HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   2 / 53

3K to 6K   out of 158.4K words

ta saka mishi ya koma cikin matasan da suke tare ya shiga ci ita kuma ta fara tattare wurin cikin natsuwa da sanyinta sai da ta gama zuba komai cikin wheelbarrown tana jiran matashin ya gama ya bata plate sai kawai ta fara jin hayaniya na tashi, Wago kan da zata yi sai ta ga wannan saurayi ne dafe da ?irji yana tari sossai da sossai har filate Win ya faWi ?asa abincin ya tarwatse ya bi abincin yana tumurmusa a ?asa, kan kace kobo wurin ya cike da mutane wasu na cewa ya mutu wasu na cewa da sauran ranshi.

"Me ya ci ne? Me ya same shi?"
Abin da mutane dayawa ke tambaya kenan, ita dai Afeefah na kafe a wurin ko motsi ta kasa sai gangar jikin da mutane suka yi wa zobe kwance ta zubawa idanu kaman daga sama ta ji Muryar wani na cewa
"Daga fa sayan abincin yarinyar chan kun ga bai ma gama ci ba...! Ku taimaka mu kaishi asibiti kar ya rasa rayuwarsa kumfa ne a bakin sa"
Cikin jimami ya ?arasa
Wata murya taji tana cewa
"hohoho asshaa dama na san aje aje sai ta fara yiwa mutane dauki WaiWai shiyasa ban taSa sayan abincinta ba, yarinyar da ri?a??iyar Mayya ce an ce ma ita ce mataimakiyar shugaban Mayu yanzu?"
Ko motsi bata iya ta yi ba taji an damketa zuciyarta kaman zai fito waje ba na tsoron abin da mutane zasu iya yi mata ba sai na tsananin tsoron mutuwa, mutuwa na daga cikin abinda a yanzu yake gigitata dole duk mai imani ya tsorace mutuwa a yanzu yaron nan ke mata magana a yanzu ana cewa ya mutu? Ta yaya? Meyasa sai da ya sayi abinci a hannunta?

Wani mai ?irar ?arfi ya hankaWata tsakiyar mutanen

"Ke tsallakeshi sau uku ki sakar masa kurwa yanzu wallahi ko mu she?a ki barzahu.."
Yayi maganan da karaji yana zaro wu?a mutane suka fara kananun maganganu masu zaginta na yi, wasu har labari suke bayarwa na ta kashe iyayenta ai maitar gado ne tun a ciki ta fara kisa, hawaye masu zafi ne suka shiga gangaro mata a sadda take tsallakeshi a dole, kalaman da suke shiga kunnuwanta sun yi mata girman da ba zata iya Wauka ba, abin tashin hankalin ma shine yaron bai tashi ba, ya tabbata ya riga ya rasa ransa ko kan ta gama fahimtar kanta har tayi wani yun?uri an rufe ta da duka, ko yunkurin kare kanta bata yi ba don a yanzu ita ma ta fi ?aunar mutuwar da rayuwa, da kyar wasu dattijai suka kwace ta fuskanta har ya fara sauya kamanni wasu sassa na jikinta na zubar da jini, kwanukan inna larai da kulolinta an yi daga daga da su, ko kasheni ka Waukanta (lalitar kuWi) bata gani a jikinta ba.

Wani irin deep kuka take yi mai taSa rai, dattijon ta kalla
"Don Allah baba ka bar su su kasheni kawai nima ina so in huta, don Allah ku bar ni su kasheni"
Abin da take ta maimaitawa kenan tana gunjin kuka ya ri?o hannunta
"Ki natsu yarinya babu mai kashe ki, shima kwananshi ne ya ?are ya mutu kiyi hakuri ki tashi mu raka ki gidan ku"
Cikin in-inaa take cewa
"in naje gi..gidan ma ba..ba tsira z..Zan yi ba kuWin inna larai da kwanukan ta duk babu"
Ta sake rushewa da kuka, tausayinta ne ya kama su suka haWu suka tasa ta gaba har gidan, kawu suka fara nema ko da ya fito da kallon tsana ya shiga bin ta.

