HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   19 / 53

54K to 57K   out of 158.4K words

yatsa ma na ciwo ki ga an apka feldin yawaitar shan su akai akai to su suna zuwa ne su rufe jijiyar da yake kaiwa koda jini, a cikin jikin mu kuma koda na daga cikin organs da suka fi kowanne bukatar jini, Sai kuma hawan jini ya fi yawa ma a ?asar mu yana taimakawa sossai wurin kashe koda waennan dalilan bayan ciwon sugar su kan iya haifar da ciwon ?oda, a kan iya chanzawa a dace amma ni an chanza min duk biyu ba'a dace ba yanzu haka ina zuwa dialysis ko wani wata."

Tamkar Afeefah za ta zubar da hawaye take juya maganganun Mammin
"Mammi Allah ya baki lafiya ya sa kaffara ce duk kika yi ta yi"
Mammi tayi murmushi tace
"Ameen, kila Allah ya ajiyeni ne don ?addarar haWuwarmu kila alkhairi zai haifar, bana fita kwata-kwata sai da Saraki ranar kawai na ji ina son fita ashe da rabon mu haWu ne"
Afeefah tace
"Na ga Yaya..."
Sai ta kasa cewa Rayyan a hankali tace
"Ya Saraki! Ya damu sossai da rashin lafiyar naki"
Mammi ta Wan murmusa Allah ya sa kar Rayyan ya ji tana ce mishi Saraki don baya so, shiyasa ko su Abeeha ma Ya Rayyan su ke cewa
"Afeefah ba zan iya misalta miki yadda hankalin Saraki ke tashi a kan ciwo na ba, ko kin san hatta me dafa min abinci ta karantu ne sossai akan cimar masu ciwon mu? Saraki ya tafi yayi courses akan likitanci ne bayan ciwon sugar na ya haifar min da wannan ciwon ?odar in ba haka ba burin shi ya zama soja ne kawai ba Army medic ba, duk don ya san irin taimakon da zai bani a cikin gida ba sai mun yi ta zarya asibiti ba sanin bana so"

Jinjina irin kaunar da yake mata take yi, lallai Rayyan na son mahaifiyarshi.
Cigaba da mata hirar irin gudumawar da Rayyan yake bayarwa a rayuwarta take yi. A yadda dai ta gansu kaman babu wani namiji a gidan bayan Rayyan to mahaifinsu rasuwa yayi? Bata da wannan amsar sai dai ta san idan har tana gidan za ta sani ne.

Abeeha ce ta shigo
"'yan makaranta ashe an dawo?"
Tayi maganan tana zama hannun kujerar da Afeefah take
"Na dawo Adda Abeeha, makarantar akwai daaWi they are all nice to me basu yi min dariya ba"
"Ai na faWa miki babu mai miki dariya, wasu da girman da suka fi naki ma suke zuwa suyi karatu bare ke da jikinki ba nuna girman yake yi sossai ba"

"Aikam na gani kuma na ji daaWi, ga malaman sun iya karantarwa komai fa fahimta nake kaman na sani tun da chan"
Mammi da Abeeha suka murmusa, za ta sake magana kenan Ya shigo parlorn da sallamar da shi kaWai yake sanin yayi kayanshi.

Kai tsaye kusa da Mammi yaje ya zauna, da ita da Abeeha suka haWa bakin ce mishi
"Sannu da dawowa"
Kai ya Wan gyaWa bai kalli kowaccensu ba, mammi ma ta mishi sannu da dawowa yake tambayarta ya jikinta ta amsa da da sau?i.

"Yauwa Mammi Wazu na haWu da Samha a school ashe auren ya salim wani sati?"
Abeeha Tayi maganan da Wan mamaki, Dukda da ta kalli Samha sai da ta tuna abubuwan da suka yi wa Afeefah kuma haushin su take ji har ranta ko da samhar tayi mata magana da kyar ta daure ta amsa, wurin kokarin janta da hira ne take sanar mata auren salim Win kuma suna gayyatarta.

