HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   40 / 53

117K to 120K   out of 158.4K words

gidansu ne kuma kun fi kusa kusa sossai don First cousins kuke har gobe idan babu jininka wani daga gidansu yana da damar zama Sarki.

Kana kuma da Fulani Aminatou da aka baka ita daga masarautar Kamaru Dukda Na samu maganganu masu yawa akan masarautar na shigo ne a mace ta uku da shekaru sha shida kachal, kai shaida ne irin wahalar da na sha kafin nayi blending da rayuwar cikinta ban shekara biyu ba ka cike mata huWu, dukkanmu daga kan Fulani Adama har Fulani Salimah babu wanda ya taSa ko da Satan wata ne, dayawa sun fi damuwa da ita kasancewar ta fi mu jimawa tsawon shekaru kusan goma kuna tare, kwatsam na samu juna biyu an yi farin ciki kwarai kuma babu wanda bai sani ba ana kuma tattalin wannan ciki watanni biyu zuwa uku nayi mummunan mafarki ko da na tashi ciki ya bare duk mun yi bakin ciki amma muka sallamar Allah ne ke bayarwa kuma shi ya karba kayansa abin mamaki sai da na jera Sari biyar a ?asa da shekaru biyu, abin ya dame mu duka neman taimako da adu'o'i babu abin da bama yi har na sake samun wani cikin wanda kai ka hana mu fitar da zancen na tafi Mambila ban dawo ba sai da jaririna Wan watanni har uku kowa yayi mamaki Dukda an zargi hakan don jimawa ta kuma an yi ta kananun maganganu ban damu ba don zuciya Waya na Wauki kowa, abin bakin ciki yaron nan Aliyu na watanni biyar ya ce ga garin ku... Babu wanda ya san halin da nayi going through sama da kai mai martaba Dukda dukkanmu mun san ba haka kawai bane amma muka bar wa Allah kwatsam cikin Sameer ya bayyana wanda daga ni har kai bamu san da zaman cikin ba ma sai da yayi watanni kusan biyar.

Babu irin wahalan da ban sha ba, babu irin ciwon da ban yi ba kaman ba zan rayu ba kaman zan rayu har Allah ya kawo min shi duniya, mun yi Adu'a kuma mun sa idanu da tsaro sossai kasancewar ranar da na haife shi kwana BO?EJO tayi kukan murna Ganguna suka yini dokawa na maraba da sarkin gobe, Dukda hakan sau uku cikin shekaru biyu na Sameer ana poisoning Win shi da fargaba nake kwana nake tashi, kullum damuwata kar a samu nasara a kanshi mai martaba na rokeka sau ba adadi mu nesanta shi da masarautsr nan don ba zan juri rasa shi ba amma ha?uri da Adu'a shi kace mu cigaba da yi ba zaka iya nesanta da shi ba, kowa ya san Sameer ya taso ne kaifi Waya ga zuciya da jarumta, tun yana ?arami ya san menene sarauta kuma ya san makiya da masoya Dukda haka bai tsira ba yana da shekaru huWu ya ci poison da ya kwashi wattani tara bai san wanene a kanshi ba har mun fidda tsammani Allah ya sauko mishi da waraka ya farka, tsakani da Allah tun daga sannan na saka a raina cewa zan nemi hanyar bullewa don samun ya tsira da rayuwarshi, a haka na yanke kaishi ?asar Hausawa na san namiji ne zai iya rayuwa kuma zan dawo in ta mishi Adu'a har karshen numfashi na.

Wannan decision da na yanke daga ni sai Drivern da ya kaini wanda kusan amintaccen gidan mu ne da kuma kuyangata Kande da na san har abada ba zasu taba faWa ba idan ba ni ce na faWa ba, saboda in tseratar da rayuwarshi ya sa...."

