HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   35 / 53

102K to 105K   out of 158.4K words

ana so a yi gaggawar sau?e mishi duk wani nauyi har gado, Toh zaman dai ya kamata mu yi da Abeeha da jannah ne amma sanin kana gaba da su kuma kai uba ne a gare su yasa na fara kiran ka, wannan takardu"
Ya mi?a mishi ya karSa yana dubawa Dukda komai na Mammi ya sani, haka komai na su Abeeha da jannah na wurin babansu dake hannunshi wanda Mammi ta sakar mishi yake kula musu da shi duk ya sani.
"Mamanka ta ce in tabbatar maka ita ta baka halak malak har abada baya cikin abinda za'a
raba nata"
Da sauri ya kalli Uncle Musa.

"Rabin dukiyar ta ne fa anan"
"Eh, ta saka hannu zaka gani lawyer Winta ya saka akwai kuma shaidu akan hakan. Ta mallaka maka rabin abinda ta mallaka wanda gado ne daga wurin mahaifinta kyauta"
Dukda arziki baya gabanshi kyautar ya kaWa shi sai yana jin sabuwar Soyayya da kuma tsananin kewa na Mammin, idanunshi suka sauya sossai ya kalli uncle da ya sake cewa

"Wannan kuma sauran rabin abinda ta mallaka ne na su jannah shima ta ce ne in bari a hannunka kai zaka zauna da su idan suna bukata ka basu idan sun bar maka ajiya ta tabbatar za ka juya musu yadda ya kamata"
KarSa yayi yana jin wani iri sossai da sossai. Da kyar ya haWa natsuwar shi wuri guda yayi godiya wa uncle Win kan ya fice daga gidan ya nufo gida.

Yana parking wayanshi ya Wauki ringing ganin ogansu ne yasa yayi picking tare da saluting maganan mintuna biyar suka yi ya sauke wayan tare da bude media group dinsu, news dake yawo ya zubawa idanu sama da mintuna goma ba tare da ya sani ba kan yayi baya baya ya jingina da kujera wani irin abu na tsaya mishi a tsakiyar zuciya, sossai news din ya jijjigashi amma yana iya kokarinshi wurin ganin ya danne don in ka kula har jikinshi rawa yake sai lumshe ido yake yana buWewa lip dinshi na ?asa a Wan datse tsakankanin hakwaranshi.

Sai da ya gaji ya buWe murfin motar ya fita ya nufi cikin gida, a babban parlor ya samu jannah da Abeeha suna zaune shima ya zauna suka gaishe shi ya amsa da kulawa ya dubi jannah
"Yaushe kike shirin komawa ne kam?"

"Dama yau ne to kuma ya tafi Abuja Wazu yace in zauna kawai gobe zai dawo in ya dawo zai biyo ya daukeni sai mu wuce gida"
Cikin girmamawa tayi magana. Ya gyaWa kai
Nan ya musu bayanin gadon su tare da fitar da papers Win ya ajiye.

Abeeha tace
"Ni dai Yaya bana bukatar rike komai a hannuna gaskiya, babu abinda ka rage mu dashi ko da Mammi ke raye baka barta ta mana komai da kuWinta ba don haka ka haWa duka ka ri?e a wurinka kawai."
Jannah ma tace
"Gaskiya nima dai babu abinda zan yi dashi a yanzu, kana min ko da nayi aure baka daina ba shima kuma bai rageni da komai ba for now ka bar wannan a hannunka yaya"
Kai ya gyaWa ya dubi Abeeha

"Gobe zan tafi wani aiki chan Gabas maso yammacin ?asar nan ban san adadin kwanakin da zan yi ba don haka ki duba ki rubutu duk abinda za ku bukata da safe zan kaiku shopping sai a saya"
Godiya ta mishi da Adu'a. Ya mi?e ya nufi sashensu.

Afeefah na zaune shiru cike da tunaninshi, bai karya ba hakan ya dameta sossai har take jin babu daaWi sai tunani take ko ina ya je? Ko yana lafiya? Tsoronta ma ya sha magani? Kar zazzabi ya dawo mishi yana ta yawo a rana duk ita kaWai dai ta yanke dole zata bashi hakuri ta kuma fahimtar da shi ba da wani manufa ta aikata abinda ta aikata ba.