"Yau kuma magana kika janyo min ko? Kayan uban wa kika sata ko uban wa kika kashe??"
Dattijo Waya daga ciki yace
"A'a malam labaran ya kamata ka fara tambayar raunin jikinta ne amma damuwarka wani abu daban? Ka san yaran zamani da kansu a koyaushe baya gayamusu daidai akwai wani yaro da ya sayi abincin 'yar wajenka yana cikin ci sai Allah ya turo da ajalinshi a take ya tafi shine suka yi yunkurin kasheta a cewar su ita ce ta cinye kur..."
Tuni ya katse su
"Ai da kun barsu don ni baku burge ni ba sam, da kun barsu don ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba ita ce nan ta kashe shi, sai ki shiga ai ki jira zuwan iyayenshi tunda ba kowani mahaukaci bane zaki mishi asarar rai ya barki ki sha ba"
"Ashshaa amma...."
"Babu ruwanku! Tunda kun kawo ta zaku iya tafiya" ya cigaba da mita kaman zai ari baki yarinya ba jari zata kawo mishi ba, ba auruwa za tayi ba babu wani amfanin da take mishi sai cin abincinshi amma kullum bacin ranta ya fi na kowa a ranshi.

Dattijan suka juya suka tafi ita kam kanta ?asa zuciyarta na wani irin karta, hawaye kuwa sun ki kafewa a idanunta kafafunta da suka matu?ar yi mata nauyi take kokarin Waga wa ta shiga cikin gidan taji an fusgo ta har tana taga taga zata faWi wuyan hijabin jikinta aka sha?o
"Ina kudina da kayana?"
Kakari take don ko numfashi ta kasa sha?a, idanunta da suke manya suka sake fitowa ainun sun rine sun chanza gabaWaya.

Inna larai ganin zata yi kisa ya sa ta HankaWata bata damu da kokawar saisaita numfashin da take tayi ba ta daka mata tsawa
"nace ina kuWina?"
"In...nn..a B..ban san ya ak...a yi ya fice daga ji..jikina B.."
Hayewa ruwan cikinta tayi ta shiga Wirkarta kaman an aiko mata ita
"kaman kuwa yadda ya fice baki sani ba haka sai na rabaki da numfashinki baki farga ba, wlh dukan kuWina yau sai na yi miki shi"
Ko karfin kare kanta bata dashi sai da dukan yayi yawa ne kawu Labaran da ke kishingiWe yana sakace ha?orinshi ya fito ya Waga inna larai
"ke kar ki yi min kisa a gida"
Yana kai nan ya juya ya bar wurin ta cigaba da sababi da zage zage karshe ta tafi ta barta nan yashe.
Yaran gidan bayan sun gama kwasar dariya kowa ya kama gabansa

Inna Asabe ma na girki tana zaginta da tsine mata don yau ta yi mata asarar tallar yamma tunda yanzu ko ta fita ba su da tabbacin akwai mai sayan abin hannunta irin wannan suncewar zani a kasuwa da tayi musu, ta fi mintuna goma a kwance a wurin kan da rarrafe ta shiga akurkinta ta faWi bisa taburma tana kuka kaman ranta zai fita.

Ko mintuna biyu bata yi da shiga Wakin ba tana yashe a inda take ta soma jin hayaniya tamkar ana ya?i, idanunta sun kumbure ko iya buWewa da kyau bata yi, bata san ya aka yi ba sai ji tayi an janyota tamkar tsumma an fitar da ita, sama sama take jin mutane na ta hayaniya tana hangar sanduna da makamai na tashi sama ana ikirarin kasheta kaman yadda ta kashe musu Wa matashi, bata san ashe rigimar har su kawu ya shafa ba don sun rantse in ba'a fita da ita ba gidan gabaWaya za su ?ona, tashin hankalin da bata taSa shiga ba ta shiga a ranar, bata san ya aka yi 'yan sanda suka iso wurin ba don ana ta janta tamkar kaya ko takarda Muryar kawu na ihun kar su ?ona masa dukiya ita suke so don haka ga ta nan su kashe ta. Fusgar ta aka yi aka wulla ta motar 'yan sanda suka ja suka yi ofishin su da ita...



