HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   4 / 53

9K to 12K   out of 158.4K words

bakin Aunty zee Win
"Na zaci da babana nake kama don mutane kan ce ina kama da inno(kakarta da ta rasu)"
Mi?ewa Aunty zee ta yi ta shiga Waki ta Wan jima sossai kan ta fito da wasu hotuna hannunta, a lokacin Afeefah ta koma kan taburma ta zauna ta bar alelen ya dafu gefenta Aunty zee da cikinta har ya turo sossai ta zauna.

"Jini ne kawai tsakanin ki da inno amma kamanninki tsaff Yaya Aisha ne, kin ganta nan lokacin bikinta ne da babanki"
Karo na farko kenan da zata ga mahaifiyarta sai ta ji zuciyarta ya cika da rauni, hannunta na Wan rawa ta sanya ta karSa hotunan da ne Black and White matar da ta kasance mahaifiyarta da bata sani ba zaune sanye da zani da riga tare da Ali goggoro, hawayenta ne suka tsinke ganin yadda matar ta zauna tamkar ta kirata ta amsa, da gaske hatta yatsun hannu da na kafar ta irin na mamanta ne, ba?in fatarsu mai she?i, manyan fararen idanunsu, tsinin hancin su, karamin bakinsu da fararen hakwaransu hatta dimple guda Waya da maman nata ke dashi a gefen hagu itama tana da shi.

RaWaWin maraici ne ya mamaye zuciyarta, in ba mutuwa ta zama dole ba wa zai so maraici? Maraici ma irin nata marar gata da tushe? Maganganun mutane a kan iyayenta take tunawa sai taji kaman yanzu ne ake jefanta mugayen kalamai, tsintuwa da hantara a kan waenda duk duniya idan da za'a ce me take bu?ata ayi mata ko da abu na ?arshe ne za ta zaSi su yi rayuwa na har abada amma ake mata ?azafin kashe su, anya zuciyarta za ta taSa warkewa? Anya za ta iya yafewa masu alhakinta?

?ago raunannun idanunta tayi ta Kalli Aunty zee
"Aunty don Allah yaya maita yake? Ya ake yi? Yaya mutanen su ke? Kila baka sanin sadda kake yi in ba hakan ba ta ya zan zaSi wannan rayuwa akan iyayena? Kila ko cikin fitan hayyacine ake yi ko? Menene ribar yin? Suna yin kuWi ko Aunty? To me yasa ni ban yi ba? Yanzu wannan pure soul Win ni na kasheta ko?"
Duk ta rikice ta rasa me zata ce, kalaman suna zuwar mata ne kawai ba tare da ta san fitan su ba, kuka ne ya kufce mata, kukan da ke fita daga ?asan zuciyarta na ciwo da raWaWi...






=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Ku yi ta Adu'a mu ?are a haka ina jin karsashin typing, ina jin daaWin comments Win ku Allah ya bar ?auna*

*005*

Hannunta ta ri?e cike da tarin tausayinta da kuma ?aunar da take jin tana mata fiye da ?ima ta shiga cewa
"Na san ba ki kashe kowa ba Afeefah, ?age ne kawai da ?azafi irin da jahilai daga cikin al'ummar mu, ?arancin ilimi yayi yawa ta yadda mutane suke kasa yarda komai daga Allah ne, a ?ar?arorin mu ne musamman wanda babu addini sossai za ki samu ko tuntuSe bawa yayi sai an faWi dalili da silar shi basu yarda cewa komai Allah ne yake yi ba.
Afeefah Kowacce rayuwa akwai ?alubale ciki ke kuma ta ki kalar ?alubalen kenan, amma fa na faWa na sake kar ki saka hakan a ranki saboda babu mai kashewa da raya wa sai ubangiji, duk kuma wanda kika ga ya rasa ransa tabbas lokacin shi ya riga ya ?are ne ko da sanadi ko babu dole babu ma?awa sai ya tafi, tsakanin ki da su Adu'a ne shine zai ba su tabbacin irin ?aunar da kike musu. Afeefah mahaifiyarki ba za ta so ta ga kina zub da hawaye ko kin ?untatawa kan ki saboda ?addarar da ba ke kika Worawa kan ki ba, kaman kowace uwa ni ma zan baki shawara ki saka zuciyarki gaba, ki yi Adu'a ki kuma jajirce ki zama tamkar bishiyar gamji sara ko sassa?a ba su isa su hana ki toho ba"