Ta mi?e zata fita wurin su Abeeha kenan shi kuma ya shigo, kallo Waya ya mata ya Wan Wauke kai sai yayi sallama yadda zata ji ta amsa tare da cewa
"Sannu da dawowa Ya Saraki"
Ya Wan lumshe ido ya buWe kan ya ce
"Yauwa"
Daga haka ya wuceta ya nufi Wakin shi bai bata daman magana ba kenan har yanzu fushi yake, jiki a sanyaye ta fice wurin su Abeehar anan take jin labarin wai zai tafi wani Assignment gobe ba lallai ya dawo kusa ba jikinta ya sake yin sanyi ?warai har bayan Magrib bata san me zata yi ba, luckily ko da ta ajiye mishi abincin dare ya ci.

Bayan tayi isha ta gama shiryawa cikin cotton Light blue riga da wando dogo na kayan bacci ta Wora navy blue hijabinta har ?asa ta nufi Wakinshi don ta yanke zuwa kawai ta bashi hakuri kar ya tafi yana fushi da ita.




=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*Tsakani da Allah ba ni da abin da zan ce da masoya sai na gode, ina ganin irin ?aunar ku gareni. Na gode kwarai da gwalagwalan adu'o'inku. Ta Baba Makkah kin faranta min kwarai, sai masoyinka na ha?i?a ne zai tuna da kai a gaban Wakin Allah har yayi maka Adu'a da Fatan alkhairi don haka wannan Page Win sadaukarwa ce gareki Allah ya bar zumunci har a aljannah, Allah duk ya dube mu ya biya mana bu?atunmu na alkhairi.*

*43*

Ta Wan jima tsaye jikin ?ofan tana tunanin ta shiga ne ko kar ta shiga? Da kyar ta tattaro kuzarinta ta Wan yi knocking kan ta tura kofar ta shiga gabanta na tsananta faWuwa.

Hasken Wakin ba shi da wani yawa don haka tsaf take kallonshi zaune tsakiyar gado jingine da pillow gabanshi system ne yana kallo, idanu ya Wan zuba mata tana tahowa a hankali har ta isa jikin gadon ta Wayan side Win inda shi kuma yana jingine ne da side Win da ya saba kwanciya.
Muryarta na fita a hankali cikin tsoron faWan shi ta shiga furta
"Na na..zo ne mu yi sallama na ji wai za kayi tafiya, kuma ina so ne in baka ha?uri wlh ban san kalmar ba zata yi maka daaWi ba. Don Allah kayi ha?uri."

Tun da ta shigo ya Wauke kanshi daga kan system Win ya zuba mata ido sau?ar muryarta a kunnuwanshi ya sa Ya Wan lumshe idanun ya sake buWewa a kanta. chan ?asan muryarshi yace
"Zo nan."
Bai cigaba da kallonta ba sai ya mayar da idanunshi kan system dake aiki gabanshi wanda kallo yake na wani horror movie, tun da yayi shirin kwanciya tunaninta ya so ya dameshi sam shi bai ma san me yake damunshi ba daga dan kusancin da suka samu kwana biyu shikenan kuma sai a ta shiga lokacin hutawarshi ta hana shi hutawa da tunaninta? System ya jawo ya fara kallon dole sai kuma Allah ya jefo ta.

A hankali ta hau gadon kamshinta na dukan shi har yana jin bugun zuciyarshi na sauya wa.
Idanunshi ya kai ga kallonta ganin tana chan nesa ya ce
"Matso nan"
Ya taSa gefenshi, a Wan tsorace cikin bugun zuciya ta matsa tana dana sanin zuwanta Wakin don ji take kaman zuciyarta za ta fito daga madaukarta don tsabar bugu, inda hannunshi yake ta matsa kaman an ce ta kalli fuskan computern aka nuno wani abin tsoro da ya firgigita don ta tsani film mai abin tsoro za ta gudu ya ri?o tsintsiyar hannunta babu zato sai gata bisa kirjinshi daga gefen kafadanshi ya mayar da hannunshi na wurin ta bayanta inda tayi saurin binne kanta a kirjin nashi sihirtaccen kamshin shi na sake shiganta yana ?ara bugun zuciyarta, baya baya yayi ya jingina da gadon yana sake kara kusantar da ita jikinshi.

