HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   15 / 53

42K to 45K   out of 158.4K words

ba don bata tantama har zobunan gwagwalanta suna ciki amma bata ko buWe ba bare tayi tunanin yi mata sata, hakan ya matu?ar burgeta.

"Saraki mu kai ta gida ko? Ina so in ga gidansu in yi ma iyayenta godiya kuma in basu hakurin rashin ganinta kan lokaci"
Ta kalleshi shima ita ya kalla bakinshi ne yayi mishi nauyi, kuma ba ya son dogon bayani sai ya kalli Afeefar da kanta ke ?asa kaman daga sama ta ji ya ce

"Kina da gida?"
Yayi maganan yana Wage gira Waya.

Mammi ta Harare shi
"Wani irin tambaya ne wannan akwai wanda ya faWo daga sama ne?"
Ita dai tambayar ya zo mata wani iri sai hawaye suka cika idanunta a lokacin ta tuna ashe bata da inda za ta je, da alamu kuma ya sani don maganar shin ya fi yi mata yanayi da gatse, a hankali ta kalli Mammi

"ba sai kun kaini gida ba Aunty, kina bukatar hutu saboda jikinki daga nan zan koma da kaina"
Tayi saurin juyawa amma duk da haka ya ga hawayen da ya silalo mata, Ado ya kalla

"?auki akwatin nan mu tafi"
Yana kai nan ya fara kokarin kama mammin

"She has No where to go, for now za mu tafi tare"
Cike da tausayi Mammi take kallonta, so take ta ji karin bayani me ya sa bata da inda zata je? Ina dangin ta in bata da iyaye? Amma sanin duk ba yanzu bane lokacin maganar ta saki Rayyan ta ri?o hannun Afeefar galala yayi yana kallonta ko ta tsaya don ta san rigimar shi, haWe fuska yayi sossai ya biyo bayansu.

Sanin halinshi ya sa Mammi ta zauna gaba Afeefah ta shiga baya, ya ja motar a hankali ya fita daga asibitin, Ado ma ya bi bayanshi har yanzu zuciyarshi bai dawo daidai ba yana tantamar ko Rayyan ya barshi ko sai ya Wauki mataki a kanshi don abin da duk ya shafi Mammi baya wasa da shi sam kaman yadda ita ma bata da kaman Rayyan a duniyarta.

Shiru motar yayi don Mammin na bu?atar hutu so ganin ma kaman ta gaji da zaman ya nemi wuri yayi parking, ya Wan koma baya ta yadda ya sake birkita Afeefah dake zaune saitin kujeran shi ya sa hannu ya kwantar da seat Win mammin a hankali, ta buWe ido ta kalleshi ta Wan yi murmushi kawai ta sake lumshe ido ya furta
"Sannu"
Cikin tsantsar kulawa, sai kallonsu Afeefah take yi. A iya zaman nan ta fahimci matar tana da matu?ar muhimmanci a rayuwarshi Dukda bata ga kama ba don matar ba?a ce kaman ita shi kuwa farin shi har ya Saci, ba zaka taSa cewa bai hada dangi da Larabawa ba barin ma kasumba da gemun da ya ajiye Wan daidai da shi ba?i sidik.

Motsin kirki bata iya yi kamshin motar har yana hawa mata kai a haka suka isa wani tsararren unguwa shiru ne unguwar kaman ba titin da suka baro ke Wauke da hayaniya da jama'a ba, nan Win gidajen manya manya ne, sai dai ka hangi su dawisu da su jimina a gidajen da gininsu ma na zamani ne, gaban ko wani gida kuma akwai securities zaune kusan kowanne sanye da uniform ko yellow ko blue, a hankali ya gangara gaban wani golden gate mai girma fuskar sai sheki take horn yayi, sai gashi an le?o wannan Win ma na sanye da blue riga da bakin wando, Gaisuwa ya shiga mi?awa Ogan nasu ya Waga mishi hannu kawai don Window na sau?e saboda rashin Ac. Tamfatsetsen gida ne don yayi na su Saleem sau uku ko biyu da rabi, gidan tamkar ginin sarauta saboda fari ne kal an mishi ado da golden paint har kwanon golden Color ne, harabar na shimfide da interlocks Wauke da shukoki masu tsananin kyau da Waukar ido, Dukda akwai parking lots har uku jere da motocin alfarma bai yi parking a ciki ba sai da ya je dab kofar shiga yayi parking ya sau?a ya zagaya ya buWewa Mammin kofa.