Jikin Aunty zee kawai ta faWa tana shesheka da kyar ta lallasheta ta bar kukan kan ta Wago
"Na miki al?awari in shaa Allahu Aunty za ki yi alfahari da ni nan gaba, ba za ki taSa kuka a kaina ba"
"Allah ya amince hajiya ta"
Dariya Afeefah ta saki jin ta kirata hajiyarta wadda babban burinta kenan ta zama shahararriyar 'yar kasuwa don tana so tayi kuWi saboda wani dalili nata. ?aurin kamawar leda da suka ji ya sa ta tashi da gudu taje ta sauke tukunyar alelenta daga kan gano tana furta
"Aunty alele na so yayi mana bu?ulu"
Aunty zee na dariya tace
"Hira ta yi daaWi ba, duba ki ga Allah ya sa bata yi komai ba"
Sun ci sa'a bata yi komai ba sai na ?asan guda biyu da ledar ya ?one nan ta zuba musu tare da Auntyn ta zuba na uncle a kula suka zauna suka ci tare suna hirar su gwanin sha'awa bayan sun gama ita ta yi wanke wanke, ko da ta dawo kan taburman hoton Aunty zee ta bata
"Gashi na bar miki, ki ajiye a wurinki"
Murmushi ta saki kan ta karSa tana godiya.

Wasa wasa cikin Aunty zee ya shiga watan haihuwa, ta Sangaren Afeefah tana nan tana ?o?arin karatu ka'in da na'in don 2nd term da suka koma ita ta Wauki na Waya kuma 3rd term nan suna ?are ta tare da ita za'a zana Junior waec ta tafi ss1, a yanzu hatta turanci ya zauna a bakinta ba kaman baya ba da bata wani jin komai, duk wani sayayyar haihuwa tare suke zuwa saboda a hankali ciki ya sa Aunty zee Win ta shigar da Afeefah cikin business Win ta, wani lokacin ta kan aike ta ita kaWai ma kasuwa wurin customers Winta kuma ta zo ta raba wa clients Winta kayan, asusu Aunty zee ta yi mata ta kan ware ladar ta na kasuwanci ta saka mata ciki duk da Afeefah ta nuna ita bata so, tufafi, karatu da kuma cima sau uku da ake bata ya wadatar da ita. Amma Aunty zee ta nuna hakan shine adalci kuma ko nan gaba zata iya anfani da kayanta idan bu?atar hakan ta taso.

A yau Aunty zee take cika wata tara da kwana tara kuma a ranar ta kwana da labour mai zafi, hankali tashe da asuba suka tarkata asibiti har da kishiyarta da ta zo ta kwanan musu kasancewar tun da abin ya fara mijin ya ?irata, ta fi kowa shiga damuwa an ?arbe ta zuwa Wakin haihuwa sai jiran abin da hali zai yi, duk Afeefah ta fi ruWewa babu abin da take tunawa vividly sai irin wahalar nakudar da innarta tayi ?arshe daga ita har babyn suka koma wannan abu ba zata taSa mantawa ba, duk kuma ta ga mai ciki sai hantar cikinta ya kaWa a yanzu Allah kaWai ya san halin da take ciki na tsoro da fargaba duk adu'ar da ta zo Bakinta ita take yi.

