HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   44 / 53

129K to 132K   out of 158.4K words

bane kuma bashi da yawa, gashi na kusa gamawa!"
Wuyanta yake shunshunawa
"Shi wannan turaren kam kaman a fatarki aka haWa so sweet"
Ganin ya fara bata kisses a wurin ya sa ta Wauki shinkafar da ta gama wankewa
"Ya Saraki abincina zai ?one"
Bai saketa ba haka suka koma bakin gas din ta juye shinkafar ciki ya lumshe ido yana shakar kamshin
"Hannunki daban ne a girki do you know that?"
Tana zuba tafasashen ruwa madaidaici ciki tace
"Lokacin da nake yi wa su Inna Larai Talla mutanen kasuwa kan faWi hakan amma wannan training Win dai na abincin birni na same shi ne ta sanadiyar Mammi Allah ya gafarta mata"

Ya ce
"Ameen"
Fuskarshi na nuna rashin jin daaWin halin da ta taSa tsintar kanta a baya, suna kitchen Win har ruwan shinkafar ya Wan tsotse ta juya kan ta rufe da foil ta rage wuta ya kara 15mins ta juyo musu a plate ta Wora kan tray shi ya KarSa suka koma parlor, shi ya Wauki spoon Win ya shiga bata yana ba kanshi, a lomar farko ya lumshe ido ya buWe yana taunawa
"Wow My love shi kuma wannan menene sunanshi?"
Tayi murmushin farin cikin ganin yana yabon abinda ta dafa tace
"Supreme Rice sunanshi"
"I love it, Allah yayi miki albarka"
Ta amsa da Ameen suka ci gaba da ci har suka gama ya bata ruwa ta sha kan ya tattare kwanukan za ta karSa ya ture hannunta.

"Ya Saraki..."
Ya ma yi gaba bai saurare ta ba ta mi?e ta bishi
"Kar fa a kama ni dumu-dumu da laifin saka Saraki aiki"
Ya ajiye kwanukan yana Waukatarta gabadayanta
"Girmanki ne hakan, ina so har abada in zama mai hidimta miki har sai na kasance ni ne ma'anar farin ciki a rayuwarki"
She's just blushing daga jiya zuwa yau bata san matakin da zata Wora farin cikin dake ratsa zuciyarta ba hakika tayi dace kwarai da masoyi, kai tsaye kan gadonshi ya shimfiWeta ya zare rigan shi ya kwanta tare da janyota jikinshi sai ta fara zare idon tsoro.

Fahimtar hakan don har a jikinta ya ji hakan ya sa yayi murmushi yana shafa kumatunta dake kan kirjinshi yace
"Bacci za mu yi Gimbiya just stay calm okey ai na san baki warke ba, ko kin warke?"
Kukan ShagwaSa ta fara ya saki murmushi mai sauti yana shafa bayanta a haka suka yi baccin kuwa, basu tashi ba sai la'asar yanzu ma da kanshi ya mata wanka duk yadda take dojewa ya ?i barin ta, gudu wa tayi ta barshi a bayin don ta kasa natsuwa yayi tashi wankan gabanta sai take jin kunyar duniya na rufeta.

?akinta taje ta shirya cikin wata atampha doguwar riga dinkin ya zauna mata tsaff ya fitar da duk wani sura na jikinta tayi wanka da turare isashe a ranta tana mamakin shine ya kori har su Adda Abeeha ko su ne suka yi tafiyar su yini guda basa nan, tana kokarin fitowa parlorn taji sallamar GaabWo sai ta koma don yanzu ranshi zai iya Saci.

Shi kuwa ya fito ma ganin GaabWo ya sa ya samu wuri ya zauna sai ya koma Sarakinshi ya Wora kafa Waya kan Waya yana relaxing ba tare da ya kalli GaabWon ba yace
"Menene?"
"Allah ya baka yawan rai kana da ba?o ne babba, na sanar dashi ka ce baka son ganin kowa yau amma ya dai tabbatar min lallai lallai in ce yana son ganinka"
"Waye?"
Ya tambaya yana kallon GaabWon don bai san wani isashen bane zai ce lallai lallai sai ya ganshi bayan ya ce baya bukatar ganin kowa a yau.

"Allah ya baka yawan rai ranka ya daWe Ameer ne na gidan Galadima"
Da sauri ya Wago
"Ameer?"
Kai ya gyaWa cikin tabbaci
"Kwarai da gaske ranka ya dade."