Katse ta yayi yana jin gabaWaya mood dinshi na sake sauyawa zuciyarshi kaman akan wuta
"Hakan ya sa kika yi mai gabaWaya da rayuwata wai HAIHUWA DA HANJI ko? Kika kashe ni da raina Ammie... Har yau ina tambayar kaina me nayi da na chanchanci hakan ashe wannan ne dalilin? Idan ba don mutanen kirkin da na haWu dasu waenda suka zama ba ni da tamkarsu a sanadiyarki ba zan iya cewa gwara na mutu da irin rayuwa cikin tsananin duhu da na yi a baya don bashi da maraba da rayuwa cikin ?abari, Mahaifina da irin darajar shi da ?imarshi an kalleni an ce min shege marar tsatso sau babu adadi wasu in ji wasu ban ji ba babu wanda ya fi tsaya min sai da aka hana ni aure saboda wannan dalili, kullum ina wurin likita ban taSa bacci lafiya na tashi lafiya ba shine rayuwar da kike tunani ya inganta mini?"

Hawayen da ya tarar mishi a idanu ya mayar ya mi?e kawai ya fice daga sashen, Ammie dake kuka sossai sai ji tayi mai martaba ya dafa kafaWunta ya Waga ta sama sai kawai ta rungumeshi tana ci gaba da kuka mai tsuma rai.
"Ha?i?a ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
kin yi kuskure amma har da laifina ciki, na sani ina da tarin makiya na ciki da waje, na san irin ciwon da kike ji a duk sadda kika rasa cikin ki na kuma san me kika yi facing a rasuwar yar ki ta fari Dukda mace ce, duk jinyar da Sameer yayi tare muka yi kuka amma ban yi tunanin nesanta ni dashi bane ba saboda bana son ya tashi a rago, na so ya san idan ya rayun ma cikin wuya da tsanani abinda yake gabanshi zai fi hakan, na so ya goge ne barazana ya zame mishi tamkar kuda da zai iya bugewa da tafin hannunshi ta inda na so kaina kenan na mance raWaWin da uwa za ta iya ji a sadda aka cutar mata da rayuwar da, amma FaWimatu da sai ki tuna da idan rayuwarshi ya lalace fa? A wanchan wurin da kika ajiye shi zai iya zama Wan daba, ko ya zama dan ta'adda ko dai ya faWa wani mawuyacin halin da zai karar da rayuwarshi cikin mugun yanayi wanda duk alhakin zai iya zama a kanki ne!"

"Sai da na bar wurin na fara wannan tunani mai martaba, ha?i?a na yi ragon azanci wlh nayi nadama daga lokacin bayan kwana biyu da dawowar mu bana iya ko runtsawa gashi kana cikin halin ciwo da damuwa na tura driver sai dai ya dawo ya ce min bai same shi ba duk inda ya duba bai ganshi ba, daga ranar Adu'ata ta koma a kanshi na roki Allah kar ya bar min shi rayuwarshi ta tabarSare na roki Allah da yakinin zai dubi zuciyata ya raya min shi har ma na samu cikin Aisha ban yi wani farin ciki ba, itama babu wanda ya san cikinta don kowa ya san ina jinya bana zuwa ko ina bana rabo da hijabi da chasbaha sai haihuwarta aka ji, nayi hamdala ganinta mace barazanar ta kuma ya zo min da sau?i. Don Allah ka gafarceni ranka ya dade! Na tuba"
Ya ja ta suka zauna ya ri?e hannunta.

"Na yafe miki FaWimatu na yafe wlh, wannan damuwa da kukan duk ya dameni ya hanani sukuni..."
Yayi maganan yana share mata hawayen fuskanta, numfashi mai nauyi ta sau?e.
"Saura Sameer...!"
Ta faWa da wani yanayi.
"kar ki damu zai sau?o ne a hankali, don ma rayuwarshi bata lalace ba Alhamdulillah"
"Ya baka labari?"
Kai mai martaba ya gyaWa nan ya shiga bata labarin abin da ya faru kabb yadda Rayyan ya bashi labari, tayi kuka sossai ta yi wa Mammi Adu'o'in da bata san iyaka ba, taji kaunar jannah da Abeeha tun kafin ta gansu taji cewa sun samu uwa har sai itama kasa ya rufe mata idanu in shaa Allahu yadda bata bar yaronta yayi maraicin uwa ba suma ba zasu yi ba.

