HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   52 / 53

153K to 156K   out of 158.4K words

yau kin tarawa kanki damuwa! Kan na ciwo ne?"
Ya kai tafin hannunshi yana dafe goshinta hawayen ta sake farawa
"Ban san da wani baki zan fara maka godiya ba Ya Saraki... Ko baka faWa ba na san aikinka ne Allah ya biya ka ya saka maka da alkhairi ka yi min komai Ya Sa..."
Hannunshi ya sa ya rufe mata baki yana dan Wauke hawayen da take zubarwa yace
"Kin chanchanci fiye da haka a gareni Afeefah don haka ba komai ba ne, na so ko gidan haya ne mu kama a gyara wannan amma bai samu ba idan ba damuwa za su dan koma Kaduna ko ma su je ganin Wakin ki a Fombina kan su dawo sai a gyare nan Win"
Rungume shi kawai tayi ya sa hannu yana dan shafa bayanta kan ta Wago sai ta sake jin jirin yamutsa fuska tayi, ya shiga mota don bai kula ba itama ta zaci ma stress ne don haka ta koma ta musu bayanin za su je Fombina ko sati biyu su yi za'a Wan gyare nan Win kuka kam kawu har ya rasa hawaye ya rasa bakin godiya a haka suka Wauki duk abinda za su Wauka aka adana kayan abincinsu a daki guda suka Wauki duk wani abu mai muhimmanci, yaranshi maza manyan uku da mata shidda na Inna Asabe uku na Inna Larai biyar suka bar garin zuwa Kaduna.

Kai tsaye gidan Mammi suka yi masauki jannah ta turo abinci ko da Abeeha ta gaya mata da ba?i suke ta turo daga restuarant, a masaukin baki aka sauke su suna ta mamaki da santin gidan, Ita dai Afeefah su Suhaila ta ja zuwa Wakinta ta musu wanka ta duba cikin tsarabarsu da ta musu na musamman ta fidda kaya ta saka musu suka haWe babban parlor aka ci aka sha kan kowa ya nemi makwanci don sun gaji, sai da ta tabbatar sun yi bacci ta watsa ruwa ta shirya cikin wani Red kayan bacci da yayi mata kyau sossai marabarshi da babu kaWan ne ta nufi Wakinshi...

Yana jingine da gado yana jiranta suna haWa ido suka Sakarwa juna murmushi mai ?ayatarwa, yanga tayi ta mishi Dukda kunya dake Wawainiya da ita barin killer looks da yake binta da su har ta iso gadon ya fusgo hannunta ya manna ta kirjinshi yana matse ta a lokaci Waya suna sau?e ajiyar zuciya a tare
A kunnenta ya raWa mata
"Kina kashe ni da raina Gimbiyata"
Ta Wan Wago bai tsammata ba ta haWe lips Winsu kaman jira kuwa ya mirginata kasanshi ya mata rumfa yana bata wasu kisses da suka sake matar da ita a kaunarshi hannunta na yawo bisa bayanshi zuwa keyarshi tana mishi susa, gasping air yayi ya raba lips Win suka yi murmushi mai sauti ya sake mayar da lips Win yayi mata kyakyawar Kiss

Ta raba fuskansu tana shafa kanshi hancinsu haWe da juna suna musayar numfashi ta ce
"Na gode sossai Na gode kwarai ha?i?a Allah ya wanke min zuciya ya ba ni mijin marainiya, ya ba ni kai ba tare da wayo ko dabara ta ba a koyaushe ba ni da abin faWa a gareshi sai Alhamdulillah. Ina ro?on Allah akan duk ranar da za ka haWu da shi, Fuskarka ya zama mai annuri da sheki fiye da yadda yake a yanzu, ya rabautaka da karSar kyawawan sakamakonka a cikin tafin hannunka na dama sannan ya ce
"I am pleased with you" ya haWa mu gabaWaya a aljannah madaukakiya ya ba ni dama da ikon Zama shubagar matayenka a aljannah. Ina ?aunarka Ya Sameer...Ina ?aunarka Ya Rayyan ina matukar sonka Ya Saraki"
Hawayen dake zuba mata yake bi a hankali da harshen shi yana Waukewa cikin wani salo zuciyarshi ?al yayi fixing gaze Win shi cikin idanunta