*****

"Fulani kin yi shiru baki ce komai ba, tun da abin nan ya faru muke ta so mu zauna amma baki ba mu dama ba yau kuma kin kira mu kin yi shiru...! Kar fa mu tsaya kallon ruwa kwado yayi mana ?afa shekaru nawa muka Wauka muna shiri ba zai yiwu lokaci Waya komai ya warware ba. Ba zai yiwu ba"

Ta kalleshi fuskarta babu Wigon walwala tace
"Baka kai ni damuwa ba Yaya, baka kai ni ba?in ciki ba... Ba kuma ka kaini takaicin dawowar wannan shegen yaron ba mai idanu a tsakar ka, ni kaWai na san gwagwarmayar da ni tsawon shekaru ba zan ga kwaba na yana son yin ruwa in ja baya in zuba ido ba, sai dai ba na so mu yi gaggawa ne komai ya zo ya ?arasa lalace mana! Dole za mu yi maganin abin"

"A yanzu menene mafita Adda?"
?ayan namijin yayi magana
"Abu Waya ne tak, dole za mu gabatar da plan Win mu tun na farko a kanshi... A yanzu matsalarmu Waya ubanshi, amma zan san yadda zan yi dole ya amince da ?udiri na mu kuma za mu yi amfani da daman mu salwantar da rayuwarshi da ta iyayenshi gabaWaya don na tabbatar salwantarshi daidai yake da nasu salwantar don ba za su jure ba..."

?ulle ?ullensu suka cigaba da yi sama da awa biyu suna nan zaune kan suka mayar da badda kamarsu suka fice daban daban kowa yayi hanyarshi.

****

Yinin su Abeeha a sashen Ammi ya musu daaWi don da kanta ma ta tsefewa jannah kai akan za su yi kitson Fulani tunda gobe akwai taron Matasa na Fuunange, hira suke yi sossai tun Aisha na Wari dari da su har suka sake da juna Ammi kam kaman ta mayar da su ciki don kulawa musamman da suna bata labarin irin kalar rigimar Rayyan da Mammi suna ta raha da dariya. Ammin na jin kaman ta zama Mammi ko na seconds ne ta samu irin wannan kulawa da kauna daga y?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 aron nata.
Jin ma mijin jannahn zai zo goben yayiwa Rayyan Win ma murnan dawowa Ahalinshi sai su koma jibi yasa ta kira a zo a mata gyaran jiki na musamman, sai yau suka ji kaman sun samu madadin Mammi don duk abinda Mammi zata iya yi musu gashi Ammi na yi musu, bayan Azahar da kaWan suna cin abinci ne ma an gama yi wa Abeeha kitson da yayi mata kyau ainun sai suka ji an turo kofar parlorn.

Aisha ce ta fara kallonshi ta yi tsallen murna tana kwala kiran Ammi
"Ammi! Ammi"
Fitowa daga Waki Ammin tayi tana cewa
"Aisha bakya rabo da autanci ihun nan fa? Sai idanunta ya sauka a kanshi fara'arta ne ya ninku a hankali ta isa ta kama hannunshi
"Wa nake gani haka? Ko dai idona ne?"
Yana dariya ya ce
"Sam ba gizo bane nine Ammina, Na same ku lafiya?"

*Kun ga readers marasa cewa thank you ko yin comment nan kuna bani mamaki, na faWa pages dayawa a baya na nanata Weekdays ina da ayyukan dake gabana sai dare nake posting amma idan na kai daren nan su masu ma comments Win ainun da nuna jin daaWinsu basa damuwa kaman Marasa cewa ko ci kanki..Allah ya kyauta*


=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*53*

https://chat.whatsapp.com/HUJI7tg9TOU941grP60r4S?mode=ems_copy_c

Kinaneman group din dazaki ringa sarinkayan kitchen cikin farashin sari...tayadda koda kinje kasuwa bazakisamu kasa d farashinmuba snn zaki iyazuwa har hargida kisayi dukkan kayan dakike bukata cikin kwanciyar hankali kokisaya ayimaki delivery zuwa dukkan inda kike afadin Nigeria da dama makotan kasashenmu kikarbi kayanki cikin farinciki da aminci!!!.....kiyi joining a mai nono kitchen utensils and household........gaskiya d amana sune takenmu!!!=?O?
*******