Ta roki mai martaba da ya bata ri?on Abeeha har tayi aure ya ce
"wannan na ga yaron ki ne Fulani..! A yanzu kam bana tunanin zai amince bamu san gaba ba"
Mai martaba ya ce
"Amma ya kike tunani batun Zara'u kuwa? Kin san a yanzu da ya bayyana za'a saka mana ido ne a jira a ga me za mu ce tunda yarinya dai ta riga ta isa aure, kina ganin zai karbi auren?"
"Ranka ya daWe kai ka karance shi tun daga dawowarshi zuwa yanzu na dai san shi tun yana ?arami da kafiya da taurin kai ban san ko ya chanza a hakan ba amma zan roki wani alfarma, ko da ya amince Don Allah batun jiyan matarshi da ka bani labari a barshi a rufe kaman yadda shima ya roke ka, mu ne kadai ke da alhakin sani a yanzu labarin na fita babu kananun maganganu da ba zaka ji ba, hakan zai iya zame mata barazana a zamanta cikin masarautar nan"

Ya gamsu kuwa, su basu wani damu da jiyanta ba don sun yarda Mammi bata mishi zaSen tumun dare ba kuma tunda ta gamsu da ita suma sun gamsu.
Mi?ewa Ammie tayi
"Zan je na zaSi kuyangin da zan tura musu da kaina, kuma zan tabbatar da cewa ba'a samu kuskure a hakan ba"
Ya gyaWa kai
"Ki kwantar da hankalinki da fushin shi zai sau?o with time musamman idan macen kirki yake dashi na tabbatar ba zata barshi ya cigaba da fushi dake ba nima kuma ba zan barshi haka ba"
Tayi murmushi ta gyaWa kai kan ta fice.

Ta isa sashen kuyangi da kanta ta nemi kande ta nuna mata jikokinta ta zaSi guda biyu da kuma Wiyar wata Kuyangarta sa'ade ta tura su sashen Afeefah da sunan sune nata amintattun kuma ta tabbatar ba zasu cutar dasu ba, bata ma isa sashen ta ba ta samu labarin isowar ba?in masu muhimmanci.

Ko da isowarsu Rayyan na tsaye a harabar masaukinsu inda ya tabbatar da komai ya tafi yadda ya kamata kuma masauki ne mai kama da apartment da babu wanda zai takura wani komai da komai akwai intact, hannayenshi harWe a kirjinshi ya zubawa motocin idanu kawai yana so yayi tozali da ita ne ko zai samu sassauci, yadda yaji kewanta musamman a yau da ya san tana zuwa gareshi Allah ne kadai ya sani, kaman kuwa ta sani ita ta fara buWe side Win da ke fuskantarshi ta sanyo kafa waje ta sau?o, lumshe idanu yayi yana jin wani chill abu na ratsa shi daga inda yake tsayen, sanye take da wani 2 in 1 Abaya fari da ja da ya mugun amsarta.

Gyalen mai bakin lace ne sai ta kawo lace Win Goshi kan ta zagaye sauran ya bar dankunnayenta Red colour fashion waje amma wuyanta ruff yake a rufe, hannunta jan jaka haka takalmin kafarta ma Red ne sossai ya shagala da kallonta sam bata lura dashi ba, ta ri?e kofan Jannah ta sau?o tana tsokanarta akan ta rufa mata asiri kar a ga Gimbiya na buWe mata kofa a zane ta ita kuma tana dariya tayi mishi kyau kwarai zuciyarshi sai motsi yake, da kyar ya iya kawar da kanshi ya mayar kan su Uncle Musa kan ya nufe so ba tare da ya bari ya sake kallonta ba don urge na jin ta jikinshi yaji yana ji kallon kawai ya mishi kaWan, yana so yaji ni'imtaccen kamshinta a hancinshi, yana so yaga tana kallonshi da wannan tsoron a idanunta mai mai?o idan ta tara hawaye, yana so yaji tana mishi magana a karye cikin tsoro da ya zama ShagwaSa ko jan hankali a wurinshi amma duk ya bar wa anjima.

