself da kin faWa min zan bar duk abin da nake zan zo na kai ki na kula da ke har mu koma, Its my fault da nake emphasizing akan zaman gidan am sorry you get bored"

Hannunshi ta Wan matse tana murmushi har lokacin, Wago ta yayi ya buWe ruwa ya bata ta karSa babu musu ta sha sossai kuwa don masu ciwon su na bu?atar enough ruwa a jiki.

Basu wani jima ba suka fito yana ri?e da ita, har lokacin in har ka san shi sosai za ka hangi akwai damuwa a fuskar shi, Afeefah da har lokacin tana zaune a wurin tayi saurin Mi?ewa ganin su tare, dama ya san matar?
Menene ala?arsu? Ta ya aka yi ya san tana nan? Su ne tambayar da ta tsaya yi tana daga tsaye tana kallon su.

Idanun Mammi ne ya kai kanta, sai ta dakata tana tunani ga jakanta dai hannun stranger a hankali take tuna abin da ya faru yarinyar ce ta taimaketa, ta yi mamaki ?warai ganin yarinyar har lokacin kuma ri?e da jakanta da alama ko ajiye shi bata yi ba, tana tuna kalaman yarinyar na ban ha?uri a sadda ta Wauki Wari biyar ciki.
"Saraki wanchan yarinyar ita ta taimakeni ta kawo ni nan, da ban san me zai faru ba"
Kaman bai fahimta ba ya sake kallon Afeefah, chan ?asan ranshi ya ji daaWi kuma ta samu wani ?ima a idanunshi saboda duk wadda ya kaunaci Mammi ko da bai kaunaceshi ba shi ya bashi daraja na musamman, sai dai har lokacin fuskar shi bai nuna ba sai nufanta da Mammin ta sa suka yi, ita abin da ya kaWa ta ma tahowarsu tare, ita dai ta rasa wannan irin razani da take shiga da kwarjinin wannan bawan Allahn, ko da suka tsaya gabanta sai ta ga ya cike wurin gabaWaya, kuma kallonta yake don Mammi ta sake shi ta kama hannunta.

"?iyata yaya Sunanki?"
"Sunana Afeefah, Aunty ya jikin ina fata komai lafiya?"
Tayi maganan kaman mai tsoron wani abu zai kama ta
"Alhamdulillah Afeefah, na gode ?warai da kyakyawar tunanin ki ba kowa ne zai iya irin taimakon da kika yi min ba, Allah ya saka da alkhairi"
Afeefah tayi murmushi
"Babu komai Aunty, ga jakarki ki yi ha?uri na cire Wari biyar a ciki mun hau adaidaita saboda ba ni da ko biyar"
Murmushi Mammi ta saki ta Wan kalli Rayyan da bai ce komai ba ya zuwa yanzu ya kawar da kai daga kallonta sai dai yana sauraren su.

"Gaskiya samun irin ki a wannan zamani sai an tona"
Idan ta tafi da jakar nan ba karamin abu za ta samu

14 / 53