"Ameer! Yaushe rabon da a gana? Ashe za ka zo?"
Ya shafa kanshi yana rike hannun Ammin yace
"Ammi abubuwan mu ne sai a hankali amma kuna raina wlh"
"Da muna ranka ba'a waya kaWai zaka dinga jin mu ba da kana zuwa shekara nawa rabon da ka waiwayi gida?"
"Na tuba Ammi yanzu kam zan dinga zuwa, yanzu Win ma labarin bayyanar Sameer ya saka ni zuwa dole."
Suka kai zaune, Aisha ta kawo mishi ruwa yayinda jannah ta gaishe shi ya amsa, Abeeha ma ta gaishe shi ganin shi mutum mai fara'a kwarai da wasa ya burge su.

"Ammi ina kika samu wasu yaran babu labari?"
"?annenka ne, Abeeha da Jannah ga wani yayan naku Wan wajen babban yayana ne Galadima, abokin Sameer ne don tare suka tashi kaman 'yan biyu a Wakin nan Sacewar Sameer bai sa ya bar nan ba anan yayi rayuwa har ya gama secondary ya tafi karatu chan kasashen turawa ya gama da jimawa ya ?i dawowa"
Sannu da dawowa suka sake yi mishi ya amsa da kulawa.

"Ammi ina Sameer Win? Wani sashe yake?"
"Ka ci abinci ka dan huta sai kaje yana chan tare da matarsa"
Wara ido yayi
"Har ma aure yayi abin shi"
"Eh ya bar ku da gaurantaka"
Yayi dariya, Abeeha ce ta taya Aisha presenting mishi abinci kan suka koma suka zauna suna ta jin hirar su da Ammi wanda suke tuna baya tasowarshi da Sameer, hakika zata iya cewa shine na uku a damuwar rashin Sameer don sai da yayi jinya tunda tun ba'a yaye shi ba ya yaye kanshi ya dawo wurinta saboda Sameer sun shaku sossai ta zama sanadiyar raba wannan ?aunar.

Bayan ya gama sashenshi da bai da nisa da nata ya ?arasa don ana gyarawa akai akai kuma zaman cin abincin nan da yayi ta aika wasu hadiman sun sake kakkaSewa ya tafi yayi wanka yana fitowa ma yaji ana kiran la'asar don haka sai da yayi sallah ya fita ya tambayi wasu fadawa suka fada mishi inda sashen na Sameer yake ya nufi wurin.

"Amir Galadima..!"
Rayyan ya faWa fuskarshi Wauke da fara'a shima Amir cike da fara'a ya rungume shi suka raba hug Win suka tafa irin na mazan dai da aka manta rabon da a haWu.

"Sameer kana duniya ashe? Baka kyauta mana ba! Ka Sace babu traces? Hankalinmu ya matu?ar tashi har ka bayyana ban daina tunaka ba, sa?on bayyanarka na daga cikin news mafi jin daaWi da na taSa ji a duniya"
Murmushi kawai Rayyan yake.

"Mu isa ciki, wannan labari ne mai tsawo and ka san ban da bakin ba dashi"
Suka nufi yana furta
"Har yanzu ana nan da ba?in hali"
Murmushi yayi yana tuna kalmar Afeefah wai ta mishi shaidar Rashin kirki a baya yace
"Tunda matata ma ta faWa hakan don ka faWa ba komai bane"
Dariya sossai Ameer ke yi har suka ?arasa parlorn suka zauna, nan hira ya fara don Ameer na daga cikin waenda a bayan ma suka san dariyar Sameer, daga shi har mahaifinshi suna da muhimmanci sossai a rayuwarshi Dukda tun dawowarshi sau Waya yaje wurin Galadiman kuma tun da ya kawo mishi maganan Ammi bai sake komawa ba.

Ita kam Afeefah jin hirar su yasa ta nemi gyale mai girma ta saka ta Wora wata alkyabba marar nauyi shara shara a kai ta fito, tayi kyau sossai don ya kasa dauke ido a kanta Dukda bata shafa komai ba, gaisawa suka yi da Ameer cikin natsuwa da girmamawa kan ta kawo ruwa da su snacks ta ajiye mishi, ta kalli Rayyan

"Ya Saraki bari na je wurin su Adda Abeeha yanzu za mu dawo"
Bai ce komai ba don baya son abinda ke tsakanin shi da mahaifiyarshi ya shafe su dukkansu.

