HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   51 / 53

150K to 153K   out of 158.4K words

duk wanda ya ba?anta miki a da a yanzu yana a karkashin kafafunki, na ji daaWi da kika nufi saka musu da alkhairi bayan sun bi ki da sharri amma ki sani wannan yunkuri naki na basu ilimi makami ne mai girman gaske a duniyarsu ladar ki sai a wurin ubangiji"
Daidai nan suka isa cikin Dutsen-wai ita ke kwatanta musu har kofan Gidan Kawu Labaran.





=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

"Last Page na zuwa anjima in shaa Allah. Wlh jiya na yi gajiyar da ban san adadi ba ina buWe ido da niyyar typing idon na rufuwa ganin ba zan iya ba yasa nayi bacci and yau ma same thing zan lallaSa in ba ku shafin karshe in shaa Allah. Na gode da ha?uri da ni*

*59*

A gaban gidan ta tsaya ta ?ura mishi idanu kaman yanzu ne komai ke faruwa da ita, tana tuna ba?ar wuyar da ta ci daki-daki cikin wannan gida, hawaye ne suka cika mata idanu shaidan na raya mata ta juya ta koma kawai don basu chanchacanci duk wata alfarma daga gareta ba, da kyar ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a wuya tana tuna ni'imomin Allah a gareta sai ta furta Alhamdulillah don ko daga fasalin gidan zaka san cewa rayuwa ya ?ara taSarSare musu wane wane don daga inda take tana kallon har kofofin dakunan gidan saboda rushewar ginin ?asan dake zagaye da gidan, yunkura wa tayi zata shiga sai ta ga Fitowar wani dattijo a yanayin shiga da fuskarshi ya nuna kamilalle ne wanda kai tsaye bata kawo ko kusa Kawu Labaran bane sai da suka haWa idanu, Chakk ya tsaya yana ?are mata kallo kaman yadda ita ma take ?are mishi kallo.

Sanye yake da jallabiya ba?a har da hula taSani ka ji hadisi da chasbi ri?e a hannunshi sai wani littafi da ya nuna mata na addini ne, ya rame kam gabaWaya ya lalace, shi karan kanshi bai gane ta ba sai da yaga kallon da take mishi da hawayen dake zuba mata don kaman an yi mata wankin inji ne, kaman bata taSa sanin menene wahala ba a rayuwarta, muryarta na rawa tace

"Ka..kawu"
Tana tuna ranar da ta zo da Saleem yayi mata kora irin ta miyagun aljannu da kayan tsubbu da komai.
"Af...Afee..fah??? Ke ce Afeefah? Da gaske ke c..e?"
Cikin wani irin karyayyen murya yake maganan, ta Waga kai sai gani tayi ya iso gabanta ya zube gwiwowinshi ?asa da sauri itama ta durkusa yadda yayi suka saki kuka a tare, nata dai bata san me take ji ba don abubuwa ne suka haWe mata shaidan na tuno mata duk wani minti da tayi a gidan cikin azabtarwa yana tuna mata irin muggan kalaman kawu a kanta da rayuwarta yana nuna mata basu chanchanci komai na alkhairi daga gareta ba ta wani Sangaren tana jin babu daaWin yadda ta zo ta ga inda suke rayuwa da kuma lalacewar da kawun yayi kaman kuWin guzuri.