Wani irin faWuwa gaban Afeefah yayi
"Aure Ya Saleem zai yi?"
Bata san a fili tayi maganan ba sai da ta Wago idanunta suka faWa cikin nashi da a lokacin ya Wago ya kalleta jin furucinta, da sauri ta Wauke ido gabanta na dokawa sam bata son suna haWa ido bata san me yasa ba, sai dai yanzu maganar auren saleem Win sai ta ji shi wani iri duk ta ji babu daaWi, Abeeha ma sai da tayi maganan kan ta tuna da Afeefar.

Mammi ce tace
"Eh aure zai yi Afeefah wani sati, kar ki wani sa damuwa a ranki in shaa Allahu Allah zai musanya miki da abin da ya fi alkhairi"
Kunya ne ya rufe ta sai ta du?ar da kai tana kallon yatsun ta sautin tsakin shi ne ya shiga kunnenta, Mammi ta fara mishi faWa akan yawan tsakin kaman wani tsaka, Abeeha ce ganin yanayinta ta ja Afeefar akan su je su ci abinci suka fice daga parlorn.

****

Hidima fa ya kankama Sangaren Amarya sai shiri ake wane, tun saura sati aka fara bikin 'yan karya don Mommy sossai ta ajiye musu kuWi Dukda ma angon ya ja mata gargadi akan duk abin da za su yi kar su sake su saka shi, bai ma je gidan ba ko sau Waya sai ranar da suka yi kauyawa bayan Magrib yana zaune harabar gidan su da dangi suka cika, shiru kawai sam ba ya jin daaWin komai kuma komai ba ya burgeshi kaman daga sama ya ji Muryar Mommy.

"Saleem yanzu ka rantse sai ka nunawa duniya duka ba ka son auren nan dole na maka ko?".

Shi bai san me yayi ba, kaman zai yi kuka yace
"Me nayi kuma mommy?"

"Ko sau daya ka je kofar gidan su Sabrina da sunan zance? Ko ita ba mutum ba ce? Ka hana ta saka ka cikin duk hidimar ta da kyar ma na bugi cikinta ta nuna min kai ne baka so ba ba bata sanar da kai bane, baka bata komai ba haka ake yi?"

"Amma mommy ni nace tayi wani hidima ne?"
"Au in kai kana ?unci da ba?in hali a kan wata chan da na tabbatar yanzu ta rabarwa maza kanta sai aka ce ita ma ta biye ka kuyi ?uncin tare?"
Runtse ido yayi ya buWe tuni suka sauya Meyasa mahaifiyarshi ke yin abu kaman bata je islamiyya bane? Ya subhallah maganar da ta faWa ya mugun ?ona mishi rai amma ya zai yi ne? Uwa uwa ce.

"Zan je, zan ba ta kuWin"
Abin da kawai ya iya faWa kenan ba tare da ya kalli mahaifiyar tashi ba, sai da ta wuce ya bita da kallo yana jan Astagfirullah don yana tsoro, 'ya'ya mata ne garesu yana tsoron Allah ya hukunta mahaifiyar tasu da daya daga cikin yaranta, yana tsoro ta fahimci kuskurenta in a Hard way.

A lokacin ya mi?e ya nufi mota kan ya shiga aka wangale Gate, motar Rayyan ne ya shigo cikin gidan dole ya fasa tafiyar sai ya nufi wurin Rayyan Win suka gaisa.
"Fita za ka yi ne?"
"Eh wai zan je ne in ba Sabrina kudaWen da ya kamata su yi hidimar bikin"
Kai Rayyan ya gyaWa yana furta
"zagayo mu tafi"
Zagayawa yayi ya shiga motar, shiru yayi dama shi ne mai hirar muddin suna tare da Rayyan to shi ma baya cikin yanayin hiran, hakan kuma sai yake sa Rayyan ke jin wani iri sai ya ga kaman bai kyauta mishi ba Soye mishi da yayi Afeefah na gidan su amma zaman lafiyanshi kenan tunda mahaifiyarshi ba amincewa zata yi ba ko ya faWa mishi Win.

