HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   27 / 53

78K to 81K   out of 158.4K words

kanshi a gefen kafaWarta sai ta ji hucin zafin jikinshi na sau?a Mata, hannunta ya kama
"Mammi in shaa Allahu zan yi amfani da duk abin da kika ce"
Daga haka bai sake magana ba, ta san a takure yake ta kuma san akwai abinda ke cinshi a rai a yanzu haka wanda bata tantama shi ya haddasa mishi zazzabi kuma muddin ya cigaba a haka ba zai yi bacci ba amma sam ba zata tambaya ba, ba za ta matsa mishi ba.

"Ka tashi ka sha magani Saraki"
Ta faWa, da kyar ya buWe lumsassun idanunshi da suka rine ainun ya mi?e zaune, karbar pills Win yayi ya sha wanda ta haWa da panadol a hankali ya kalli time karfe tara ne da wani abin, Mi?ewa yayi yana mayar da hannayenshi cikin aljihun hoodien jikinshi cike da dauriya yace
"Sai da safe"
"Allah ya baka lafiya"
Ya amsa da Amin kan ta mishi sai da safe ya fice da kallo ta bishi ta san sai a hankali zai saba da wannan sabuwar rayuwar kuma, ta san sai Afeefah tayi ha?uri ta kara juriya kafin ta samu yadda take so da shi matsalar kawai ya kasance ta shiga ranshi murmushi ta Wan saki kan ta sha nata maganin itama ta shiga don kwanciya saboda kowa ya tafi ba?i kam duk babu kowa.

Wani iri yake ji a haka ya kutsa kanshi cikin parlorn bakinshi Wauke da sallamar da iya shi kaWai ya san yayi kayanshi, taku biyar yayi ya samu kujera ya zauna yana dafe kanshi da kaman zai rabe gida biyu, numfashi ne yake mishi wahalar fita kuma ya san yanayinshi ne da tunanin da ya saka a ranshi, wani irin zafi yake ji kaman ana Wora mishi wuta a kan zuciyarshi ina ma da zai iya da kuka zai yi da ihu zai yi ta yi sai ya samu salamar abin da yake ji a ranshi, zamewa yayi ?asa kan carpet ya Wora kanshi a kujeran yana rike zuciyarshi ya jima sossai cikin wannan yanayi sai da ya Wan samu relief ya mi?e ya nufi Wakinshi kai tsaye, ruwa ya sha har gora uku kan ya shiga zame kayan jikinshi daga wurin yana nufan bayi, ruwan sanyi ya sakarwa kanshi yana yamutsa gashin kan nashi a lokaci Waya yana dan buga glass Win wurin wankan da hannunshi.

Sai da yaji zai iya faWuwa idan bai bar wurin ba ya fito Waure da towel ya hau gadon ya kwanta ko ruwan jikinshi bai tsaya tsantsanewa ba ya ja bargon ya rufe har kanshi ba wai don zai yi baccin ba don ko ya rufe ido abin da ya tsana yake kallo.

Ita kam Afeefah dama ta san ba zuwa zai yi ba, bayan kowa ya tafi ta mi?e tana kallon Wakin har lokacin zuciyarta ke maimaita mata wai ita ce fa matar aure, yanzu ita ta tashi daga buduruwa matar auren ma wai matar Rayyan, Allah buwayi gagara misali Allah mai yadda ya so a lokacin da ya so, a hankali take bin Wakin da kallo ya ji kaya iya kaya yayi kyau fiye da misali gashi wadatacce don za ta iya komai free ciki yana da girma, akwatunan da aka jera mata ta bi da kallo guda goma sha biyu wai akwatunan aurenta ne, ita dake da kayan da basu wuci biyar ba ita dake fama da allura da zare a kullum tana facin kaya ita dai Afeefah Annoba kuma Mayya, sai hawaye suka fara sintiri a idanunta tana jin karin imani tana jin wani irin yarda da ubangijinta.

