HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   20 / 53

57K to 60K   out of 158.4K words

ba na gani ne? Yau kam ma na tashi jikin sai a hankali ai ni kaWai na san me nake ji"
Tayi maganan da 'yar haki tana kishingida.
"Sannu! Ko zaki ?ara magani?"
"Kayya bar zancen maganin nan Afeefah, je ki kira min Yayanku nayi ta gwada layinshi bana samu tun bayan asuba da ya shigo nan muka gaisa ban sake ganinshi ba"

Idanu ta Wan waro gabanta na faWuwa, Dukda ta san ta inda Sashenshi yake amma bata taSa gigin shiga ba to me zai kai ta? Yanzu Win ma jiki a sabule ta mi?e ta fice daga Wakin, Abeeha bata nan tun safe taje gidan jiddah za ta raka ta asibiti wai bata jin daaWi da ko ita zata iya zuwa amma ita har yanzu ganinta ba?uwa a gidan take, ko ba ma haka ba ina zata iya da wannan da ba'a mishi gwanintar? Mutum sai faWin rai da masifa... Da kyar ta Waga hannu tayi knocking kofan parlorn sai dai shiru babu amsa, ta sake yin knocking karo na biyu nan ma shiru, a hankali ta tura kofar da sallama a Bakinta ta shiga yana kishindige very relaxed a cikin kujera, parlorn da hasken shi ba sosai chan chan ba sai tashin kamshi yake, kaman waya yake yi amma ba da wayar da ta saba ganinshi dashi ba gabanshi system ne shima a kunne kaman dai aiki yake yi ya tsaya amsa wayar.

Daga Wan nesa ta tsaya kanta a ?asa tana jin yadda yake magana wane wani sarki, murmushi tayi a chan ?asan ranta take raya dole Mammi ta kira shi Saraki don shi komai nashi ya fi yanayi da jinin sarauta, bayan ya gama wayan ya Wan kalleta ba tare da ya ce komai ba ya Wauke idanu itama jin shiru ya sa ta Wago ganin ya gama wayan ta Wan ?ara taku biyu sai ta rasa me za ta ce.

Da kyar ta iya haWa kalmar sunanshi akan lips Winta
"Yaya Saraki..."
?agowa da yayi ya kalleta ya sa maganar datsewa, bai san ya Wago Win ba don yadda ta kira sunan sossai ya dake shi, bayan Mammi bai yarda ya ji sunan bakin kowa ba amma jinshi a Bakinta sai ya rasa me yake ji ma, haushi ne ko takaici ko bacin rai? Tsam ya mi?e ya nufo ta.

Idanu ta shiga zarewa takunshi na tafiya da bugun zuciyarta har ya matso dab da ita yace
"Maimaita abin da kika ce?"

Shiru tayi ta kasa magana idanunta da suka yi raurau alamun kuka ko wani lokaci ta Wauke daga kanshi jikinta na tsuma ta ciki, kusan seconds huWu kan ya ce
"Allah ya so ki, da kin maimaita sai na fasa miki baki ke Mammi ce da za ki kira ni Saraki? Wani Yaya Saraki...!"
Ya sake maimaitawa yana Wan harararta.

"Me?"
Ya faWa yana dan gyara tsayuwa idanunshi tsamm a tsaye a kanta ko a jikinshi.
"Yaya..."
Wlh sai ta kasa cewa Rayyan Win tayi tsai tsammm sai ma ta fasa kiran sunan da Wan saurin baki tace
"Mammi ce wai ka je!"
Ta juya za ta fice yace
"Tsaya!"
"Ba ni da suna ne? Ko da gini kike magana?"
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Ta faWa kaman za tayi kuka chan ?asa, sarai ya ji ta
"Ga musiba tsaye gabanki ko?"
Girgiza kai tayi, tsaki ya ja yace
"Bar nan"
Da sauri ta fice.

