HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   38 / 53

111K to 114K   out of 158.4K words

da ya sha Winki irin na sarauta, ya saka hular da ta dace da kayan ya zura takalmi ya fito hannshi ri?e da waya amma sai ya tattaresu ya goya a baya ya fice daga sashen dogaran na ganinshi suka rufu za su bi shi ya juyo ya kalli shugabansu.

"Sunanka?"
"GaabWo ranka ya dade" (Joy yake nufi)
"sauran su zauna kai ka biyo ni"
Yana kai nan ya juya da sauri GaabWo ya bishi har turakar mai martaba duk inda ya ratsa hadimai za su zube suna kwasar gaisuwa kai kawai yake Waga musu, sai da aka sanar da isowarshi kan ya shiga, ya ci sa'a mai martabar ma na son ganinshi da kallo yake ta Binshi har ya zauna a ?asa kaman yadda me martaba ke zaune cikin shimfida na alfarma ya kishingida da tun tun.
"Abeey barka da wannan lokaci"

"Barka dai Ciroma, na san ka ji hukunci na kuma kana tunanin bai maka daaWi ba amma abin da zan iya cewa kenan Sameer ba zan bari ko kusa ka sake subuce min ba, Kukan BO?EJO da ma sautin kalangun gado sun isa su tabbatar maka da cewa kai ne mai jiran gado"
Numfashi ya Wan sau?e yace a hankali
"Abeey ka yi ha?uri da abin da zan faWa ba zan saSa umarninka bane amma zuri'ar da na ajiye a chan sun fi karfin na sanar da su cewa na dawo nan a waya, Wiyar su ta zame min uwa da uban da na rasa a rayuwata tsawon shekaru ashirin da shidda bata taSa gajiyawa da hidimata ba, bata taSa min kallon banza ko Harara da sunan tsana ko kyara ba, ta gatanta ni ta fifitani fiye da komai da ta mallaka a duniya ciki har da miji da 'ya'yan cikinta, Abeey duk yadda zan fasalta maka irin son da Mammi tayi min Sata baki ne duk kuma ta yi bata san ni waye ba har sai da take kwance a gadon mutuwarta a haka ro?ona tayi da in dawo in samu farin cikin da na rasa, in dawo in ji uzurin...." Sai bai ce komai ba ya du?ar da kai.
Hadiye abin da ya taso mishi yayi kan ya cigaba
"Ban shirya dawowan ba na riski labarin Satan Aisha bayan ma ?iran da shugabanmu yayi min na ina cikin team da aka yi assigning wannan aiki na taho ne ba da shirin dawowa b.."

"Muhammad Sameer"
LaamiWo ya kirashi runtse ido yayi don ya san bai amince bane.
"Ka ba ni labarin abinda ya faru daga barinku gidan nan da mahaifiyarka, na dai san ta nemi izinin tafiya chan mambila wurin dangin mahaifiyarta kuma na bata izini da driver da kuma amintacciyar Kuyangarta sai labari marar daaWi aka dawo min dashi da sunan ka Sace a tsaunukan mambila an neme ka an rasa na kwashe tsawon shekaru ban bar kowani hukuma sun huta ba da neman ka har wasu suka zartar da cewa ka mutu ni ban yarda ba hakan ya sa a kullum nake Adu'a duk juma'a nake sadaka duk goman karshe na kan manta kaina ina rokar maka kariya da nasara a duk inda kake da Fatan Allah ya bayyana min kai ya tsare maka imaninka me ya faru? Meyasa daga kalamanka na yarda Ammienka na da hannu dumu dumu akan abin da ya faru?"

