HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   41 / 53

120K to 123K   out of 158.4K words

tun fitansu gida har hawansu jirgi zuwa sau?ansu magana Waya ake babu abinda basu gaya mata ba akan gidan sarauta sai ta tashi ta kama mijinta a hannu in ba haka ba ta ji a salansa.

Ruwa ta haWa a tray da cup mai tsananin kyau ta Wauka ta nufi Wakinshi, yana zaune bakin gado dafe da kanshi dake Wan sarawa ya ji sallamar ta, bai Wauka za ta shigo ba sai kuma ya ganta unexpected idanunshi masu shiga jikinta ya kafe ta da su yana yawo lungu da sa?o na jikin nata, tana sanye da doguwar riga peach mai roba ya fitar da duk wani shape Winta ta Waura dankwalin sai ta sako jelar guda Waya ya sauka har kan kirjinta tayi kyau sossai barin ma lips Winta dake shining na lip gloss.

Ruwan ta zo ta ajiye mishi tana Wan Sata fuska, fuskar yake ta bi da kallo bayan ta ajiye ta juya zata tafi karab ya ri?o hannunta ya Wan ja ta tayi baya baya ta zauna bakin gadon gefenshi har suna gogan juna ya juyo ya kalleta ba tare da ya saki hannun ba.

"HaWe ran nan fa?"
Yayi magana yana dan Wage gira guda alamun tambaya, lumshe ido tayi don maganan ta ji shi ne har cikin zuciyarta.

Bata san ta narke ba tayi shiru bata ce komai ba. Kuma sai bai ji haushi ba sai ma kyau da ta mishi yadda take yi da fuskan itama kuma ta ji daaWi da bai mata ihu ba sai ma Ruwan da ya Wauka ya sha kaWan ya ajiye yana dafe Goshi da hannunshi Waya har lokacin Wayan na cikin hannunta yana dan motsawa a hankali.

"Ba ka da lafiya ne?"
Ya ji tambayar nata sai ya buWe idanunshi da suka Wan sauya ya kalleta ya Waga mata gira Waya
"Sorry"
"Kin san Meyasa ban amsa gaisuwarki ba?"
Ta girgiza kai ashe ya san laifin da ya sakata fushin ma.

"Saboda ba haka ake gaisar da miji ba madam..."
Kan tayi wani magana ya ja hannun nata sai jinta tayi kirjinshi ya rungumeta ta runtse ido tana jin zuciyarta na chanza bugu, a hankali ta sa hannunta ta ri?e shi yayi baya baya ya jingina da jikin gadon ya Wan lumshe ido.

"Ya kike?"
Taji maganan daga sama, ita dai ta rasa gane kanshi so yake sai ya zautata ko menene?
"Lafiya ?alau, ina taya ka murnan reunion Winka da family... Na kuma ga naWi Allah ya taya ri?o"
Ya yi murmushi kaWan kan yace
"Ameen, thanks"
Suka yi shiru, ?o?arin Mi?ewa take ya matse ta

"Your perfume! Yana da daaWi"
Tayi murmushi
"Thank you, gashi na mata ne da na baka"
Dole ya saka shi dan murmusawa yadda take maganan bilhakki.
Sun dan jima haka kan aka kira azahar ya sake ta ta mayar da kanta ?asa tana wasa da bakin gyalen ta shi kuma yana kallonta.

"Kin gama exams lafiya?"
Tana mamakin yadda sai an manta wani abin shi kuma sai lokacin yake magananshi
"Alhamdulillah"
"Meyasa kika shiga toilet da waya kika jefa ruwa?"
Ta Wan zaro ido tana mamakin yadda aka yi ya sani shi kuma idanun yake kallo, haka kawai yaji baya so su daina maganan Dukda kanshi dake sarawa sai yaji in dai magana da ita ne ko za'a kwana kaman ba zai gaji ba, sanyin yanayinta, kamshinta, murmushinta da ma maganarta kashe shi suke.