Shi kuwa nadama ce, nadama da kunyar kasa ri?e amana da zumuncin Wan uwanshi yake yi wa kuka, kunya mai tsanani da ba zai iya cewa ya taSa jin irin shi ba yake ji na Wiyar cikinshi.
"Afeefah idan na ce ki yafe min na so kaina dayawa, na san na yi miki abubuwa masu yawa na zalunce ki, na ci amanar zumunci, na cutar da rayuwarki fiye da ?ima, na wargaza natsuwarki har ya kai na kore ki da kaina daga kusa na bisa tarin jahilci da ba?ar zuciyata... Ina kallo matana kowacce take abinda ta so da rayuwarki ana gara ki kaman kwallo, na dauke ki da kaina na jefawa hukuma ke don kawai ina ganin kin zame min ?ashin kifi, an zo neman aurenki har nan na lalata komai saboda kawai wani zargi wanda babu wanda ya tabbatar, saboda son zuciya irin tamu... A ?arshe na aurar dake ba tare da na ko yi binciken wanene za ki aura ba, mecece sana'ar shi, su waye danginshi don kawai sun cika ni da kuWi sun kuma nemi auren kawai suke so, tun bayan aurenki da kaddara ta faWa min bisa neman zuwa wurin ki da nayi na ci arziki na faWa hannun 'yan shan jini a ranar na san cewa ke ba Mayya ba ce yadda muke faWa, a ranar na tabbatar harkar shan jini da maita ya fi karfin kwakwalwarki nadama mai yawa ya rufe ni a kullum Adu'a ta shi ne yadda zan ganki kafin ?asa ya rufe min idanu Afeefah...."

Sossai yake kuka ta mayar da kanta ?asa tana cigaba da hawaye, hatta Aisha da Abeeha hawaye suke shi kuwa Rayyan kanshi ya kawar yana jin zuciyarshi na jagulewa.

"Ashe za ki zo inda muke Afeefah? Ashe za ki neme mu?"
Zuwa lokacin makota duk ana ma?ale ana kallon me ke wakana Larai da Asabe da ma wasu yaransu dake gida duk sun fito sai dai ita bata kai hankalinta kansu ba yayinda duk suke kuka.
Hannun kawu ta ri?e tana jin yadda zuciyarta ke kakkaryewa tace
"Dole na nemeku kawu dole duk inda zan shiga ku ne nawa, ko me za ku yi min ku ne dole na duk duniya ba ni da waenda suka fi ku. Tsoro nake ji... Tsoro nake ji kar ku ?i karSa ta.."

"Ko a ya kika zo Afeefah wallahi ba zan ki karbarki ba a yanzu, na tuba na yi nadama mai tarin yawa, na roki Allah a salloli dayawa akan ya waiwayo mana dake ya sa ki tuna da mu. Don Allah, Don darajar Allah ki dubi girman shi ki yafe min Afeefah ki yafe min don Allah"
Kai take gyaWa wa ta kai hannu ta share mishi fuska
"Na yafe maka kawu wlh duk na yafe muku Allah ya yafe mana gabaWaya"
Inna Asabe ta rarrafo
"Afeefah don Allah ki yafe mana don Allah"
Ta kallesu sai ta ga inna Larai na ja da duwawu kafa Waya kam babu gabaWaya kuma ba sanda bare wheelchair zubewa tayi tana neman yafiyarta duk ta yafe musu, Rayyan da ya gaji da kukan ya taho ya Waga ta tsaye yana kallon cikin idanunta ya fidda hanky fari tas mai cike da kamshi ya fara Wauke mata hawayen fuskarshi babu Wigon walwala.

"Am sorry"
Ta faWa a hankali.
Iso aka yi musu sai dai duk gidan an rasa ma taburma mai haske da za'a iya shimfida musu su zauna, Rayyan take kallo ta juya ta kalli kawu ta sake kallon Rayyan.
"Ko za ka tafi mota ka zauna Ya Saraki?"
Ya harareta ya samu wani dutse ya zauna a kai ta mayar da kanta ?asa ko wannan kaWai ya isa ta yafe musu, wa zai ce Rayyan zai iya zama a irin wurin nan saboda ita? Saboda kawai tana wurin idan ba don haka ba me haWin kifi da kaska?

Rayuwar mutanen gidan sossai ya chanza mata ko da ta ji irin neman ilimin da kawu ke yi tun daga sanadiyar yan shan jini da suka kama shi Allah ya nufe shi da shiriya ta tabbatar da gidan sun rabauta don ilimi shi ne ginshikin rayuwa, yaranshi duk sun dawo kan hanya sai talauci da yayi musu matu?ar yawa don Allah ya jarabcesu da babu tun bayan tuban shi abinda za'a ci ma wahala yake sai dai basu daina neman ilimi ba kuma dayake tuban gaskiya suka yi yana iya yinshi ya ga an ci wani abu ko da sau Waya ne a yini, tayi kuka har sai da Rayyan ya fara yi mata faWa ganin da gaske ranshi ya Saci ya sa ta daina, ta basu labarin duk abinda ya faru da ita har kawo yau