Ita dai Afeefah na ta mamaki don bata zata akwai wanda wannan mai zafin ran ya dauka da muhimmanci ba haka, bata taSa zaton zai iya buWewa wata macen kofa ba kila dai mahaifiyarshi ce, kila kuma kamannin mahaifinshi yayi shiyasa basa kama ko ta wani Sangare.

"Afeefah sau?o mana kin zauna ciki"
Ta faWa a hankali, buWe murfin tayi ta sau?a tana jin kanta dake sara mata na ?aruwa saboda tsabar kukan da tayi yau, kunyar hijabin jikinta take don onion colour ne kuma duk gaban da ya jike da hawaye ya bushe sai yayi wani jirwaye jirwaye,
A baya ta bi su har suka shiga cikin tsararren parlorn mai girman gaske sanyi ne ke ratsa ko ina ga kamshi, parlorn kal kal kaman a zuba maka abinci a ?asa ka ci komai na parlorn royals ne golden and milk, tana kuranta kyaun gidan su saleem wannan gida ya fi nasu tsaruwa nesa ba kusa ba.

A cikin kujera suka samu wata budurwa ganin Mammi ya sa ta tashi da gudu ta nufeta sai dai hararar da Ryan ya sakar mata ya sa ta fasa isa da gudun ta Wan natsu
"Mammi are you Okay? Me ya same ki? Na dawo daga school wai kin fita Mammi jikinki yayi kyaun da za ki fita? M..."

"Will you shut up and let her rest?"
Ya faWa ba da tsawa ba sai dai ba kuma da wasa ba, mammi ta Wan yi murmushi
"Abeeha ga Afeefah ki kai ta Waki na musamman a kai mata abinci tayi wanka ta kwanta ta huta sossai please she's exhausted daga alamunta"

Kallon Afeefah Abeeha tayi sai ta juyo zata fara jero wa Mammi tambayoyin ina ta samo ta sai suka haWa ido da Ryan tuni ta wuce ta kama akwatin da Ado ya shigo da shi suka yi wani Sangaren daga cikin parlorn.

A hankali suka isa wani matakala uku suka hau zuwa wani corridor da ya ji interior kan suka shiga wani parlor madaidaici kuma tsararre grey ne da Black colour, bai barta nan ba sai da ya sadata da cikin bedroom Winta duk ko ina suka bi kalkal yake gidan kaman kullum ake wankewa, a bakin gadon da shima Grey ya ji shimfida White ya ajiye ta ya buWe wani frigde dake gefe ya fiddo ruwa marar sanyi sossai ya bata ta sha sossai kan ta Wan kwanta
"Sannu Saraki Allah yayi maka albarka"
Idanu ya lumshe ya buWe tuni suka Wan sauya, a hankali ya amsa da Ameen kan ta Wan kwanta tana sau?e numfashi.

"Mammi ki huta sossai please, bana so in tafi in barki amma Saleem bashi da lafiya i need to go and see him, ba zan jima ba zan dawo"
Tayi murmushi
"Su fa Maryama suna nan kar ka damu take your time, kuma ma Abeeha ba ta dawo ba na san tana gamawa da Afeefah zata zo"
"Ta ishe ki da surutu dai"
Yana kai nan ya mi?e tana mishi sai ya dawo ya gaishe mata da saleem ya fice.