Bayani take mishi amma Bakinta yake kallo har ta gama bai ji komai ba, jin ana shirin shiga sallah ya mi?e ya nufi bayi bai ce komai ba, ta girgiza kai ta dauki tray Win ta fito dayake Wakinshi akwai dan hanya tsakanin shi da parlor da hakan yasa tana gab da bayyana parlor ta ji Zarah na cewa Aisha

"Aisha kina ganin Ya Sameer zai yarda ya aureni? Wlh tun ranar da ya cecemu na kamu da son shi da na fahimci shine Yaya Sameer wanda nake da alkawarin aure dashi tun yaranta sai na ji na sake kara sonshi kalleshi kiga yadda yake komai cikin wani irin aji da natsuwa...ba ki ji kishin da Naji ba da na kalli matarshi"

Aisha tayi dariya
"Zai aureki mana kin taba ganin inda aka yi alkawarin aure aka karya shi a zuri'ar nan? Kuma ai na ga matar tashi tana da sanyi bare ma dolenta ta ga kishiya har da kwarkwarori ma idan yana so sarkin gobe fa take aure"

"hakane kam duk kishi na shiyasa nake dannewa sanin a auren sarki iya ruwa ne fidda kai kowacce ta iya allonta ta wanke ne, yanzu haka ba za'a rasa ma waenda suka nemi haWin aure dashi ba ta wurin mai martaba daga bayyanar shi zuwa yau"

Sossai maganganunsun ya daki Afeefah, bata san wani irin yanayi ta shiga ba ko motsi bata yi ba sai da ta ji ya buWe kofa ya fito sai ya tsaya yana kallonta tayi kokarin danne abinda ke taso mata ta fita parlorn ya bi bayanta ya fice masallaci ita kuma kan ta isa dining ma kuyanginta sun karSa...

"Ba Za mu isa kuyi sallah ba?"
Ta tambayesu tana danne yanayinta kwarai da gaske don for the First time a rayuwarta taji zafin wani duk abubuwan da ake mata a baya tana kokarin shanyewa kuma tana kokarin ta ga bata tsani kowa ba amma yanzu ji tayi bata son sake kallon Zarah a inda take, har Waci Waci take ji akan harshen ta maganan son da take yiwa Rayyan ke ta kai koma a ranta...

"Kar ki damu yanzu za mu tafi ma ai"
Kai ta gyaWa suka mi?e suna mata sai anjima tace
"Na gode sai anjima"
Suka fice ta nufi Wakinta ta samu bakin gado ta zauna tana dafa kirjinta dake zafi zafi, duk Wan farin cikin da ta samu a tare da shi ya kau.
Bata motsa ba sai da aka mata sallama ta ba da izini aka shiga sai ta kalli wata mata ce babbar mace rike da wani tray a hannunta wata kuyanga na binta a baya da akwati

"Barka da wannan lokaci ranki ya dade"
Nauyi taji na matar tace
"Ina yini?"
Matar ta kalleta lallai wannan ba tashin masarauta ba ce.
"Fulani FaWimatu ce ta aiko mu shirya ki mai martaba na son ganinku gabaWaya"
Kai ta gyaWa matar ta shige bayi ta haWa mata ruwa mai kamshin gaske ta mata iso cikin bayin ita dai ba don su jannah sun ce mata kar tayi musu a duk abinda ake sakata ba da zata ce musu ba sai ta yi wanka ba yanzu tayi wani amma kuma da ta shiga ruwan yadda aka hada shi ya mata daaWi da ta fito kamshi duk motsinta haka yake tashi.

Turaren kolecture suka bata mai bala'in kamshi ta shafa ko ina na jikinta kan ta shafa lotion Winta, da kansu suka shirya ta cikin atampha riga da zani da ya zauna mata sossai suka bata gyale ta yafa bayan sun daura mata dan kwali suka hada gyalen da Wan kwalin suka yi pinning yadda ba zai dinga zamewa ba kan suka Wora mata wani cream colour Alkyabba da yayi mata mugun kyau kaman ka sace ta ka gudu.

Ta kara turaruka Dukda kamshin ma da take ya isheta, kan suka fito gabaWaya ta samu su Abeeha a parlor
"Masha Allah Kin ga yadda kika yi kyau uwargidan Ciroman fombina kuma Yariman matasan fombina?"
Sai ta Wan yi murmushi kadan don uwargida da aka ce ya tuna mata kalaman zarah..
Suka fice gabaWaya aka musu jagora har babban parlorn mai martaba sun samu kowa na nan na kusa kusa dangi da ya kamata a ce sun sani.

