HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   12 / 53

33K to 36K   out of 158.4K words

mai gadi, idanunshi ya Wan runtse gabanshi na Wan faWuwa yau dai Abba ya kama shi, bai so ya dawo ya haWu da Abban ba Dukda Umma ta gayamishi Abban na son ganinshi ya dai san tatsuniyar gizo bata wuce ta koki kuma shi kaman har yanzu bai shirya ba, haka dai ya sau?a yana Wan shafa kai ya matso su suka sake gaisawa da mai gadin a lokacin sun gama magana da Abban ya juya ya wuce.

"Za ka shafa kai ai Sulaiman, wai Hausawa suka ce in kere na yawo zabo na yawo watarana dole a haWu"
"Barka da safiya Abba"
Yayi gaisuwan a kunyace yana yar dariyar maganan Abban.
"Barka dai Sulaiman ya aikin?"
"Alhamdulillah Abba"
"Toh ina magananmu ta kwana? Ka dai san na gama Waga maka ?afa ko? Na fa gaji da ciyar da tuzuru don ka fi ?arfin gauro"
Abban na murmushi ya ?arasa maganan
Sulaiman Dariya yayi yace
"Soon Abba in shaa Allah"
"bari na gaji da Soon Win nan naka za ka sha mamaki, dama akwai yaran abokai da dangi da duk na yarda na kuma gamsu da nasaba da tarbiyar su sai dai ka ji an saka maka rana, kar ka ga ina murmushi Sulaiman wannan ne last chance Winka, wai kai ko kunya baka ji? Kannenka duk sun tara 'ya'ya maza da mata kana zaune abin ka?"

Har lokacin murmushi yake, ya matukar sanin mahaifinshi Alhj Abdulrasheed mutum ne mai saukin kai da sau?in hali Dukda tarin kudin da Allah ya bashi, Wan kasuwa ne da har yanzu bai daina nema ba daga shi har yaranshi suna da sau?in hali da kyautata mu'amala da duk wanda hakan ya haWa su.

"In shaa Allahu Abba za ka ji alkhairi i promise"
"I hope so, yanzu kake dawowa daga aikin kenan?"
"A'a Abba, na dawo da wuri na Wan je na duba wata patient Wina ne a gida na ba ta medication"
"Toh yayi kyau, a je a huta Allah ya taimaka"
Ya amsa da Ameen yana jera wa mahaifin nashi adu'ar ?ara girma da lafiya ya wuce Waki, haka kawai yake tsintar fuskar Afeefah a idanunshi idanunta, murmushinta da ma sassanyar muryarta na dawo mishi kaman a yanzu take yi mishi, lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya...

Kaman wasa fa sabo ya fara shiga tsakaninsu da Dr. Sulaiman kachokan yake bata dukkan kulawar shi ya kan zo kullum sau biyo har saida duka alluran ta suka ?are, kuma bai taSa shigowa hannu banza ba har ta kan rasa waye ya fi wani damuwa da ita tsakanin shi da saleem da bai taSa hutawa da yi mata sa?o ba, ko da ta samu sau?i ta komawa aikinta sai Sulaiman ya cigaba da ?iran ta tun suna gaisawa kawai su yi sallama ya fara jan ta da hira da wasa.

Yau tun safe jikinta ke a matu?ar mace, sa?on saleem ya shigar da ita rudani da damuwa marar misaltuwa Dukda ta tsammaci hakan sai dai ya daketa fiye da zato.

Sallar asuba ta farka tana buWe idanunta ta sau?a tayi alwala ta zo ta gabatar da shafa'i da wutiri kan ta mi?a sallah, tana idarwa ta janyo wayan don karatu yadda ta saba sai ta ga pending message, buWewa tayi ta ga ?arfe 2 da 'yan mintuna gabanta ne ya Wan faWi me yasa saleem zai mata sa?o tsakiyar dare? Composing kanta tayi ta buWe tana karantawa hawaye na silalo mata