Sai Azahar Allah ya taimakesu midwifes Win da suka karSi haihuwar suka fito suna musu albishir na ta samu 'yan biyu mace da namiji faWin kalar murnar da suka yi Sata baki ne. Karo na barkatai kenan da Afeefah ta ke kai idanunta kan yaran hakwaranta duk waje, yaran gwanin sha'awa kaman ta HaWiye su, sam bata san Aunty zee ta farka ba sai ji ta yi tana furta
"Suna ba ki sha'awa ko Afeefah?"
Da sauri ta juyo tana dariya
"Sossai ma Aunty zee, sannu kin farka? Ya jikin?"
Ta Wan saki murmushi.
"Masha Allah, jiki Alhamdulillah"
Ta furta hawaye na gangaro mata Dukda tana sau?a sai da ta ji Wuminsu kan wannan wahalallen baccin ya yi awon gaba da ita amma yanzu da ta farka sai take ganin kaman mafarki, kaman ba'a gaske ba ita ce yau da shekaru arba'in da biyu a duniya kan Allah ya nufe ta da ganin ?wanta? Har biyu kyautar Allah? Bata san wani irin godiya za ta yiwa mahallicinta ba don ko yau ta faWi ta mutu ta san ta bar bayan da za su iya tunawa da ita su yi mata Adu'a, bata san daaWin haihuwar ya kai har haka ba a ganinsu da take kawai ji take kaman ta rabu da ba?in ciki har abada matukar suna kusa da ita.

A hankali Afeefah take kokarin Waukar su ta kaiwa uwar, daidai shigowan kishiyar Auntyn
"A'a Afeefah me haka? Sabbin haihuwan kike Waga su anyhow? Wa kika tambaya da za ki Waga su?"
Yadda take maganan zaka zata wani gagarumin abu Afeefar ta aikata don har ta tsorata, da ta kurawa matar idanu sai ta fahimci kaman akwai dalilin maganar nata amma bata wani mai da hankali ba don Aunty zee ta amsa mata
"A'a hamdiyya ai Afeefah ba yarinya ba ce da zata kada yaran baki san ko yanzu ta yi aure zata iya haihuwa ba? Getting to 18yrs ba wasa ba"
"kin ga Aunty sabbin haihuwa ne kuma ji da abin mu muke ko kuda bama so ya taSa su bare wasu da idonsu idon sabon jini su ke Sha'awa"

Da sauri Afeefah ta mayar da idanunta kan matar, Aunty zee ma ta Wago ta kalleta
"Me kike nufi Hamdiyya?"
"Gaskiya nake faWa Aunty, hanyar lafiya sai a bi ta da shekara ba za mu so farin cikinmu ya koma ba?in ciki ba"
Hawaye ne ke kokarin zubowa Afeefah da jikinta yayi wani irin sanyi, bata ankara ba sai ji ta yi Aunty zee ta Wora mata yaran duk biyu a kan kafafunta
"Afeefah ga su nan ?annenki ne, ki ri?e su yadda kike so"
Juyawa ta yi ga hamdiyya
"A kan Afeefah za mu iya samun matsala da ke, ba zan taSa zuba ido ki tozarta Wiyata a gabana ba, kin ga yau na haife su ko? Kuma na san daaWin su ko? To wallahi zan iya zaSar Afeefah sau dubu kan in zaSe su sau Waya. Ki kiyaye kan mu yi uwar watsi da ke a kan 'yata"

"Aunty ni kike yi wa gori a kan wannan mayyar?"
Ko kan Aunty zee ta yi magana Uncle ya shigo, kafin ya tambayi me ya faru Hamdiyya ta fashe da kuka mai ?arfi tana yun?urin fita, da sauri uncle ya tare ta don shi mutum ne da baya son abin da zai kawo mishi matsala da iyalanshi, yayi kokari ?warai wurin haWe kawunansu ba zai so ko ma menene ya raba su ba, ban da ma yanzu da suka soma tara zuri'a suke kuma cikin farin ciki tsantsa.

