HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   10 / 53

27K to 30K   out of 158.4K words

take da sassanyar iskar Ac ya haWu da ni'imtacciyar kamshin shi da ma flavours da yake amfani da su na motan suka ba da wani kamshi na musamman.
A hankali sautin wa?an Alex Warren ta ordinary ke tashi, tsaki ya ja a karo na barkatai a ranshi yake shirin fara masifa don baya ?aunar bata lokaci sai ga wayanshi ya shiga ?ira, Bluetooth na kunnenshi ya Wan danna.

"Allah Saleem zan yi tafiyata ka san na tsani Sata lokaci"
Duk da a hankali yayi maganan alamun muryarshi ya nuna ya hasala kuma tabbas zai iya tafiya Win don saleem ya shiga masa lokacinsa.
"Afuwan mutumina wallahi sai yanzu na tuna inda papers Win nan suke, suna Wakina kuma kyakyawar Soyo na musu babu wanda zai san inda suke ban zaci boss zai tambaya bane da na taho da su, please help me ka je ka dubo min"
Shiru yayi saleem ya marairaice murya
"Please help a soul ba ni da mai min sai kai, ka ji Autan Mammi?"
Da magiya ya ?arasa hakan ya sa Rayyan Wan murmushi
"Don dai kai ne..."
"Eh taimaka pls"
Ko kan salim ya gama maganan ma ya ja motar cikin natsuwa yana sauraran kwatancen da saleem Win ke mishi na inda safe Win da ya Soye confidential files Win yake, Saleem ya bashi wahala don ya fi hour yana neman su a office nashi na nan head quater don mance inda ya ajiye yayi sai daga baya ya tuna da kyar.
Daga waje Ryan ya ajiye motar shi ya sauka ya shiga cikin gidan da ?afa cikin tafiyar shi mai cike da Wumbin ?asaita wane saraki hannayenshi duk zube a aljihu, wa?a still yake ji a Earpods Win kunnen nashi saidai sautin na fita ne da sanyi ba mai hayaniya ba, kamar ko yaushe a murtuke fuskar nan sai kace wanda aka zagi iyayenshi har ya shige, bai nufi ma main parlorn ba ta kofar baya ya zagaya ya haura stairs da zai sada shi da Wakin salim, a jikin kofan ya tsaya ya duba inda suke ajiye key ya Wauka ya buWe ya sanya kanshi ciki don duk sun san inda Wayansu ke barin spare key incase of emergency, dulum Wakin don komai a kashe ya kunna wuta ya wuce uwar daka direct wardrobe da ya mishi kwatance ya je ya buWe, kaya ne a jikin hangers Win ya ware bangon ya bayyana gefe wani keypad ne da ba zaka ce akwai wani abu da zai iya buWuwa ba ko da an danna.

Wasu numbobi ya saka sai ga wardrobe Win ya dare, ya turo wani box waje nan ma ya saka wasu lambobin sai ya budu bai tsaya ma duba me ke ciki ba ya zaro files Win ya buWe don tabbatar da shi ne ko ba shi ba, su Win ne kuwa yana ?o?arin scanning dilim nepa suka Wauke. ?akin ne yayi duhu sossai ba zai iya scanning haka ba sai ya nufi balcony door yana dan tsaki ya buWe ya tsaya daga saman ya fara scanning yana forwarding to salim dake online yana jira har ya gama, yana ?o?arin mayar da wayan aljihu ya Wan Wago sai idanunshi suka faWa kan ta, har ya juya ya Wan dakata ya sake waigo wa ya kalli ?asan ba fuskarta yake kallo ba irin aikin da take yi a sanyin yake gani a ranshi yana raya
'Mutane are heartless'
Ya dai san babu Wiya mace mai gata da zata zauna a wannan uban sanyin tana wanki ga tarin wanke-wanke dake jira a gefe, bai ga dacewar a ce kowa na Waki a Soye ita Win tana ?asan pampo ba, bai gama tunanin ba ta saki atishawa har huWu a jere ta ja hanci tare da Wora goshinta a kan gwiwarta, wani iri yaji sai yaji yana son kallon fuskarta, hakan ne ya hana shi tafiya har ta ci seconds kan ta Wago ya Wan ?urawa face Win idanu.