"Afeefah na san a lokacin da za ki ga wannan duniyarki za ta sake shiga rudani fiye da yadda take ciki a yanzu, na san tsoro zai mamaye zuciyarki, na san za ki yi tunanin anya saleem na cikin hankalinshi kuwa ya turo wannan sa?o? Toh duk lafiya ta ?alau kuma ina cikin hayyacina hasali ma tunani da matsuwar zuciya akan fallasa sirrin ta su suka hana ni bacci har kawo wannan lokaci, Afeefah na kasa hana zuciyata ?aunarki... Zuciyata ta kamu da Soyayyar ki ba na wasa ba, wallahi Soyayyata a gareki gaskiya ce, kuma ta ginu ne daga tushen tausayi Afeefah ina ?aunarki fiye da yadda zan furta miki"

Kuka kawai ta fashe dashi tana haWa kanta da gwiwa, wani sabon al'amari ne kuma ke shirin shigowa rayuwarta? A sadda take karanta sakon Saleem duk wani tsika na jikinta sai da ya tashi, zuciyarta kaman zai Faso kirjinta ya fito Dukda ta jima da tsammatar hakan sai dai bata kawo hakan kusa ba, ba tsoron ta soyayyar shi ba tsoronta danginshi ta ina za ta fara son saleem? Ta yaya?

Ta san saleem duk inda mace take neman nagartaccen namiji ya kai har ma ya wuce abin tambayar mahaifiyarshi da 'yan uwanshi za su karSi uzurinshi? Ta Tabbatar muddin suka ji cewa salim na son ta zamanta a gidan ya zo ?arshe kenan to in sun kore ta ina zata je? Ko da ta koshi da kukan ta fito ta ?arewa gidan kallo sai taji ma har wacece ita da namiji kaman saleem zai so ta? Har wacece ita da za ta yi mafarkin rayuwa da saleem? Ai ko da girgiza kanya ta fi magarya za?i.

Jiki a sabule ta gama dukkanin ayyukan ta, ko da ta dawo Wakin ta sake samun sabon sa?on saleem.
"Afeefah na san na saka ki a rudani sai dai nima na rasa mafita ne, wallahi ban san sadda soyayyar ki ta samu matsuguni haka a zuciyata ba, ba ni da iko da ita bare har in hana ta. Don Allah kar ki yi kuka kuma kar ki firgita idan ba kya so ba zan tilasta ki ba don wallahi na fi kaunar farin cikinki da nawa farin cikin, kar wannan dalili ya sa ki ja baya da ni kawai na sau?e wani nauyi ne da nake jin ya zame min dole na sau?e, ina sake sanar da ke cewa Na so ki jiya, na so ki yau, zan cigaba kuma da son ki har zuwa gobe sannan zan cigaba da son ki kowace rana"

Numfashi mai nauyi ta sau?e hannunta har rawa yake, hawaye kuwa ya fi pampo zuba a fuskanta, ita dai da bad luck aka halliceta mugun tabo da shaidar ta zai cigaba da bibiyar ta har abada, a yau anan ba wani ne ya mutu ba amma tambarinta shi ya ja mata tsanar da ba zai taSa sanyawa mommy ta amince da ita a matsayin surka ba ko tana mutuwa tana farkawa kuwa.

Bata san yadda yake ji a ranshi ba amma ta san abin da zai hana shi sukuni haka babba ne, ba za ta bari salim yayi kuka saboda ita ba don haka a hankali ta rubuta
"Allah ya zaSa mana abin da ya fi alkhairi"

Lumshe ido yayi daga Sangaren shi, shi karan kanshi tsoron yake ji, amma ya zai yi?
Kalamai ya cigaba da mata na kwantar da hankali gabaWaya yinin, ganin ya damu sai ta danne nata damuwar ta nuna mishi bata da matsalar komai kuma a shirye take da duk abin da zai je ya dawo, ta san bata da wannan ?warin gwiwar amma da shi kila komai ya zo da sau?i.