Gaisuwa aka yi Mai martaba ya gabatar da Uncle Musa da su Uncle sanusi matsayin dangin Rayyan tunda su suka rike shi tun barin shi gidan har kawo yanzu, yayi musu godiya marar iyaka kan ya nuna su Abeeha matsayin 'ya'yanshi don ya ce a yanzu basu da maraba da su Aisha a wurinshi sai ya nuna Afeefah don Ammi dake gefenshi duk ta nuna mishi su dama kuma ya riga ya gaisa da su Uncle kan zaman duk Ciroma yayi introducing nasu.

"Ga 'yata Afeefah ita ce matar Ciroma, ina fata za mu cigaba da zama anan cikin zaman lafiya da haWin kai yadda muke tafiya, ina marabtar ku da shigowa wannan masarauta matsayin 'ya'ya masu daraja, duk wani abu da kuke so za ku iya zuwa kai tsaye wurina dukkanku matsayin uba nake a wurin ku kaman yadda na dauke ku duk 'ya'ya na"
Godiya duk suka yi Afeefah dai na matu?ar takure kuma zuciyarta bugawa yake kaman zai fito tana jin idanu sun mata yawa a jiki amma bata iya ta Wago ba har sarki ya sallami Matan suka fice

"Afeefah!"
Ta ji muryarshi ya kira sunanta sai taji wani iri, sunanta a bakinshi daban take jinshi chak ta tsaya ya matso har tana jin kamshinshi da ma numfashin shi dake fita a hankali...

"Ba na son duk abin da za'a baki a gidan nan ki ci! Idan ma ya baki sha'awa za ki iya fada min in nemo miki amma kar ki ci komai daga kowani bangare a gidan nan ina fata kin gane?"
Kanta ya ?ulle ta Wago ta kalleshi amma ganin idanunshi a kanta ya sa ta Wan gyaWa kai.

"Ki amsa min da bakinki, bana son jin cewa kuskure ne ko akasin hakan... Ba kuma na so ki fara tunanin dalili hope am clear?"
"In shaa Allah"
Kai ya gyaWa ya juya ya koma ita kuma tayi gaba ta samu su Jannah, aka fara raka su sashen Fulani Adama duk inda ta wuce kirari ake mata.

A ?asa duk suka zauna tana kame cikin kujera suka gaisheta ta amsa tana Wan murmushi
"?a ta Afeefah sai ga ki gidan sarauta, ina fata za ki ba da haWin kai wurin ganin an zauna cikin aminci kin ga nan ba kaman normal gidaje ba"

Tayi murmushi tace
"In shaa Allahu Mama"

"Sannan za ki yi ha?uri da tsare tsarenmu anan, duk muma ha?uri muka yi muke zaune lafiya ina fata in kin ji labarin alkawarin zarah da mijinki ba za ki ji haushin mu ba kar ki ga kaman daga dawowanshi ne aka bashi mata, kin san mu anan al'adar mu in aka haifi namiji da shekaru biyu ko uku ko ma biyar daga an haifi mace to za'a yi mishi alkawari wanda sai in mutuwa ce ta karya, kin ganni nan tun ban yi rarrafe ba nake matsayin matar mai martaba haka ma Uwar shi Ciroma amma kin ga duk muna zaune ne lafiya cikin amana da kula da juna"

Ta Yi mugun ?o?ari da ta iya danne hasalan da ranta ke yi tayi murmushi
"Eyyaaa Allah ya ba mu ikon zama lafiya na gode".
Sai kallonta Fulanin take har suka tashi suka fita ta sa aka bi su da kyautarta na maraba a ?warya rufe da faifai...

