HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   22 / 53

63K to 66K   out of 158.4K words

yayi kyau, kafafunshi sanye da halfcover Milano ba?a, hannunshi na daure da wata silver agogo yayinda zoben azurfan dake yatsar shi na kusa da ?arshe ke ta daukar idanu.

Kallon duk a seconds biyar ta yi mishi don fargaba da ta kan tsinci kanta a duk arean da yake, ba?ar shade na ma?ale a idanunshi ba za ta san ya ko kalli iskar da ya kwaso su ba yau ko Sulaiman dake zaune cikin mota bai kalli sashen da yake ba ya shige gidan kamshinshi na buso musu, Abeeha ce ta iya yi mishi
"Sannu da dawowa"
Hannu kawai ya Waga mata wai shine amsar ya shige abunshi.

Motar Sulaiman suka isa Afeefah ta shiga gaba Abeeha ta zauna baya suka fice daga gidan suna sake gaisuwa.

Har suka isa shi ne yake hira da Abeeha ita kam tana zaune shiru, shi ya musu iso har cikin gidan Baaba ta taso ta rungume Afeefah dake ta murmushi a ?asa ta zube tana gaishe da mahaifiyar shi Umma ta mi?a mata hannu ta je kuwa ta kama sai ta zaunar da ita gefenta tana Wan rungumeta kaWan
"Ina ta jin labarin Wiyata sai yau Allah yayi zan ganta! Barka da zuwa barka da zuwa"
Murmushi Afeefar ke ta yi hakika ta ji matukar daaWin irin tarbar da ta samu, kayan kwadayi da su drinks aka cike musu gaba da su ita dai kunyar Ummar take ji yadda take ta jansu da hira shi Sulaiman ya fice Sashenshi da a cikin gidan yake.

Sun jima sossai har aka yi la'asar suka je suka gabatar suna dawowa parlorn Su Fauza suka fito shirye don wucewa islamiyya suka yi sallama akan su ma za su zo musu suka fice, basu jima da fita ba sai ga Sulaiman da matarshi sun shigo, kyakyawa ce kuma fara tasss bata da wani girman jiki a shekaru kuma da kaWan za ta iya fin Afeefar kila su yi sa'a da Abeeha, zama tayi tana ce musu sannu.

Gaisawa suka yi kadaran hadaran, tunda ya ce mata da Afeefah yake ta zuba idon ganin Afeefar da bata santa ba amma ta yi matu?ar haddace sunan saboda yawan Ambaton da Sulaiman ke yi musamman in tayi wani abu, sai ta ga Afeefar ma ba wai kyau ta fita ko ado ba haWiye abin da take ji tayi ta yi musu sallama ta fice.

Baaba ce ta kawo zancen su kawu tana tambayar Afeefah me yasa suke kiranta annoba? Shiru ta Wan yi kan ta shiga basu labarinta daga farko har ?arshe, Baaba da Umma sun sha kuka umma ta sake rungumeta tana cewa
"Sannu Afeefah... Sannu! Allah ubangiji ya ?ara miki karfin zuciya da imani ya wanke miki duk wannan wahalhalun"
Ta amsa da Ameen tana murmushi don a wannan karo bata yi kukan ba illa iyaka Adu'a da tayi ta bin iyayenta da Aunty zee.

Sulaiman dai bai iya ya ce komai ba a ranshi yake ayyana Dole ta sha piya-piya don kashe kanta, dole ta samu saukar jini don damuwar, ya so da ita ce a Wakin shi a yanzu matsayin matarshi ya bata duk wata kulawar da ta dace amma gani yake lokaci ya riga ya ?ure, Dukda haka zai zauna matsayin yayanta zai bata duk wani gudumawar da ya dace a rayuwarta daga yanzu.

Karfe hudu ya maida su sun bar gidan da tsaraba niki niki daga Umma ta kuma roki Afeefar da ta dinga zuwa mata, har cikin gida ya dawo dasu suka yi mishi godiya suka nufi ciki.