"I love you. love you more than anything Afeefah, ban taSa jin son wani abu yadda nake jin naki ba, I love you more than myself. I will always love you. I will love you till the end of my time. No words can express how much love i have for you. I will alwavs be here for you no matter what kin ji? Babu abinda zan miki da zan ji yayi yawa you are my favorite girl nd my only blessing"
Daga nan ta dafa chest dinshi sai ya koma kwance ta dane jikinshi da kanta ta shiga gigitashi abinda bata taSa sakewa tayi ba ta yi shi a ranar ta goge mishi hadda sai gashi yau ma yana yi mata kuka don ta gama da rayuwarshi in dai ta fannin ne.

Washegari sun tashi da mummunan labari don Uncle Usman ya rasu labarin ya kaWa ta don faWuwarta kawai suka ji hankalinsu ba karamin tashi yayi ba barin ma Rayyan a hannunshi ya Wauketa suka tafi asibiti don duk abinda za su yi sun yi matsayin shi na likita ya kasa farkar da ita yana jin panic akan ciwon Mammi amma bai san Meyasa duk abinda ya shafi Afeefah na fitar da ragwantakanshi a fili ba, tsoro da fargaba ya sa ya manta yadda ma ake aikin likitacin sai a asibitin ne aka samu ta farfado nan suke samun labarin tana da shigar ciki kuma razanar da tayi har ya fara barazana ga Wan cikin nan ya saka aka yi mata allurar bacci don ta huta sossai.

'Yan uwanshi sun yi rawan gani da su Sulaiman aka sallaci uncle Usman aka kai shi makwancinshi dogon takarda da ya roki sulaiman rubuta mishi ya ba Rayyan akan idan ta dawo daidai sai a bata.

Kwanan ta biyu kan ta dawo cikin hayyacinta tayiwa su Suhail kuka ba na wasa ba don maraici babu daaWi ta kuma yi alkawarin rike su fiye da ?a?an cikinta har illa masha Allah.

A kwana na huWun suka juya Fombina, anan ne Kawu suka san basu ga komai ba baki sake suke bin irin girma, tsaruwa da ma kyaun masarautar irin mulkin da ake shimfidawa ko a mafarki basu taSa mafarkin halartar irin wannan wuri ba sai gashi wacce suka raina ta zama sanadiyar da ake zube musu, sun yi kuka kaman me don sashe na musamman aka sauke su mai martaba da Ammi suka tura ake musu hidima wane wasu masu kuWi.

Ammi da mai martaba kaman su hadiye Afeefah jin labarin cikinta, soyayyar mijinta kuwa ya ninku fiye da yadda yake jinta a da su Suhail sun zama 'yan gata don a take aka tsara musu dakunansu Mai martaba ya sa aka cike musu wardrobes da kaya Ammi ma ba'a barta a baya ba don abinda za ta yiwa jikokinta shi take musu har ma sun Fara ?iran Afeefah da Ammah Ryan kuma Abbu, school na musamman ya saka su masu musu hidima ma daban aka ware don Afeefah laulayi mai wahalarwa take.

Satin su Kawu uku suka koma bayan Rayyan ya saya mishi babban waya an hada su da goma sha tara na arziki suka koma, gidan su ya zama daga cikin gidajen da suka fi kowanne kyau a garin Wan daidai kuma a kayace sai ya tuna akurkin da suka warewa Afeefah take rayuwa lallai Allah ya nuna musu ikonshi sun tuba har sun rasa bakin tuba, a kuma satin da suka koma aka fara gudanar da aikin gidauniyarta.