Wani motar daban ya Wauka mai Ac ya fice daga gidan bayan ya umurci Ado da ya fita da wanda ya dawo ya kai a saka Gas na Ac, kai tsaye gidan su Saleem ya nausa bayan ya isa ya bi ta baya ya haye saman zuwa Wakin saleem Win komai a kashe ya samu kaman ba mutum, hasken ya kunna ya nufi cikin Wakin sai ya samu saleem lullube da bargo, kanshi ya nufa ya janye bargon ya sa hannu a goshinshi ya janye
"Subhallah! Saleem you are burning up tashi mu tafi hospital"

"Ryan Afeefah, ban san wani irin hali zata faWa ba am scared kar Allah ya kama ni da laifi... Please help me find her please"
Da kyar yake maganan saboda zazzafar zazzabi dake kassara gaSoSinshi.
"Za mu same ta, In shaa Allah i will find her lafiyarka First ur temperature is very high"


=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Ku min uzuri da rashin amsa comments please matsalar wayata ta saka sai na nemi wani wayan nayi connecting hotspots saboda gidan sim din ta ?i gyaruwa, please bear with me idan na tara comments ina bi in karanta na gode sossai da sossai. Anjima zan samu in duba idan na ga an zuba yadda ya kamata in shaa Allah za ku ji ni da dare*

*019*

Ko sanar da mutanen gidan bai yi ba suka tafi asibiti kai tsaye Amenity ya sa aka kai shi ya fara bashi taimako saboda abin ya Buge shi sossai, tausayin Saleem Win ne ya rufe shi mahaifiyarshi bata yi mishi adalci ba amma uwa ce ya suka iya?

A chan gida kuwa Mudi ne ya shiga ya same su duk suna zaune a parlor fuskokin su babu walwala.
"Hajiya Oga saleem ne..."
Da sauri Sameera ta katse shi
"Yayi me?"
"Babu lafiya yanzu Oga Rayyan ya fita dashi jikin dai babu daaWi ban gan ku ba nake tunanin baku sani bane"
Samha ta ce
"Mun shiga uku, duk akan Afeefar ne?"
Shi dai mudi shiru yayi karshe ma ya bar parlorn, Sa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????meera ta Wauki mayafi tana kallon mommy dake zaune har lokacin, sadiqa da Samha ma suka mi?e Sameera tace
"Mommy ki tashi don Allah mu je muga ya jikin nashi, mommy kaman ba a yi mishi adalci ba wallahi..."

"Ba zan je ba ki ja ni ki kai ni, babu inda zan je ya gama ciwon ya dawo ya same ni, ba dai a kan wanchan Mayyar ba ce? Zai yi ya gama Rabuwa kam sun rabu na har Abada"

"Amma mommy ya kamata dai ki je ciwo ai ya kore komai"
Sadiqa ta faWa, Samha tayi fuskar tausayi bata san haka abin zai kasance ba da bata janyo wannan rigimar from First place ba, suna son dan uwansu basa son ganinshi cikin wani hali.

Duk yadda suka yi da mommy akan ta je ta ?i haka suka tafi su uku, suna ficewa ta sabi gyale itama ta dauki mota ta bar gidan.

Tafiya mai nisa tayi kan ta iso inda ta nufa, wani gida ne tayi parking gidan dai daga gani Talaka ne mamallakinshi don ya tsufe har ya gaji, ta sauka ta shiga ciki da sallama.

"Ah Hajiya Hussaina ce tafe? Maraba sannu da zuwa sannu da zuwa"
Matar da daga ka ganta ka san suna cikin wahala daidai gwargwado ta faWa tana Wauko taburma sabuwa ta shiga shimfida mata zama tayi suka shiga gaisawa, bayan sun gama tana Wan kallon cikin gidan tace
"Yaya fa? Allah ya sa dai bai yi nisa ba"
Tace
"Yanzu kuwa ya fita amma babu jimawa zai dawo don abu ya je karSo wa nan kusa da mu"
"Ina yaran? Ina sabreena?"
"Duk fa sun tafi Allo, ita sabreena suna bukin ?awarta ta fita"
Bata gama magana ba kuwa sai ga Yayan ya shigo.