Washegari da yamma tana zaune tana karatun alqur'ani kawai ta ga sa?on shi
"Hey dear zan dawo gobe, me kike so na taho miki da shi?"
Ta karanta text message Win ya fi sau uku zuciyarta haka kawai ya shiga bugawa amma ta dake ta rubuta
"Ka fi kowa sanin abin da ya fi cacanta da ni, duk abin da ka kawo ba zan ?i farin ciki ba"
Murmushi mai kyau ya saki, yana Fatan kasantuwar ala?arsu na har Abada yana fata da Adu'a akan muddin ya fito fili komai ya zo mishi da sau?i don babu yadda ya iya da abin da zuciya take so.

A Washegarin duk iyalan gidan suka shiga shirin tarbar breadwinner Win su, hidima kawai ake don a wannan karo ya Wan jima bai zo ba, dab la'asar ta gama wanke-wanke tana shirin shiga wanka ta ji wayanta na ringing, ta san Sulaiman ne don shi kaWai yake kiran ta sai kuma saleem da yake mata text message, dagawa tayi tare da sallama ta shiga gaishe shi, ya amsa cike da wasa kaman yadda yake mata tamkar 'yar baby ya Wauke ta.

"Yau dai haka kawai na ji ina son ganinki har mafarkinki na yi fa da na yi baccin rana, zan tafi office da yamman nan idan kin ba ni dama in biyo in kalle ki ko kaWan?"
Ta Wan sauke numfashi a Soye a hankali tace
"Ni na isa hana ka?"
Da Wan murmushi yace
"A'a ai na zaci za'a yi min rowan wannan beautiful and innocent face Win ne"
Tace hmmm, wani zuciyar na ce mata kila fa shima in da ya san wacece ita ba zai raSeta ba.
"Sai ka zo, a gaisar min da Baaba please"
"Banda ummana?"
Yayi maganan a hankali, tayi murmushi
"har da ita fa Dr. Da ma kowa da kowa"
"Toh wa zan ce mata tana gaisheta?"
"Afeefah mana?"
Ta faWa tana 'yar dariya murya a karye, shi ma murmushi kawai yayi ya yanke call Win.

Wankanta ta shiga a gaban madubi ta tsaya tana ?arewa kanta kallo, sossai ta ?ara ganin chanzawarta ba'a tsawo ba don dama chan ita Win doguwar mace ce, sai dai ta Wan kara kauri saSanin da da take lange-lange kuma fatar ta ya kara wani irin kyau da sheki, mutane dayawa su kan yabi kyaun fatarta musamman a zamanta da Aunty zee amma bata taSa yarda fatar mai kyau bane kaman yanzu, ta buWe sossai daga ?asa sai dai saman babu wani auki tsarin jikin sai ya bata wannan figuren da ake cewa coca-cola, a sadda take Dutsen-wai bata taSa kawo ko a mafarki za ta auru ba amma da ta dawo Anchau Dukda jita-jitar da ake yadawa a kanta hakan bai hana wasu tararta da sunan So ba amsar ta dai karatu ne a gabanta, ta kuma san ko ta amince da wuya ne a haifi da mai ido musamman ga 'yan uwa da abokan arzikin wanda za ta amincewar, a yanzu kuwa da babu halin karatun muddin ta cigaba da zama a gidan tana jin za ta so matsawa wani environment Win inda za ta samu so a yadda take kuma a bata rayuwa ingantacciya, amma Saleem shi ne namijin da zuciyarta ta fara aminta dashi don ya yi mata abin da kuWi ko godiya ba za su taSa biyan shi ba.

Tana wanka haka kawai tana hawaye, tana ji a ranta matu?ar komai ya bayyana kwaSarsu za ta yi ruwa ba na wasa ba, kuma wa'adin zamanta a gidan ya ?are, amma in ta saurari Sulaiman fa?

Sulaiman bai san asalin ta ba, bai san tarihi da mugun tabon ta ba idan ya sani kila shi ma iyayenshi ba za su taSa karSar ta ba. Da wannan tunani da damuwar ta fito daga wankan.

Man shafawar da Sulaiman ne ya kawo mata haWe da wasu dogayen riguna inda yake ce mata babu abin da ke karbarta kaman dogayen riguna ko don bai taSa ganinta da lace ko atampha bane amma tana matukar tafiya da tunanin shi in ta saka su shi ta shafa, ta Wauki wani maroon Abaya da ya sake fito da kyaun skin Winta cikinsu ta saka, ta Wan fesa turare tare da man leSe kaWan, mayafi ta yafa daidai Sulaiman na ?ara kiranta a kan ya zo.