=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*003*

Bayan tsawon lokacin da ba za ta iya cewa gashi ba ta ji sau?ar ruwan sanyi a kanta duk da ta farka sai dai bata da kuzarin Waga ko da yatsar hannunta ne.

" In ba kema da ja wa kai ba ina ke ina cin maita don janyowa mutane bala'i ki mutu a ce ai ba ma aikinmu ne yadda ya kamata. tashi my friend"
Ya ?arasa yana kai mata kafa.
LaluSe take har ta samu ta mi?e zaune gajimare ya rufe mata ido bata iya ganin komai. Ma?ogoronta da ke bushe ko miyau ba ta iya haWiyewa sai kartar ta yake da kyar ta buWe baki ta ce
"R..ruwa..a don Allah"
Ruwan ya tura mata ta Wauka ta afa a baki har kwarewa take sai da ta sha sossai cikinta ya murWa don dama babu komai ciki ai sai amai tana jin Wan sandan na zaginta amma ba za ta iya tsayarwa ba ya riga da ya zo, a lokacin idanunta sun washe tana gamawa ya tasa keyarta ta kwashe ta share wurin cikin layi.

A lungun cell Win ta raSe tana ta aikin ri?e ciki saboda yunwa, Waya dan sandar ya taso yana ?are mata kallo
"Ya dai?"
"Yunwa nake ji"
Murmushi yayi yana gyaWa kai yana sake ?arewa halittarta kallo Dukda rama ya yi mata yawa ainun albarkatun jikinta na daidai shekarunta ba su Suya ba sam.
"Zan sayo miki abinci amma kin san gomnati ta hana aikin banza ko? Nima za ki rama min"
Sam bata wani fahimta don yunwa ba ta da hankali samm kai kawai ta gyaWa ya fice chan sai gashi da filate ya mi?a mata ta fusga ta shiga ci hannu baka hannu ?warya sai da ta fara koshi tukuna ma ta fahimci ashe gari ya waye kenan a cell ta kwana gashi har ana batun ?iran sallar azahar tsabar rashin gata babu wanda ya neme ta, ta tabbatar ko shekara zata yi nan kawu ba zuwa zai yi ba bare ya cire kuWin shi yayi belinta don sun ce sai an ba su kuWin mai za su sake ta...

Bayan ta gama ta ro?i za tayi sallah basu hanata ba ta rama duk waenda aka bi ta. A nan ta cigaba da zama ita daya har dab Magrib wani matashin Wan sanda ne ya shigo yana dubanta
"Ya Sunanki?"
"Afeefah"
"ba ki da kowa ne da zai zo yayi belinki?"
Ta girgiza kai
"Ni marainiya ce kawu na kuma na san ba zai taSa zuwa ba ko shekara zan yi"
'dan shiru yayi
"Afeefah za ki iya komawa gida da kan ki?"
Ta gyaWa kai
"tashi ki tafi to zan biya kuWin belin naki, bana so dare ya sake samunki a nan muna da gurSatattun 'yan sanda bare har kin bari kin ci abin hannun kopur DanJuma sai ya dawo, kuma ba ni da ?arfi ko ikon kare ki"
Hawaye ne suka cika kumburarrun idanunta ashe akwai masu zuciyar imani da tausayi a cikin 'yan sanda? Godiya tayi ta mishi har da kuka a lokacin da zata fita ta ce
"Menene sunanka?"
"Sa'adu. Sa'adu Rabi'u"
"Allah ya dube ka ya shiga cikin lamuranka ya dafa maka"
Amsawa yayi ta fice da sauri lunguna tayi ta bi a tsorace kar ma ta haWu da kopur Danjuma har ta isa gida.