Sai ga kujerar Umura da Rayyan ya biya musu har da su Mai martaba za su tafi da su Abeeha, sun yi murna barin Afeefah da bata taSa zuwa ba za dai tayi kewan yaranta cikinta na wata huWu suna gama second semester exams suka chale ?asa mai tsarki ranar da ta fara ganin ka'aba tayi kukan da sai da tayi zazzabi bata taSa ganin abu me kyau da natsuwa ba irin shi duk rayuwarta, ta zube wurin ta yiwa iyayenta da yan uwanta da ta rasa Adu'a har sai da miyaun Bakinta ya kafe, sun yi sati uku chan sayayyan baby kuwa kowa yi yake ba Ryan ba ba Ammi ba ba su jannah ba, daga Saudi sun tsaya kaWan a Turkey sun yi sayan kayan Wakin su Aisha ana dawowa Nigeria Aka fara hidimar bikin su.





=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*Wannan shafin naki ne Uwar ?akin Damisa namu angon Nyla ?ani ga Didi kuma Uban Didi. Nana Halima ko na ce Leemar's delicious mai abincin 'yan gayu...Allah ubangiji ya ?ara miki basira da haza?a ina godiya ?warai>?p?*

*FINAL PAGE*
*60*

Zaune suke a cikin ?ayataccen hall Win da ake shan hidimar bikin Autan Mammi da Autar Ammi waenda duk yanzu suka zama shalelen Ammi kuma angwayen ma duka 'ya'yanta, Ryan na zaune bisa wani table ri?e da hannun Afeefah sun yi azabbaben kyau cikin outfit Winsu na Soire party wanda english party ne duk mazan shigar suite suka yi matan english dress, Farin suite ne jikinshi da ba?in shirt daga c????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
iki bakin takalmi da ba?in hankey da ya Wan le?a bakinshi daga aljihun, gashin shi ya sha gyara ainun fuskarshi sheki yake kowa ya ganshi ya ga cikakken namijin da yake cikin kwanciyar hankali da jin dadi.

Tana sanye da wani doguwar riga na tsadadden sugar lace da ya bayyana cikinta da ya taso yayi mata kyau ainun, ta saka gyale da ya tafi da kayan tayi wrapping kanta ta sha make up da ya matu?ar zama mata wanda mijin nata ke ta bacin rai akanshi don kishi ya sa ko motsi tunda suka zauna basu yi ba su Saleem sun ta kiranshi ya ?i zuwa sai Sulaiman ne yake representing Win shi, gabansu Suhail da Suhaila ne shigan ryan shine irin na Suhail haka Suhaila ma irin na Afeefah sai suka ba da wani kyau mai ma'ana.
Zarah ce da yanzu ta sake saboda janta da su Abeeha ke yi a jiki kuma tayi tuban gaskiya ta zo ta ja su Suhaila don tana kaunarsu su ma kuma sun sonta, Afeefah ta kalli Ryan

"Ya Saraki..!"
A ShagwaSe tayi maganan ya kalleta
"Matar Masu Sarauta ya aka yi?"
Yayi maganan yana Wage mata gira tace
"Eyyaa dubi ana yi wa Adda Abeeha barin kudi in je in manna kaWan mu yi hoto?"
"Wanda kuka yi kan ku zo nan ya isa ba za ki shiga cikin maza ba"
Ta Wan Sata rai har ma nadamar Kwalliyar take ji yadda ya kasa ya tsare dama bikin duk ya hanata wani hidima yadda ta so cin uwar sabada sai dai ta ga su Samha na yi don duk Fombina suka zo har Sadiqa da ake hidimar aurensu tare sun zabi su zo nan in za'a Waura aurenta sai ta koma tunda sai an Waura na Saleem an kai mishi matarshi zai ba da nata.
Har su kawu sun zo bikin da Inna Asabe sun bar inna Larai a gida, kawu ya sauya ?warai natsuwa ta shige shi haka Inna Asabe da inna Larai babu wannan rawan kan da son zuciyar sam sam sam.

A bikin ne ma take samun labarin Sabrina da iyayenta inda ta kwaso HIV da ya kasa warkewa ga talauci da yayi musu katutu ita Gaje garin zuwa boka nema mata waraka ta faWo daga tsauni sai gawa aka Wauka Yaya ne ya zo neman tuba wurin mommy kuma ta yafe musu.