A haka ta shiga bayin shima ta ?are mishi kallo komai na 'yan gayu, bata yi wanka ba don sai da tayi wanka ta saka kaya aka kawo ta karamin akwatin da Abeeha tace mata kayan bacci ne ciki ta buWe ta duba silk riga da wando cream Color yana da adon Black lace daga kirji da kuma ?asan kafafun wandon ta saka, kamshinta da kamshin Wakin har ya so yayi mata yawa ga sanyin Acn dake busawa kashe wutan tayi ta hau gado ta kwanta tana sake jin salama a ranta sam bata wani sa damuwar rashin ganin Sarakin ba don ta riga ta sakawa kanta ha?uri da juriya har Allah ya kawo karshen komai Dukda bata san yaushe ba bata san ko karshen zai zo ba amma she have her trust in Allah zai mata komai ba sai ta damu kanta ba Adu'a ne babba kuma zata cigaba.

Washegari da safe bayan tayi sallah ta Wan koma bacci, ?arfe tara ta farka ta sau?a daga gadon da kaman kar ta tashi tsabar daadinshi da take ji ta wuce bayi ta yi wanka ta fito ta fara neman kaya cikin sababbin dinkunan da telan Jannah ya chanchada mata, wani atampha doguwar riga A shape ta fitar ta shirya ciki tayi kyau sossai ta feshe jikinta da turarukanta sababbin waenda kamshin suka yi mata ta kafa Wauri, bata sa kwalli ba sai ta saka lipstick kawai accesories da tayi anfani na silver sai suka ?ara haskata tayi kyau ainun gidan ba ba?onta bane amma sai ta fara tunanin ta saka gyale ne ko kar ta saka?

Tsoro take kar ta fita su haWu don yanzu ba kaman da bane da ba lallai ma su hadu ba in ba wurin Mammi ba, a hankali dai ta sa hannu ta buWe kofan Wakin ta sanyo kai cikin parlorn, ko taku biyu bata yi ba idanunta suka sau?a kanshi a farko ta tsorata sai kuma ta fahimci kaman bashi da lafiya ne don ga matar da take matsayin likitarshi zaune a kujeran dake fuskantar shi, yayi relaxing sanye da wasu blue pjamas riga da wando complete, kafafunshi babu takalmi suna lume cikin tattausan carpet Win dake shimfide parlorn, fuskarshi yayi ja sossai haka gashin kanshi a hautsine.

Wani iri taji a ranta sai taji tausayin shi na bin jikinta kaman ruwa, ta riga ta san dalilin da ka iya kawo mishi ciwon a hankali ta shigo cikin parlorn Likitar na kallonta ta saki murmushi itama ta mayar mata a hankali ta Wan du?a ta gaisheta ta amsa da kulawa tana tambayarta Ya Rayyan da jiki? Ita dai ta amsa da da sau?i amma bata ma san bashi da lafiyan ba sai yanzu.

A hankali ta kalleshi idanunshi na a lumshe har lokacin, matar ta mi?e
"Allah ya baka lafiya zan zo gobe da safe, please make sure ka ci abinci ka sha waennan pills Win"
Ta karashe tana ajiye mishi wasu pink pills a roba.
Sai a lokacin ya Wan buWe ido
"Thank you"
Tayi murmushi ta yiwa Afeefah sallama ta fice.

Sai aka bar su su biyu a parlorn, yatsina fuska yake don kamshinta har kanshi yake ji ba tun yanzu ya fara ji ba tun ranar da suka same shi a dining da Abeeha ya iya bambance nata kamshin da na Abeeha, yanzu ma gashi ta zo ta tsaya mishi sai hawa kanshi yake tsaki ya Wan ja ya buWe ido sai karap suka hada idanu don kallonshi dama take tana tunanin ta inda zata fara gaishe shi ganin ya kalleta sai tayi saurin cewa

"Ina..kwana!"

Ya yunkura ya mi?e zaune da kyau, bata yi zaton zai amsa ba sai jin deep and calm voice Win shi da bai yi matcing da situation da yake ciki ba ya ce
"Good Morning!"