****

Karfe 3:40 ya fito ya wuce masallaci sai wuraren 4:20 ya koma cikin gidan kai tsaye sashen Mammi ya nufa don ya duba ta, tana zaune kan sallaya sai dai kanta na kife ne a bakin gado, da Wan hanzari ya isa gareta

"Mammi! Lafiya kike kuwa?"
Ta Wago ta sakar mai murmushi ya runtse ido da ?arfi, da gaske murmushi take sai dai a cikin murmushin wani irin ciwo yake hanga da damuwa haWe da gajiya, a idanunta wani abu mai wuyar fassara yake karantowa, tausayi da rauni suka rufe shi wanda basu Suya ba sam don a kan Mammi baya iya danne damuwarshi.

"Saraki..! Ina lafiya, ka zauna za mu yi magana"

A gabanta ya zauna kasancewar akwai turkish center carpet mai tsananin taushi da tsada dake malale tsakar Wakin.

"Ina muka kwana da zancen mu? Saraki babu lafiyayyen namijin da zai iya dawwama ba tare da mace ba, aure na sani ba dole ba ne amma babbar sunnah ce ta ma'aikinmu sannan akwai wani hadisi da Manzon Allah yayi magana akan bayan mutuwar mutum komai nashi zai tsaya chak sai abu guda uku, sadaka mai gudana, ilimin da ya samu ya kuma bayar da shi sai Wa nagari mai mishi Adu'a ashe baka Fatan ka ajiye 'ya'yan da za su yi maka Adu'a bayan baka nan? Bana so in sake ji ka ce min ba zaka taSa aure ba wanchan kuskure aka samu da akasin rashin sanin nagarta da kyaun halinka... Ba duka aka taru aka zama Waya ba"

Kallonta kawai yake idanunshi duk sun sauya sun zama red har jijiyar kanshi na tashi, sam baya so baya son jin zancen wani aure daga bakin Mammi, a baya dai ya so yi amma bai san mummunar taSonshi zai sa a hana shi aure ba, bai san za'a iya kallon cikin kwayar idanunshi a faWa mishi kalmar da har abada ba zai taSa mantawa ba, baya so a maimaita baya so samm.

"Mammi..."

"RAYYAN...!"
A razane yake kallonta jin yadda ta katse shi, ta katse shi da asalin sunanshi da bata taSa ?ira ba... GabaWaya sai hankalinshi ya sake tashi a raunane ta ce

"Rayyan kana so in mutu ban ga ka samu cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali ba? Kana so in tafi wurin ubangiji ina tunanin rayuwar ka zai iya taggara bayan babu ni? Kana so in tafi in barka ban cika alkawarin da na Wauka wa rayuwarka ba?"

"Yaaa ilaihil alameen..."
Ya faWa a rikice sai ya mi?e tsaye don wani irin tashin hankali yake ji, taku biyu yayi gaba ya juya yayi biyu baya yana shafa kanshi zuwa fuskarshi ji yake kaman ya tsala ihu ko zai fahimtar da Mammi abin da yake ji a cikin zuciyarshi.

Zama yayi ya kalleta
"Mammi saboda ke don ke kaWai zan amince da zancen aure! Amma ban san kuma ta yadda zan je in cewa mace ina sonta ba, ban ma san menene son ba, ban san ta ina zan fara ba kuma... Na bar miki, na bar miki wuka da nama duk abin da kika yanke ni mai karSa ne"

Shiru tayi tana kallon shi, ya ri?o hannunayenta

"Mammi kin san yadda na Wauki al?awari, na miki al?awari zan yi iya kokarina a duk abinda za ki yanke a kaina, wanene ni da ba zan miki biyayya ba a duk abin da kike so? Ki kawo ko wacece zan zauna da ita yadda kike so matu?ar hankakinki zai kwanta, matu?ar za ki daina yi min zancen tafiya ki bar ni... Mammi kika ci gaba zuciyata za ta iya tarwatsewa"

Hawayenta ne suka zubo, ta gimtse hannunshi dake cikin nata tana murmushi a lokaci guda ko babu komai zai tuna da ita ta zaSar mishi mata, zai tuna da ita ya yi mata adu'ar alkhairi a duk sadda zai ga wannan mata ya ji farin ciki, in shaa Allahu ba zata yi zaSin nan da kanta ba za ta bar wa Allah, za ta tsaya tsayin daka ta ro?i ubangiji yayi mishi zaSi da kanshi ta san sai ya fi dacewa duniya da lahira...

