HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   3 / 53

6K to 9K   out of 158.4K words

sani da jimawa, a hankali sanyi ya shiga ratsa ta. Sanyin farincikin sanya mace guda da ta rage mai ?aunarta kaf faWin duniya a idanunta, tashi ta yi cikin azama da 'yar fara'a ta rungume ta.
"Afeefah....!"
Kiran sunanta da ta yi tare da fincikar da tayi mata daga rungumar tana ?arewa fuskarta da ma jikinta kallo ne ta ji tamkar ta sosa mata inda ke yi mata ?ai?ayi. Dama me neman kuka ne aka jefe shi da kashin shanu. "Wa ya yi miki wannan lahanin?" Ita dai ba baki sai kunne don haka ta ci gaba da kukanta yayin da ta shiga rarrashinta itama hawayen take zubarwa. Da ?yar Afeefah ta yi shiru kan matar ta buWe jakar hannunta ta fiddo biredin da ta yo mata tsaraba. Kamar mayunwaciyar zakanya haka ta afka masa da ci ba ji ba gani har tana ?warewa, matar ta Wibo ruwa ta ba ta hawaye na gangaro mata, daidai lokacin da kawu ya fito shirye da alama kasuwa za shi..


"Labaran ka ji tsoron Allah, wallahi ka kwana da sanin kai ma ba ka fi ?arfin ?addara ba. Rayuwa da kake yi da 'ya'yanka ?ar?ashin kulawarka ba wayonka ba ne ballantana dabararka, a yau za ka iya faWuwa ka mutu, shin za ka so a yi wa 'ya'yanka yadda kake mata?"

Kanwar mahaifiyarta ta jefa masa kalaman cikin jin haushin yanayin da ta zo ta iske Afeefar Kallon banza ya watsa mata.
"Kina da gida ko Zainabu? Toh ki tarkata ta ku tafi tun kan mu yi Sacin Sacina kuma ki daina haWa yarana da wannan annobar... Ni ban haifi maye ko Waya ba, ban kuma shirya mutuwa ba. Zaman ma da kika ga tana yi saboda ba ni da yadda zan yi ne, amma yanzu tun da ga ki Allah ya raka taki gona...!"
Har ya nufi fita ya dawo ya sake kallon ta.
"Af! Idan ?arshen saduwar kenan to ubangiji ya sa can ta fi miki nan."
Mi?ewa tsaye ta yi a zuciye.

"Zan tafi da ita Labaran, dama rashin sani ne ya sa kaza ta kwana da yunwa a saman dami, idan ka ga na mutu lokacina ne ya yi. Ke tashi mu tafi."
Ta watso ma Afeefahn sauran kalaman nata tana kallonta, tun farkon rasuwar mahaifiyarta Aunty zainabu da ita kaWai ce ?anwar mahaifiyarta ta so karSar ta sai dai kakarta ta ?i har ma ya kai ga sun yi rigimar da ta sa tayi matukar fushi, sau Waya ta taSa zuwa ta duba ta a gidan kakartata sai lokacin da take wurin innarta ma ta zo ta duba ta, haka ma tana gidan kawu ta zo sau biyu sai dai bata taSa wuce awa Waya ba tana ganinta ta kawo mata tsaraba ta tafi don wani kauye gaba da su sossai take.

Duk da chan ta san Afeefahn na cikin damuwa sai dai bata san ya kai har haka ba, ganinta a yanayin da ta sameta ya matukar Waga mata hankali.
"Afeefah da ke nake yi!"
idanunta da kaman za su faWo ta saisaita ta mi?e da sauri ta shige akurkin Wakin nata. Wani tunani da ya Warsar mata ne ya sa ta nemi gefen kayanta ta tsuguna, hawaye ne ya cika idanunta Aunty Zee ce ta shigo tana ?arewa Wakin kallo cike da tausayawa ta du?a gangarta tare da dafa kafaWarta
Kaman ta karanci yanayin da take ciki da tunanin da zuciyarta ke yi.