Kanshi na a ?asa ya shiga magana kana jin Waci a saman harshenshi a kuma hankali yake maganan
"Abeey bayan mun yi muku sallama mun bar nan tafiya ne mai nisan gaske muka dauka ba tare da na san inda muka nufa ba, na taSa zuwa mambila sau Waya don haka inda muka nufa bai min kama da hanyar ba, idan nayi bacci na gaji na farka na tambayi Ammie har yanzu bamu isa ba sai ta mayar da ni jikinta ta rungume tace har yanzu da saura ban sa????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ni ba ashe nesanta ni take da asalina, nesanta ni take da inda na fi wayo da kuma farin cikina duk ku biyu, yamma ne sossai muka isa inda ban sani ba hatta yaren su kaWan kaWan nake ji shima saboda akwai wasu kuyangai dake yi anan ina sha'awar iya yaruka na saka su a gaba ina koyo, ko da ta saka driver tsayawa kuka take yi ta bani ?ullin kayan marmari da abinci waenda basa lalacewa da wuri cikin guzurinmu tace in ri?e, muka sauka muka bar driver da Kuyangarta Kande a mota mun yi tafiya sossai har muka kawo gefen wani juji da babu hada hadar mutane sossai ta kalleni.

"Ka yi ha?uri Wana ina sonka amma dole ta sa zan rabu da kai babu yadda na iya!"
A karye na ce mata
"Ammie Meyasa tunda muka fito kike kuka? Meyasa za mu rabu? Me muke yi anan?"
Ta ja numfashi tana share hawayen dake kara gangara tace mini
"Nan shine inda na ji ya kwanta min ka cigaba da rayuwa, ka yi aiki kaman na jaruman maza ka nema da kanka ka samu har ka tsaya da kafafunka, idan da rabon mu gana watarana za mu gana amma a yanzu ka cire cewa kai Wan sarki ne jikan sarki, ka jingine ka taSa sanina ko mahaifinka, ka manta ka taSa ko da amsa suna Ciroma Sameer ka samu sabuwar rayuwa zan maka sdu'a ba zan gaji ba amma daga yau ka gama zaman masarauta..."
Hankalina ya tashi da kalaman ta na rikice ina tambayarta
"Meyasa Ammie? Me yasa zan manta ku? Meyasa zan manta Abeey?"
"Saboda Dole ne Sameer!"
Ta daka min tsawar da bata taba min irinshi ba Dukda na razana kuma kuka ba ya daga cikin al'amarina ban san na fashe da kuka ba na ri?o hannayenta ina ro?onta kar ta bar ni anan ban san kowa ba, kar ta bar ni anan ba zan iya rayuwa ba Ammie ta zame hannunta ta tureni har na faWi na rarrafa ba tare da na damu ba na rike kafarta ina kuka sossai da ro?onta ta tafi da ni amma ce min tayi

"Ko a mafarki ka biyo baya na ba zan taSa yafe maka ba Sameer!"
Baya baya nayi na zube a ?asa a zaune ina kallonta har ta Sace min, na ji na tsani duniyar na ji na tsani kowa da komai kuma a lokacin zuciyata ta kafe Abeey na ji ba zan iya sake yi mata kuka ba tunda bata so na ta tsaneni, babu abin da yafi kona min rai irin bolar dake gangana nan uwata tace min in ci gaba da rayuwa, nan fa ta zaSa min. A inda ta barni anan na zauna har dare ban motsa ba dare da naga karnuka na zuwa wurin cin abinci na bar musu duk abinda ta bani don ba zan iya amfani dasu ba na koma wani gini da ba'a ?arasa ba na zauna daga ranar na rasa bacci na Abeeyy daga na rufe idanu kalaman ta su ke farautar numfashina....A ranar Ammie ba rabuwa da ni kawai tayi ba ta kashe ruhi da zuciyata kisa mafi muni na yi kwana biyu ban iya cin komai ba sai ruwa kan wani almajiri ya ja ni muka fara sana'ar wanke gilasan mota Dukda ban taSa mishi magana ba amma shi yana min surutu sossai, kayan aikin nashi ne idan ya gaji zai bani in yi ko kwanaki goma ba'a yi ba garin wanke gilasai mota ta kaWe shi ya rasu, kayan aikin nashi na cigaba da amfani da su har Allah ya haWa ni da Mammi.."