Ta juya ta fice, tana tafiya ana jefa mata gaisuwa har ta kusa isa sashen suka haWu da Fulani Adama, ta Wan rusuna ta gaisheta
"Lafiya ?alau ya ba?unta Afeefah?"
Ta amsa tana ?are mata kallo ganin yadda ta sake wani kyau da haske.

"Alhamdulillah Mama"
"Masha Allah."
Tana kai nan ta wuce ta itama ta wuce ta nufi wurin Ammin, zaune kuwa ta same su har lokacin ganinta yasa jannah fara cewa
"Amarsu ta ango"
Murmushi tayi tana sunkuyar da kai saboda Ammi dake wurin ta du?a ta kwashi gaisuwa.
"Lafiya ?alau Gimbiya Afeefah, ya zaman ba?unta da rashin sabo?"
"Alhamdulillah Ammi"
"Masha Allah, yanzu kuwa Mamanku ta kawo min ?ararku sai dai na bata uzurin da cewa laifina ne tunda ku ba?i ne baku wani san tsare-tsaren ba, ni kuma rigimar Sameer ne yasa ban yi maganan ba"

"Allah ya sa ba laifi muka yi ba Ammi"
"A kan zuwa gaisuwa ne, ya kamata duk safiyar duniya ku bi ku gaida iyayen naku musamman ke Afeefah da kike matar Ciroma"
"Ayi mana afuwa bamu san da tsarin ba amma za mu gyara in shaa Allah"
Ammi tayi murmushi tana yaba Yadda Afeefar ta iya magana.

"Adda Abeeha kitson nan yayi kyau masha Allah"
"Kin ga nawa ni ma, kitson na da kyau wlh"
Jannah ta faWa tun kan Abeehar ta bada amsa tana nuna mata kanta.
"masha Allah duk sun yi kyau"
"Afeefah zo kema in tsefe miki sai a yi miki tunda duk gobe shigan al'ada za ku yi"
Tace
"Ai Ammi kaina a tsefe ne"
Wacce ta yi musu kitson ta kira aka kawo kayan kitso na musamman itama aka shiga yi mata kuwa suna hirarsu.
Dab Magrib aka gama yayi kyau ainun ya amshe ta don har a fuskarta zaka san ta chanchada kitso yadda ya ?ara sheki.

Ana gamawa kuwa sai ga wani hadimi ya nemi a sanar da Fulani Afeefah Ciroma ya aiko a yi kiranta, Mi?ewa tayi ta kalli su Abeeha
"Adda Abeeha ku tashi mu tafi please"
"A'a yi tafiyar ki muna wurin Ammin mu"
ShagwaSe fuska tayi
"Ni kaWai za ku bari a chan? Ammi kina jin su?"
"Ba ke kaWai ba kam, ki faWi tsakaninki da Allah ko sanin mun taho ma kin yi in ba da kika ji shiru ba?"
Hararar wasa take yiwa Abeehar suka yi dariya har Ammi ganin ta kasa cewa komai yasa ta juya zata tafi sai ta juyo ta kalli Aisha da itama sun fara sakewa sossai da juna tace
"Ko za mu tafi kawai Aisha?"
Aisha ta zaro ido
"Ni?? Raba ni da shiga shirgin mijinkin nan yanzu su Adda Jannah suka gama labarin rashin mutuncinshi in je ya zane ni?"
Zaro ido tayi
"Yaya Sarakin ne bai da mutunci? A kunnenshi to!"
Mi?ewa suka yi suna ce mata ta tsaya ta ji ta rufa musu asiri su ba haka suke nufi ba tuni tayi gaba tana dariya suma duk dariyar suke har Ammi, saura ?iris ta ci karo da Zarah suka tsaya suna kallon juna, a hankali maganganun Fulani Adama suka shiga dawo mata kaman yanzu suke yi, barin ma da ta ga kyaun da Afeefar ke ?arawa ga iya ado kaman sarauniya, ga kamshin ta da in ka shaka zaka san ka shaka ko ita da ta tashi a masarautar bata irin dressing da daukar ido haWe da kamshin da Afeefah ke yi, abinda ya sake sa taji kaman da gaskiyar Adama shine dariyar da ta samu duk suke wanda take da tabbacin yana da alaka da Afeefar idanunta ta sauke akan Aisha dake tsakiyar su Jannah sai kawai ta juya ta tafi.