Bai ce komai ba ya cigaba da kallon yayinda tayi shiru kawai tana sauraran bugun zuciyarshi, sun kwashe sama da awa guda a haka ko da ya gama ya Wan Wago ta zai yi magana kawai ya ga tayi bacci, ya san kwanakin tana ?o?ari kuma bata samun isashen bacci yadda baya yi itama bata yi, gwara ma shi da safe ya kan taSa amma ita ko da safen baya ganin tana yi sai zirga zirga.

Hijabin ya zare mata ya jefar ya zubawa fuskarta idanu yana kallo, bai san me ya ri?e shi a fuskar ba ya dai tabbatarwa kanshi da she's Drop-dead gorgous wanda bai taSa fahimtar fuskar ba irin yau, kallon natsuwa yake binta dashi da ya rasa dalili a hankali ya furta
"what's wrong with me?"
Ya kai hannunshi Waya yana jin zuciyarshi na pounding har sound Win na iya shiga kunnuwanshi...

Yana so ya kwantar da ita akan pillow amma sai ya ji ba zai iya ba don haka ya gyara kwanciyarshi ya gyara mata ta yadda rabin jikinta na a nashi ya lumshe idanu ga mamakinshi tunaninta ya cigaba da yi Dukda gata jikinshi da kyar bacci ya Wauke shi.

Basu farka ba har aka shiga masallaci suratul Fatiha da ake karantawa shi ya farkar dasu duk su biyu lokaci Waya ta yi saurin Mi?ewa zaune tana Wan matsawa kanta ?asa, ya Wan kalleta kadan yadda tayi kaman wacce aka kama tana sata ya sa ya Wan yi murmushin da bai fito ba ya sauka ya shige toilet, hijabinta ta Wauka ta sau?a ta gudu.

A bayi ta tsaya tana kallon kanta, bacci fa ta sake yi a jikinshi comfortably? Wayyoo Allah ta ayyana a ranta tana dafa zuciyarta, gashinta da tayi parking cikin messy burn ribbon Win ya fice bata ma san ta baro a Wakin ba, da kyar ta haWa tunaninta wuri guda tayi alwala tazo tayi sallah ta kwanta a wurin, sai Eight ta fito a shirye cikin Abaya Grey da yayi mata kyau sossai hula ne a kanta kai tsaye taje ta dubo abincin taga wanda zai iya ci ne ta kwaso ta kawo sashen nasu ta shirya dining ta saka turaren wuta a parlorn don a gyare yake tsaff yana kyalli ta juya zata koma ya buWe kofa ya fito, kallonshi tayi yana sanye da wani Army Green riga tare Black wando da ya amshe shi, rigan ya kama shi ya fitar da kirarshi sossai bai mishi ruwa ba sam sai taji wani nauyin shi ya rufeta ta mayar da kanta ?asa, ya kalleta ya Wan shafa gashin kanshi kaman zai yi magana kuma sai ya nufi dining kawai.

Binshi tayi sai da ya zauna tace
"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya?"
Ya bata amsa ko numfashi bai bari ta ?arasa saukewa ba idanunshi na akan fuskarta sai kawar da ido take daga kallonshi wanda hakan ma dariya ya bashi amma ko a fuska bai nuna alamu ba, ta haWa mishi abin kari da yau English breakfast suka yi a gidan ta tura mishi, bata so ta tafi tayi laifi don haka ta Wauki omlet Waya ta haWa tea ta ja kujerar da take zama chan nesa dashi ta zauna tana karyawa, bai ce mata komai ba itama bata ce ba.