Nan ya cigaba da bashi labarin komai da komai mai martaba banda hawaye babu abinda yake, a lokacin da ya zo rasuwar Mammi sai da hawaye ya ziraro mishi ya sa hannu ya Wauke jijiyoyin kanshi duk sun tashi raWa raWa idanunshi sun yi ja sossai da sossai.

Shiruuu ne ya ratsa parlorn fiye da mintuna biyar Abeey a hankali ya ce
"Mahaifiyarka ta cuce ni ta ci amanata Sameer! Ban san me zan yi na huce wannan zafi da raWaWin da nake ji ba... Bata da uzurin bani na wannan laifi da ta aikata. Hakika na so Mammin ka tana raye in ganta ido da ido in yi mata tarin godiya marar adadi akan kaunar da ta nuna maka sai dai kash! Allah bai taSa barin wani don wani yaji daaWi ba idan ajali ya zo babu mai ?ara ko da second guda ne sai an tafi, a yanzu ma bata Saci ba za mu tabbatar mun yi tarin abubuwan alkhairi masu yawa da sunanta don ladar ya je mata a makwancinta. Allah ya musu rahama ita da mai gidanta ya sada su da annabin rahama"
Ya amsa da ameen
"?auki ipad Win chan ka kira min Mahaifinta video call za mu yi magana"

Ipad Win ya dauka ya saka numbern uncle Musa ya kira aka taki sa'a yana online ya Waga zaune yake da Uncle sanusi da Uncle Mansur suna tattaunawa ganin fuskar Rayyan ya sa suka yalwatu da fara'a ya shiga gaishe su yadda ya saba suka amsa kan ya mayar da fuskar kan fuskar Abeey ba tare da ya ce komai ba.

"Assalamu Alaikum warahmatullah..."
Amsawa suka yi suna ta kallonshi kan Uncle Mansur ya zare idanu
"LaamiWon Fombina mai girma Muhammadu Modibbo Aliyu.."
Duk sai lokacin suka Wago suka shiga gaishe shi da girmamawa don shima ba ?arami bane idan bai girmi uncle Musa ba za su yi sa'anni. Sannan ko babu girman shekaru akwai na mulki da sarauta mai girma.
"Na yi muku laifi ina Fatan za ku yi ha?uri ku yafe min kuma ku dubi uzurina, kaman yadda kuka sani sunana Muhammadu Modibbo LaamiWon daular kudu maso arewacin Kasar nan, a cikin tarihina ina da Wa namiji tilo da ya Sace da kananun shekaru inda an yi neman duniya an rasa shi sai satuttuka da suka wuce Allah ya bayyana min shi. Wannan yaro ba kowa bane face Wan ?ar wurin ku mai rasuwa wato Rayyan a chan anan kuma Muhammadu Sameer"

"Allahu Akbar kabiran! Allah mai girma! Allah mai yadda ya so iko sai Allah ashe dama Rayyan Wanka ne? Kai Alhamdulillah wannan abu na farin ciki ne Alhamdulillah ina ma Mamanshi na raye ta ga wannan rana..."
Uncle Musa ke fada cikin tsananin farin ciki suka shiga taya su murnar saduwa da juna. Bayan gama barka da jaje Mai martaba ya Wora

"Laifin da na muku shine na sanar da ku a waya, shi Ciroman ya so ya je ne don martabarku ya shallake haka a gareshi amma ban ba da goyon bayan hakan a yanzu ba, zai iya zuwa ziyara ko wasu kananun al'amura da bai kamallah ba amma sai ya gama blending da dangi ina fata hakan bai Sata muku ba, in shaa Allah zan yi tattaki na zo da kaina na kawo ku kuga inda yake"

Uncle Musa ya ji daaWin martaba da ?imar da aka basu yace
"Ba sai ka zo ba ranka ya dade da kanmu za mu zo har nan mu taya ku murna in shaa Allahu"
"Sai abu na ?arshe ban san ko za'a yi min wannan alfarma ma"

"Alfarmar ka ya wuce ka ro?a mai martaba sai dai umurni"
Uncle sanusi ya faWa don basu taba zaton sarkin haka yake da saukin kai da iya mu'amala ba Dukda tarin dukiya da irin rigar mulkin da yake ciki hakan bai hana shi yi musu magana cikin girmamawa da fahimta ba.