Sai da ta ganta tsakiyar babban parlor kan ta dafe kirjinta tana sau?e numfashi, Rayyan na son kasheta da ranta, yaushe ya iya ma dogon magana haka bata sani ba, shi da komai ko oho ne me yasa zai saka ta a gaba yayi ta razana ta!
Jiki a sabule ta ?arasa wurin Mammi
"Wai yana zuwa"
Zama tayi kawai bata sake cewa komai ba, mintuna basu wuci uku ba sai gashi gaban Mammin kawai ya ?arasa ya fara taSa temperature Winta, numfashinta baya fita yadda ya kamata hankalinshi tashi yayi, a take yace su tafi asibiti duk yadda Mammin za ta ?i ya nace ya dubi Afeefah yace ta Wauko mata mayafi, da sauri taje ta Wauko duk sai ta shiga damuwa ganin yadda hankalinshi ya tashi, kuma dai a fili Mammin bata yi tsananin da ya kamata ya Waga hankalin nashi haka ba, bata zauna ba itama gyalen da ta Waura a kanta na Jersey ta warware ta yafa akan doguwar rigar atamphar dake jikinta ta bi bayansu, a gaba ya saka mammin ta buWe baya ta shiga suka fice daga gidan.

Tafiyar mintuna ashirin ya kai su asibitin shi ya sake kama mammin suka yi inda za'a duba ta don ya riga yayi call, tuni suka karSeta don a yi mata gwaje gwaje a tabbatar da babu abin da ya sake tsananta ko chanzawa.

A reception ta zauna idanunta na kan yatsun ta sai adu'ar samun lafiya take yiwa Mammi mata mai kirki da mutunci, macen da ta zame mata uwa kuma garkuwa a yanzu.

"Afeefah...!"
Da Wan karfi ta ji an kira sunanta har bata san ta Wago a razane ba sai...




=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*25*

Sulaiman kaman zai kama hannunta haka ya tsaya gabanta yana kallonta.

"Da gaske ke ce? Ashe zan sake ganinki Afeefah? Ina kika shiga? Kin san irin neman da na miki?"

Idanunta na sau?a kanshi ta mi?e tsaye, ganin irin kusancin su ya sa ta Wan yi taku biyu baya fuskarta a sake tace
"Ina nan Dr. Allah ya haWa ni da mutanen kirki"
"Afeefah me yasa ba ki zo office na ba? Me yasa ba ki neme ni ba da mahaifiyar saleem ta kore ki?"
Idanunta ne suka cika taf da kwallah a hankali tace
"Ban san inda zan sameka bane ban san sunan asibitin ku ba ko in ce ban ri?e ba, ko ma na ri?e ba ni da ko biyar da zan hau abin hawa in ce a kawo ni"

Idanu ya Wan runtse kaWan ya buWe da sauri sai ya ga kaman za ta iya Sace mishi any moment
"Ina kika shiga to? Waye ya taimake ki?"
"Na haWu da mutanen kirki sun tallafeni daidai lokacin da na bu?ata kuma suna ri?e ni tamkar Waya daga cikinsu yanzu haka ina makaranta"
"Alhamdulillah!"

Zama yayi saboda a lokaci Waya daaWi da ba?in ciki duk suka haWu mishi, itama ta zauna a hankali ya ce

"Afeefah har Dutsen-wai na je nemanki"
Da sauri ta Wago ido suka haWa idanu ya gyaWa mata kai alamun tabbaci.
"Gidan kawu ka je?"
Kai ya gyaWa cikin nuna damuwa ya ce
"Abin da muka tarar ba karamin tsoro ya bamu ba Afeefah, ban so ba, ban san hakan zai kasance ba da ban yi ganganci da kuskuren tafiya da manya na ba"

A lokaci daya ta zama very confused sun je gidan kawu? Me suka tarar? Me yasa yaje da wasu?.