"Hajajju ke ce a gidan maraba sannu da zuwa"
Gaisawa suka yi Dukda yayanta ne sai dai shi ke bata respect duk saboda kuWi masu gidan rana.
"Ina soja marmari daga nesa? Sati biyu kuwa da ya shige ya aiko mana da kayan abinci wane Allah dai yayiwa rayuwa Albarka ya cigaba da buda mishi"

"Ameen yaya, dama maganan da ta kawo ni kenan ma akan shi... Ka san akwai batu a kanshi da sabreena da take ta mutuwar sonshi shi kuma yana nuna baya so, to yanzu zancen da nake maka wata yaje ya Wauko chan wani kauye ta asirce shi tun kan ma ayi auren sai maganarta yake ji yanzu haka saboda na raba su yana chan kwance gadon asibiti"

Gaje da Yaya suka hada baki suka ce
"Eyeee ka ji min yaran zamani ki samu mutum da uwar shi ki so raba su? Amma Saleem dai yayi ragon azanci ina shi ina irin waennan matan?"

"Shiyasa nake so a tado magananshi da sabreena da na Wauka wata mai hankali zai Wauko mana ashe dai shima hankalin bata ishe shi ba, na kuma ga gida bai koshi ba ai ba za'a kai waje ba, idan ba damuwa ma bana son auren nan ya Wauki lokaci ko wata bana so ya rufa ta zo tayi jinyarshi"

Gaje ta washe baki, Yaya dai ya Wan yi shiru kan yace
"Toh ai wani hanzari ba gudu ba, kin san bamu ajiye komai ba na shirin aurar da sabreena"
"Yaya duk wannan ba komai bane, ni ce nan uwarta ni ce ubanta ita kaWai nake so"
"Toh ai shikenan Allah ya shige mana gaba"

Suna cikin maganan sai gata ta shigo sanye da hijabi har ?asa ganin mommy ta tsuguna
"Sannu da zuwa mommy"
"Sabreena ba zan amsa ba, yaushe rabon ki da gidan mu? Tun su Samha na jaje har suka gaji"
Baki ta Wan taSe tana ayyana su kuma dayake basu san inda nake ba ba, ai ina sane da kyamar gidan mu suke ji shiyasa basa zuwa.

"Mommy islamiyya ne duk ya ri?e ni kin san muna ta shirin sau?a"
"haka ake so ai Allah ya taimaka"
Daga nan bata wani jima ba tace zata tafi suka raka ta har mota kan suka juyo gida.

Wani irin guWa gaje ta saki
"Malam!!! Kukanmu ya kusa yankewa nesa ta matso kusa"
Shi dai wani kalar murmushi yake, Sabreena ta cire hijabin jikinta ta jefar
Sanye take da wata fitted gown na lace da aka yi wa arniyar Winki da ya bayyana komai nata, kanta attach ne da ya zo har duwawu ta ja tsaki.

"Ke 'yar gari ya aka yi kika ankare tana nan?"
Gaje ta faWa tana kai mata duka kamar kawarta
"Motar ta na gani nayi maza na shiga makota na ari hijabi na wanke fuska na cire eyelashes da nails Wina gashi a banza bata bani ko biyar ba mata sai makon bala'i"

"maganar aurenki ya kawo ta, nima zan so a zo ayi saboda na gaji da gani gani da ake yi min a unguwar nan, ita kuma Hussaina a zaton ta banza ya faWi ne zata Wauka bata san ta daukawa kanta wuta ba... Ai yadda uwata bata taSa kaunar nata uwar ba nima ban taSa ?aunarta ba kuma ita ma haka da tana ?aunata da bata barni nan cikin wahalar talauci ba"

Haka suka dinga tattauna yadda za su ci arziki don mommy ta jima da tsaya musu a wuya kaman kashin kifi, don ma saleem mutumin kirki ne mai son zumunci baya wata bai turo musu wani abu ba amma ita kam bata tunawa da su sai in bukatarta ne ya tashi, ta watsar da dangin tamkar kashi an Wauki ?awaye masu kuWi an manna a jiki har kunyar nuna su take.