"Me ya faru hamdiyya? Zainab me ya haWa ku?"
Aunty zee dai komawa ta yi ta zauna sai hamdiyya ce ta kara karfin kukanta
"Ka yi ha?uri ni ce da laifi na zaci da ni da Aunty duk Waya mu ke kuma 'ya'yanta za su iya zama nawa amma ashe na yi kuskure, in shaa Allah ba zan sake ba"
"Zainab!"
Uncle ya furta sunan cikin rashin jin daaWi
"Gori kika yi mata?"
"Amma dai ka fi kowa sanin hali na Usman, ban yi mata gori ba kuma ba zan taSa yi mata ba don nima babu wayo na bare dabara ta Allah ya ba ni, abin da take shirin shigowa da shi ne ba zan lamunta ba sam"
Hannunshi dake cikin nata hamdiyya ta janye

"jita-jita bai taSa wanzuwa ba matukar babu kamshin gaskiya, an sha tare ni ana gargadina a kan Afeefah amma na Wauke kai saboda ganin yadda Aunty zee ke ?aunarta, abin da nake tsoro an ce suna kaunar sababbin jini to don na ce Afeefar ta yi ha?uri da daukar su har su yi kwari shikenan na yi laifi...? Ku yi ha?uri bari na je gida"
Tana kai nan ta fice uncle bai ce komai ba don shima karo na ba adadi an tare shi an faWa mishi abubuwa dayawa kan Afeefah amma baya bari ya shige shi, sai dai kuma bai ji daaWin reaction na zainab ba da sai a bi abin a hankali tunda dai already akwai maganganu kan Afeefar.

"Amma ba ki kyauta ba zainab, na sani kina kaunar Afeefah kasancewar ta marainiya kuma abin tausayi amma kuma sai ki duba kokarin hamdiyya wurin ganin ta bai wa jininki kariya, tun fa jiya tana tare da ke ko runtsawa bata yi ba, ko da kika sauka kika fara bacci haka ta koma gida ta dafo miki ruwan zafi ta biya ta sayo kayan tea saboda kar ki tashi da yunwa babu abunda zai taimaka miki, ai gyara kayanka baya zama sau?e mu raba"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Idanunta ta mayar kan Afeefah dake hawaye sossai, rabon da taji raWaWin zuciya tun ranar da uncle ya amince ta zauna da su sai yau.

Yanzu ko da tana cin naman mutum wani bala'in ne da rashin tausayi haWe da rashin imani zai sa ta ci naman waennan talikan da isowarsu duniya kenan? Me zai sa ta cutar da 'ya'yan wacce ta rungumeta ta cicciSota ta zaro ta daga cikin bala'i da ?uncin rayuwa?

"Afeefah..."
Auntyn ta ?ira sunanta a hankali sai kuma ta kasa magana duk suka yi shiru tsawon lokaci kan nurses suka shigo, hakan ya tilastawa Afeefah barin Wakin kai tsaye fita tayi daga asibiti ta tsare abin hawa ta faWa mishi inda za ta, gidan Hamdiyya ta nufa don ta tabbatar a chan za ta samu Uncle usman da ma ita karan kanta hamdiyyar.
Hasashenta ya tabbata don kuwa ta same shi tare da hamdiyyar yana ta kokarin bata baki tana tuburewa, maganganu take gayamishi cikin Waci da nuna kaman shi ne ai ya zaSi ya ba Zainabun ciki har ta haifi 'yan biyu tana mata gori.

"Haba hamdiyya kema kin san da mutum shi ke ba kanshi haihuwa da yanzu mun tara yaran da bakya zato saboda Zainab macece mai kaunar yara, tun aurenmu na shekara duk inda taji magani muddin bai saba shari'a ba nema take amma da Allah bai turo ba ba gashi yanzu ta haihun ba? Ba'a cire rai daga rahamar ubangiji kema kuma ya san dalilin da ya jinkirta naki namu Adu'a ne kawai da neman zabin alkhairi daga rabbissamawati".

"A'a Usman ai ka fi ?aunar Zainabun idan da Zainabun ta haihu tun farkon aurenku da baka auro ni ba, silar rashin haihuwar ne ta saka ka kara aure ba don kana so na ba kuma ta haihun ai..."
sallamar ta ya katse musu maganar duk suka mayar da hankali kanta.