Har suka isa unguwar da saleem ne ke ta mishi kwatance hira ba sossai ya hada su ba, a cikin Layin aka yi kauyawan ana ta shirye-shiryen kiran sallahn isha su kam suna nan suna chasewa 'yan mata sai zuba rawa suke, Rayyan ya samu wuri yayi parking yana kallon arean da abin da suke yi a ranshi ya ja tsaki yayi dubu, auren saleem ne ake yi ake wannan haukan? Babu natsuwa a lamarin nasu babu kama kai, ba'a hana hidima ba amma sai a yi shi da tsari ba irin wannan ba ko daga rawar da ake ka san an zubar da mutunci.

Wayanta ya shiga kira ringing na karshe ta Waga
"Hello Ya Saleem"
Ta faWa da Wan ?arfi saboda kida dake tashi
"Ki zo ina daga bayanku kaWan"
Babbar kawarta ta janyo jiki na tsuma suka nufi motar, baya suka bude suka shiga suna gaishe su.

"Amma mun yi fushi sai yau abokanan ango ke neman mu?"
Ci kan ku Rayyan bai ce ba, arzikin kallo ma basu samu ba yana wurin ne kawai saboda Saleem ne da wani ne waennan Win sun mishi kaWan ya haWa numfashi da su a mota guda.

Bundles na 'yan dubu dubu guda uku ya buWe dashboard ya fiddo ya ajiyewa saleem a kan kafafunshi dole ya Wauka ya juya ya mi?a mata
"Ku yi hidima."
Jiki na rawa suka karSa sai kamshi kudin ma ke fitarwa na sabunta.

"Akwai wani abu?"
Ya tambaya saboda kawai mommy ta mishi dole
"A'a ya saleem wannan ma ya isa mun gode sossai"
Daga nan suka fice don shi maganan soyayya ma ba wai hada su yake da ita ba.

"Ka ga abin da mommy ta ja min ko Rayyan?"
Saleem ya faWa bayan sun fice daga unguwar.

Hakika shima ya ga wautar mommy, da ya ga yarinyar sai ya hasko Afeefah a idanunshi ko a kusa bata da abin da za'a haWa ta da Afeefah bai ce komai ba dai har ya mayar da saleem gida.

Su Gaje sun yi shiri matu?a na wannan aure, yayinda amarya tayi shagali sossai kuma ta kullaci kannen angon da babu wanda ta gani a hidimar ta har aka Waura aure ranar Juma'a, Dukda aure ne da babu wani sanarwa ko hidima saleem ya ga mutane kwarai an mishi kara, saboda shi ma na jama'a ne Rayyan na a gefenshi yana yi ne kuma saboda saleem ne don baya son harkar hidima da hayaniya har aka ci bikin aka watse, amarya dai ta tare a sashen saleem na gidan inda duk mommy ce ta tsara hakan sai fatan Allah ya basu zaman lafiya.





=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*24*

Da misalin ?arfe Waya na dare ta jefar da mayafin kanta tare da dira daga saman gadon tana jan tsaki, me salim ke nufi ne? Babanta ya tabbatar mata shirin da aka yi akan shi ba mai sau?i bane da zai iya resisting amma me ya faru har yanzu bai shigo ba? ?aukan maganin da Gaje ta bata a gefen bedside tayi ta jujjuya
"To bai ma zo bama bare in sha wannan Win" ajiyewa tayi ta janyo wayanta kaman ta ?ira su Gajen kuma sai ta fasa ta nufi parlor, kasancewar sashen nashi Waki daya ne da parlor sai kitchen in har dai ya shigo to ba zai wuce yana parlorn ba sai dai idan a waje zai kwana.

Shi kuwa salim tun karfe tara ya shigo gidan yanayinshi baya mishi daaWi sam, fuskarshi babu walwala haka ya tura kofan da sallama ya shigo, yana taka door mat Win ya ji kanshi yayi wani diimmmmm jiri na shirin kwashe shi a hankali ya furta
"Subhallah!"
Ya tsaya a wurin sama da mintuna biyu kan ya sau?e numfashi ya nufi three seater ya kwanta hannunshi dafe da goshinshi, duk yadda zai yi ya samu sauki ya yi sai dai wani irin tension yake ji, sai juye juye yake Sabrina da a chan ?asan ranshi ya san bai damu da ita ba sai kai komo take yi a ranshi, bai san adadin lokacin da ya dauka ba shi ba mai bacci ba shi ba ido biyu ba, ko matse shi zaka yi ba zai ce maka ga abin da ke damunshi ba sai jin Fitowar ta yayi.