Daga haka ya mi?e ya wuce ta ya shige Wakinshi, ta sauke numfashin tsoro tana nufan kofa saboda knocking da ake, masu aiki ne rike da baskets na abinci kai tsaye suka jere mata su a dining suna gaisawa don sun saba da juna dama, plates, cups da spoons taje ta Wauko ta zo ta ?arasa haWa dining Win amma bata sani ba ta kirashi ne ko ta kyale shi, ta san ba zai so shisshigi ba in ta dameshi ya iya karyata don ya sha ambata kalan ya zo ya faru ta shiga uku, abincinta ta zuba ta ci har ta gama karyawa bai fito ba don haka tayi sashen Mammi don ta duba ta.

A zaune ta sameta ta gama karyawa tana shan magani tana ganinta fuskarta ya washe da fara'a
"?iyata ni da nace yau za ki huta sossai sai ga ki da sassafe? Sannu da zuwa"
Yadda take mata sai ya saka kunya kamata kaman wacce ta fito daga wani unguwar, a ?asa ta du?a ta gaisheta tana mata ya jiki.

"Alhamdulillah dawo nan gefena Afeefah, ina shi Sarakin?"
Wani kunyar ne ya sake lullubeta ta kasa magana Mammi tayi dariya kawai ta janyo wayanta ta kirashi
"Jiya ya tafi anan ban gamsu da yanayinshi ba, kun gaisa da safen nan?"
Kai ta gyaWa
"Eh na fito na same su da likitan shi suna magana"
"kin ga ko, sai in rasa Meyasa yake ajiye damuwar da baya bayyanawa yanzu baya so in sani ne ya ?i zuwa nan tun sassafe na kira ban same shi ba je ki ce ya zo"

Gabanta ne ya faWi rassss, ta ya zata fara kiranshi? A hankali ta mi?e ta fice zuciyarta na racing har ta shiga parlorn inda Allah ya taimaketa ma ta samu yana parlor a zaune kan dining yana karyawa wayanshi na a speaker alamu waya yake, a gefenshi ta ja ta tsaya sai ta ji Muryar dake tashi kaman ta san Muryar kuka me Muryar take har tana shidewa a hankali take cewa

"Ya Rayyan bakin cikin Ya Saleem zai kashe mana Mommy, duk abubuwan da ya dinga yi a baya mai sau?i ne yanzu ya kore mu ya saka surakanshi a gidan, bai damu da mun ci ko bamu ci ba, mun yi karatu ko ba mu yi ba muna lafiya ko babu tun muna zuba ido yanzu wata kenan da ko mun je gidan ba'a bari mu shiga, ga mommy kwance a asibiti saboda damuwa da hawan jini...!"
Dukda maganan da take yi Win ya shige shi sossai, damuwa ya nuna a kan fuskarshi sai dai bai tanka ba har ta gama ta cigaba da kukan.

"A wani asibiti take?"
Ya jefa maganan a hankali

"Tana 44 ne, anan muke da file"

Kai ya gyaWa kan ya katse wayan, Afeefah dake tsaye jikinta ne yayi wani irin sanyi a hankali zuciyarta ke motsawa da wani irin yanayin damuwa ba dai saleem da ta sani ake magana akai ba? Amma ai wannan Muryar ta Sadiqa ce, saleem ne har ya kori mahaifiyarshi a gidanshi? Ko jikinta duka kunnuwa ne ba zata yarda yana cikin hankalinshi yayi hakan ba, Wani irin tashin hankali ne ya zo mata har ta kasa boyewa ta manta waye a gabanta tace

"Yaya Saleem ne cikin wannan hali? Shi ne ya kori mahaifiyarshi da kanshi? Su Samha ne ke cikin irin wannan damu..."
HaWa idanu da suka yi ya sa maganar ta katsewa idanunta har sun cika da kwalla suna shirin zubowa, gani irin kallon da ya mata ya sa ta saukar da idanun ?asa, ajiye spoon Win hannunshi yayi ya zari wayan bai mi?e ba yana nuna ta da wayan ya ce

"Kika kuskura kika sake hawaye Waya ya zubo miki a kan fuska za ki gane ba ki da wayo...!"