"Idan za ku taho Win ba matarshi kawai za ku taho da ita ba, za ku taho min da 'ya'yana Jannah Da Abeeha ita jannah za ta koma ne kawai saboda auren dake kanta Abeeha kuwa ta zama tawa aure ne zai fitar da ita daga wannan gida bi'izinillahi"
Sun gamsu suka yi godiya don martabarsu ne Dukda suna da dukiyar da zasu iya rike Abeeha amma Mammi Rayyan ta barwa shi kuma duk inda Rayyan yake dole ta zauna dashi...

Bayan sun ajiye kan sadarwan Mai martaba LaamiWo ya dubi Ciroma
"Alhamdulillah! Yanzu ka je kayi shirin juma'a idan an sau?o akwai media team da suke son ganawa da rundunarku da kuka ceto su Aissatou to amma su sun tafi bayan na sallamesu don komawa ga iyalan su bayan sun bar nan shugabanku ya kira ni akan ba za su iya zama har Washegari ba dole na wakilta Galadima ya je ya min godiya ya kuma sallamesu kai za ka gabatar da shirin madadin ku gabaWaya"
Bai so ba amma ya ya iya dole ya amsa ya yi godiya ya mi?e ya fice.

Yau suka yi finals jiya garin gigin baccinta an dauke musu wuta kuma ba'a yi rana ba don ruwa suka samu basu samu chargy a solar ba kan a kunna gen ta tafi fitsari ta jefar da wayanta a ruwa, ta ji haushi saboda bata da wayan kallonshi tunda ba ya kira yanzu, sossai take jin kewanshi kaman sun wani saba sukuku ta shigo parlorn abin da ya kamata tana murnar kamallah secondary da aka yi da kyar amma damuwar da zuciyarta ke ciki ya hana ta.

A babban parlor ta samu Abeeha na kai da komo wa tamkar ruwan cikin kwano ta kasa zaune ta kasa tsaye ganin Afeefah yasa ta daka tsalle ta ri?o hannayenta
"Afeefah mun warke... Innalillahi wainna ilaihi rajiun khaihhh farin ciki zai kashe ni...! Afeefah Albishirrinki.."
Cike da zumuWi take maganan har jikinta na rawa
"Goro.."
Ta faWa cike da mamakin me ya saka Abeehar farin ciki haka
"Afeefah kin zama Gimbiya matar yarima ko in ce Sarauniyar gobe matar Saraki... Ashe Saraki da Mammi ke kiran Ya Rayyan ba'a banza ba? Afeefah mijinki ashe Wan babban sarki ne mai tarin daraja da tushe me kyakyawar asali? Ashe ya Rayyan jinin sarauta ne ke yawo cikin jikinshi? Kaii amma Allah ya isa wa mahaifin yarinyar nan da ya kalleshi yace kila ba tsatso mai kyau aka samo shi ba ya ci mutuncin sarauta.."
Afeefah dai ta kafe a tsaye tana ta kallon Abeeha na zuba chan tace
"Anya Adda Abeeha lafiyarka kuwa? Wani irin magana kike tayi ba kan gado...? Wani yaya Sarakin?"






*Wayyo Hannun mar'atussaliha=?)?



=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*47*

"Yaya Rayyan mijinki nake magana a kai girlll wlh da gaske nake miki yanzun nan Baba Musa ya ?ira ni yake cewa za mu shirya tafiya Fombina gobe sun sayi tickets already, ya ce mu shirya kaya kuma mu kintsa komai don za mu iya Wan jimawa bamu zo kd ba."

Bata san me ta ji ba a lokacin mamaki ko tsananin farin ciki, tayi matukar taya shi murnar reconsiling da iyayenshi don dole su Win su ne dolenshi ko ba jima ko ba dade, ashe yana da ala?a da sarauta? Fuskarta cike da murmushi tace
"Alhamdulillah Allah mun gode maka"
Wani sashe na zuciyarta kuma tsoron tafiyar take don bata san me kuma zata tarar ba, hakika ta fi jin natsuwa da kwanciyar hankali a gidan na Mammi, sai ta fara tunanin idan basu karSeta ba fa? Dama gashi ba sonta yake ba kila suna ce mishi ya rabu da ita zai rabu da ita a yadda ta san tsarin gidan sarauta.