Anan suka bar maganan ya mi?e ya fice, ta bishi da kallo ta tabbatar yau bacci rabi da rabi zai yi hannu ta Waga sama tana cewa
"Allah ga bawanka nan Rayyan! Allah ka sassauta mishi Allah ka yaye mishi matsalarshi Allah ka sada shi da duk wani farin cikin wannan duniya ka bashi dacewa a ?iyama..."
Ta shafa.

Daga wannan rana Mammi ta dukufa adu'ar neman zaSin Allah, ko sau daya bata yi tunanin wata mace ba damuwarta kawai Allah ya zaSa mishi mafi alkhairi cikin mata, ya zaSa mishi matar da za su tabbata har a aljannah wacce zai so ta, wacce idan ta tashi barin duniyar za ta kular mata dashi ta yadda ba zai yi kukan rashin ta ba don har a yanzu jin Rayyan take kaman yaro ?arami da kan ri?e hannunta yayi kuka yayi kuka matu?a idan an faWa mishi abin da ya taSa zuciyarshi, har yanzu ganinshi take kaman wannan dakakken yaron mai tsananin juriya da ?arfin hali wanda duk wani abin da zaka mishi baya bari a ga rauninshi sai in yana gabanta.

Ta Wauki tsawon sati biyu tana wannan ro?on Allahn a cikin uku bisa Wayan dare lokacin da Allah ya ce mu ro?e shi zai amsa mana, lokacin da ubangiji ke sama na Waya yana neman bayinshi masu ro?on shi ya amsa musu babu hijabi, a yau daren Alhamis safiya juma'a bayan ta gama nafilfilunta ta kwanta kaWan saboda dan ciwo dake damunta a ciki, dole bacci ya lallaSa ya dau?eta ana ?iran farko na assalatu ta farka a Wan firgice ta mi?e zaune, a hankali ta saki murmushi mai kyau kan tayi Adu'a ta mi?e ta nufi bayi don gabatar da Alwala.






=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Comments Win ku shi zai yi determining Page na dare>?8?
@&?*

*28*

Tun ?arfe goma sha Waya na safe Rayyan ya bar office don ya je da wuri yau din saboda wani aiki da ya taso, gida straight ya koma yayi wankan juma'a don yana so ya fita da wuri yana so ya fara biyawa wurin salim da ya rasa gane kanshi a kwanakin.

A shirye ya fito cikin shigan manyan kaya don fa shi yana son manyan kaya haka kawai bai cika son sa kananun kaya ba kaman yadda yake saka manya Win, governors yard ne da aka yi wa dinkin zamani ya zauna mishi sossai da sossai, ko da ya fito Wakin Mammi ya fara yi ya sameta zaune tana azkar Winta da bata rabo da shi.

"Sannu da hutawa Mammi"
Ya faWa yana zama gefenta
"Sannu Saraki ashe ka dawo har ka yi wanka"
Ya gyaWa kai
"Ina so zan fita da wuri ne zan biya wurin Salim"
"kwana biyu kam bai shigo ba, ko da shike lafiya shi ke Suya ko?"
Murmushi kawai ya Wan yi zai yi magana sai ga Afeefah ta shigo hannunta ri?e da tray mai dauke da plate na abinci.

Bata san yana nan ba da bata shigo ba don fa ita duk abin da zai haWa ta dashi kiyayewa take saboda yadda bata samun natsuwa a area Win da yake gashi abin laifi baya mishi kaWan yanzu ya hau faWa da masifa, a gaban Mammi ta ajiye tray Win ya bi trayn da kallo kan ya kalli Mammi dake godiya ya ce

"Ba dai wannan abin za ki ci ba?"