Kawar da idanun yayi ya mayar hannunta dake wani irin rawar Wari duk kakkarwa suke, sun sandare saboda sanyi ga hijaban da ta lafta rabi a ji?e shakaf. Tunanin inda ya san fuskan yake sai dai ya kasa ya Wan sake kallon gashin idanunta da suka yi fari fat ya ja tsaki tare da barin wurin gabaWaya, mayar da takardun yayi ya fice daga sashen ya nufi harabar gidan don tafiya sabgar gabanshi sai ga Sadiqa ta fito taryar ?awayenta da Shigowar su kenan kowacce na ?o?arin sau?a a motar ta, ganin shi ya sa ta wani zaro idanu shi kam kallo Waya tak yayiwa gefen da suke ya Wauke kanshi ya cigaba da tafiyarshi with steez bai ma san su waye ba bare ya tantance mutane ne ko aljanu.

"Ya Ryan"
Ta ?ira sunan a hankali sanin baya son ihu ko hayaniya, in ka cika ko magana da ?arfi ne sai Ranshi ya Saci kuma muddin nashi ya Saci kaima sai naka ya Saci haka yake, ya Wan Wago ya kalleta a kan rigar sanyi jibgege dake jikinta ya soma sau?e ido kan ya Wan ja tsaki matsalar shi kenan, da wuya ya ga abin da ke cutar da wani ya iya Wauke kai, baya son zalunci sam a rayuwarshi Dukda ana yi mishi kallon miskilin mai murWaWWiyar hali sai dai yana da tsananin tausayi, 'yan aikin gidansu sun shaidi hakan don shi mutum ne dake so ya ga an baiwa Wan Adam ha??insa na mutum cikakke kaman yadda Allah ma ya karrama dan Adam ya kuma ba shi daraja.
Yanzu dubeta killace cikin shigar da ba zai bar iskar bazarar cutar da ita ba amma 'yar aiki zaune ?asan pampo hannayenta da kafafunta duk cikin ruwa cikin halin rashin lafiya don a matsayinshi na likita kallo daya tak yayi mata ya san bata da cikakken lafiya hakan sai ya sake Sata Ranshi amma sam fuskanshi na nan a yadda take bata sauya ba

"Ina kwana? Ashe ka shigo?"
Kai ya gyaWa kawai ya zagaye ta ya wuce abin shi, da kallo ta bishi tana murmushi a fili ta furta
"Miskili ka fi mahaukaci ban haushi"
"Waye shi?"
?aya daga cikin ?awayenta da duk suka bi shi da ido yuuu tayi tambayar.
"Ryan Khamis kike ji da gani, sojan da ko a cikin sojoji ake ji dashi, likitan da ko a cikin likitoci babu kamarsa... Ga sanyi ga zafi, ganin dariyar shi ko murmushinshi sai ka yanki tikiti"
"Wow shi ne Surgeon General Ryan Khamis? Da gaske don Allah? Dama yana zuwa gidanku haka a bati?"
Sadiqa ta saki murmushi
"Abokin yayana ne, yana zuwa sossai ma musamman idan suka samu saukin aiki saleem na gida don ba'a raba su, mahaifiyarshi ma na zuwa har gidan nan, shine dai Ryan Khamis"
No 1 matashi ne da ake ji dashi mata suke rububinshi don duk inda ya shiga akwai masu kyasawa amma fa shi duk basa gabanshi, yana flatforms sai dai babu wanda ya san handle nashi don akwai handles dayawa da sunayenshi na ?arya ana yaudarar 'yan mata, shi dai kam kaman dutse yake mace bayan mahaifiyarshi duk a maza ?an uwanshi ya Wauke su.

Da zancen shi suka shiga parlor nan aka baje ana cigaba da hiranshi kala kala da kyar suka saki suka kama wata.