"ko da ban furta miki ba kin dai san Sonki nake ko Afeefah?"
Lumshe ido tayi kalamar na sauka mata wani iri a zuciya.
"A lokacin da na samu labarin tafiyar ki i was very disturbed na Wauka chan gida za ki koma, ko da na koma gida na samu mahaifiyata da labarin ban gama bata ba Abba ya shigo ya ji zancen, dama ya matsu kuma da maganan aurena dole ya haWa ni da Yayyenshi kuma ya kafa hujja ne da cewa a musulunce ma bai halatta namiji ya fara taran mace ba tare da sanin iyayenta ba.. Dole ta sa muka tafi tare da su ba don na so ba"

Hawaye ne ya zubo mata a kan fuska ta Wan yi murmushi mai yanayi da wani ciwo a ?asan rai ta ce
"Sun ji kunya ko? Na tabbatar ba su amince maka ba kuma ba za su taSa amince maka ba..! Ka yi ha?uri, da na san za ka aikata hakan da ni da kaina na faWa maka wacece ni kafin ma ka je"

Ya Wan haWiye wani abu mai ciwo a hankali yace
"Afeefah sun yanke min hukunci mai girma a yanzu haka ina da aure, an Waura min aure last week saturday amma har yanzu zuciyata ke take so, ke take marararin rayuwa da ba wata ba. Na ha?ura na karSi auren ne saboda ban san inda zan ganki ba ban san inda zan sameki ba, a ina ne gidan da kika koma? Idan kin ga da takura za ki iya dawowa wurin Umma na tabbatar ita me ri?e ki ce tamkar Wiyar da zata haifa a cikinta"

Rayyan ne ya fito sai idanunshi ya faWa kan su, a kan hawayen dake bin ?uncin ta ya Wan tsayar da idanun kan ya Wauke kai ya zo ya wuce su kaman bai gane su waye ba, Afeefah da suka haWa ido ta sa hannu ta share hawayen fuskarta ta dubi Sulaiman
"Zan tambayi Mammi zan zo in gaishe Da Umma! Amma batun soyayya don Allah ka ajiye shi a gefe Dr. Kai fa ka gayamin irin abubuwan da Kawu ya muku na ba da kunya, taya za ka yi convincing iyayenka su sake komawa irin gidan chan?"

"Zan iya Afeefah kawai ki ba ni dama!"
Ta girgiza kai
"Aurenka fa?"
Zai yi magana ta ce
"Ka yi ha?uri Dr. Yanzu ba lokacin wannan maganan bane marar lafiya muka kawo"

Shigowar Abeeha da Jannah ne ya sa ta ?arasa share fuskarta ta ?ir?iro murmushi ta saka, suka ?araso kusa da ita
"Afeefah ya jikin Mammin?"
Ta ce
"Da sau?i sossai amma tunda Ya Saraki ya shiga da ita ba'a fito da ita ba"
"Amma Yaya Rayyan Win yanzu muka wuce shi a waje yana waya"
"Eh shi kadai ne ya fito"
Gaisawa suka yi da Dr. Sulaiman yana mamakin jin ana ambaton Rayyan, gidan su Rayyan ta koma?

"Afeefah ko zan iya samun Layin da zan yi magana da ke?"
Ya faWa yana kallonta, kallonta Abeeha tayi sai ta Wan yi murmushi tace mata
"Dr. Sulaiman kenan!"
Shima ta juya tace
"Yayyena ne Addah jannah da Adda Abeeha"
Murmushi yayi lallai Afeefah ta samu wurin zama idan har ta sake da ahalin haka sun zama tamkar jininta ya tabbata ba zata iya barin su ta dawo wurin ummanshi ba yadda ya ci buri.

"Dr bamu natsu ba har yau bamu samu mun je mun sayi waya ba, bari na baka layina za ku iya dinga gaisawa kan ta samu nata"
Godiya sossai yayiwa Abeehar, ta bashi contact Winta ya tafi da sauri ta juyi wurin Afeefah tana murmushi sai ta ga damuwa a kan fuskarta, dafa kafaWarta tayi
"Ya dai?"
"Adda wai Shima aure yayi last week saturday"
Duk sun ji maganar wani iri amma sai suka dinga nuna mata babu komai kila ba rabonta bane ko kuma Allah ya kaddara za ta zama matarshi ta biyu bata san ta cewa Abeeha ba
"A yaushe kenan? Aure last week Adda Abeeha kina tunanin ko shekara daya ne zata amince ya mata kishiya a kusa haka?"

"Duk ba mu san tsarin Allah ba, mu yi Adu'a kawai duk abinda ya kaddara daidai ne"
Ta gamsu amma har lokacin ranta na suya da abinda kawu ya aikata, kenan akwai Wan sunnar da zai aureta a duniya kenan? Waye zai yarda Wan shi ya auri irin ta matukar za su bincika asali da tushenta?