Fuska a sake ya tarbe su, ita kuma sai da ya isa ya Wan yi hugging Saleem kan ta yi noticing Win shi gabanta na ta dukan tara tara don tunda suka shigo gate Win masarautar ta rasa natsuwa, kanta har lokacin ya kasa dauka da ita ce matar magajin wannan masarauta mai girman gaske da ?awa, mai tarin kuyangi, dogarai, bayi da hadimai. Mai dumbin tarihi motocin da aka dauko su ma kawai abin kallo ne sai dai ta ji jikinta ya sake sanyi ?alau ganin ko kallon inda take bai yi ba.

GaabWo ya kalla da sauri ya zube ?asa
"Allah ya baka yawan rai!"
"Yi wa Uwar Wakin ka iso zuwa sashenta"
Yayi maganan yana dan kallonta sai suka haWa idanu, kanta ta mayar ?asa GaabWo ya matso ya zube gabanta don kallon da ya mata ya faWa mishi ne wacece a cikinsu.

"Lale Maraba da Uwar Wakina Zinariyar masarauta mai daraja fiye da tagulla.. Maraba da hasken Masarauta mai haske tamkar farin wata... Sannu da isowa Gimbiyarmu Gatan Fada! Gimbiya mai rairayi cikin gaskiya...ma?i gani sai dai ya kau da idonsa hasken rana kike hannu baya karewa.. Allah ya ja da zamanin hasken zuciyar Ciroman duk duniya!"
Duk sai ta rikice ta rasa ma me zata ce ta gigice ta kamo hannun Abeeha ta ri?e.

"Barkanka dai!"
Ta faWa cikin rawar murya, Abeeha da Jannah sai dariya suke danne wa don tuni Rayyan ya jagoranci su Uncle sun shige ciki, yadda Afeefar duk tayi wuri wuri ne na rashin sabo ya saka su dariya shi dai cikin ladabi yayi gaba suka bi shi wasu dogaran suka Wibo kayakinsu har zuwa sashenta.

Kuyangin na zaune sai ga su duk zubewa suka yi suka fara miko gaisuwa ita Afeefah kuka ne kaWai ya rage bata yi ba, Jannah ce tace
"Wacece shugaba a cikin ku?"

Suka nuna sa'ade
"Nuna mana Wakin uwar Wakin naku tana so ta huta"
"An gama ranki shi dade"
Ta mi?e don da suka zo suka sanar da mahaifiyar Ciroma ce ta turo su GaabWo bai hana su ba kuma shi ya nuna musu Wakunan masu ?angaren Wayan suka kaita yayinda Abeeha da Jannah suka shiga daya don su yi wanka su dan huta.



=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*49*

Bayan sun yi wanka suka fito parlorn, sun samu an jere musu abinci gashi nan kala kala suka zauna Afeefah na shirin serving Winsu Wayar hadimar tayi saurin karSa

"Ranki ya dade duk wannan ba aikin ki bane"
Shiru tayi tana kallon ikon Allah har ta gama serving ta koma chan gefe ta zauna.
"Ni kam ina ganin ikon Allah"
Sai lokacin ta tanka, Jannah tace

"Ina baki labari kina ganin wasa nake yarinya, kin san ina karanta royal stories sossai wannan kadan kika gani"
Abeeha tace
"Ni fa in na samu irin gidan nan mi?e kafa zan ko wanka sai an min"
Jannah ta maka mata Harara
"DaaWi na dake ragwantaka, kar ki sa in miki adu'ar aure inda za ki Wora tukunya lamba goma"
"Allah ya kiyaye ya kyauta wlh"
Ita dai Afeefah dariya take musu chan tace
"Ni dai kin san Allah duk waennan abubuwan basa burgeni, ni fa na fi so in yi rayuwata ba takura amma yanzu duk jina nake wani iri wlh"

"za ma ki saba ne yarinya"
Suna yar hirar su har suka gama suka dawo cikin parlor.
"amma fa sashen nan naku wlh ya haWu ?arshe, ni kayakin nan ma na kasa tantance irin masifar tsadarsu ji kujera kaman bread tsabar taushi"
Abeeha tayi maganan Afeefah tace
"Kema kenan da kuka saba yawace yawace har kasashe ni ko da na shiga bayi sai da nayi kauyanci, wai ni Afeefah ce cikin masarauta har wani zube min ake a ?asa abin nan ya kasa fita a raina"
Jannah zata yi magana sai suka ji sallama.