"Allahu Akbar... Allahu Akbar kabiran lallai shi mahakurci mawadaci ne kuma mai ha?uri shi yake dafa dutse... Yanzu Afeefah har 'ya'yan sarki mai tarin daraja biyu ne a gidana ta sanadiyar ki? Ashe ke ce kike gina wannan tamfatsatsen gini da masallacin juma'ar da babu irinshi a wannan gari? Allah mai girma Allah mai yadda ya so"
Kawu ke magana cikin hawaye da tabbatar da girman zatin ubangiji.

Kallon Inna Larai tayi tace
"Kawu me ya sameta?"
"Maciji ne ya sare ta mun yi gargajiya har mun gaji kafan ya rube dole muka nemi taimako dai da kyar muka hada kudi aka yanke kafar sai dai babu kudin ko sanda ne bare kujeran guragu a dole take yawo a haka da ja da duwawu"

Lokaci Ryan ya kalla ya mata umurnin su tafi ana jiran su wurin taron da suka gayyata, kawu da iyalan shi duk suka tafi dasu wurin taron kusan duka jama'ar garin suna Wakin taron barin ma fankoki dake kaWa su ya sa sai nishadi suke.
Mai gari ne ya fara yin bayani da kuma godiya ga wacce ta dubi garin ta zaSi inganta rayuwarsu ta hanyar ba su ilimi wanda ta wannan hanyar ta riga ta gama musu komai, da ya zo wurin kiran suna sai ya ce
"Wannan Win ba kowa ba ce illa mata ga Ciroma Sameer, Ciroma mai jiran gado kuma Yariman Matasa na ?asar Fombina Afeefa..h Afeefah kamal??"
Sai yayi saurin kallon matar da ake cewa ita ce Afeefahn, duk yan garin ido suka zuba mata suna mamaki da ikon Allah, wasu kunya na rufe su a yayinda tayi murmushi ta mi?e ta haura podium Win ta karSi mic

"Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata
ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga
sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar babu mai Satar da
shi, wanda kuma ya Satar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta
da gaskiya sai Allah, shi kaWai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa
ne. Bayan nan ina yi mana Sallama irin ta addinin musulunci shi ne Assalamu Alaikum warahmatullah"
Duk suka amsa, ta Wan sauke numfashi
"Ba gixo ba kuma ba mafarki ba ha?i?a ni din ce Afeefah kamal wacce kuka fi sani da Annoba ko kuma Mayya a wannan gari, ha?i?a na jure abubuwa dayawa daga gare ku 'yan uwana, yayyena, ?annene na da kuma iyayena. A baya na zama mujiya cikin tsuntsaye Abar kyamata da gudu. Abar tozarta wa da wula?anta wa, Abar muzantawa a cikin al'umma saSanin a yanzu da nake da miji nagartacce nake kuma da surakan girma waenda suka taka rawar gani bisa inganta rayuwata daga Wacce ta sallamar da farin ciki ta sallamar da jin daaWi zuwa wacce ta zama mai cike da buri da alfahari. Da na zauna nayi nazari da tunanin Meyasa nawa iyalan kuma dangina suka yi min abinda suka yi a baya sai na fahimci babu wani abunda ke damun ahalin wannan gari na mu sai rashin ilimi da sanin daidai. Na fahimci mun samu tawaya da koma baya a wannan Sangaren iyayen babu bare su tarbiyatar da yara akan daidai, a sadda na sake zurfafa tunanin me zan yi na taimaki al'ummata sai na ga babu abinda ya fi dacewa irin in wayar mana da kai in taka rawa wurin ganin mun samu ilimi har ma muna aiki dashi, in ga cewa wata mace ko wani yaro bai WanWani irin Wacin da na WanWana ba, in ga cewa yadda rayuwata ta inganta kowa ma a yankina rayuwarshi ta inganta gobenmu mu samu tsatson da za mu yi alfahari da su daga wannan gari namu.