Shi kuwa Sulaiman a sadda ya gama shiryawa ya fito parlorn ya ci karo da mahaifiyarshi da ?annenshi.

"Sai ina Ya Sulaiman?"
?ayar ta faWa.
"Ina ruwan ki? Sa ido...."
Ya faWa yana hararanta.
Wacce suke tsananin kama da wacce suka yi maganan da farko tace
"Sana'ar banza ba, ai yaya ka fita sabgar fa'iza ta cika saka ido. In zo in raka ka ne?"
"Kema bana so gulmatu"
Dariya suka sheke da shi ganin yadda ya ke hararinsu. Tsaki ya ja

"Umma na tafi"
"A gaishe min da surkar tawa"
Narkewa yayi
"umma wai har da ke a biye wa waennan yaran?"
Ta Yi dariya tana cewa
"Sai dai ka dawo"
Ya fice abin shi a jikin mota ya tsaya yana kokarin shiga sai ga Fauza ta mi?a mishi wani leda wai in ji Umma ya kai mata, yayi murmushi ya karSa kawai bai ce komai ba.
Gidansu akwai sau?in hali da haWin kai shi ne babba, yana da imediate kanwa da tayi aure sai wani namiji kafin twins Win nan mata biyu, mahaifinshi fitaccen Wan kasuwa ne inda mahaifiyarshi ke aiki da federal government, ba su taSa raina talaka ko ya yake musamman Sulaiman da shi ko na kasa da shi ya kan girmama, babu mai cewa ga wani tambari nashi ko hali marar kyau Dukda kowani mutum tara yake bai cika goma ba.

Sai da ya biya ya kara mata sayayya akan na Umma kaman koyaushe matukar zai je wurinta bai taSa zuwa hannu banza ba ya nufi gidan, bayan yayi parking ya ?ira ta, Bata kai ga fitowa ba aka wangale Gate Win gidan Motar Ryan ta kutso kai ciki a hankali...






=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*016*

Kaman yadda ?a'idarsa take ba ya hanzari ko gaggawa a koma menene sai ya sha ?amshin nan dai wane saraki haka a yanzu ma, sai da saleem dake sanye da khakin sojoji full 6/6 don hatta agogon da Ke Waure a tsintsiyar hannunshi da ?atuwar backpack na bayanshi duk na sojojin ne ya sau?o kan ya buWe motar ya sanyo jiki.

Yau sanye yake da wata farar kaftan da aka yi wa Winkin zamani ya matu?ar zauna mishi kuma farar fatarshi ya ?ara haskaka, daga takalmi har agogon fatar dake Waure a tsintsiyar hannunshi farare ne, kanshi babu hula sai kwantaccen gashin shi na ainihin Fulanin asali da ke she?i, ganin Dr Sulaiman ya Wan ba saleem mamaki shi ma kuma Sulaiman ganin su ya sa ya taso daga jikin motar shi ya isko su Saleem ya fara mi?awa hannu fuska a sake suka gaisa kan ya mi?awa Ryan shi ma ya karSa suka gaisa cikin 'yar nuna sanayya amma fuskar nan kadaran hadaran.

Magana suka cigaba da yi da salim da ta shafi Lafiyar Afeefah shi dai Rayyan tun da suka gaisa ya zaro wayanshi ya kuma mayar da hankalinshi kai don hirarsu ba huruminshi bane.

Tun da ta hango su gabanta ya yanke ya faWi, abin da za ta cewa saleem ya kawo Sulaiman gidan ke ta kai komo a ranta, tafiya take tamkar hawainiya saboda bugun zuciya, su ukun duka kwarjininsu ya wani rufe ta tun kan ta iso inda su ke, Zaratan samarin masu jini a jika cikakkun maza kuma kamilallu, kowanne kuma gwani ne a nashi fagen kyaun da kamala.