Bayan ya gama ya mi?e ya koma Waki ta bishi da kallo tana Wan taSe baki mutum kaman hawainiya, tattare wurin tayi tsaf kaman ba'a ci abinci yanzu ba ta wuce nata Wakin, monday za ta fara waec don haka dole ta fara duba takarda kafin taje ta faWi sai ta fara lalabo takardunsu na makaranta ta Wauko wayanta ta fara bincike akan past questions da take son fara dubawa.

Shi kam kusan sai da ya gama haWa duk abin da zai bu?ata lokaci lokaci yana dan daakatawa ya tafi nazari kaman wanda baya kaunar tafiyar kan ya Wauki keyn mota da wallet Win shi ya fito sanye da wata White sneakers da ta sake fito da shigar tashi idanunshi ya rufe da ba?ar space sai ya zama kaman wani model ya san kan wanka ba laifi, a babban parlor ya samu su Abeeha suna ganinshi kuwa suka mi?e tsaye don dama sun shirya saboda sun sanshi yadda ya washi jira sai dai a jira shi...

Har sun nufi kofa yace
"Ina take?"
Duk tsayuwa suka yi Abeeha na so ta tambayi ita wa amma fuskar shi da ba'a sake ba yasa tace
"Afeefah ina ga bata san da ita za'a yi fitan ba bari na ?irata"
Ta ?arasa tana nufan sashensu a ranta tana adu'ar Allah ya sa ita yake nufi kafin ya fara mata masifa, sai taga ya fice daga parlorn jannah ta bi bayanshi.

Zaune ta sameta hankalinta kwance
"Tashi maza Wauki gyalen ki muje"
"Ina za mu?"
"Shopping Ya Rayyan ya riga ya fita yi sauri kafin ya hasala"
"amma ni ba abinda nake bukata fa Adda Abee..."
"Ke wlh tunda ya neme ki sai kin je, gwara kin tashi"
Bata fuska tayi don wlh bata son zuwa ko ina, kai Abeeha ta gyaWa
"Ki same mu a mota kuma ki yi sauri"
Mi?ewa tayi ta chanza Abayar jikinta zuwa wani orange, ta saka farin takalmi tayi wrapping kanta da farin Jersey veil ta Wauki wayanta ta nufi waje har lokacin fuskarta ba'a sake ba.

Tun da ta fito ya zuba mata idanu ta cikin glassses na idanunshi yana kallo, a fuskarta ya tsayar da idanu yadda take dan Sata ran ya bi jikinta da kallo Dukda ko ina a rufe yake sai da ya Wan ji wani iri, tafiyar ta kaman tana rausaya Dukda ita sauri take, bai ji haushi ba idan ma zai yi judging wani gefen na zuciyar tashi akan gaskiya zai ce he enjoyed the walking ba tare da ya san dalili ba, tuni su Abeeha suna baya dole ta buWe gaba ta shiga ya Wan lumshe idanu saboda kamshinta da ya shige shi ya buWe tare da tada motar ya fice daga gidan.

Su Abeeha sun zaci ba zasu wuce shopping malls da suka saba zuwa ba na nan kusa kusa ko market square ko barnawa shopping complex sai suka ga ya mi?a ma yayi chan unguwar rimi bai tsaya ko ina ba sai Kaduna Galaxy Mall yayi parking suka sau?a tana shirin sau?a yace

"Ki ji!"
Ta Wan kalleshi tana dawowa ta zauna

"Na'am Ya Saraki?"
Ya zare glass Win ya kalleta sai ta kawar da kanta, kaman zai mata gargadi akan wannan sarakin da take faWa take motsa mishi zuciya sai ya fasa.

"Kina Sata rai babu abin da kike bu?ata ne?"
Ta Yi mamakin yadda ya karance ta Dukda tunda suka fito babu wanda yayi magana a cikinsu.

"Kin min shiru ina magana?"
Ya faWa ba da faWa ba...

"A'a akwai, za mu fara waec monday akwai abubuwan da nake bu?ata na makaranta sai da na fito na tuna"
Bayan ta gama bayanin kuma sai ya mata shiru ta Wan sake haWe fuska shi baya son shiru amma ya ?ware a yi wa mutane banza, sau?a tayi ranta ba daaWi su Abeeha har sun shige ita yanzu ina ta nufa ba zuwa ta taSa yi ba ganin a kyau da tsarin shi ya bambanta da wanda suke zuwa da Abeeha.