Shi kam Rayyan yana tada motar shi ya danna ?iran Salim
"Don iskanci ko godiya ba za ka min ba ko?"
"Afuwan Ryan ka san ina gani printing kawai nayi na tafi presenting don ana jirana, yanzu kenan fitowa ta ko wayan ban fitar ba na ji ?iran ka"
Driving yake slowly duk zantukan Salim Win bai tanka ba sai ya daka tsalle ya kama wani zancen da ya kasa bari a ranshi sai yake jin kaman shima Allah zai kamashi da laifin wulakanta dan Adam tunda ya gani bai yi magana ba

"I saw someone familiar kaman na san fuskan but i cant recall"
Salim ya Wan tafi nazari kan ya ce
"A gidan mu kuma?"
Kai Ryan ya gyaWa sai kuma ya tuna voice call ne suke yi a hankali yace
"Yeah, choculate tall young lady haka"
"Afeefah ka gani?"
Salim yayi saurin katse shi, a ranshi ya maimaita sunan 'Afeefah' ba tare da yayi magana ba, Salim ya cigaba da magana

"Ka santa mana Rayyan, yarinyar da ka ceta wacce ta taSa shan poison a Anchau?"
Sai lokacin ya tuna inda ya san fuskar but Meyasa take aikatau gidan su salim? Ina iyayenta da family Winta? Kaman salim ya shiga Ranshi wai aka ce sanin hali ya fi sanin kama bai wuce magana ne a bakinshi ya kasa fitarwa ba don haka ya shiga bashi labarin yadda ya mayar da ita da irin wulakancin da suka sha yadda ta bashi labarinta daga farko har karshe sai da ya gama tsaf Ryan dake parking tsakar gidansu ya ce
"Hmmm"
Ya ?arasa yana dan taSe jajazir Win laSSanshi ba tare da ya ce komai ba bayan nan, har salim ya zaci ya katse kiran sai ya ji Ryan Win ya watsa mishi tambayar
"Then taimakonta kenan ka yi to be lowly house help?"
"No! No!! Wallahi ba hakan bane a raina Rayyan na rasa yadda zan yi ne, mommy ta katange min duk wata ?ofa da zan iya inganta rayuwarta, abin is hurting me badly... Ka kuwa san akwai Allah ya isa a kaina muddin na yi magana da ita na fatar baki na sama da minti Waya?"
?an zare shanyayyun idanunshi Rayyan yayi
"Wow! Why?"

"Saboda kawai sun yarda da champin mutane da ?agen da ake yi mata" nan ya shiga bashi labarin gumurzun da suka sha da mommy a kanta kan ma aka barta a house help Win.
Rayyan ya Wan lumshe idanu ya buWe a ranshi mamakin mutane yake yi, Sai ji salim yayi yana cewa

"Idan bata kashe ku ba ku ai kun Wauki hanyar kasheta!"
Yana kai nan ya yanke wayar don ya gaji da magana, Salle murfin motar yayi ya nufi cikin gidan cikin natsuwa da takunshi na ?asaita haWe da izza.

Kasake salim yayi rike da wayan a hannu yana juyawa, jikinshi ne ke bashi ba haka kawai Rayyan yayi maganar Afeefah ba, ya kuma san a yanzu ko ya sake kiranshi ba lallai ya bi ta kan zancen Afeefah ba kuma bare yayi mishi bayanin me yake nufi da za su kasheta? Hankalinshi ne ya ji yana neman tashi. Allah ya sani daga lokacin da tausayinta ya yi tsanani a ranshi ya juye ya zama mishi so ba tare da ya farga ba, har ranshi sonta yake kuma so yake ya aureta saboda ?aunar da yake mata not out of pity, ko da ya ajiye ta kaman yadda mommy ta umurta yayi iya kokarinshi wurin ganin ya manta da rayuwarta ya bar wa mommy Win sai dai hakan ya gagara mishi dole ta sa ya waiwayeta ya dawo ya kawo mata waya don ya dinga jin lafiyarta da bukatun ta, layinta ya lalubo ya zubawa idanu sama da mintuna uku kan ya danna mata ?ira sai da ya jera sama da 10missed calls bata Waga ba sai hankalinshi ya fi na da tashi ya tura mata text message sama da biyar ba reply.