Abeeha ta wuce ta shige sashensu zuwa Wakinta ta samu bakin gado ta zauna
"Allah mai girma annabi mai dumbin daraja! Yanzu ni ce Afeefah ke da matsayin matar Wan sarki mai daraja a wannan ?asar? Anya? This is too good to be true... Hankali ba zai kama ba ni Afeefah dai ta Dutsen-wai annoba Mayya ajalin duk wanda ya raSe ki!"
Bata san adadin lokutan da ta dauka zaune a wurin ba har lokacin sanye da uniform don ba sallah take ba bare tayi tunanin azahar da aka idar a wasu masallatan, tana nan zaune sai ga Abeeha ta shigo da sauri bayanta jannah tana cewa

"Zo ki ga wani abu Khaihh Ya Rayyan duniya ne! Sarakin Maammi ne a gasken gaske an tashi kaina!"

****

Yana fita daga sashen LaamiWo Saleem ya ?ira yana tafiya a hankali suna magana sun jima sossai suna wayan Saleem ya san komai a kanshi ya kuma taya shi murna kwarai shima kuma yana cikin masu tahowa gobe Win, idanun Rayyan ne suka sau?a akan Fulani Adama dake tahowa hanyar sashen mai martaban, bai wuce ba sai ya tsaya yana cigaba da wayan idanunshi na a kanta yadda take tafiya cike da izza da takama bayi da kuyangi na zube mata ko kallo basu isheta ba Wauke ido yayi ya cewa Saleem

"Zan saka maka wani abu ka sallami duk ma'aikatan gidan ka kuma ba su ha?uri na barin aikin ba tare da an sanar da su da wuri ba, za'a basu abin da zai ishe su jarin wata sana'ar in shaa Allah. Please a rufe komai yadda ya kamata don zan dawo ba na zo kenan ba!"

Kalamanshi na karshen karab a kunnenta, idanu ta zuba masa Dukda kaWuwar da tayi na namijin da ta gani a gabanta ta wani sashen ta Wan ji sanyin kalaman nashi har hakan bai Suya a kan fuskarta ba sai da tayi murmushi ya sake kawar da idanu a kanta yace

"Na gode Saleem za mu yi magana please ka sanarws Sulaiman kafin na ?ira shi, Sai na ganku a gobe Win..."
Yana sau?e wayan ya kalleta
"Barka da wannan lokaci Mama..!"
Ya faWa da Wan murmushi mai dauke da dumbin ma'anoni.

"Ashe rai kan ga rai Sameer? Ko da shi ke na zaci ka manta da mu gabaWaya ai shiyasa ban ga ka kawo gaisuwa ba..."
Har lokacin yana dan murmushi yace
"Wani abin ake mantawa amma wani ya fi ?arfin mantuwa Mama, zan zo in shaa Allahu ban gama warware gajiyar aiki bane. Na bar ki lafiya"
Yana kai nan ya wuce ta GaabWo ya bishi da sauri.

Da kallo ta bi bayanshi sama da mintuna biyu kan ta juya ta nufi sashen na mai martaba.

****

Saleem na sauke waya ya kalli Mommy dake zaune cikin kujera a sabon gidansu da suka dawo komai na ciki sabo ne kuma a tsare gwanin kyau da Waukar ido yace

"Mommy kin ji ikon Allah ko?"
Duk su Sameera idanu suka mayar kanshi mommy tace
"Me ya faru?"
"Mommy ashe Rayyan jinin sarauta ne, mahaifinshi shine LaamiWon Fombina."
"Da gaske kake ko wasa?"
Cike da dumbin mamaki mommyn ta jefa mishi tambayar
"Wallahi da gaske mommy yanzu haka yana masarautar su

38 / 53