Bata san Rayyan ya dawo ya wuce ba chan sai ga shi sun fito da Mammi, duk Mi?ewa suka yi suna mata sannu tayi murmushi
"Duk rigimar Saraki ne amma jikin nan bai kai zuwa Asibiti ba, Jannah ya jikin naki?"
"Da sau?i Mammi, sannu Allah ya baki lafiya"
Ta gyaWa kai.
Idanunta ta kai kan Afeefah dake ta murmushin yake
"Afeefah kina lafiya? Na ga damuwa a fuskarki"
"Babu komai Mammi sannu da jiki"
Kai ta gyaWa ba wai don ta yarda ba suka nufi mota, ?in shiga motar Rayyan tayi don wlh tsoron ko motsi take a gabanshi, motar Jannah ta tafi suka haWu su uku suna hirarsu har gida.

A babban parlor suka yi masauki don Rayyan ya riga su isa kuma ya shigar da Mammi ciki ko da ya fito a babban parlorn ya tsaya yana nuna su da yatsa
"Ba ku parrots ba? To in ga watan ku ta shiga ciki tana damunta da surutu ko wata taje tana saka ta gaba da kukan banza ku ga abin da zai faru"

Yana kai nan ya wuce abin shi basu motsa ba sai da ya Sace Abeeha da Jannah suka tafa suna sheke wa da dariya, Afeefah na murmushi.

"Mutum yayi ta muzurai kaman a filin daga yake"
Jannah ta faWa, Abeeha tace
"Ai ke baki ganin komai tunda yanzu kin bar gidan nan da sau?in ki"
Jannah ta girgiza kai
"Kema kin san babu wani sau?i wlh sai dai in ban yi wani abin ba Ya Rayyan bai game shi ba ya je har gidan auren nawa ya zane ni tsaff"
Ita dai Afeefah bata ce komai ba idanunshi kawai take gani, a hankali ta Wan yi murmushi tana girgiza kai.

Jannah bata tafi ba sai dare, sun sha hira sun ci sun sha, kuma sai da suka cika Mammin da surutu don yana fita daga gidan suka yi Wakin suna bata labarin gargadinshi tana dariya ta dubi Afeefah
"Afeefah ke ce me kukan banza kenan? Me aka yi miki za ki zo ki min kukan?"
"Ba ayi komai ba fa Mammi"
"Afeefah ki faWa min damuwarki wlh ina hangar damuwa a tattare da ke"
Kanta ta du?ar Mammi ita uwa ce, uwar ma ta wannan baudadden mutum ai dole ta san expression na kowa.

Abeeha tace
"Mammi Dr. Sulaiman yayi aure shima ashe"
Mammi ta kalli Abeeha kan ta kalli Afeefah tace
"Auren ne ya dame ki Wiyata? Kin ga fa duk abin da Allah ya hanaka ba rabonka bane wanda kika ga kin samu shi ne rabon ki, in shaa Allahu za ki samu miji na nunawa sa'a"
A hankali tace
"Mammi ba auren shi bane damuwata"
"Toh menene Afeefah?"
"Mammi bana tunanin zan auru, Musulunci ya yarda a auri mace don kyaunta, dukiyarta ko nasabarta, sannan bincike a aure kaman dole ne a musulunci akwai dangi na ?warai da za su je bincike a kaina su yarda su bar Wan su ya aureni? Mammi kin ji abinda su Sulaiman suka samu kawu suna yi a kan layi? Kin ji abinda aka fada musu a kaina daga shigar su kauyenmu?"
Hawaye ne ya tsinke mata ta fashe da kuka tana jin ciwon TaSon ta da bata tunani har Abada zai gogu.

Jannah da Abeeha har sun fara tayata hawaye don idan ka ji yadda take maganan za ka san abin na mata ciwo kwarai da gaske..