Su Jannah maimaita maganan suke da damuwa ita dai bata ce musu komai ba har suka shiga wurin Ammi suka gaisheta
"Afeefah kina lafiya kam?"
Ta gyaWa kai basu jima sossai ba don su Zarah suna wurin suka mata sallama itama kyauta sossai ta basu a ?warya suka nufi wurin Fulani Ameenatou kadaran-hadaran suka gaisa ta basu kyautarta suka nufi wurin Amarya Fulani Salimah itama suka gaisa kan suka nufi sashensu alkyabbar kawai take so taji ta cire ta huta gashi ana ta kiran la'asar, suna zuwa kuwa ta zame kayakin tas ta Wauki karamar riga marar nauyi mai hannun singlet dogo ne sossai silk Brown ta saka yana da tsagu gefe da gefe har wurin gwiwa ta hau gado ta kwanta kawai bata motsa ba.

Maganganun da ta riska yau kawai a gidan ta ji ya sire mata, bata san ta fashe da kuka ba zuciyarta na squeezing yana mata zafi ta ma rasa me ke damunta.
Ta Yi kuka har tayi bacci a haka sai Magrib ta farka ta dauki hijabi ta saka bayan ta wanke fuskanta idanunta dai har lokacin sun dan kumbura kuma sun yi ja ta fito parlor ta samu su Abeeha suka Wan yi hira ta ci abinci kaWan kan ta ce musu za ta kwanta kanta na ciwo daga haka ta shige Waki.

Abeeha tace
"Addah jannah baki kula Afeefah na da damuwa ba?"
Tace
"Na kula Abeeha ko nima ina taya ta damuwa ace daga zuwa yau an fara mata zancen zata yi ha?uri mijinta aure zai yi, na san zai iya yi probably tunda dama haka tsarin su yake amma kuma bai kamata ana fada mata ba gaskiya."
"Gaskiya sai Naji da ma bamu zo ba ni da nake murna, ashe abin da za mu tarar kenan ni haushina ma ko fa gama fahimtar juna basu yi ba."

"Dole mu san abin da za mu yi akan hakan Abeeha, ki ji mana ko mu yi amfani da kishin nata ne mu ?ara kusanta su?"
Shawara suka fara suna murmushi, Abeeha ta mi?e ta shige Waki jannah ta cigaba da zama don ita ce ma take dan iya magana da Rayyan Win ba tsoro ba komai tana nan zaune sai gashi kallo daya zaka mishi ka san ya gaji tiSis.

"Sannu da dawowa Yaya"
Ya amsa da
"Yauwa"
Zai wuce tace
"Wai da ma kai nake jira ne!"
"Allah ya sa lafiya"
"Da sau?i dai Yaya Afeefah ce tun Wazu take kuka wai kanta na ciwo ta sha pcm ma bai sau?a ba"
Ya Wan yi jimmm yace
"Meyasa baku kira ni ba? Kun san tana da low BP sai ta fara suma ne za ku yi aiki da hankali?"
Da faWa ya ?arasa ta Wan du?ar da kai
"Ka yi ha?uri"
Ya ja tsaki kan ya juya yayi Wakin Afeefar.

Ta saki murmushi ta juya ta nufi Wakinsu Abeeha na jiranta suka kashe suna dariya har da kwaikwayon masifar shi, shi kam yana shiga....




=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*50*

Kai tsayen bakin gadon ya nufa ya kai hannu ya yaye duvet da take lulluSe ciki, a hankali ya sau?e hannunshi a goshinta hakan ya sa ta Wan buWe ido ta kalleshi sai ta mayar ta rufe, ta sake buWewa idanunshi a kan wuyanta zuwa kan kirjinta da har saman ke a bayyane, muryarta yaji tace

"Ya Saraki!"
Sai ta sake mayar da idanun ta rufe, ?arasa yaye duvet Win gabaWaya yayi ya kai zaune gefenta yana kai tafin hannunshi ya shafa wuyanta da shima ya Wan yi dumi amma ba zafi ba.

"Kuka kika yi? Me ya sameki?"
Shiru tayi bata buWe idanun ba shi kuma bai daina shafa wuyanta da ya Wauki hankalinshi sossai ba, jin yana ta da mata da tsikar jiki yasa ta kai hannu ta ri?e hannun nashi cikin wani irin murya ta sake kiran sunan nashi

"Ya Saraki!"
"Na'am Matar masu sarauta."
Yadda ya amsan sai da ta buWe idanunta, sunan ya shige ta har inda bai kamata ya je ba.