Daga ita har Afeefah kallonshi suka yi abinci ne ya zama abu?
"Me yayi?"

Bai amsa Mammi ba sai Afeefah da ya kalla da idanunshin nan yace
"Kashe ta kike son yi?"
Wani irin faWuwa gabanta yayi jin zancen kisa, hankalinta sai ya so tashi idanunta duk ta zaro waje tana so tayi magana amma Muryar rawa yake, tana da trauma na batun kisa da ita kanta bata sani ba, amma yadda ake jefanta da kalmar kisa yayi affecting mind Winta ta yadda ko ya aka ambaci kisa aka danganta ta da shi sai hankalinta ya tashi.

Tsawa ya daka mata cikin muryarshi da ke razana ta
"Na ce kashe ta kike son yi? Me yake damun ki da za ki dafa kowani shirme ki kawo mata?"

Ganin yadda ta sake firgita Mammi ta dafa shi.

"Saraki...! Wai me haka ne? Meyasa kake haka? Idan ka bi ta a hankali ai za ta fahimta ba sai ka yi mata faWa ba, kuma ni na saka ta dafa min ba gaban kanta tayi ba"

"Mammi ina Merry?"
Yayi tambayar ranshi a hasale, idan da bayanan sai Mammi ta ci abincin nan don ya tabbatar ko don wahalar da wannan yarinyar tayi ta dafa zata iya ko loma kadan ne don yarinyar ta ji daaWi, Dukda Couscous ne amma akwai abubuwa masu yawa da bai kamata ta saka mata ba ciki.

"Merry bata ji daaWi ba jiki da jini, Abeeha na school shiyasa nace ta dafa Win amma na tabbatar bata gane bayanin da na mata bane ba da gangan tayi hakan ba"
Tsaki ya ja ya Wauki tray Win ya fice.

A ?asa ta zube tana sau?e numfashin tsoro yadda yake zaro mata ido kawai take gani, Mammi ta dafa ta
"Ki yi ha?uri Afeefah duk ya firgitaki"
"Mammi ban san akwai abubuwan da bai kamata ki ci ba ciki kiyi ha?uri laifina ne"
"ba wani laifin da kika yi na kirki Alaiyahu da kuma tomatoes da kika saka ciki duk are high potassium veggies da bai kamata in ci ba su ne fa kawai sai zubin da yayi yawa kasancewar Couscous Win daga wheat ake samun shi, amma ai ina da ido kuma zan iya miki gyara shi dai kawai zafin kanshi ne dayawa"

Dukda halin da take ciki sai da ta Wan murmusa kaWan, yau public holiday shiyasa bata je school ba itama Abeeha wani research take yi shiyasa ta tafi Merry wacce ke da karatu na musamman akan nutrition Win irin masu ciwon Mammin bata da lafiya shiyasa ta shiga kitchen Win ta girka ba wai don gwaninta ko nuna iyawa ba, jikinta ya yi sanyi bata ma zauna wurin Mammin ba ta fice kar ya dawo ya sameta.

Shi kam kitchen Win ya koma, a hankali masu aikin suka zame suka fice sanin kila da kanshi zai yi girkin kaman kuwa sun sani, a take ya fara shirya abincin Mammin, idan ka ga yadda yake aiki za ka zaci wani professional Cook ne cikin taka tsantsan da tsantsar tsafta da Allah yayi mishi, wanke hannu kuwa ko me ya taSa sai ya je ya wanke hannu da handwash ya dawo, ko sau Waya kayanshi bai taSa komai ba har ya gama Wan small portion na chicken salad wanda da breast Win kawai yayi amfani duk wani ?ashi babu ciki, babu gishiri ya gasa da herbs kawai da lemon, ya haWa salad din wanda lettuce ne sai cucumber da Bell peppers da albasa kaWan, ba mayonaise ko cream ya saka ciki ba sai ya zuba man zaitun pure one a cikin dan karamin bowl ya saka 1 tsp na vineger ya kaWa da 'yar habbatussauda kaWan ya juye a cikin salad din ya gauraya ya zuba a cikin wani bowl mai kyau. Shinkafa ce 'yar kaWan ya dafa mata half cup ya haWa da ruwa don bata shan wani sugar ko juice ya Wauka ya nufi Wakinta.