Ya ku 'yan uwana musulmai ku sani cewa
addinin musulunci addini ne na ilimi. Umarni
da neman ilimi shi ne farkon abin da Allah
MaWaukakin Sarki ya umarci Annabinsa
(S.A.W) da shi, yayin da ya saukar masa da
faWinsa :
'BR1N'R (P'3REM 1N(QPCN 'DQN0PJ .NDNBN! .NDNBN 'DR%PFR3N'FN EPFR)
9NDNBM 2 'BR1N'R HN1N(QOCN 'DR#NCR1NEO 3 'DQN0PJ 9NDQNEN (P'DRBNDNEP 4 9NDNEN
.['D9DB: e - a] ('DR%PFR3N'FN EN' DNER JN9RDNER 5
Ma'ana : (Ka yi karatu da sunan Ubangijinka
da ya yi halitta. Wanda ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu kuma Ubangijinka shi ne mafi karamci. Wanda ya sanar da alqalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba). (Alaq : 1 - 5)
Addinin musulunci ya kwaWaitar da mabiyansa akan neman ilimi, domin ba zai yiwu mutum ya bauta wa Allah ba sai da ilimi. Allah madaukakin Sarki yana cewa :
A'71:] (%PFQNEN' JN.R4NI 'DDQN EPFR 9P(N'/PGP 'DR9ODNEN'!O28)
TA].
Ma'ana : (KaWai waWanda suke jin tsoron Allah daga cikin bayinsa su ne masu ilimi)
Idan na ce zan kawo muku faWar Allah da kuma hadisan da suka yi magana akan ilimi da amfaninsa gare mu za mu kwana bamu ?are ba amma tabbas da akwai ilimi da duk ban fuskanci abinda ya faru da ni a wannan kauyen namu ba, Ajalin mahaifina ya same shi ba tare da na zo duniya ba, mahaifiyata ta rasu bisa rashin kula da rashin zuwa asibiti a yayin daukar ciki zuwa haihuwan gida, kakata shekarun ta ya ja ?warai wacce dole a yi mata tsammanin mutuwa a sadda ta tafi haka Goggona ta tafi bisa sakaci da zaman jahilci da dabbanci da ake yi a cikin gidanta, bamu san kan mu ba bare mu nemi sanin hakko?in da suka rataya mana, hakko?in matayenmu, hakko?in iyayenmu bare hakko?in 'ya'yayenmu wanda duka sai ta hanyar ilimi za mu sani, na koma wurin Aunty zainabu ta gamu da postpertum wanda ciwo ne da ake samun shi bayan haihuwa duba da bata taSa ba ga yawan shekaru babu wanda ya fahimci hakan sai da lokaci ya ?ure ta tafi duk ba mu dubi ajalin su ne yayi ba, mun manta Allah ya ce ba zai taSa jinkirta ajalin dayanmu ba idan ya zo dole za mu tafi. ku sani na yafewa kowannenku da wanda yayi min na sani da wanda ban sani ba duk na yafe muku, a wannan gidauniya tawa tafiyar duk na neman ilimi ne da kuma tsayuwa akan kafafunmu don Allah ina ro?on mazaje da ku bar matayenku da ma ku karan kanku ku nemi ilimi don Allah ba ya ?arbar uzurin bawa akan rashin sani saboda ya mana umurnin nema.

Akwai ma'aikata da za su koyar da sana'o'i ga yara da matayenku su ma ku bar su don zai amfani wannan al'umma tamu, duk lokacin yaye Walibai idan yayi zan zo kuma idan Allah ya amince za mu dinga raba kyaututtuka da suka shafi sana'ar da mutum ya koya don ya cigaba daga inda ya tsaya ina Fatan ganin chanji daga gare mu bakidaya na gode"