=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*006*

"Uncle, Aunty hamdiyya don Allah ku yi ha?uri, ban zo da niyyar wargaza zaman ku ba, na sani Auntyna ta faWa miki magana ne saboda irin ?aunar da take mini amma ni na san gaskiya kika faWa, don Allah ki koma asibitin ki cigaba da kula da ita da jariran ni zan koma gida zan cigaba da jira har lokacin da ya kamata a ce na Wauke su Win"
Cikin wani kalar sanyin murya take maganan, idanunta har lokacin ba su daina zubar da hawaye ba. Uncle Win tausayinta ya ji yayinda hamdiyya ta taSe baki ta ce

"Toh ai shikenan, ni ba na yi magana ba ne da wata manufa kawai dai ina kare yaran da yanzu ne muka fara morewa wanzuwar su ba za mu juri dare Waya a yi abincin meeting da su ba"
Uncle ne ya katse ta
"ya isa haka, ki tashi ki koma asibitin. Afeefah tashi mu je in sau?e ki a babur na"
Mi?ewa ta yi suka fice daga gidan, har suka iso gidan Auntyn nata magana bai haWa su ba ta sau?a ta shige yayinda ya juya ya koma asibitin.

Bata bari abin ya cigaba da damunta ba ta kintsa gidan tamkar Auntyn na nan ta Wora girki marar nauyi ta ci ta zuba saura a kula kan ta Wan kwanta bacci, har ga Allah ta tsame kanta ne saboda gudun abin da zai je ya dawo sam ba zata so wani ya yi kuka sanadin ta ba bare Auntyn ta don haka tana ganin shawarar da ta yanke shine daidai

Sai da Aunty zee ta kara kwana biyu a asibiti saboda postpartum ciwon ciki da ya matsa mata amma duk da haka sai damun uncle usman take akan maganan Afeefar har fushi ta yi ta matsa a sallame ta saboda tunanin ta kar Afeefar ta ji an ware ta ko ta sanyawa kanta damuwa, duk da sun shirya da hamdiyya sai dai har aka yi sallamar hirar arziki bai haWa su ba don ta matu?ar jin zafin abin da ta yiwa Afeefar.

Tana sanya kai cikin gidan ta soma kiran
"Afeefah! Afeefah!!"
Da gudu Afeefah da ke zaune a parlor tana kallo ta fito ta rungumeta tana murmushin ganinta, Auntyn ta Wago fuskarta sai ta sauke ajiyar zuciya
"Afeefah ni kika yasar a asibiti ko?"
"A'a Aunty ban isa yasar da ke ba wallahi, na bari ne Aunty hamdiyya ta kula da ku ni kuma sai in kula da gida ba gashi ba gidan ma ya ji daaWi, da missing Win mu da zai yi sai yayi mishi yawa"
Dariya Aunty zee ta yi tana girgiza kai, a parlor suka ya da masauki kan a natsa ma ma?ota da abokan arziki an fara shigowa barka tuni gidan ya soma Winkewa da jama'a nan Afeefah ta shiga jeka ka dawo.

Zamanta da hamdiyya na kwanaki shidda ba karamin wahala ta sha ba ta kuma danne zuciyarta, ko Aunty bata bari ta san hamdiyyar tana matukar musguna mata ba ta yadda ko satan kallon yaran ta yi sai ta yaSa mata ba?ar magana, har tsoron kallonsu take Dukda tana jin son su tamkar jini da tsokarta ta sha Suya tayi kuka sossai na mummunar shaidar da take dashi don bata tsira ba ranar suna har nuna ta hamdiyya ta saka ake yi saboda kananun maganganu duk Aunty bata sani ba.

Auntyn Ta yi matu?ar kyau cikin milk leshin ta yayinda yaran suke sanye cikin kyawawan tufafinsu pink da blue, Afeefah ma cikin leshin da Auntyn ta yi mata musamman na suna maroon ta shirya ta yi mugun kyau Aunty zee har ajiye ta tayi ta zana mata liner a baki ta saka ta

4 / 53