"Sau tari ?addarorin da ke zagaye da mu su ke taimaka mana wurin tabbatar da imaninmu ko akasin hakan, ina so ki zama tuwon hatsi mai yawan juriya, dukkan tsanani yana tare da sau?i. Mu tafi."
Taya ta tayi suka haWa yar Ghana most go Winta da babu wasu kayan kirki suka fice, bata damu da ko sallaman su Baba Larai ba su ma kuma dariyar Allah ya tura ?eya suka bi su da shi don yanzu Afeefahn bata da anfani a rayuwarsu.

Tasha suka tafi suka hau mota, ita dai jikinta ya matu?ar sanyaya damuwar da ke ranta ko kusa bai ragu ba saboda tsoron kar wani abu ya sami Auntyn nata da take ji da, ya haWu da bata taSa shiga mota ba a rayuwarta don bata taSa barin garin nasu ba wannan ne karo na farko, bata san akwai titi kwantacce irin hakan ba sai da suka Wauki titin cikin garin Anchau daga kauyensu chan cikin Dutsen-wai na Kaduna state, tun tana kalle-kalle har bacci ya sure ta, sai ji tayi Aunty zainabu na tashinta tana bude ido ta ga har sun iso inda za su sau?a ba ma su isa tasha ba don Auntyn gidan ta na daga wajen garin Anchau duk under kubau LGA of Kaduna state ne, sau?a suka yi ta Wauki kayanta a kai suka gangara layin har zuwa gidan, layi ne na masu matsakaitan ?arfi da rufin asiri gidan Auntyn ba wani babba bane sai dai ciki biyu ne da parlor sai tsakar gida da take da tarin shuke-shuke.

A madaidaicin parlorn ta yi mata masauki ta buWe karamin frigde Winta ta fiddo mata ruwa
"Sha ruwa bari na samu na Wora mana wani abu ko? Sannu. Ki sake jikinki a nan babu mai takura miki in shaa Allahu kin ji?"
Kai ta gyaWa tana ya?e dai, bayan ta sha ruwan ta fita zuwa kicin na tsakar gida don kamawa Auntyn nata aikin da take yi Dukda ta ?i tace ta je huta amma sai da ta saka mata hannun suka shiga yi tare tare har suka gama, shinkafa fara da Miyar jajjage da tayi ta saka mata a filet
"Wauka ki koma ?asan mangoron chan ki shimfida taburma sai ki ci"
Yadda ta ce haka tayi Auntyn ta kawo mata ruwa again tuni ta yi nisa a cin abincin.

Aunty zainabu dai na ta kokarin haWa na mijinta don ta san yana gab da shigowa shima cin abincin ranan, dama daga ita sai shi ne gidan Dukda ta fi shekaru goma da aure sai dai har yanzu bata haihu ba, ya sake aure bayan ita amma ba gida daya suke da matar ba itama dai har yanzu babu wani labari na haihuwa kam suna kuma zaman lafiya sossai.

Tana ?o?arin kai loma yana sallama, ta amsa ya Wan yi turus yana kallonta gabanta ne ya Wan faWi don ganin fuskanshi ya Wan sauya ko da ta gaishe shi da kalma Waya ya amsa kan ya nufi ciki yana kiran zainabu...



=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Ba lallai ku ji ni anjima chan ba saboda wani uzuri na so pls bear with me ku ri?e wannan as na chan anjima Win tunda Its already friday.*

*004*

A wurin ta cigaba da zama jiki a saSule har dai Aunty zainabu ta fito tana kallon fuskanta da har ya Wuri ruwa saboda ?una daga gefe zuwa ?asan idanunta, Allah ya ta?aita ma bai taSa idanun ba ta ce
"Har kin gama ci Afeefah?"