Mukut haka ta haWiye kukan zuciyarta na cigaba da racing cikin mixed feeling ga idanun da ya zuba mata yana jira ya ga zata yi kukan ne ko ba zata yi ba ga damuwar halin da ta ji wai saleem na ciki.

"Mam..mi na ?iran ka"
Ta faWa a Wan tsorace. Kwafa yayi ya mi?e ya fice daga wurin da sauri ta dafa dining Win tana jan kujera ta zauna....




=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*34*

*Don Allah readers ina Wan so ne in ja hankalinmu a kan wani abu da na fahimta, zan Wan yi magana ne da miyaun marubuta. A duk sadda marubuci ke rubutu ba duba iya zallar nishadantarwa yake ba ko da kuwa littafin akan nishadi ne, ba son rai ake dubawa ba saboda ba shi ne ake son isarwa ba, duk sadda marubuci ya Wora alkaminshi a kan Littafi tunanin farko da zai fara shine me ya kamata na isar? Shin wani sa?o ne nake da shi a cikin labarin nan da zan ba al'umma kuma su amfana da shi? Kar mu raja'a ga iya fannin nishaWi ko soyayya don rayuwa bai taSa tafiya babu ?alubale ba... Don haka don Girman Allah mu daure muna karatu ta fuskar Waukar darasi don akwai darusa masu yawa da marubuci kan jefa a cikin kowani labari wanda ba sai an fito fili an ce yi kaza kar ka yi kaza ba mu dinga kokari muna fahimtar hakan saboda mu marubuta mu samu ladar ku=?O?=?O?*

****

Da kyar ta iya danne kukan da ke taso mata, tsoron Allah na ?ara rufeta tana tuna irin iko da isan mommy akan saleem ashe har za'a iya samu macen da za ta raba wannan iko da isar cikin lokaci kankani haka?
Mi?ewa tayi ta nufi sashen Mammi, ba za ta zuba ido rayuwar saleem ya cigaba da tafiya a haka ba don salim ya cika mutum cikakke Wari bisa Wari ya taimaketa a sadda bata da mai taimako bayan Allah, shi ne namiji na farko da ya fara nuna mata so tsakani da Allah ba tare da kyama ko tsoron tabbatuwar zancen al'umma a kanta ba, ya hana hawayenta zuba ya kuma ?arfafa mata gwiwa akan jajircewa da ha?uri da rayuwa, ta san babu abin da zai saka saleem saSawa mahaifiyarshi don ya san darajar ta fiye da kowa face sharrin asiri. Abin da ya sake bata mamaki ya Waure mata kai shine ta yaya wacce mommyn ta yarda da ita har ta aura mata saleem ba tare da yana so ba ta zama sanadiyar rabuwarta da Wanta? Sam bata kawo cewa ko alhakinta bane saboda ta san ita Win ba dolen su ba ce da su taimaketa da kar su taimaketa duk wannan tsakaninsu da ubangiji ne yo waenda suka zama dolen nata ma basu mata ba sai bare ne za su mata?

Ta saka a ranta son zuciyar mommy ne ya janyo mata wannan wahala da suke ciki, tayi negleting duty Winta a matsayin uwa tana ganin dabararta shi zai sa 'ya'yanta su cigaba da zama ?ar?ashin ikon ta alhali 'ya'ya ba ababen iko da gadara bane ta manta Allah ne ke da dukkan iko akan bayinsa kuma shi ne ya san abin da yake fili da na Soye.
Ko da ta isa wurin Mammi bata samu Rayyan ba, zama tayi cike da damuwa tace

"Mammi Yaya saleem na cikin masifa"
Ta ?arasa idanunta na cika da kwallah, Mammin ma ta fahimce damuwar Afeefar don Saraki ya sanar da ita komai kuma tausayin Saleem Win duk ya rufeta itama.