"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Wata ?awar Aisha ce ta yi musu sallama, Afeefah ta kalleta da mamaki don ta kula yarinyar na ji da uban ta wani ne tun fara bikin sai rawar kai take bata zaci Rayyan zai wani kula ta ba sai ta ji ya amsa, a take wani abu ya taso mata zuwa wuya wato ita ce bata da kishi shi ya hanata tashi saboda maza ita kuma tana kallonshi yana magana da wata macen.

"Yayanmu barka dai, mun jima muna kallon irin kokarin ka akan rayuwar matasanmu a koyaushe His Excerllency ba shi da zance sai taka gaskiya samun shugaba irinka abin alfahari ne in kuwa da irin ku rayuwar matasanmu ba zai taSarSare ba"
Ya san mahaifinta Gomna ne mai ci a yanzu don haka yana martaba gidansu sai ya Wan murmusa
"Thank you"
"idan ba damuwa ga wannan na jima ina so na baka ban samu ganinka ba Its a small gift don Allah kar ka ce a'a"
Ta ajiye wani karamin paper bag tayi murmushi ta juya ta wuce.

Kaman an ce ya kalli Afeefah ta haWa gabas da yamma kudu da arewa, idanunta har shekin kwalla su ke, hannunshi dake cikin nata ya Wan murza don ta kalleshi amma ta Wauke kai sai ma ta mi?e chadak ta nufi waje, da sauri ya bi bayanta yana dan kiranta amma bata waiga ba dab wurin mota ya ri?o damtsen hannunta a hankali ya janyota bayanta ya sau?a kan kirjinshi yana dan lekan fuskanta yace

"Tsaya mana BoWWi fushi kika yi?"
Fuskarta babu walwala ta janye tare da Juyowa ta kalleshi
"No, Meyasa zan yi fushi?"
"Me yasa kika fito to ina ta magana kin ki kulani?"
Ta kalleshi
"Gashi na kula ka, ina jinka"
Numfashi ya sauke
"It seems kin gaji mu tafi gida"
Ta juya ta nufi motarshi bata ce komai ba, numfashi ya sauke yana Wan shafa gira ya nufi motar tuni ta buWe ta zauna ya shiga shima drivern shi ya ja suka nufi Sangaren su tunda akwai tafiya sossai, hannunta ya ri?e ta zame tare da juyawa tana kallon Window.

"Akwai abinda ya faru ne? Ko na miki ba daidai bane?"
"Babu, me kuwa zai faru?"
"Ta ya zan sani Afeefah na ga kina fushi"
Ta Wan bashi side eye tana sake juyawa
"Ni ba fushi nake ba"
Lip dinshi na kasa ya Wan lasa har ga Allah bai zaci wai kishi take ba a hankali yace
"Ok"
Ya kalleta sai ya ga ta sake haWa rai ya sauke numfashi har suka isa ta sau?a tun kan ya zagayo ya buWe mata.

?akinshi kai tsaye suka nufa don suna shiga parlorn ya ri?o hannunta, bata ga amfanin make up Win ba bayan hotunan da suka yi musamman nata dashi da yayi kyau ainun hannunshi kan cikinta yana murmushi yalwatacce ita kuma tana kallon hannun nashi tana murmushi wanda har ta mayar wallpaper to bayan shi bata ga amfanin adon ba.

Wanka ta shiga bayan ta goge Kwalliyar shima ya kwaSe ya bi bayanta, tana tsaye shower ta ji ya manne da ita yana bin wuyanta da tafiyar tsutsa, zamewa take har ta gama Wauraye jikinta ta fice ta bar shi ya bi bayanta da kallo, bata wani tsaya drying kanta ba ta duba shirt din shi ta saka don tana jin daaWinsu sossai ta zame towel Win tana bottuning shirt Win da iyakarshi rabin cinyarta ya fito Waure da towel a kugunshi da wani irin kallo yake binta ganin ta nufi bakin gado ya isa ya kama hannunta
"Kina so ki yi mura ko?"
Bata tanka ba yaje ya ajiye ta gaban madubi ya zaro hand drayer ya shiga busar mata da gashin cikin kulawa.