"Eh Aunty na gama"
Ta faWa a hankali don yanayin Auntyn bai mata yadda suka dawo ba idanunta kaman ta yi kuka.
"Bari na ba uncle Winki abincinshi sai na zo mu tafi gidan mai mazari ya duba miki wannan ?unar kar ya zama miki damuwa"
Daga haka ta yi kitchen, Afeefah ta mi?e ta shiga parlor zuwa Wakin da ta ajiye mata kayanta daidai ta sauya hijabi zata fito ta ji mijin Auntyn nata murya a sama yana magana
"Babu inda za ki da ita zainabu idan ba mayar da ita inda kika Wauko ta za kiyi ba"
Itama Auntyn a sama ta amsa shi
"sai dai kuma idan za mu bar maka gidan tare da ita Usman"
"Zainabu...!"
Da mamaki ya ?ira sunan don a zamansu ba zai ce ga sadda ta Waga mishi murya ba sai yau. Kuka ta fara
"Haba Usman na fa faWa maka maganan nan a wurina bashi da matsuguni, Afeefah Wiyar yayata ce daidai take da tawa wacce zan iya haifa a cikina tana cikin matsi da takurar rayuwa ina tsoron nima Allah ya kama ni a kan banzatar da rayuwarta don Allah ka kalleta da kyau ka ga depression na neman kasheta tun a kananun shekaru..."

Ya katse ta
"Zainabu ba wai 'yar uwarki na tsana ba ina tsoro ne, ina tsoron abin da zai je ya zo daga nan Anchau har Dutsen-wai babu wanda bai san da labarin yarinyar nan ba, ko kwanan nan ta ci kurwar wani matashi a kasuwa kowa tsoron hulda da ita ya ke sai ni zaki Wauko ta ki kawo min cikin gida?"

Tana kuka sossai tace
"Wallahi duk babu gaskiya a lamarin mutane Allah ba zan taSa yarda Afeefah zata yi maita ba, babu mai mutuwa sai wadda kwanakin shi suka ?are idan ko don ka zauna da mutum kwana ya ?are ka zama maye ne da dukkan mu nan Mayu ne don idan baka rasa iyaye ba ma ka rasa makusanta. Idan dai har Afeefah zata bar gidan nan zan bita mu tafi tare ba zan iya sake mayar da ita gidan labaran ba wallahi"

Numfashi mai karfi ya sau?e
"shikenan zainabu ai sai ta zauna, amma duk abin da ya je ya zo babu ruwana"
"Babu ma abin da zai faru sai alkhairi"

A lokacin Afeefah ta sulale ta ma?ale jikin gini kamar kadangaruwa ta chusa kanta cikin kafafunta, bata ga laifin mijin Aunty zainabu ba rayuwarsu yake karewa da ya wajaba a kanshi amma Meyasa ita ta zama Mayya? Taya aka yi ta zama Mayya? Amsar da ta kasa ba kanta kenan har yau bata ma san Shigowar Aunty zainabu ba sai dafa ta da tayi ta ji, ta Wago kai
"Aunty don Allah ki yi ha?uri ki mayar da ni gidan kawu zan cigaba da juriya ni karan kaina hankalina ba'a kwance yake ba, tsoro nake ji ina tsananin tsoron kar wani abu ya same ki ta dalilina ba zan iya yafe wa kaina ba..."
Kuka ne ya ci karfinta Auntyn ta share mata hawaye

"bawa baya taSa wuce ?addarar shi Afeefah babu wanda ke da ran wani a hannunshi face ubangiji don Allah ki kwantar da hankalinki kin ji? Ba zan taSa iya sake barinki ki zauna wurin 'yan uwan mahaifinki ba muddin ina numfashi. Tashi mu je"
Tashi tayi suka fice daga gidan suka je aka saka mata maganin ?una a wurin kan suka dawo.

Washegari suka sake fita dayake Aunty zainabu yar kasuwa ce tana saya da sayarwa sossai babu wanda bai santa ba a unguwar da ma unguwannin da suke ma?otaka tana saya kuma ta sayar, hatta kayan jikinta in zaki ce kina so ta kan iya cirewa ta sayar miki haka take bata zauna ba, shiyasa take da rufin asirinta a karan kanta makaranta suka je aka yi wa Afeefah interview da kyar aka barta a js2 duk da shekarunta sun wuce ajin, private ce da bai wuci dubu shidda ba termly don haka Aunty ta karbi sample na uniform suka tafi kasuwa ta yanka mata yadi aka ba tela akan zai Winka kan su gama sayayya, sayayya sossai ta yi mata da saida tayi ta zub da hawaye tana da sauran gata ashe bata sani ba soyayyar Aunty zainabu ya shige ta tamkar yadda zata so mahaifiyarta.