Sabreena dai da farko yarinya ce natsatsiya amma zamani ya zo mana da wani abu, iyaye ba ruwansu bane yaro ya tsaya yayi karatun islama ko kar yayi, damuwarsu dai a nema ko ta wace hanya, babu kwaba babu cikakkiyar tarbiya, tun tana dai yin abin saffa saffa yanzu babu wanda bai san Sabreena 'yar karya ba, barta da son karya yau wannan saurayi gobe wanchan don tana da kyau kuma suna kashe mata amma dai ita ta riga ta saka saleem ne mijinta tunda iyayenta suka kwadaita mata hakan a ganinsu duk samarin ta ba zata yi mai kudin saleem ba.

Ita kuwa mommy tana shiga mota tayi murmushi
"Gwara ka auri wacce ko kwanciya na ce tayi in bi ta kanta zata kwanta, wacce dole ku haWu ku bi umarnina tare akan ka kwaso wacce zata raba ni da kai ko ta hanyar soyayyace kuwa bare uwa uba asiri"
Daga haka ta ja motar ta bar unguwar tana kwafa.

****

Afeefah kam suna shiga Wakin da Abeeha ta kaita ta tsaya tana karewa Wakin kallo, Wakin yayi kyau kwarai kuma full furnished don kayan Wakin milk da gold a gyare yake kaman akwai mutum ciki alhalin ba mai zama Wakin tunda mai dakin tayi aure.

"Feel free Afeefah ki yi wanka bari na sa a kawo miki abinci, in kin ci sai ki hau gado ki huta ko?"
Ta kalleta sai taga murmushi take mata saSanin ranar da ta fara haWuwa da Samha ta tuna har wanke bayi Samha tayi da sunan tana kyamarta don kawai ta shiga tayi alwala, murmushi ta mayar mata tace
"Na gode"
"Mind not"
Ta faWa tana ficewa, a ?asa Afeefah ta zauna tana dafe kanta da kaman zai faWi, ta fara tunanin halin da Saleem ke ciki sai dai kuma tayi tunanin ba zai damu sossai ba idan Ryan ya faWa mishi tana gidan su, jiri sossai yake damunta a haka ta lallaSa ta mi?e ta shige bayin, wanka tayi tana raya a komai ma fa gaba da gabanta tana tunanin abubuwan bayi da ?awa na gidansu saleem ne ?arshe bata san akwai irin wannan ba, sai kuma ta fara tunanin kila suma akwai wanda ya fi nasu shiyasa Allah ma da ya tashi bai yi yatsun hannu daidai ba kowa da matsayinshi.

Amma me yasa kirkin waennan ya bambanta da waenchan Dukda waennan sun fi su dukiya? Bata da amsar wannan tambaya ta wani Sangaren kuma tana da shi don uwa nagartaccciya da suke dashi ya gama amsa mata komai, dafe da gini ta fito riga kawai ta saka ko abincin da aka kawo mata ta fito ta samu shirye a babban tray bata iya ta bi ta kai ba ta hau gadon ta dukunkune, zazzabi ne ya saukar mata ciwon kai da jiri kuma suke contributing.

Kusan awa biyu tana cikin wannan yanayi tana ta hawaye, hawayen tunanin saleem bata san itama tana jin wani abu a kanshi ba sai da suka rabu, ko babu komai shine mutum na farko da ya bata dukkan kulawa da lokacin shi, ya nuna mata itama mutum ce kamar kowa, tana kukan maraici da tsananin kewan iyaye saboda shi ne sila tun farko.

Knocking aka yi mata sai aka turo kofar da sallama aka shigo Abeeha ce
"Afeefah"
Ta ?ira sunan tana zagayawa ta kanta, ganin halin da take ciki ya bata tsoro
"Subhallah! Baki da lafiya ne? Sannu bari na faWawa Mammi ta kira Ya Rayyan ya zo ya duba ki"
Bata jira amsar Afeefah ba ta fice da sauri.
?akin Mammi tayi ta shiga da sallama ta samu mammin ta idar da la'asar tana zaune ne kawai tana lazimi a hankali.

"Mammi Ya Rayyan bai dawo ba? Ko za ki kira mana shi?"
"Me ya faru?

15 / 53