A lokacin tana ?o?arin tattara kwanukan da ta gama wankewa ta kai bakin kitchen, jikinta babu inda ba ya rawa har hakwaranta na haWuwa, bayan ta ajiye ta koma inda ta tashi ta Wauki wayan da karatun ma yau bata samu ta iya kunnawa ba ta nufi Wakin tana tafiya da kyar, hijaban kawai ta zare ta zubar a wurin ta shige bargo tana hawayen tausayin kanta, jin kaman vibration na wayan nata ya sa ko ido bata buWe ba tayi picking tare da ma?alawa a kunnenta, Sheshekarta ne ya fara shiga mishi kunne yaji wani abu ya sauka mishi har cikin zuciyarshi hakan ya rikita masa lissafin kwakwalwa...

"Afeefah menene? Me ya sameki?"
Shiru sai kuka da itama jin muryarshi ya sa ta ?ara karfin kukan, kaman shi ma zai fashe da kukan cikin sanyi ya shiga cewa
"Don Allah ki yi min magana Afeefah, hankalina tashi yake da kukan nan naki talk to me please, menene?"
Sau?e wayan yayi ya kalli time saura seconds goma
"Help me Afeefah ko ta text ne ki rubuta min Meke damun ki? Kar ki yi kisan kai ki taimaka"
Yana kai nan ya sau?e wayan ya kashe tare da jingina kanshi jikin motarshi, ji yake kaman yayi tsuntsuwa ya ganshi Kaduna sautin Muryar kukanta ke ta amsa kuwwa cikin kanshi...



=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*014*

Shigowar sa?o wayanshi ne ya sa da wani irin hanzari ya mi?e daga jikin motar yana duba wa.

"Ba ni da lafiya"
Abin da kawai ta iya rubutawa kenan, sai ya ji hankalinshi ya fi na baya tashi don bai san wa zai kira ya taimaka mata ba, idan ma ya ?ira su Samha ya san abin ba zai yi kyau ba mommy kuma za ta iya Waga hankali a kan ya aka yi ya san bata da lafiya yana Maiduguri tana Kaduna?

Wani tunani ne ya faWo mishi, nan ya shiga neman Layin wani friend dinshi da yake nan capital hospital Kaduna Win a kan ya taimake shi da Layin Dr. Sulaiman, cikin mintuna biyu sai ga Layin a take ya shiga ?iran Layin ringing uku aka Waga "Dr Cap. Saleem ne don Allah wani taimako ne nake nema daga gareka please in ba damuwa"
Ya faWa bayan sallama da gaisuwa, Nan ya yi ta mishi godiya bayan sun gama disussing, ko gida bai iya ya je ba yana zaune ne kawai cikin motar shi cike da tsumayin sake ganin ?iran Sulaiman.

A chan Kaduna kuwa sallamar da ake ta doka wa ne ya sa sameera Mi?ewa ta nufi ?ofan, Sadiqa suna dining da ?awayenta ana cin abinci ana hira, mommy ke karyawa a tsakiyar parlorn, Samha na wani research a system Winta hakan shine ma ya tilastawa sameera da ke danna waya Mi?ewa tana mitar irin uban Sallamar da ake tayi, tana bude kofan ta yi niyyar masifa ne sai idanunta suka sau?a kan Dr. Sulaiman da ke jingine Wan nesa kaWan da jikin motar shi, daga ganinshi ka san responsible matashi ne da yake kan ganiyar samartakarsa daga yanayi shiga da kuma tsarin motar shi zaka san ko shi ba mai kuWi bane daga gidan kuWin ya fito, Baaba jummai ce dake doka Sallamar ta katse ta "Har na fara tunanin babu mutane ne gidan 'yan nan ashe kuna ciki"
Ta Wan harareta a fakaice "eh muna nan, lafiya kam?"
Ta ?arasa tana sake kallon Dr. Sulaiman da har yanzu hankalinshi ke kan wayanshi.