Ganinshi ya sa ta nufe shi.
"Ya salim dama ka shigo? Shine kayi kwanciyarka anan ina chan duk tsoro ya rufe ni?"
Bai ce komai ba sai ido da ya Wan zuba mata.??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
"Ka tashi mu je ka kwanta a ciki idan baccin ne ma"
Ta faWa tana ri?o hannunshi, kasa mata musu yayi haka ya bi bayanta kaman rakumi da akala, a bakin gado ta ajiye shi ta shiga rage mishi kayakin jikinshi, wani sashi na zuciyarshi tsantsar mamaki yake na wannan bushewar idon wani sashen kuma na faWa mishi ba laifi bane, har ta gama cire mishi kayan shi dai bai tanka ba kuma bai motsa ba, hannunshi ta ja wai tunda ba ya jin daaWi su je ta mishi wankan, tana tura shi bayi ta dawo da baya ta sha wannan maganin da gaje ta bata don ta tabbatar mata yana kusantarta da maganin babu kuma wani abu da zai gane, babu wacce zai gani nan duniya bayan ita.

Tun daga chan cikin bayin zancen ya sauya, ita ce ke jan ragamar komai kaman ba amarya ba har dai ta samu nasara a kanshi Dukda ita ce tayi kidinta kuma tayi rawanta abinda zuciya bata so gangar jiki ko an tilasta ta ba zata ba da abinda ake so Win Wari bisa Wari ba, shi dai ya san bayan nan bacci mai nauyi ya Wauke shi tana kwance jikinshi tana zabga murmushin nasara.

Washegari da kyar ya iya tashi yayi sallah a makare, yana zaune kan sallaya idanunshi na zube a kanta tana ta baccinta, duk ya rasa me yake tunani ko me yake ji kaman an yi blocking kwakwalwarshi da daidaitacciyar tunani, knocking da ake ta yi shi ya Waga shi daga wurin ya nufi kofan ya buWe Samha ce.

"Ina kwana yaya?"
Kai ya gyaWa bai ce komai ba.
"Gashi in ji Mommy wai in kawo muku"
KarSa kawai yayi ya juya ya koma, ta tsaya tana kallon kofan for seconds kan ta tafi.
Shirya abincin yayi kan ya nufi cikin Waki ya nufi bakin gadon ya shiga bubbuga hannunta.
"Sabreena! Sabreena!!"
"Uhmmmm"
Ta faWa cikin baccin tana haWawa da tsaki
"Wai menene?"
"Kin yi sallah?"
Ta sake jan tsaki kan ta buWe idanu tare da Mi?ewa zaune
"Ka san gajiyar da nayi? Ai koyaushe na tashi zan yi Sallar yanzu ka tashe ni sai in yi ciwon kai ai"
Da mita tayi maganar.
"Ai in sallah bai tashe ki ba yunwa zai tashe ki, ga abinci chan ki fito mu karya"
Yana kai nan ya mi?e ya fice yana ji kawai ya gamsu da something is off with him amma ba zai iya pointing menene ba.

Sama da mintuna arba'in sai gata ta fito shirye cikin wasu riga da wando masu fadi, yana zaune yana jiran ta ganinta sai ya fara kokarin sanya musu abincin bata hana ba ya saka plate Waya zai saka wani ta ri?e hannunshi
"Wannan ma ai zai ishe mu Ya salim mun riga mun zama Waya ai ko ba haka ba?"
Kai ya gyaWa yana zame hannun nashi ya Wauki spoon ya saka, ita ta haWa musu tea tana wani irin murmushi.

Tun daga wannan rana saleem sai da ya kwana bakwai bai fita ko ina ba yana tare da ita, wani lokacin haka za su yini duk abinda tace zai gyaWa kai kuma zai iya yi mata amma ba zai yi magana ba, itama kuma tana abunta da taku ne, ko sau Waya basu sauka sun gaida Mommyn ba suna gida Waya abinci kuwa safe rana dare daga wurin mommyn ake turo musu, wayanshi ma kashewa tayi kar ma a kira shi don dama ya Wan samu hutun aiki.