Wasu hawaye suke yi suna tuna abinda suka mata amma dayake tana da zuciya mai kyau dubi Alkhairin da ta nufe su dashi, kawu ta mi?awa mic Win don ya taso yana son yin magana, a gaban tarin al'ummar yana kuka ya ba da duk labarin abinda yayi mata da wanda aka mishi ta sanadiyar son zuciyarshi da yadda ilimi ya sauya shi daga mummuna zuwa kyakyawa har ya kara da
"An karSo daga Kasir Wan Qaisi ya ce, ina
zaune tare da Abud Darda'i a masallacin
Dimashqa, sai wani mutum ya zo wajensa ya ce masa, Ya Abud Darda' i na zo wajenka ne daga Madinar Manzon Allah (S.A. W) saboda
wani hadisi da aka ce min kana faWa daga Manzon Allah (S.A. W), kuma babu wata buqata da ta kawo ni nan sai wannan. (wato jin wannan hadisin) Sai Abud Dar' da'i ya ce,
"Na ji Manzon Allah (S.A. W) yana cewa :
"Duk wanda ya bi wata hanya yana neman ilimi a cikinta, to Allah zai sanya shi akan hanya daga cikin hanyoyin Aljannah, kuma haqiqa Mala'iku suna sanya fika - fikansu ga Waliban ilimi, don yarda da abin da yake nema, sannan duk wanda yake sama da qasa yana nema wa malami gafara, har ma da
kifayen da suke cikin ruwa. Falalar malami a
kan mai bauta kamar falalar wata ne a daren
goma sha hudu a kan sauran taurari, kuma haqiqa malamai magada Annabawa ne,
Annabawa kuwa ba su bar gadon dinari ko dirhami ba, kaWai sun bar gadon ilimi ne don haka don Allah kar mu raja'a akan boko don shi iya na duniya ne mu nemi lahira kuma mu koyar komin kankartarsa, ko uwa malama ce akan yayanta kar mu saka finafinai ko wa?a gaba mu ta rawa da nishadi da yara mu koya musu abinda zai amfanesu a gaba. Ni a karan kaina misali ne kuma Aya ne ubangiji ya nuna min akan Afeefah"

Duk jikin mutanen wurin yayi sanyi kuma sun gamsu Wari bisa Wari da lallai suna da nakasu ta wannan fannin dole rayuwarsu ya tafi a jiSance, Afeefah da manyan gari a gefenta mijinta ne da ya bata support Wari bisa dari suka zaga wurin tassss ta yabi kyau da tsarin komai na wurin kuma duk abin bukata akwai.
Kawu ta dam?awa wurin ta ce ta bashi amana ya ri?e mata ya kula da komai yadda ya kamata bisa tsari shi dai babu bakin magana don ya rasa me zai ce.

Cikin jami'an tsaro masu kula da taron kawai idanunta ya sau?a kanshi, da sauri ta nufe shi tana kallonshi shima ita yake kallo a hankali ta nuna shi "Sa'adu? Sa'adu Rabi'u kai ne?"
Kai ya gyaWa yana murmushi ya gane ta amma bai zaci zata nuna ta sanshi ba ta juya ta kalli Rayyan ya matso
"Ka tuna shi Ya Saraki?"
"Wannan police da ya ceceki daga sharrin gurbatattun 'yan uwansa"
Za Ta cire zobenta na gwal ya mi?a hannu ya ri?e nata, ya zari kati daga aljihunshi ya mi?a mishi
"Ka ?ira ni in shaa Allah kyautarka ya fi karfin kuWi za'a mayar da kai cikin Kaduna da matsayi mai kyau"
Hawayen murna ya fara yana godiya.

Ko da aka watse taron suka koma gidan Kawu akan za'a saka date na fara daukar Waliban da suka kamata za kuma ta turo waenda za su taimaka mishi wurin fahimtar komai da komai kan a sakar mishi, a tsakar gidan suka samu an jibge kayan abinci babu abinda babu wanda za su iya ma watanni goma zuwa ashirin basu nemi kayan abinci ba, a gefe crouches ne da wheelchair na inna Larai Afeefah tayi saurin kallon Rayyan ya girgiza mata kai yana dan Wage kafada sai ya juya ya fice ta bi bayanshi

Za tayi magana jiri ya Wan dibeta da sauri ya ri?o ta
"BoWWi menene? Ba kin ga illar kukan da kika dinga yi ba duk

51 / 53