Murmushi ta saki tana mishi godiya, ita bata yi mamaki ba don kafin yayi hiring merry da kanshi yake yi mata duk abinda zata ci shi ya uzzurawa su Abeeha har suma suka iya duk cimar ta da yanayin awon duk sun haddace, godiya ta mishi yace
"Mammi babu fa wannan tsakanin mu har Abada, abin da ya zama min dole ne nayi"

Daga nan ya mata sallama ya koma Waki ya sake gyara jikinshi kan ya kara turare ya fice daga gidan.

Kai tsaye gidan su Salim yayi, kasancewar yanzu ba kaman da ba ta babban parlor ya shiga da sallama, Mommy da ke zaune ta zabga tagumi ta Wago ta amsa a hankali, ya zamu wuri ya zauna yana gaisheta

"Lafiya ?alau Rayyan ka shigo?"

Samha dake kuka ya Wan kalla kan ya kalli mommyn
"Lafiya kam mommy?"

"Ba ?alau ba Rayyan, ban san me zan ce ba ban kuma san ta ina zan fara ba amma tabbas Salim baya cikin lafiya da natsuwar shi... Rayyan ko za ka bashi shawara? Ko zaka mishi faWa? Don saleem bai Wauke ni uwa ba kuma, saleem ya fi gane maganar matarshi akan nawa yanzu ya bar nan bayan ya fasa bakin Samha don kawai ta ro?e shi kuWin makaranta suna shirin exams bata biya ba matarshi ta sa baki sai tace mata ba da ita take ba da Wan uwanta take shikenan har ya kai abin duka kuma yace ba zai biya Win ba rashin kunyarta ya biya mata? Saleem dai ina mishi magana ya Waukeni banza? Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."

Wasu irin hawaye masu zafi take zubarwa bata taSa zato ko tsammanin irin wannan butulcin daga Sabrina ba, shi karan kanshi Rayyan yayi mamaki don kowa ya san saleem ya san yadda ya Wauki mahaifiyarshi da ?annenshi, shi Win mai biyayya ne ko da ko baya so zai yi don ya faranta ran mahaifiyarshi, ya san dai saleem ya chanza mishi amma bai zaci har mahaifiyarshi da yan uwanshi ba, sai ya kira shi ba zai Waga ba kuma ba zai kira shi back ba, sau biyu yana zuwa headquarter baya samun shi shiyasa ma ya yanke ya zo gida ya same shi, Dukda shi namiji ne kuma ba kaman sauran maza ba amma daga maganan mommy ya fahimci akwai ayar tambaya mai girma akan saleem.

Bai gama tunanin ba aka fara sallama, sameerah dake zaune shiru gefe ta mi?e ta nufi kofar.

"Mun zo daga companyn gadaje da kujeru ne mun kawo order Win da aka sanya wannan address Win..."

"Anya gidan nan ne? Ko zaka kira Layin da aka yi order Win?"

"Toh bari na ?ira"

Kira yayi cikin mintuna biyu sai ga saleem da Sabrina sun sau?o, ganin Rayyan ya sa ya je ya bashi hannu suka gaisa
"Saleem kana lafiya?"
Yayi tambayar yana sake nazartar abokin nashi da ya ji wani irin tausayinshi ya tsarga mishi.

"Lafiya me ka gani?"
Girgiza kai kawai yayi ya ce
"Zauna za mu yi magana"
Babu musu saleem ya zauna Sabrina za tayi magana ya Waga idanu ya zuba mata haka kawai kwarjinin shi ya wani irin cika ta, duk yadda ta so tayi magana kasawa tayi sai ta nufi kofa ta fice tana kwafa.

"Me ya sameka? Me ke damunka abin da baka yi ba tun kana ?arami zaka yi shi yanzu da ka mallaki hankalin kanka? Saleem uwa ba Abar wasa bace ba kowace uwa ba, ba irin mahaifiyarka da tayi

22 / 53