Yau mommy na zaune a parlor tana mamakin wannan sabon hali na Saleem kasa shiru tayi ta kalli Sadiqa tace
"Yayanku kam duka cikin daaWin auren ne za'a kwana bakwai muna gida Waya bai iya lekowa ya gaishe ni ba? Daga shi fa har Sabrinar tunda aka haura da ita ban ga keyarsu ba"

Sadiqa tayi murmushi
"Ai za ki musu uzuri Hajiya mommy kin san sabon shiga, amma na san dai duk yadda ake ciki yau kam kila su sau?o kin san har da gajiya duka na hidima ya tarar musu"
Samha dai bata gamsu ba amma ganin mommy bata sake cewa komai ba sai itama ta share.
"Amma mommy ba kya tunanin akwai abin da yake damun Sameera? Yarinyar nan duk ta zama kaman ba ita ba don damuwa?"

"Toh Sadiqa ya zanyi? Na yi tambayar duniya ta ce babu komai kila ku in kun saka ta gaba zata faWa muku damuwarta"
Sadiqa tace
"Wlh ni dai ta ?i faWa min ban san ko Samha ba"
"kawai karatu ne fah! Kin ga tana ta shirin shiga final year abin babu sau?i"
Ba wai sun yarda ba suka bar maganan, Sameeran ce ta fito ta zauna za tayi magana suka ji motsin takowa kaman ana saukowa daga stairs duk ido suka zubawa staircase Win sai ga Sabrina da Saleem suna jerowa idanunshi na kallon ?asa yayin da take murmushi mai faWi har tsakiyar parlorn suka zo bai Wago ba, ganin zai fice mommy ta mi?e tsaye

"Saleem"
Waigowa yayi ganinsu ya Wan shafa kai
"Oh mommy ashe kuna nan, barka da safiya"
Speechless ta zama ta kasa furta ko A, Sabrina ta kalleshi
"Kayi sauri don Allah Ya Saleem idan ka dawo za'a yi gaisuwar"
Ba musu ya juya ya fice, ta juyo tana murmushi ta zo ta samu kujera ta zauna
"Mommy barka dai Fatan kina lafiya?"
Ido kawai suka zuba mata, da kyar mommy ta kawo musu uzuri a ranta ta zauna tana cewa
"Lafiya ?alau Wiyata ya zaman sabon wuri?"
"Lafiya ?alau mommy ai ba wani sabunta da yake duk gida ne kuma yayan yana kula da ni yadda ya dace"

Kai mommy ta gyaWa, samha da Sabrinar take sa'a da ita tace
"kin tashi lafiya?"
Murmushi tayi
"Lafiya ?alau ?anwar mu"
Harara ta maka mata Sabrinar tayi wani murmushi tana kallon su sadiqa tana jira su gaisheta.
Mommy ce ta musu ido duk suka gaisheta ta amsa kuwa hankali kwance ita matar yayansu
"Mommy kin ga ya fita yana sauri ko? Wlh Gaje ce bata ji daaWi ba kuma Bakinta babu taste kwadayi take ji shine na ce ya je ya sayi kayan kwalam sai ya kai musu gidan ya kuma bata kudin magani"

Mommy da kanta ya sake Waurewa tamau ta zubawa Sabrina ido sabon salo wai gada a kotu yaushe kuma aka fara hakan?
"Ah yayi kyau"
Abinda ta faWa kenan, Sabrina ta mi?e
"Bari na koma ciki"
Tana kai nan ta haura saman ta Barsu da tunanin me ke faruwa? Sai dai babu wanda ya je da nisa saboda mommyn na mata uzuri kuma tana son ta da Saleem Win sai suka kama wani hirar daban.

****

Yau sunday tun safe Afeefah ke tare da Mammi, hira suke yi kaman 'ya da uwa kafafun Mammin na kan cinyar Afeefah tana Wan matsa mata take cewa
"Mammi yau ?afafunki sun kumbura dama yana miki haka?"
"Yana yi Afeefah, ni kam me

19 / 53