Wayanta ta duba don ta ?ira Abeehar ma ta ji inda suke su tafi da ita taga katin ta ya kare ta Wan yi taku biyu tana furta
"Oh! ashe ba ni ma da katin, to yanzu ina zan yi??"

A karye tayi maganan tana sau?e hannunta ?asa, babu zato babu tsammani taji ya sanya hannunshi na dama cikin nata na hagu ya gimtse, da sauri ta kalleshi kaman ba shi ba dole ta fara Binshi sun zaga sossai har wurin kayan makaranta ta Wauki duk abinda take so suka dawo wurin turaruka ya Wauki turarenshi ita bata bukatar komai don kayan aurenta duk babu abinda ma ya dauki hanyar ?arewa suna nan set set, a wurin biya suka ga su Abeeha.

Abeeha da ta hange su daga nesa ta taSa jannah
"Addah Jannah kalli ki ga...!"
Jannah ta waiga tana kallonsu suna tahowa sun yi matu?ar kyau da dacewa fiye da yadda baki zai fasalta, da sauri ta Waga wayanta ta fara musu hoto tana murmushi ganin zai Wagota tayi saurin sau?e wayan tana cewa Abeeha

"ha?i?a ba ?aramin sa'a Afeefah ta taka ba, samun soyayyar namiji irin Ya Rayyan....Ya Allah i just can't imagine.."
With so much excitment tayi maganan. Abeeha ma tace
"Wlh shima yayi dace Mata Kaman Afeefah are very rare sun dai dace kawai duk su biyun they Look so breathtaking"
Gab da su ya saki hannunta ya zaro Atm ya biya aka hada musu komai nasu suka nufi mota, bayan ya shiga ya kunna Ac Win sai yaji baya ba da iska kaman gas babu tsaki mai ?arfi ya ja ya kunna motar suka fice yana sau?e glass a hankali.

Kwanciya tayi ta lumshe ido jikin kujera tana sauraron dukar da zuciyarta ke yi, hannunta da ya ri?e throughout ta kaishi fuskarta ta shafa tana sake sniffing kamshin da ya bar mata har lokacin tana jin softness na hannun cikin nata, bata san sun yi nisa ba sai da suka zo last danger na Waukar hanyar gidansu ta Wan buWe idanu sai taga wasu maza a cikin napep suna kallonsu kaman an ce ya kalli wurin ya sake jan tsaki ya mi?a hannu ya dage glass Win Sangaren ta har sama, ta Wan kalleshi bai ko kalli inda take ba ana sake su yayi kwana zuwa gida.

A yanzu bai Sata lokaci ba don idan ya tsaya batawa zai iya makara gashi takeoff din nasu 12 ne dot. Wurinta ya fara shiga tana zaune kawai ta ganshi ta mi?e tsaye.

"Zan tafi."
Tayi mamaki kwarai don ita yana kasheta da mamaki a tsakankanin.

"Allah ya tsare ya ba da sa'a ya kuma dawo da ku lafiya."
Ya amsa da Ameen a kan lips Win shi yana kallonta.

"Ina fata kina sane da jiya ba yau ba ne, bana son yadda kike fita school anyhow make sure kin saka ko hijabi ko ma Abaya before going in ya so in kin isa ki cire, just focus on abin da ya kai ki. Ki kula sossai don ina da matu?ar kishi akan abin da nake so."
Yana kai nan ya ajiye mata bundle na 1k guda biyu a kan gadon Wakin ya juya ya fita.
neman faWuwa tayi ta samu wuri ta zauna tana jin kalaman nashi na dawo mata
"Kishi akan abin da yake so? Waye yake son?"
Da sauri taje gaban madubi tana kallon kanta sai ta girgiza kai ba dai ita ba kila bata ji da kyau ba ko kuma kariyar nashi irin na ya da kanwa ne.

Jikin Window

35 / 53