"Uban wa yayi belinki?"
Kawu dake kofar gida ya daka mata tsawa
"Su...su suka sake ni"
Takalman shi ya wuwuro ya jefa mata
"shegiya natacciya dama shiyasa ake cewa mutum maye mana in ya cika naci, kin rantse sai kin kasheni ko? To kafin nan sai na yi ajalinki marar anfani kawai"
Da gudu ta shiga gidan don ya mi?e ya biyo bayanta kaman zai faWi.
?akinshi ya shiga ya haWo tarkacen da ya karSo na kare kai daga sharrin Mayu yayi Wakinta dorinarshi ya samu ya rufeta da duka wai na hawan jinin da ta saka mishi jiya ta kusa ja mishi asarar rai da dukiya babu wanda ya kula su duk ihu da neman agajinta sai da ya gaji ya kyaleta. Ya sa aka kawo mishi garwashi ya turbune su da uban haya?i mai bala'in ?auri bayan ya gama ya tafi ya barta nan yana cigaba da sababi.

Bata san iya adadin lokutan da ta Wauka a kwance cikin yanayin ba, tun tana kuka da hawaye har suka ?afe sai dai zuci na cigaba da zubar da kwalla cikin ?unci da raWaWin da bata san ranar tsayuwarshi ba, yunwa ne kaman zai yi ajalinta hakan ya sa ta dole ta lallaSa ta fito, yadda garin yayi shiru sossai za ka san cewa dare ya riga da ya tsala murhu ta isa akwai sauran gawayi ta dibo ruwa tana layi ta Wora, a wurin ta zube tana kallon kicin Win babu alamar an ajiye mata wani abu da zata iya ci, busashen miyau da ya ?afe a Bakinta ta lalaSo da kyar ta HaWiye.
Sai da ruwan ya tafasa ta juye hadari ne sossai a garin don har an fara iska da walkiya sai dai dayake zuciyarta a kafe yake yasa babu tsoron komai cikin ranta ta shiga ta gasa jikinta sossai ta fito, kicin Win ta koma da kyar ta samu wani kanzo ta Wan bubbuga ta zuba ruwa yayi laushi ta Wauka ta nufi akurkinta tana da Wan maggi da yaji da mai kaWan ta saka a ciki ta ci bata ma gama ci ba taji sau?ar ruwa kaman da bakin ?warya, ko da ta kwanta baccin sai ya ?i zuwar mata sai tunanin rasuwar yaron jiya take ko wani hali iyayenshi ke ciki? Tana kuma tambayar kanta da gaske ita Win Mayya ce? Da ?yar bacci da ya fi kowa iya sata ya lallaSo ya sace ta...

Rayuwa ya Wauki yi mata zafi a gidan fiye da baya saboda a yanzu tallar bata yi inna larai ta yi mugun tsanarta don ta karya mata kasuwa hakan yasa ko abin da zata ci a girkin inna larai gagararta yake, ba'a isa a aike ta ba haka zata dawo da hawaye saboda maganganun mutane da ma yunkurin illata ta da wasu kan yi, bautar gidan duk ya dawo kanta yanzu har girki ita ke yi musu su zo suyi rabo kuma a hanata don daga an sau?e za'a aike ta kan ta dawo an raba in ta tambaya su ce sun manta da ita, ita dai gata nan amma rayuwar baya yi mata daaWi ko ta wani Sangare.