"Afeefah zo nan"
Mammi ta ?irata, Mi?ewa tayi ta isa kusa da ita Mammin ta Wora ta akan kafaWarta tana shafa mata kai.
"in shaa Allahu Afeefah sai kin auri mijin da kowa sai ya ji sha'awar kasancewa ke, nagartaccen namiji kuma mai tarin ilimi da baiwa na musamman, kawunki ko mutanen garinku ba su isa sun shafe abin da Allah ya rubuta ba, ko kin manta Allah da kanshi ya faWa mana yana fitar da mummuna cikin kyakyawa ya kuma fitar da kyakyawa cikin mummuna? Ba fa a suffa ko sura ake magana ba ana magana ne akan hali da Wabi'a. To ki sa a ranki mijin da Allah ya zaSa miki yana nan kuma idan lokaci yayi za ki aure shi ba makawa kar ki wani damu kanki kin ji?"

Kai ta gyaWa cike da gamsuwa
"Na gode Mammi"
"na ?ara ji sai na Buge bakin godiyar"
Murmushi duk suka yi don da wasa tayi maganan.


*****

Hajiya Hussaina tun fa tana tunanin abin na Saleem da Sabrina wasa ne har ta fahimci da gaske ne, domin yau tana zaune a parlor Sabreenar ta sau?o ta Wan kalleta tace
"Sannu Mommy"
Bata jira ta amsa ba ta wuce kitchen ta samu Talatuwa na aiki, ta ce
"Talatuwa me kike dafawa?"
"Tuwo ne da miyar egusi shi mutanen gidan suka ce a dafa musu"
"Toh bari ki Wora min fried Rice da kaji iyayena za su zo ganin Wakina ba zan tarbesu da tuwo ba"
"Amma S..."
"Kin yi abinda nace ko sai na bi ta kanki? Har kin isa ja da ni typical 'yar aiki? Toh wallahi ki kiyaye ni"

Sadiqa da ke shigowa ne tace
"Haaa me ke faruwa da ihu haka?"
Talatuwa ce ta mata bayani sadiqa ta kalleta sama da kasa
"Amma ba ki da hankali yanzu su Gajen ne ba?i da har za'a dafa musu kaza da wani fried Rice? Dama shi suka saba ci a gida?"
Sabreena ta ri?e baki tana kallonta na seconds kan tayi wani murmushi kawai ta juya fuuuuu ta fice.

Mommy na nan zaune tana tunanin wannan lamarin da bata gane kanshi ba bare ?asan shi ta ga wucewarta kamar iska, ba'a fi mintuna biyu ba sai Ga saleem rike da belt nashi na sojoji ko mommy bai kalla ba ya shiga kicin ya ya kuwa samu Sadiqa ya rufeta da dukar kawo wuka....






=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Ku lallaSa wannan kaina ciwo wallahi kaman zai faWi*

*26*

Ihu take yi sossai na neman agaji, shi kuwa tamkar wanda ake zuga shi dukan ta yake kaman an aiko shi cike da wani haushi nasu da dama yana kwance ?asan ranshi, Mommy da ta shigo da gudu ne ta ri?e belt Win a tsorace take cewa

"SALEEM! SALEEM!! Me haka? Me ya hau kanka? Sadiqa fa kake yi wa wannan duka kaman wanda ya kama Sarawo? Sadiqa fa ba sameerah ko Samha ba?"

"Na kula rainin sun ya fara yawa ne, kuma wallahi kaWan na mata ko kallon banza ta sake yiwa Sabrina ta gani bare zagin iyayenta sai na yi ?asa ?asa da ita, marasa kunyar yara kawai..."
Yana kai nan ya wuce fuuuuu mommy dake tsaye kaman an dasa ta jiri ya kwashe ta ta tafi zaune.

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun me ke faruwa?"
Sadiqa da ba?in ciki kaman ya kasheta tana dukunkune gefe tana kuka sossai don ba laifi ta bugu ta ce
"Me kuwa mommy? Duk wa ya ja mana? Wlh babbar alamar tambaya ne akan yarinyar nan dama ni ba sonta nake ba kika saka shi dole aurenta yanzu wa gari ya waya? Tun fa ba'a je ko ina ba mommy wlh ba zan iya zama da yaya a wannan gida ba, ni zai daka? Akan Sabreena

20 / 53