"Mu je ki gayamin dalilin wannan kuka"
Ko motsi bata yi ba, ganin ta ?i motsawa Ya sanya hannu ya Wauke ta chadak sai jinta tayi cikin hannunshi bai sake cewa komai ba ya fice da ita zuwa Wakinshi, a kan shimfidadden gadon shi ya yi mata masauki zai kalleta don tunda ya Wauketan a bazata kallon fuskanshi take tana jin soyayyarshi na shiga jini da bargon ta tayi saurin rufe idanu, bai ce komai ba ya mi?e yaje ya watsa ruwa ya sanya kayan baccin shi ya rage wutan Wakin kan ya zo ya hau gadon ya kwanta.

Duk abinda yake tana jinshi, kwanciyarshi da janyota zuwa jikinshi duk lokaci Waya hannunshi zagaye da kwankwasonta Wayan a haSarta ya furta

"uhmm faWamin"

Da kyar ta iya samo kalmar
"Mene?"
Ta furta
"Abin da ya saka Matar Saraki kuka har ya ja mata ciwon kai"
Shiru tayi for seconds tsantsin rigar jikinta da kamshin dake fita daga jikinta har gashinta ya shagaltar dashi a hankali yake Wan bin jikin nata yana shafawa ba tare da ya sake magana ba. Chan tace

"Wai da gaske ku nan tun yaro na ?arami ake mishi mata? Da gaske sarki ba zai iya zama da mace Waya ba?"
Shiru yayi, chan ya ce
"Wa ya faWa miki wannan magana?"
"Kawai na ji ne a wani labari..."
Murmushi mara sauti yayi kishi ne ya sakata kuka kuma ya san tabbas faWa mata aka yi don wulakanci daga zuwanta an tarbe ta da abin da zai sakata kuka a banza, kwafa yayi bai ce komi ba
"Da gaske ne kenan?"
Ya ji muryarta na Wan rawa tayi tambayar.
"Shhhh ki yi bacci, za mu yi maganan wani lokaci"
Dole tayi shiru, hannunshi yake Wan bubbugawa a bayanta kaman mai rarrashin 'yar baby har tayi bacci ya sau?e numfashi yana sa?e-sake mai dumbin yawa har bacci ya sure shi shima a haka.

Washegari ko da ya tashi sallah ya san bata yi so bai tashe ta ba, ya gyara mata kwanciya kan ya mi?e ya shige toilet yayi alwala ya fice masallaci, daga nan ya tsaya suka gaisa da su Uncle sun jima suna magana da Saleem da duk yau suke zancen juyawa, sai da gari ma yayi haske sossai ya dawo bai sameta Wakin ba amma ta gyare tsaf ta saka turare ya tsinci kanshi da murmushi kaWan kan ya wuce yayi wanka bayan ya shirya yana ma shirin fita ne ya ji sallamar ta.

Ya amsa yana mayar da idanu kanta sai ya lumshe su ya sake buWewa, yarinyar tana fusgar hankalinshi fiye da yadda zai misalta sanye take da wani coffee doguwar riga mai shige da material amma yana da kauri an tattare kirjin ?asan a sake wane umbrella suna haWa idanu ta kawar da nata don bata iya jure kallon cikin idanunshi barin ma in yana binta da mataccen kallon nan da ya tsira, gaban kujeran dake dauke da table ta ajiye mishi tray Win da ta shirya abincin kaman ka kwace don kyaun da yayi a ido, doya ne dafaffe da sauce na manja kana ganin kifi nasha nasha a ciki da kuma dafaffen kwai cikin Miyar, sai dafaffen plantain da ta musu wani yanka mai kyau, da tea mai kauri cikin mug sai da ta ajiye ta Wago lokacin ya matso dab da ita.

"Good Morning!"
Ta faWa har lokacin bata wani fara'a don ba wani daaWin zuciyarta take ji ba, hannunshi na dama ya mi?a mata alamun su yi musabaha sai ta sanya nata ciki a hankali, da sanyawar

41 / 53