Da kaya sossai suka dawo niki niki, a Wakin Aunty zainabu inda Afeefahn take suka ya da zango nan ta sake shirya mata kayanta dama ta cire nata masu Wan dama suka tafi da su kasuwa aka rarrage mata yadda zai ?arbe ta duk na gidan kawu zubarwa tayi.

Rayuwa ne mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali ta shiga gudanarwa gidan Aunty zee da uncle usman, tun yana tsoro har ya sake barin ma da ya ga Afeefar yarinya ce mai kwazo, natsuwa da hankali ga ibada da son karatu boko da arabi komai na gidan yanzu ita ke yi don babu wani yawa bata bari Auntyn nata tayi komai muddin tana nan, haka a makaranta malamai sai yabawa kwazonta suke don tana da ilimi kuma akwai saka kai, suna ganin ma a karshen shekara za'a iya bari tayi Junior waec ta tafi ss1 in dai aka tafi a yadda take a yanzu, haka islamiyya tana kokari sossai kusan kowa ya san ta a unguwar saboda yadda Aunty zee Win ke nuna ta matsayin Wiyarta.

Sauri sauri ta gama shiri don ta so makara ta fito goye da school bag Winta, fuskanta ya fito fess a cikin sky blue hijabin makarantar kyaunta ya sake bayyana na ainihin Black beauty, skin Winta har wani sheki yake na samun natsuwa, fararen idanunta take warawa ta inda za ta hango Aunty zee sai dai bata ganta ba, a parlorn ta tsaya ko zata fito daga Wakin uncle usman ta samu ta mata sallama sai shi ta ga ya fito ta Wan duka ta gaishe shi ya amsa cikin natsuwa

"Dama uncle ina son yin sallama da Auntina ne ko ta koma bacci?"
"Eh ai tun da ta fito ta ga kin kamalla komai tana komawa ta sake bingirewa da bacci"
Afeefah tayi murmushi
"Toh shikenan na wuce makaranta"
"karSi"
Ta matsa ta karSi Wari biyu da yake mi?a mata
"Sai kin dawo a mayar da hankali"
Ta amsa tana ficewa da murmushi fal fuskarta kaman ba Afeefar da ba da take yawo da tsananin damuwa da hawaye a ko da yaushe.

Ko a makaranta natsuwarta bai kau ba, sam ba zaka ganta tana wasa ba koyaushe littafi na hannunta tana dubawa har ta fara presenting abubuwa a assembly da participating a wasu programs na makarantar, bata da ?awa har yanzu don duk ajinsu ba sa'annin ta shirin exams ake don haka yau revision ?arfe sha biyu suka tashi ta nufo gida cikin natsuwa.

Sai dai ta samu babu kowa, ta karSi key a ma?ota ta shiga sai da ta zare uniform Winta ta sauya da wasu kananun kaya wando ne da dogon riga da ya zo mata har gwiwa kan ta Waura dankwalin ta fita zuwa kicin, abinci ta Wora musu tana mamakin inda Aunty zee ta tafi don bata ce mata za ta fita yau ba kuma kila wani abu ne dai ya taso a chan cikin dangi, ita dai ta san suna da dangin nesa nesa ta Sangaren mahaifiyarta amma su ma ba wani karbarta suka yi ba ko daukar ta da muhimmanci Dukda ita kanta Aunty zee Win ba ta su take ba abinda ke gabanta ma ya fi karfinta.