"Wanchan likitan Afeefah ne mun zo duba ta da jiki"
Ta haWe fuska kan tace
"Ina zuwa"
Ciki ta koma kafin mommy ta tambayi waye ta shiga ce mata
"Mommy wai sun zo duba wanchan Mayyar da yaya salim ya kawo wai likitan ta"
?an shiru mommy tayi tana tunanin Allah ya sa ba salim bane ya aiko su, sai kuma ta tuna ai bai ma san halin da take ciki ba, kila ma ya zuwa yanzu ya mance da ita ko ma bai mance da ita ba ta san ba zai taSa saSawa umarnin ta ba itama kuma hankalinta ya fi kwanciya a yadda yayi uwar watsi da rayuwar yarinyar yake kuma mu'amala da ita da ?annenshi lafiya ?alau.

"Tura Talatuwa ta kai su, su suka sani"
Ta Wan zauna kaWan kan ta mi?e ta nufi Wakin Talatuwa ta tura ta, Baaba jummai har ta gaji da tsayuwa sai ga Talatuwa, suka gaisa kan tace su tafi Wakin Afeefar don yadda ta gantan nan ta tabbatar ba za ta iya fitowa ba, Dr. Sulaiman Baaba ta yiwa magana ya bi bayansu har Wakin da Afeefar take su biyu ya bari suka fara shiga, Baaba jummai na ta sallalamin yadda ta gantan kan ta fito ta kira Sulaiman cikin sauri
"Alhaji ?arami zo ka ga yarinyar nan jiki babu daaWi sam"
Ita kaman uwa take wurinsu don gabanta aka haife shi har ya girma tana gidan su, kuma shine babba a yadda ya Wauke ta kaman uwa haka ?annenshi suka tashi suka gani su ma kuma suka yi following footsteps Win shi a girmama ta, shiga dakin yayi ya isa gabanta ya du?a.

"Afeefah"
Ta amsa da "uhmm" ba tare da ta buWe idanunta ba.
"Menene yake miki ciwo?"
Ta Nuna mishi kanta da kaman zai tsage.
"Akwai amai?"
Ta girgiza kai.
"Jiri fa?"
Ta gyaWa kai.
"Mura fa da tari?"
Nan ma ta gyaWa kai, plate na abincinta na safen da ke rufe a gefe ya buWe ko spoon Waya bata yi ba.
Ledojin da ya shigo dasu a hannunshi ya shiga buWewa babu bukatar zuwa asibiti drip ya haWa ya Waura mata ya haWa allurai yayi wasu a jikin canular wasu kuma jikin ruwan, ya dubi Talatuwa
"Kin san magungunan da suka shafi na mura da zazzabi da sa bacci, bare ma jininta ya yi ?asa sossai tana Wan bu?atar hutu na kwana biyu ba tare da ta yi hulda da ruwa ko abu mai sanyi ba"

"Toh fa, ranka ya daWe ni ma 'yar aiki ce kamar ta ba ni da ikon bata hutu da dai Hajiya da kanta ka yi wa bayanin da sai ya fi"
Ita dai Baaba jummai ta zabga tagumi tana kallon Afeefah dake bacci ji take kaman ta yi mata kuka ashe itama aikatau take yi gidan su Saleem Win? Muryar Sulaiman ne ya katse ta yana cewa Talatuwa
"ko za ki kai ni wurin hajiyar?"

Duk da basu yi haka da Saleem ba amma ba zai iya kau da ido a kan yarinyar ba she's too young and fragile kaman she's having a lot a cikin zuciyarta.
Fitowa suka yi Baaba dai kaman ta tsaya haka take ji Don Allah ya saka mata ?auna da tausayin Afeefah kaman jikar ta.
Talatuwa ta du?a gaban mommy bayan ta bar su a waje "Hajiya da ma wai likitan ne yake son gani ki".
Kan mommy ta yi magana ma sameera tayi saurin cewa
"Ki ce ya shigo, mommy bari na ba ki mayafi"
Samha ta Wago ta kalleta, mommyn bata ce komai ba har sameerah ta kawo mata mayafin daidai Sulaiman ya yi sallama ya shigo.

Kamshinshi ne ya cika parlorn duk yadda mommy ta so ta kame nagartarshi

10 / 53