Ji ta yi kafafunta ba za su iya daukar ta ba a sadda mai fararen kayan ya Wago idanu suka shige zuruf cikin nata.
"Rayyan!"
Sunan ya yi ringing da matukar ?arfi a kwakwalwarta, wannan idanu ba za ta taSa manta shi ba tuni ya mayar da kanshi kan wayanshi amma ita ta daskare ta kasa motsa kowani gaSa na jikinta, idanunshi sun fi yanayi da na maguna kwayar wani surkin kala ne da kan rikita lissafin duk wadda ya zubawa su, ?asan lid Win tamkar an zana mishi kwalli zirrr ba?i sidik hakan sai ya kara saka idanun zama na daban da sauran mutane, idan idanun suna du?e za ka zaci a rufe suke saboda tsawon lashes Win sa ga su ba?ake kaman gashin kansa da na girarsa.

"Afeefah!!"
Saleem ya faWa da Wan karfi a karo na uku, firgigit tayi ta dawo hayyacinta.
"?araso mana kin tsaya daga chan"
Bai sake magana ba har ta ?araso inda suke daga shi har Sulaiman idanunsu na a kanta.
Da kyar ta iya buWe baki tace
"Sannu da isowa Ya Saleem"
"yauwa Afeefah"
"Ina yini?"
Kai kawai ya Wan gyaWa mata hakan ya sanar da ita cewa lokacin da ya kamata yayi magana da ita ya wuce.

"Yaya Sulaiman ina yini?"
Muryarta da ya karye ya ?ara sanyaya yana fitowa a slow, Wago ido Ryan yayi ya kalleta daidai tana ce mishi shima Ina yini? Ya kau da kai kaman bai gane da shi take ba, daga shi har saleem sun fahimci chanzawar muryarta, shi Ryan kam ma mamaki ne fal ranshi don a yanzu abin da ya sa ya sake kallonta tuna abin da saleem ya gama faWa mishi bayan ya Wauko shi daga Airport wai son yarinyar nan yake, in ba janyowa kai raini ba shi bai ga abin ba ya tabbatar a auren ?auye sun kusa ajiye irin ta. Tsaki ya ja a fili yana furta

"Man we talk later!"
Ya faWa cikin muryarshi mai cike da ginshira sai Muryar ya bata tsoro ta tuna ranar da yake daka mata tsawa da hanzari ta Wago idanu ta sake kallonshi, ya mi?awa Sulaiman tender fingers Win shi da kaman zai fidda jini don haske da taushi suka yi musabaha, yana kokarin buWe mota idanunshi suka sake shige wa cikin nata, daga ita har shi suka yi saurin kawar da idanun ya shige ya ja ya bar gidan.

Saleem ya dubi Sulaiman ya ce
"Nima kaman zan shiga daga ciki jikina kaman an min duka"
Sulaiman na murmushi yace
"Ai dole, a huta gajiya mazan fama"
Suka yi musabaha kan ya nufi ciki, ya zaci Afeefah ma za ta yi wa Sulaiman Win sallama ta biyo bayanshi sai ya Wan waiga nan ya ga sun matsa jikin motar Sulaiman Win yana mata magana a hankali ita kuma tana dariya, tuni duk wani walwalar fuskarshi ta kau, ranshi ya shiga suya bai iya ya shiga main parlorn ba ya bi ta baya ya haye sashenshi, backpack Win kawai ya ajiye ko zama ya kasa yi ya dawo jikin Window yana kallonsu, kusan mintuna talatin suka yi suna hira kan ya ga Sulaiman ya buWe mota ya fiddo wasu ledoji ya mi?a mata.

"Ga shi umma wai na kawo miki"
Tayi murmushi mai kyau cike da jin daaWi tace
"Allah sarki umma, ka yi mata godiya na ji daaWi sossai Allah ubangiji ya kara girma da lafiya"
Wayanshi ya zaro yana furta
"Ko kuma ki yi mata da kan ki ba"
Ido ta zaro kan ta yi magana ya shiga ?iran ummar, bayan ta Waga da sallama ya ce
"Ummar mu ga Afeefah tana so ta miki godiya"
Kaman za ta nitse haka ta karSa

12 / 53