"Yanzu Saraki ya gama sanar mini, nayi mamakin yadda aka dau lokaci bai zo ba har ma aka yi auren Saraki saleem ba ya a kusa da shi ashe abin da ke faruwa kenan, laifin mahaifiyarshi ne Allah ya sa wannan abu da ya faru ya zame mata Aya ya sa ta hankalta"
Kai Afeefah ta gyaWa tana amsawa da
"Ameen ya rabbi, Mammi ina so in taimaki Saleem Dukda ban san me Ya Saraki zai yi ba amma ina so in ba saleem gudummawa kaman yadda ya ba ni a sadda na rasa madafa don Allah ki taimakeni akan hakan"
Ta ?arasa a karye.

"Me kike tunani Afeefah?"
Mammi tayi tambayar cike da kulawa.
"Mammi ina so ki yi convincing Ya Saraki akan za ki dinga bashi magani yana saka saleem sha ni kuma zan dinga haWa zobo ko wani kalar drink da ayoyin da mafificin annabin mu annabi Muhammad (SAW)
Yayi mana umarnin amfani da shi don karya sihiri, ko da kurba bibbiyu zai yi Allah zai ba mu nasara kuma ina so zan yi wani abu na sadaka da tawassilin Allah ya dube shi ya dawo dashi hayyacinshi kar mahaifiyarshi ta mutu da damuwarshi"
Sossai Mammi ta yabawa hankalin Afeefah ta kara jin kuma tabbas bata yi wa Rayyan zaSen tumun dare ba, ta gamsu kuma da shawarar don haka ta tabbatar mata zata bata duk wani taimako da take so.

Afeefah ta ji daaWi ta koma Waki ta fara neman takardar ta da tayi rubutu akan hakan a sadda malaminsu na islamiyyat ke koyar da su, ta kuwa samu bayan dogon bincike Adu'a kawai take a ranta Allah ya taimaketa.

****

Rayyan na fita Asibitin ya wuce kai tsaye ya samu kuwa mommyn na jin jiki yaran sai kuka suke yi, har ranshi tausayinsu yake ji kuma yana jin su ne tamkar su Abeeha, shi karan kanshi a yanzu ya gamsu cewa asiri ne ke dawainiya da abokin shi in ba haka ba ko mahaukaci ai ya san girma da darajar uwa.

"Kukan nan me zai yi mata? Ko ba ku san Adu'a shi ne makamin ko wani mumini ba? Ko kukan lafiya zai bata?"
Da Wan faWa yayi maganan don sun cika mishi kunne, duk shiru suka yi don sun san shi baya Waukan nonsense da likitan da ya duba ta yaje yayi magana don anan Win ma yana da office kuma yana aiki da nan Win Dukda ya fi zama Capital.

Daga nan ya shiga ya duba ta tana bacci ya dawo ya kallesu yana so yayi magana da hankalinsu zai kwanta bai iya ba sai cewa yayi
"Komai zai wuce in shaa Allah"
Daga haka ya zaro kuWi mai yawa ya basu kana ya fice, yana shiga mota Mammi ta ?ira shi a waya.

"Saraki idan ka samu Saleem ko da a waya ne kar ka yi mishi magana da tashin hankali, ka bi shi da lalama kuma kar ka tsananta magana akan mahaifiyarshi da 'yan uwanshi ka nuna baka damu ba don kar matar tashi tayi yunkurin shiga tsakaninku don akwai abinda nake so kullum ka tabbatar kana bashi yana sha, shi ramin ?arya a koyaushe ?urarre ne zai wuce ne kaman ba'a yi ba"
Ya gamsu kuma ya san Mammi wani abin zata sama mishi na karya sihiri ya ji daaWi don bai san ya zai yi ba, ya tabbatar saleem a gidan ba zasu barshi yayi komai na malamai ba bare yace zai kaishi wurin wani mala??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????mi. A kan ibada da azkar ne zai

27 / 53