''Ina ma mutum na da zaSi kan rayuwarsa! Ina ma a ce bawa ke da ikon rubuta ?addararsa! Da ban zaSi maraici ba. Duk bala'i na san ko da kowa zai guje ni su Win ba zasu taSa guduna ba" a hankali take furta hakan wani irin kewa da maraici na taso mata, har ?asan ranta bata son yadda ta zama tamkar mujiya a cikin tsuntsaye, bata son wannan suna na Annoba da yanzu kowa ke ?iran ta dashi... Kanta a du?e ?asa ruwan hawayen da bata rabo da su na sulmiyowa cikin ruwan kunfar wanke-wanken da take yi wani irin zafin da zuciyarta ke yi kaman zata fito daga madaukarta
"Wai zama kika yi kina maitar da kika saba na shanye kurwuwowin mutane ba za ki yi ki kawo mini kwanuka in raba abinci ba?"
Inna larai ta watso mata kalaman cikin hantara.
sharSe hawayenta ta yi, cikin mintunan da ba su wuce biyar ba ta kammala.
Tattara kwanukan ta yi ta kai gaban murhu ta ja jikinta gefe ta tsaya tamkar ji?a??iyar kaza da ta rasa mafaka yayin ruwan sama.
"Ungo sayo min kuka da daddawa."
KuWin da ta wullo mata a wula?ance ta sanya hannu ta Wauka ta juya tana jefa singallin kafafunta masu kama da zaren lipton saboda rama tayi waje, ko da ta dawo zaune ta tadda zuri'ar gidan suna karyawa cikin natsuwa.
"Ga shi inna larai"
Fusga ta yi suka ci gaba da kai lomar zazzafan Wumamen tuwon dake turiri ita da Inna Asabe
"Abinci...cina fa?"
Ta yi tambayar zuciyarta na rawa. Amsar da take tsoron ji ita Win dai ce ta ratsa kunnuwanta.
"Kin ga na manta da ke a rabo, sai ki jira na rana."
Wani irin raWaWi ne ya ziyarci idanunta tamkar wacce aka watsawa borkono. Ba ta sauya zani ba ba kuma ta tunanin za ta sauya Win abu ne da ta riga ta sani a kullum idan har za a raba abinci aka aike ta shi kenan rabonta ya faWi ?as.

Ita take kallo sai dai tuni zuciyarta da ?wa?walwarta suka tafi nisan kiwo, hanjin cikinta jin shi take kamar ana daddatsawa tsananin yunwar da ta kwana da ita. Ba ta da shi ba ta kuma da wanda zai ba ta babu mai Wigon tausayinta a gidan a cewarsu mayu sun fi cinye kurwan wanda ya ji tausayinsu ko ya taimaka musu.

Sau?ar ruwan zafin da ta ji a fuskarta yasa ta sakin ?arar azaba a firgice ta mi?e daga dur?uson da ta yi a gabansu tana dirza fatar inda wani irin zafi ke ziyartar ta. A take ta Waile, daidai lokacin inna larain take faWar
"Wallahi kurwata kur! Maye sai dai ya ci kansa."
Baya ta matsa ta sake zubewa bisa gwiwoyinta hawaye na sake tsinke mata cikin shesshe?a ta fara ro?on su taimake ta da abinci.
"Inna don Allah ko da loma biyu ne ku taimake ni da ita, cikina babu komai hanjina murWa suke, yunwa za ta kar ni."
Kamar dabba haka ta sa ?afafu ta hamSare ta ba tare da ta ko damu da raunin ?unar da ke jikinta ba.
"Ba za ki taSa samun nasara a kaina ba, wuce ki fara shirin Waura mini abincin rana."
Jiki a saSule ta mi?e ta nufi wurin murhu, a haka cikin raWaWin gangar jiki da zuci ta fara aikin. Bata yi nisa a aikin ba suka gama karyawa suka kai kwanukan mawanki kowa ya nufi Wakinsa don hutawa. Ta rarrafa ta isa bigiren saboda ko ?arfin mi?ewa tsaye babu jikinta tsabar yunwar dake dawainiya da rayuwarta.

?an sauran wanda suka rage take kwarfewa tana afkawa a bakin salati, ta haWe da tukunyar ta kankare ?asan tana ci tana zub da hawayen tausayin kanta da irin rayuwar da take. Ko kula inna Larai dake mata gargaWin kar ta yi mata lamba a tukunya bata yi ba. Ta mi?e ba don ta ?oshi ba sai don babu wani abin da zata sake samu ta ?arasa ta kwalfi ruwa ta afawa cikinta. A gindin randar ta raSe cike da fatan sanyin ya taimaki zuciyarta wurin kashe wutar dake ruruwa a cikinta har take neman kai ta ga kushewarta.

"Afeefah! Afeefah!!"
Sam bata san bacci ya sure?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ta a wurin ba sai da ta ji ana jijjiga ta tare da kiran sunanta.

"Lafiya kike bacci a nan?"

Idanunta da ba su da maraba da na mashaya saboda gajiya da jigata ta ware tana kallon mai maganar da muryarta yayi kama da wacce ta

2 / 53