Miyau take hadiyewa tana bin ginannen jikinshi dake bayyane da kallo, ganin zai kalleta ta Wauke kai yayi murmushi ajiye drayer Win yayi ya du?a sossai yana shunshunar wuyanta da baya rabo da kamshin da yake masifar so, a yanzu har da lips Win shi yake goga mata zuwa sajenshi da ya sa duk numfashi na kwace musu barin ma shi da yake a kunne, hannunshi ya mayar ta gaban rigar nashi dake jikinta ya fara unbottuning saman shirt Win yana sauke wahalallen numfashi mai rikitarwa.

"Ya Saraki ka bari, bacc..."
Hannun da ya tura cikin rigar ya sa ta Wauke numfashi ganin zaunen ba zai kai su ba ya Wagata chadak zuwa gado yana ?arasa unbottuning shirt Win, tun tana resisting har ta sallamar suka rikice a duniyar masoya sai da komai ya kamallah ta zame za ta sau?a ya dawo da ita yana shafa lallausar Fatan bayanta

"Kika cigaba da fushin nan zuciyata za ta iya shiga matsala Ya Alami" (Duniyata)
Yana cigaba da shafata a natse ya cigaba
"A faWa laifina in yi gaggawar tuba kin san Sameer mai biyayya ne a fadarki"
Ta Wan yi murmushi ta isa? Sarkin gobe ya zama bawan ta?
"Shine har da yiwa wata murmushi a gabana har da karSar gift Winta"
"O'ooo am very sorry ban san dalilin fushin ba kenan, kin fa san babu macen da take da daraja ko kima a idanuna bayan ke da Ammi, Afeefah ke ce mahadina daga ke kuma Ryan ya gama kallon 'yanmata"
Wani sanyi ne ke kwarara mata yana mata son da bata san adadin shi ba, Wagowa tayi ta mayar da kanta kan pillown da yake sai ya juyo suna kallon juna tace

"Na sani ba zaka taSa zama da mace daya ba amma na rasa Meyasa duk sadda wata macen ta kallar min kai sai in ji mutuwa ne kawai ya saura mini tsabar zafin zuciya"
Yayi murmushi yana ri?o hannunta a tsakiyarsu
"Wa yace miki hakan?"
"An ce sarakai ba sa zama da mace Waya"
"Za'a fara a kan Sameer Muhammad Modibbo don daga ke na rufe kofa a gidana"

Soyayyarsu suka cigaba da sha yana bata duk kulawarshi ta so ta tafi Kd ya hana don haka ta mayar da hankali kan lectures Winta da kulawa da shi da kuma cikinta har Allah ya kawo ta watan haihuwa, wani ranar Alhamis da dare labour ya saka su nufar asibiti babu shiri a safiyar juma'a ta santalo katoton Wan ta fari tas mai kama sak da mahaifinshi wanda a ranar BO?EJO ta sha kuka ganguna da kalangu sun yini dokawa kowa ya gifta Masarautar Fombina sai ya san ana cikin alkhairi dumu-dumu.

Yaro ya zo da tarin alkhairi don Mai martaba ji yake kaman ranar ne ya fara ri?e Sameer a hannunshi tuni lungu da sa?o sun samu labari hotunan kuwa har ya je Kaduna uwar jego ta sha ?auna iri iri, ko da suka dawo masarauta sashenta take wata dattijuwa ta shiga hidimar kula da ita da bata cikakken kulawa na masu jegon gargajiya, ranar suna an yi bidiri Aisha ta zo da cikinta kuwa haka sulaimi ma ta zo da nata tamfatsatsen cikin Haihuwa yau ko gobe sai Jannah da take shirin zuwa amma labour ya hanata itama a ranar sunan ta haifi danta namiji, Abeeha ma na fama da laulayi aka yi hidimar suna na ji da gani kuwa yaro ya ci

52 / 53