"Zarah kin tabbatar za ki iya aikata duk abinda za mu saka ki? Sannan za ki iya ri?e mana sirri?"
"Mama kin raine ni ne akan kafafunki kaman Wiyar da kika haifa da cikin ki, har manta cewa ni Win Wiyar dan uwanki nake don ban taSa neman abu na rasa daga wurin ki ba, don na taya ki ya?i akan cikar burinki na tsawon shekaru ban faWi ba sai ma halarci da na mayar. Dukda Na ji Son Ciroma Sameer a raina hakan ba zai hana na isar da Manufarki yadda ya kamata ba"
"Masha Allah, haka nake son ji yanzu na san ban yi rainon banza ba. Zarah!"
Ta amsa
"Za ki auri Sameer dole sai dai bana so ko kadan zamanku yayi nisa"
Kallonta take da neman karin bayani
"Ba haka aka so ba kuma duk Shigowar wannan Afeefar ne ya Sata mana komai amma a yanzu za mu gyara, za ki shiga a mata ta biyu amma ke za ki haihu za mu yi duk yadda za mu yi mu hana Afeefah haihuwa da Sameer, ke muke so ki sama mana Wa namiji daga nan kuma za mu shafe Sameer"

"Mama ko da yaron bai girma ba? To waye zai yi sarautar?"
"Mahaifinki shine first cousin na sarki kuma yana da ikon yin sarauta zai iya ri?on ?warya har dan da zaki haifa ya girma ya bashi kin ga kenan Sarautar gabaWaya ta dawo gidan mu kaman yadda dama tun chan yake a tarihi aka yi mana fin karfi aka hana mu"
Shiru zarah tayi Fulani Adama tace
"Ke kar fa ki tsaya wani kokonto don a sarauta babu kokonto ko tsoro, sannan kar ki bari wani soyayya yayi tasiri saboda babu wannan a tarihin jajirtaccun da suka yi mulki, ko ni na auri mai martaba ba don ina so ba sai don burin haifar Sarkin gobe, a yadda ban haihu ba na so kowa ma ya rasa har shi mai martaban ya mutu a haka dole 'yan uwana su karSa amma Yarinyar chan FaWimatu ta lalata min shiri don haka dole ne ta ga ba daidai ba"

WaWan nan sune maganganunsu da Fulani Adama da farko tana wasu-wasi amma yanzu ta ji lallai zata iya, za ta iya aikata hakan ba Sata lokaci.

Afeefah na isa ta samu yana zaune a parlor kafanshi Waya a kan daya yana Wan karkadawa ganinta bai sa ya saki fuska ba tace
"Barka da hutawa Ya Saraki"

"Sai yanzu?"
Ya faWa yana kallonta, tuna irin kirkin Ammi take da irin damuwar da take ciki ko a murmushinta za ka iya fahimta hakan yasa ta mi?e daga inda take ta dawo kusa dashi tare da zame alkyabba da gyalen kanta haWe da Wan kwali tace a ShagwaSe
"Wai fushi ka yi na jima Ya Saraki? Kitso fa nayi kalli ka ga bai yi kyau ba?"

Ya kasa Wauke ido a kanta ta mishi kyau da Kitson sossai ya ri?o hannunta
"vooWi masin boWWiyel am"
Dukda bata ji ba ta Wan yi murmushi
"Me ka ce kenan?"
"Mai kitson Fulani bata iya yaren ba?"
"Toh ai bana ji, kaima na yi mamakin yadda na ji kana yi fluently"
Ta Wan kwanta a jikinshi yana sake kallon kitson da ya fidda fatar kanta fesss yace
"Tun daga ranar da na bar gidan nan ban sake yi ba sai da na dawo"
Ta sa hannu ta zagaye cikinshi kanta na a kafaWar shi duk tausayi suke bata daga shi har Ammin.
"Toh ka faWa min me ka ce?"
"Ya yi kyau sossai kyakyawata. Abin da na ce kenan"
Tayi murmushi mai sauti tana ?o?arin maimaita abinda yace da fulatancin, yadda ta shirmata dole ta saka shi murmushi har ma ya manta da yana kokarin yin fushi ne ta tafi sashen

44 / 53