Dukkansu kofan suka mayar da hankali wata doguwar matsakaiciyar macece mai cike da kamala ta shigo sanye da rantsatsen alkhyabba fari tass daga ka ganta ka ga mulki fuskarta dauke da fara'a bayanta wasu 'yan mata biyu ne sanye da dogayen riguna suma kyakyawa don duk ruwan Fulani garesu.

Kallo daya suka yi mata suka hangi kamanninta da Aliyu kan ma suyi magana kuyangin ta sun zube suna kirarin da ya sa suka fahimci wacece Dukda Sameer suka ji ake kira.
Dukkansu suka yi yunkurin kaiwa kasa don gaisheta tayi saurin rike Abeeha da Afeefah ta Wago su kan ta Wago jannah duk ta rungumesu
"Barkanku da zuwa 'ya'yana, Maraba lale da isowa masarautar Fombina"

"Mun gode mama"
Suka fada duka da murmushi a sadda ta sake su suka zauna tana rike da hannun Afeefah Dukda bata ma san wacece wace ba a cikinsu amma dai duk sun kwanta mata ganinsu hakan

"Sannunku da zuwa"
Aisha ta faWa suka amsa da godiya.
Zarah tace
"Sannunku dai"
Itama suka amsa.

"Ni sunana Ammi ku daina cewa Mama akwai mamar taku Fulani Adama za ku je ku kai mata gaisuwa anjima, wannan ita ce Aishatu ?anwar Sameer Yayanku su biyu Allah ya bani kan Sacewarshi sai wannan Wiyar wurin Makama cousins suke da su Sameer ko in ce Rayyan yadda kuka saba faWa. Ina fata za ku dauke ni matsayin Uwa da kuka yi rashi gabaWaya. Allah ya gafartawa Mammi ya kai haske makwancinta"

Suka amsa da Ameen kan jannah tace
"Ni ce Jannah, wannan kuma Abeeha ita ce kanwata Ga Afeefah ita ce matar Ya Rayyan"

Ammi tayi murmushi tana kallonta
"Masha Allah, Allah ya cigaba da baku zaman lafiya ya kawo zuri'a masu albarka" kunya ya hana Afeefah amsawa

"Da ma na kasa ha?uri ne nace dai bara na zo na ganku, Abeeha duk abin da kuke so ko ya shige muku duhu ku kama sa'ade za ta kawo ku har inda nake ku tambayeni kun ji? Ke kam ma sashe na zaki dawo ba da jimawa ba"
Suka yi murmushi ta dubi su Aishatu
"Sai ku zauna nan duk abinda basu fahimta ba za ku iya fahimtar da su da kuma bayani akan family Dukda sai a hankali za su san kowa"
Suka amsa kan ta mi?e ta fice suna mata sai anjima.

Yadda su Aishatu suka kame haka dukkansu suka kame sai hirar ya koma tsakanin junansu kawai ita jannah ma waya take da mijinta yayinda Abeeha ke hira da Afeefah suna yar dariya, kaman daga sama sai ga shi ya shigo. Ko Aisha yau ne suka fara ganin juna dashi face to face, zama yayi a one seater ya kame yana kallonsu daya bayan Waya, jannah ta fara gaishe shi ya amsa ta mishi murnan dawowa cikin family Abeeha ma ta gaishe shi.

Zarah ce ta gaishe shi ya kalleta yana son tuna sunan
"Aammm.."
"Zarah"
"Oh Yeah lafiya ?alau"
Ya kalli Aisha da ta gaishe shi last itama ya amsa, Afeefah ce ta gaishe shi ya Wan yi shiru kan ya kalleta sai ya mi?e ya nufi Wakinshi.
Abeeha ta mi?a hannu ta mistineta, kallon jannah tayi sai jannah ta harareta dole ta mi?e don sun cika ta da lectures kaman me akan Rayyan

40 / 53