Tana sau?e faten doyar sai ga su sun shigo
"wannan kamshi haka me ake dafa mana ne Afeefah?"
Aunty zee ta le?o kicin Win tana tambaya
Dariya Afeefah tayi
"Aunty faten doya ne fa, amma ya Naji muryarki kaman ta marasa lafiya?"
Tana zama a kujeran tsuguno ta janyo filet ta mi?awa Afeefahn, Afeefah ta karSa ta shiga saka mata kan tace
"Eh Afeefah ban jin daaWi ki taya ni murna kin kusa samun kanwa ko ?ani"
Wani irin zaro ido Afeefah tayi kan ta saki ihu tana rungume Aunty zee Win sai ta hau hawayen murna, zuciyarta tamkar takarda haka take jinta oh ashe Aunty zee na da rabon ganin 'ya'yanta a duniya?

Ita Aunty zee ture ta tayi tana share mata hawaye tace
"duk na murnar ne? Yanzu na gama share wa uncle Winki da ma Wayar Auntyn taki da suka tasa ni gaba suna kukan farin ciki shine kema za ki fara? Oya ni sa min abinci in ci cikina kaman ana yasa"
Tana murmushi ta ?arasa saka mata ta dauka mata zuwa gindin bishiyar dake ba da iska mai ni'ima, taburma ta shimfida mata kan ta ajiye mata abincin taje ta kawo mata ruwa tuni ta yi nisa a cin abincinta.

Dukda karatu da Afeefah ta saka a gaba saboda tana son fitowa da sakamako mai kyau a term Win don Aunty tayi alfahari da ita hakan bai hana ta jajirce wurin kulawa da Aunty zee Win ba, ko tsinke in ta ga zata Waga za ta karSe duk abin da take so ko a hira tayi maganan Afeefah za ta yi kokari wurin ganin ta dafa mata shi tunda uncle usman bai Gaza da gidan ba ko ta wani Sangare, kishiyar Aunty zee Win ta kan zo sossai tun samuwar cikin itama da ita ake haduwa ana ririta cikin Dukda Afeefah dai jininsu bai wani haWu da matar ba tunda iyakarsu gaisuwa, ko hira Aunty zee ke yi da Afeefah in dai ta sa matar bata amsawa ita dai Afeefah bata damu ba tunda babu abin da ya haWa su duk kuma a je a zo bata wuce awanni biyar zuwa goma a gidan so bata damu ba sam.

Kaman yadda ta ci buri ranar hutu sai ga Afeefah da position 3rd ta yi murna kwarai, haka ta dawo gidan da farin ciki. A tsaye ta samu Aunty zee tana tattare kayan da Afeefah ta wanke da safen don shigarwa ciki sai ji tayi an rukunkumeta
"Aunty ki taya ni murna"
Result Win ta mi?a mata
"Masha Allah, Alhamdulillah yarinyana kai ya fara ja Allah ubangiji ya sa ki fi haka ya dafa miki a dukkan lamuran ki, Allah ya nuna mana ranar da wannan karatu zai anfanemu ina fata za ki yi kokarin ci gaba da tafiya a haka next term mu ga First rubuce wannan wuri"
Kai ta gyaWa tana ta dariya.

****

Aunty zee ce zaune tana ta aikin kallon Afeefah dake yi musu alele don yau da sha'awar shi ta tashi hakan ya sa tana furta wa Afeefah ta hau yi, tana aikin cike da tsafta tana kuma jefawa Aunty zee Win hira kaWan kadan da ya shafi islamiyya da kuma boko da suka koma sati huWu kenan.

A ranta take raya abubuwa dayawa game da Afeefah Win tana da matu?ar buri a kan rayuwar Afeefah yadda take very jovial bata fata nan gaba ko ma menene ya karya ta, tana adu'a yadda ta samu farin ciki ta dawwama a haka haske ya cigaba da bibiyar rayuwarta, bata san me gaba ya tanadar ba amma tana mafarkin ganin Afeefah a kololuwar matsayi cike da kwanciyar hankali, danne tunaninta da ya so juyewa ta yi tana cewa Afeefah
"Wai kuwa kin san kamanninki har ya Saci da Yaya Aisha?"

Afeefah ta Wago ta kalleta yau ne karo na farko da maganar mahaifiyarta ya fito daga

3 / 53